499 Views

wata mata ta kashe kishiyarta har lahira ta hanyar buga mata Tabarya a ka

 wata mata ta kashe kishiyarta har lahira ta hanyar buga mata Tabarya a ka

Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category News
Uploaded On 30 Nov, 2022
Upload Time 6:59 am
Comment No Comments

Wata mata ta kashe kishiyarta har lahira da tabarya a jihar bauchi.

Hukumar ƴan sandar jihar bauchi sun sanar cewa sun cafke wata mata da ake zargi da kashe kishiyarta.

Ahmed Walil jami’in hulda da jama’a na hukumar ƴan sandar jihar bauchi ne ya sanarwa manema labarai da afkuwar lamarin inda ya ce mijin wacce ake zargin ne ya shigar da kara ranar 22 november a ofishin ƴan sandar dake Maina Maji.

Ranar ashirin da biyu ga watan nuwamba misalin karfe shida na yammaci, Ibrahim Sambo magidanci mai shekaru arba’in dake zaune a unguwar Gar kauyen Pali, karamar hukumar Alkaleri, ya shigo ofishin ƴan sanda dake Maina Maji ya shigar da rahoto cewa “

Misalin karfe sha biyu matarsa ta biyu mai auna Maryam Ibrahim mai shekaru 20 ta shiga ɗakin matarsa ta farko mai suna Hafsat Ibrahim mai shekaru 32 inda ta bugeta da tabarya aka.

Wacce aka kashen ta samu munanan raunuka inda cikin hanzari aka garzaya da ita asibitin dake kauyen Gar inda acan aka tabbatar da cikawarta.

Yayin da ƴan sanda ke yiwa wacce ake zargi tambayoyi kai tsaye ta amsa laifinta ba bisa jayayya ba inda ta sanar cewa.

Ranar talata 22 nuwamba 2022 kishiyarta wacce aka kashe marigayiya hafsat ibrahim ta aiko ɗan ta mai suna Abdulaziz ɗan shekara 5 da ɗunkulen nama gareta. Bayan data amshi taci sai cikinta ya fara mata ciwo hakan yasa ta tuntubi kawarta Faiza.

Kawar tata tace mata ƙila ulcer ne, a cikin dare kuwa Maryam ta shiga cikin kicin ta dauko tabarya ta shiga dakin hafsat ta isketa tana barci inda ta kwatsa mata tabarya aka.Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

About Mr Hausa Ebooks 1438 Articles
The Power of pen

Be the first to comment

Leave a Reply