88 Views

Gwamnatin kano ta jefa ɗan TikTok a gidan yari bisa batanci gareta

 Gwamnatin kano ta jefa ɗan TikTok a gidan yari bisa batanci gareta

Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category News
Uploaded On 02 Nov, 2022
Upload Time 8:31 pm
Last Modified Date November 7th, 2022
Last Modified Time 12:09 am
Hits 88 Views
Comment No Comments

Gwamnatin kano ta jefa ɗan TikTok a gidan yari bisa batanci gareta

Kotun majistri mai lamba hamsin da takwas dake kano ta aike da mubarak uniquepikin da dan uwansa Nazifi mai ja masa baki bisa zargin cin mutuncin gwmanatin jihar kano.

Also read The 2022 NECO results is out

Anyi zaman kotun a yau laraba inda dukkansu masu wasan barkwancin basu baiwa kotu wahala ba suka amsa laifukansu na yin ɓatanci ga gwamnan da iyalansa.

Kai tsaye lauyansu da ƴan uwansu sun nemi afuwa a wurin alkali.

Laifin da ya aikata

Hukumar tace fina finai ce ta shigar da masu wasan barkwancin kara kotu bayan fitar wani bidiyonsu inda suke cin mutuncin gwamnatin jihar kano a ciki.

Shidai mubarak unique Pikin yayi shuhura matuka a sahar TikTok wurin wasannin barkwanci da ban dariya.

Magidanci ya kama matarsa da abokinsa auna cin amanarsa

Kana kuma ya kasance mawaki, a cikin wasannin barkwancin nasa ne yayi batanci ga gwamnan jihar kano Alh. Abdullahi Umar Ganduje.

Yanzu haka mubarak da maja bakinsa suna can gidan ɗan kande bisa ga daga shari’ar da alkalin yayi zuwa bakwai ga wannan wata.

Abokan sana’ar mubarak sun nuna alhininsu ga faruwar wannan lamari, musamman ma abokan barkwancinsa na sahar TikTok irinsu Murja Kunya, Ali Nuruddeen da sauransu sun fito suna nema mai afuwa a wurin gwamnatin jihar kano.Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

About Mr Hausa Ebooks 2238 Articles
The Power of pen

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*