291 Views

DUNIYA TA AMNA Page 41 – 50 COMPLETE by Asma Baffa

 DUNIYA TA AMNA Page 41 – 50 COMPLETE by Asma Baffa

Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 16 Dec, 2022
Upload Time 10:30 pm
Author

Writer Group Unknown / NIL
Novel Genre

Comment No Comments

DUNIYA TA AMNA Page 41 – 50 COMPLETE by Asma Baffa


10/26/21, 8:52 AM – A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA AAMNA🌵🌵

Page 41-45

FREE PAGE

DUNIYA TA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

      NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

ZEE NANDU
KALTUMA ZANNA
SADEEY(QUEEN)
TEEMA’S COLLECTION

.Aamna daga kitchen ta fito tana amsa Masa wakar tasa tana girgiza Kai ta kwala da karfi Ohhhhh…..yeyi..yiye…your…..bappalo soldier….tsit Ahmad yayi murna ta koma ciki da Alama Bata da Niyyar tafiya,Girar sama data kasa ya hade kamar an Aiko Masa da Mummy ta rasu,Aamna kuwa Bayan ya fita zuciyarta ce tayi sanyi ta huce,kafin ya dawo Allah ya yayyafawa zuciyarta sanyi da Hakuri sai ta fasa,Siyama kuwa tunda ta tafi tana sa ran Aamna zata bar gida take ta murna tana uban Kiran Aamna akan taji ko ta bar gidan Amma karshe ma Sai Aamna data Kira Aamna tana dagawa sai taji tana dariya Tace ke Siyama na fasa tafiya na huce,na tuna ma fa Dan kwaya ne ba a ba’a hankalinsa yake ba nayi Masa Uzuru,ko ba komai ma ai Ibada nakeyi,aure Ibada ne zanci gaba da Masa Addua Allah ya shirye shi,Siyama ta danno Mata ashariya Tace wannan bazai taba shiryuwa ba,Ibadar me aure ne kadai Ibada a duniya,Aamna Tace Sanda Zaki auri Faisal ai masifa kika Kama Yi min akan nace kinyi gaggawa yanzu Kuma Ni da gidan mijina Zaki shigo kina min katsaladan a gidan aure na,kin fa Sanni Siyama ki daina uzura min Ina ta Miki Kara bakya gani,Ya kashe Ni ma Mana Ina ruwanki,Siyama Tace Iyyeee….Mrs Ahmad shike Nan kije ki zauna a wahalar,Tsaki Aamna tayi tare da kashe wayarta. Yana Zaune sai kunci yake faman yi,Aamna ta kamo Sunna tv taci sa’a kuwa an saka Wa’azin Malam Ahmad Tijjani,Yana magana akan hatsarin shaye shaye,Yace yanzu Duniya Malam ta lalace da shaye shaye,maza,Mata,Yara,manya,Dattijai,abin haushi ma Yara kanana matasa sun Gama kashe kansu da shaye shayen kayan Maye,abin Allah wadai matashi lafiyayye ya jefa Kansa a halaka,ya Zama marar amfani a rayuwar Musulmai,Musulunci bazai Yi alfahari da su ba,Shan Alkhabis,baza a Sha Aldayyib ba,Mene Alkhabis? Alkhabis shine abinda idan anci ko an Sha bashi da dandano me Dadi a Baki sannan a jiki Yana cutarwa,Aldayyib shine a Baki da Dadi a jiki Kuma Yana da amfani me kyau. Ko matasa jira kuke sai an lissafa muku a Alqurni ance Giya,taba,Wiwi,har Ana kawo ayar Allah Kuna cewa babu Aya,Ina Iyaye wallahi ku farka,Matasa maza da Mata Kuna da hankali,shaye shaye na kwaya,na hayaki na ruwan barasa da sauransu bashi da amfani ga rayuwarku sai cutarwa,Kun Zama marasa amfani a cikin Musulunci,shaye shaye shi kadai yana barna ba adadi a wajenka matashi,na farko shine Kai da lafiya kunyi bankwana,zai kassara maka lafiyar kayan ciki da dama,sannan babbar Illa zai rabaka da Allah,zai rabaka da addinin Allah,zai hanaka Sallah ko kayi ma kana cikin maye baza a karba ba,Azumi ma Sai ya hanaka domin zaka dauka ka kasa kaiwa sabo da dole sai ka Sha kayan Maye zaka zauna lafiya ya Gama bin jininka,sannan zaka sabawa Iyayenka babbar matsala sabo da dole sai ka kangare,ka bijire musu zaka cutar da su. Kasan kuwa wa ake cewa iyaye,ya ku matasa wallahi wallahi ku guji fushin iyaye,masifa ne Mahaifiyar ko Mahaifi su zubar da Hawaye a kanka,basai sun maka Addua ba Kai da ganin dai dai a rayuwarka sai in ka tuba sun yafe maka,wani abin haushin ma Iyalinsa zai dinga zalintar matarsa da yaransa,ya mazaje ku San hakkin matanku mataye Kuma wallahi wallahi kuji tsoron Allah duniyar Nawa take,bakwa ganin halin da ake ciki mafi yawan alamomin tashin kiyama sun bayyana,nuni ake mana mu Kara gyara Hali lokaci Yana matsowa,wallahi a Haka Ana da saura da saura Ana ganin kamar da saura a Haka za a wayi gari aga manyan alamomin tashin Alkiyama sun fara Bayyana….. Ahmad Yana ji ko a gefen rigarsa sabo da yaji Wa’azin Daya fi wannan zafi ma, Canja Chanel yayi yace idan Kinga dama ki gayyato malaman Nigeria kaf su zagayeni ki gani idan zanji na gyara,Aamna Tace ikon Allah a ranta Tace lallai wannan bazai canja ba gwara na nemi mafita,Giyarsa ma taga ya dakko ya Balle Yana korawa, Tsoronsa ya sake shigarta,jiki a sanyaye ta koma dakinta,a palon ya dinga zage zage tana ji,Haka tayi kwana Uku lokacin tuni taje ancire Mata plasta da aka manne Mata ido,sai ganin Idonta yayi tar da Alama ba abinda ya sameshi,Kallo daya ya Mata yace makaryaciyar banza,Shuru tayi sabo da ta gaji da kulashi Yana dukanta,da Yamma kwayarsa ta motsa Aamna taga yanayinsa ba mutunci,taja mutuncinta tana zaune a Palo Siyama ta kwada Sallama,tana shigowa Ahmad ya daka Mata Tsawa yace koma inda kika fito,da sauri ta juya ta fita,Ya zaka koreta?Aamna ta tambaya yace ke wallahi idan Baki daina min magana ba Zan sa wuka na Miki yankan rago,Aamna Jin irin kashen kashen rayuka da akeyi yanzu sai ta tsorata tayi sama da sauri kayan sawarta akwati biyu da duk wani abin bukata shi ta kwasa tayo kasa,Murna wajen Ahmad ba a magana,ko kulashi Bata Yi ba tayi waje,da kanta ta Bude gate sabo da me Gadi baya Nan,Tana fita Napep ta Shiga da kayanta sai gidansu. Su Mama suna ganinta sun San ma matsalar,Baba yace ya Koro ki ne? Aamna tana Hawaye Tace a’a nice Naga bazan Iya Zama ba Yana min barazana da rayuwata shi yasa na taho Kawai,Mama Kamar gaske Tace Allah sarki kiyi Hakuri komai zai dai daita,dama nasan wannan ba abin yarda bane,karki koma ko Iyayensa sun zo Kuma ko me za ayi karki koma,Aamna Tace dama bazan koma ba,kin San shagona yanzu sai kici gaba da kular min da shi kawai sai na sallami Yaron ciki,Aamna da murna Tace Kinga na huta da zaman Kawai,Mama Tace ae kina hada hadarki da customers me ya dameki da wani banza,Zauna ki huta sai gobe ki fara zuwa cewar Baba,Allah sarki Aamna sai murna takeyi. Washe gari kuskuren Aamna da su Baba sun Aamna matar aure da igoyoyi a kanta Bata nemi Izni ba ta shirya ta nufi kantin Mama,Yaron Dake ciki shi ya nunawa Aamna komai yanda abin ke tafiya sannan ya tafi gida shi dadi ma yaji sabo da Mama Bata biyansa Hakkinsa yanda ya kamata sai wahala a banza,Wayar Aamna ce tayi Kara ta duba sai taga Mummy ce,Sai lokacin ta tuna da Aurenta,dagawa tayi Suka gaisa sannan Aamna Bata boye ma Mummy ba ta fada mata komai,Mummy cike da damuwa Tace kinyi kokari Aamna bazan ce ki koma ba,na hakura kiyi zamanki Kawai Ina Jin Ahmad bashi da rabon shiryuwa,Zan ci gaba da Masa Addua,to Mummy Maganar fita fa?ko naje ya bani takardar saki,Mum Dariya tayi Tace karki nemi saki Ni na Baki Izni ki fita duk inda ya Dace Amma ki kula ki Kama kanki ki sani da Aure a kanki,to Inshaallah cewar Aamna sannan Suka Gama waya ,Siyama ta Kira ta Bata labari,Siyama sai murna Tace kinyi dai dai wannan shine magana karki sake ko da Wasa ki koma,ai dama bazan koma ba cewar Aamna kin ganni Ina kula da shagon Mama,Kinyi dai dai kawata Nan suka Sha Hira sannan suka kashe Wayar,Aamna Ana zaune a kujera ga table da kayan aikinta na calculation,Haka ta kwashe kwana Uku tana zuwa Kantin ta Gama Gane komai tana ta ciniki. Ahmad kuwa Bayan Aamna ta bar gidansa shi Bai ji wani damuwa ba ko a jikinsa,ci gaba yayi da shakatawarsa musamman da ya samu Mummy bai ji ta Masa fada ba,Su Mashkoor suka dawo gidan suka tare kullum sai shaye shaye sukeyi,Ranar da Aamna ta cika sati Daya cif da barin gidan Ahmad ya fito a machine a hankali Yana tafiya a nutse,Aamna ta fito kenan tana aunawa wani yaro barkono karaf suka hada Ido da shi zai wuce,Ido ya tsura Mata itama Haka ya Mata kyau da yawa,Machine dinsa ya karawa wuta ya bar wajen,fasa zuwa yayi inda yayi Niyya ya koma gida abinsa,tunda ya dawo Aamna ce ke Masa gizo a fuskarta,Kawai fuskarta yake tunanowa,Tsaki Yaja ya shige Bedroom dinsa ya kwanta Nan take bacci ya kwashe shi,Mafarkin Aamna ya Shiga Yi suna zuba soyayya tana jikinsa a kwance. A Matukar zabure ya farka Shuru yayi Yana tunani,yace ah….wannan wanne irin tsafi ne? Gashinsa ya girgiza Kamar Yana korar kuda Haka yake karkade Fuskarsa Yana masifa ki bar Fuska na daina ganinki,a’ahhh…..ki daina fito min a Fuska Ina kallonki,wannan wanne masifa ne Haka?…..Ni…..ya nuna Kansa da yatsa ni Zan zauna Ina tunanin mace,kamata Ni a’ahhhh….chaiiii……mikewa tsaye yayi ya kaiwa Iska Naushi yace Zan fasa Miki Baki fa……shi kadai yake ta abinsa a bedroom kamar sabon kamu,Zama ya sake Yi sai Kawai ya tafi tunanin Aamna…Tsaki Yaja yace again….Wai wannan wacce irin yarinya ce ki fitar min daga ido na daina ganinki….kasa ya sakko ya durkusa ya daga hannaye sama Yana Allah ka gani dai Yarinyar Nan sai Tunaninta nakeyi,Ina ta ganinta a Ido na,bazan Iya ba….nasan ni me laifi ne a gareka,nayiwa mutane da yawa laifi Allah karka Yi Fushi Dani ka jarabce Ni da yarinyar nan,Allah kasa na daina ganinta,Allah na tuba,ya Mike tsaye ya sake juyowa da karfi Yana tangadi yace Allah nayi Addua Kuma ban daina Tunaninta ba,kirjinsa ya dafe tare da furta wayyooo….my Heart woooo ….Ina ta ganinta fa ya Allah,Ya girgiza Kansa ya shiga zaga dakin Yana safa da marwa Yana Ohh….ohh…..Ni ta fita daga Ido na,ta fitaaaa…..a Haka ya yini Yana sambatu har dare yayi Bayan ya jero sallolinsa na yini Guda yace Bari na kwanta bacci da wuri ko Zan daina ganinta a idona,Yana kwanciya ya kasa bacci sai tunanin Aamna tana Masa gizo,Shi kadai yace kunga yau bazan iya bacci ba sai tunaninta yau an shiga Uku…..mikewa yayi zaune yace kaiii….yau bazan Iya bacci ba sai na ganta….naji idan ban ganta bazan samu nutsuwa ba,…Amma Bari naje na ganta nasan idan na ganta zan daina ganinta a idona…waiiii….ya akayi ne nake so sai na ganta,Kawai so nake Naga Yarinyar Nan yanzu yanzu,Kawai gidansu Zan tafi yafi sauki ai Zan Gane gidansu ko na Kira Mashkoor ya raka Ni gidan sabo da ai sunje daurin Aure zasu Gane gidan,a hankali yace Amma idan na Kira Mashkoor asiri na zai tonu Kuma na Gama kuri da cika Baki a gabansu abin kunya ne a ganni naje wajen mace,macen ma wannan yarinya,Amma fa gaskiya idan ban ganta ba bazan samu nutsuwa ba Dole na tafi,agogon Dake hannunsa ya duba yaga 9pm yace Bari naje ko ta katangar gidan ce na haura na ganta,gashi wani kunyarta nake ji da tsoronta bazan Bari ta ganni ba. Cikin dare ya dauki pcap ya saka sannan yasa face Mark a Fuskarsa Wai Dan kar a ganshi yaji kunya an ganshi a wajen mace,Musa Wanda jiya ya dawo shi ya bawa key din machine yace Musa zuciyata yau wani Bugawa takeyi bazan Iya tuki ba kaini wata Unguwa,Musa ya karbi key ya hau shima Ahmad ya hau sanye cikin kayan baccinsa wando gajeren da Riga me gajeren Hannu ko a jikinsa Haka Suka tafi,Yana ta nunawa Musa Hanya da kyar ya samu ya gano gidan tunda an taba zuwa dashi sau daya,can nesa da gidan yace Musa ya ajiyeshi,ya sauka yace ka jirani a nan bance ka biyo Ni ba,Musa yace to Oga,Face mark dinsa ya gyara ya bi ta can bayan gidan,Kamar Biri Haka ya Dane saman katanga Dake Bata da tsayi Haka ya haura gidan su Aamna lokacin Baba ya fito zai rufe gida. Ahmad ya labe Bai ganshi ba,Baba ya kulle ko Ina ta gidan,Bai San ya rufe kofa da barawo ba,Ahmad yace yanzu Ni ba abin na shigar musu gida ba,Kuma yanzu Taya zata fito na ganta? Ai wallahi idan Zan kwana bazan tafi ba sai na ganta,Yana tsaye har wurin minti goma sai yaga an Bude kofa an fito sai yaga Aamna ce sanye cikin kayan bacci ta fito da bucket,Ahmad ya Kara labewa ya gyara tsaiwa Yana kallonta Yana zuba murmushi yace kalli Hanci Dan Allah me kyau a Nan wajen…..Uhmmm …..Allah yayi baiwa, panties yaga ta Shanya Guda Uku da Bra Guda biyu,Aamna tafi so ta Shanya Rana ta dake su sabo da kashe kwayoyin cututtuka,Bata son Shanya su a inuwa tasan gobe Rana zata dake su. Ta Gama shanyawa Yana ta kallonta Mama ta fito tace Aamna ki shigo da kujera ciki Tace to,Ahmad yace kaji sunan ma Aam….nah…..my Aamna…no sunan gayu Ahmnaa….Yes…Ahmnna vs Ahmad…A&A kenan a’a wannan Dadi Haka…..kumatunsa ya Mara kadan yace to yanzu Zan Iya tafiya nayi bacci,Zabura yayi yace Kai Nafa haukace,wannan fa hauka ce,Ahmad Ni king Haka Kawai na zauce akan Yar Yarinyar nan,Tsaki Yaja yace Nafa haukace gaskiya….lallabawa yayi ya sake haurawa ya bar gidan,Musa ya hango shi ya taho Yana ta murna Yana murmushi Bai San dalili ba,Machine ya hau Suka koma gida,ranar wani irin bacci yayi me dadin gaske. Washe gari Yana farkawa da Aamna ya farka a ransa,Tsaki Yaja yace Wai na ganta ma bazan huta ba…Haba zuciyata me yasa Wai kike min Haka ne,jiya kinsa naje na ganta yanzu ma so kike ki Kara ganinta Baki koshi ba wannan wanne irin tsafi ne Yarinyar Nan tayi min ne,da safe sai na farka da ita Haba which kind juju be that? Ni ba sonta nake ba duk harkar love…love ba ruwana da shi Amma Kuma so nake na sake ganinta Haba nooooo…..ya Furta cikin karaji,Sannan cikin slow Yana yarfe Hannu yace idan na ganta anjima ai shike Nan Kuma sai na huta,ai abin kunya ne kamata Ina son ganin Yar yarinya,zuciyarsa ya dafe yace sai wani tsoronta nake ji zuciyata tana wani bugawa Haka Kawai idan na ganta to daga yau bazan sake zuwa ganinta ba aikin banza,tunani ya shiga Yi yace Naga kamar ma samari na zuwa wajen Baby dinsu da Kaya Decent,to Amma Ni ai ba Baby na bace,Kuma fa sai taji Dadi idan idan ta ganni da kayan hausawa? Murmushi yayi ya koma Gaban Mirror ya duka Yana karewa Kansa kallo ya shafa calabarsa yace gani kyakyawa ai dole ma na birge ta,hannayensa ya Buda a Gaban mirror ya saki murmushi yace chaii….see fine Boy…..oh..oh….baya Yaja sosai Yana kallonsa yace huuuu…Kalar birgewa kaga Kalar birgewa yesss…..Bari nayi wanka, Fuska ya Bata yace to Mene sai wani murna kakeyi zaka ganta aikin banza,Ni wallahi wani banza ne ma akan mace Subhannallahi ya Dan Mari kumatunsa kadan yace Bari na gwada Kalar murmushin da Zan Mata Nan fa ya shiga sakin murmushi kala kala Yana kallon kansa a karshe ya Dan yake kyawawan hakoransa yace ae tsaya dai dai Nan wannan yayi yawwa ae….sai ya wuce toilet.

Tunda ya shiga ciki Yace yau wankan na musamman ne so nake na Kara haske Nan fa ya shiga dirzar fatarsa ba ji ba gani,yace bana wanka da soso yau Zan koma Yi da soso sabo da na fita fes,dubawa yayi bashi da soso,towel ya daura Bayan ya dauraye jikinsa ya fito a Haka daure da towel har wajen me gadi,kudi ya mikawa Musa yace ungo maza ka siyo min soson wanka,karka sake ka dakko min na jarirai me laushi me karfi zaka siyo Wanda Ina wanka Ina Jin radadi,Musa yayi Dariya yace irin namu na talakawa kenan? Karka Bata min time sauri nakeyi Ina da abin yi akan wannan soson wallahi Zan iya sallamarka daga Aiki Matukar baka siyo Wanda zai wanke min fatata sosai ba,Musa ya karba da sauri ya fice,Minti biyar ya dawo da soso me shegen karfi ya bashi.

Wanka ya sake Shiga Yana dirje jikinsa Yana rumtse Ido sabo da zafin soson,Haka ya Gama tas ya fito Yana goge jikinsa yace yawwa Iska tafi shigata Ina Nan Ashe Ina ta cutar kaina da ace da irin wannan nake wanka tun farko ai da nafi Haka haske da Zama Fresh. Lotion dinsa ya shafa me kamshi ya shiga gyara kitsonsa yace ya kamata nayi sabo wannan kwanansa biyar ya fara tsufa Amma Bari dai naje,sai da ya Gama feshe feshensa sannan ya Bude ma’ajiyar kayansa Yana binsu da kallo yace Suit Zan saka ko me?can ya hango shaddoji da yadika masu tsada da kyau Wanda Mummy ta kawo Masa lokacin da za a daura aurensa kala bakwai,Wata Shadda ya dakko sea Blue Tasha dinki me kyau Hannun dogo me links,Nan ya sa Boxers ya fara kici kicin saka wando Wai Bai iya ba,da kyar da wahala Yana uban Nishi ya saka cif cif shi dinki ya zanu,Singlet ya saka yanda Mummy ta koya Masa sannan ya saka Rigar Shaddar wacce ta Sha guga ga kamshi Shaddar nayi sabo da me tsada ce,calabarsa ya gyara ya shafe Kansa da man gashi me kamshi Nan take ya dauki sheki,Fuska ya kalla ya matsa baya Yana kallon kansa a mudubi ya hau taje Sajensa da gemusa,fuskar ya goge sosai ya gyara sai gashi ya fito fes da shi,Sarkar azufarsa wata sabuwa ya dakko ya saka,Yana cewa duk da hausawa basa so Amma tana min kyau sai na saka sabo da wannan shine wankan sugar sai da ya Gama ya fesa turaruka masu kamshi,Ya tsaya jikin mirror ya kame a wajen yayi mutuwar tsaye yace ya Ilahi Ashe Haka nake? Dan Allah kalli kyau a wajen Nan ai Dole ma na birge,ya sake kallon kansa yace ah.. ah kalli kyau Dan Allah,irin wannan saurayi ai sai an wanke Hannu daka taba,wani Dan lipgloss na maza ya dauka ya Dan goga a lips dinsa yace yawwa…..Kar Kuma na Zama Dan Daudu Mana ya Isa haka….tsayawa yayi yace to me zance Mata idan naje Kantin nasu? Tunani yayi yace na tuna ma Bari naje,Illar idan na ganta sai naji tsoronta Kuma Haka Zan daure,Fitowa yayi Yana Taku dai dai Yana wani Gadara,yace me kyau sai da takama Nan ya Shiga wata tafiya Yana takama Yana basarwa,Musa Baki ya Bude tunda yake a duniya Bai taba ganin me kyau irin Ogansa ba,Bai taba ganin wankan da yayi ya zuba Uban kyau Haka ba sai yau,Musa yace Oga gaskiya kayi kyau,Murmushi yayi yace Allah Musa? Musa yace wallahi Oga Kar fa kasa Mata su haukace,Dariya Ahmad yayi ta Jin dadi yace Musa yanzu kana ganin duk wacce ta ganni zan birge ta? Bafa soyayya nake nufi ba Kai Musa Ni kasan ba ruwana da soyayya,Musa ya kalli sama ya nuna sama da yatsa yace Na rantse Oga duk wacce ta ganka sai ta kwana tana tunaninka yau ita da bacci haihata haihata,Machine Ahmad ya hau Wanda Musa ya wanke Masa Shar,a hankali yake tukin sai binsa ake da kallo da gani an San Yafi karfin yawo a Machine ko Ina ya gifta sai an koka.

Aamna kuwa yau wanka tayi ta shirya cikin doguwar rigarta peach color ta lefe ce tayi rolling da mayafi ta dauki hand bag da takalminta me Dan tudu Kalar adon rigar Golden tayi kyau ta dauki bokitin chin chin da takeyi da kanta tana siyarwa a shagon wannan da kundinta takeyi tana samu Yar riba,da kanta ta gyara kantin fes ta shirya komai sannan ta zauna tare da dakko Wayarta tana karanta novel,idan masu siyan Abu sunzo ta Basu ta koma karatunta.

Tana zaune ta dukufa taji machine yayi parking a bakin wajen,kanta ta dago da sauri Jin wani kamshi na daban me Dadi,Ahmad ta gani Wani tafiya yayi da Imaninta ita kanta sai taga kamar yau ta taba ganinsa,zuciyarta ta hau Bugawa da karfi,Kallonsa takeyi ba kyafta Ido tare da Mikewa tsaye,Babu alamun fara a Fuskarsa Yana wani Isa,a cikin ransa Kuma wani kwarjini ta Masa yaji wani tsoronta da shakkarta,duk kwarin gwiwarsa sai ya neme shi ya rasa,jikinsa yayi sanyi a hankali ya taka zuwa gabanta ya tsareta da idanunsa,Itama shi take kallo,can ganin Shirun yayi yawa sai Tace am…me kake so zaka siya Ahmad? Yayi Shuru ya kasa magana,ta kalle shi tayi murmushi Tace wow kayi kyau Wannan shigar tayi maka kyau,Wani sanyi yaji a ransa dama Dan ita yayi Kuma ta yaba,a hankali yana Ina Ina yace shi…shigar…ta…tayi Miki?da sauri ta daga kai Tace sosai wace zata ce ma baka Yi kyau ba,Yaji wani Dadi ya jinjina Kai kawai,sharewa tayi Tace me zaka siya? Kasa magana yayi sai da kyar yace Uhm….uhmm…..Yana ta kallon shagon Yana so yaga me zai iya siya….gumi ya hada Nan take tsabar abinda yake ji a ransa da kwarjinin da ta Masa gashi Bai Iya yiwa mace magana ba tunda ya taso a rayuwarsa wannan ne na farko,Tace Kayi magana Mana me zaka siya? Yace Uhmm….ahhh….ehmmm…..can ya hango chin chin yace Chin chin tare da nunawa da yatsansa,murmushi tayi Tace na nawa? Yace na….naira dari…..murmushi ta saki ta bude ta zuba Masa Guda uku dari cif a farar Leda ta Mika Masa,karba yayi Yana ta kallonta yace Zan….Zan…Iya Zama a Nan naci? Tace me zai Hana shigo ciki,kujera fara ta jawo Masa a ciki ya zauna Suka jere taci gaba da karatun Novel dinta. Kallonta Kawai yake ta faman Yi idan yaga zata dago sai yayi sauri ya dauke Kansa,Daya gaji sai ya fara cin Chin Chin din,harga Allah baya son chin chin Amma Haka yake ta ci Yana kallonta,ita Kuma tana ji a jikinta Yana kallonta duk sai ta kasa sakewa da kunya,juyowa tayi karaf suka hada ido,Tace ya kake kallo na? Yace kallo? Kallo Kuma? Ni na kalle ki ai kece ma naga kina ta kallo na tun dazu ya fada Yana dauke Kai,Tace Ni nake kallonka din? Yayi Murmushi yace ae Mana,Kai ta girgiza taci gaba da karatunta,cikin Wayar ya leka yace me kike karantawa? Novel ta bashi amsa, ko kana karanta Novel? Yace No…me zanci da Harkar love ai Ni sai dai dambe, murmushi tayi Kawai.

Yace me yasa Mata kuke son Love ne? Wannan duk Bata lokaci ne,Dariya tayi Tace Kai baka so ta juyo tana murmushi wani kyau ta Masa ya gigice zuciyarsa taci gaba da bugawa,kasa magana yayi ya rike Hannunta wani mugun shock taji ko Ina a jikinta yace Ring din ya Miki kyau,Tace na gode Hannunta ya dauka ya maida Mata saman cinyarta yace kina boye Hannun Nan Kar wani yaga ya Masa kyau da yawa ya yanke Miki shi ya tafi dashi gida,Dariya ta dinga Yi shi kuwa ita Kawai yake kallo,komai nata Dariya a ransa ya furta,Yana sani ya dinga cin Chin Chin din kadan kadan sai da ya Dade lokacin Azahar tayi sannan ya Mike yace Zan tafi Tace ka Gaida gida yace to Zan fada Masa,Dariya ta sake Yi ta rako shi har bakin machine dinsa ya hau ya tafi da mugun gudu,Tun kafin ya karasa gidansa ya tsaya a Hanya ya cire rigar Shaddar tasa sabo da zafi yake ji ta dame shi Bai Saba ba,a kafada ya sakale ta har zuwa gidan.

Da murna ya shiga Yana sauka a machine ya zaro dubu biyu ya damkawa Musa yace je kaci pizza Musa yau Ranar murna ce,Musa yace Allah Oga? Allah kuwa cewar Ahmad ya sake zaro dubu biyu yace kudin lemo ne wannan,Musa ya daka tsalle Yana murna da Ihu har Ahmad ya tafi ya sake dawowa ya zaro dubu Daya yace ungo Musa ka sawa matarka Kati a waya ku kwana kula hirar ku ta Yan karya Kuma karka sake ka Bata duniyar mu Dan Bamu San Inda zamu shiga ba idan ka bata.,,Musa yace Allah Kai sai kayi,Ahmad ya daga hannaye sama yace nine nan yayi ciki Yana wata tafiya ta musamman.

Yana shiga ya cire duka kayan jikinsa ya watsa su a inda yake Tara wanki,saitin zuciyarsa ya dafe tare da furta shu’uma har ta dawo dai dai,Wato har wani bugu kike Yi a hankali da kika ga bana gabanta ai shike Nan kin kyauta,zuciya kin kyauta hakan ya Miki kyau kin Mai Dani wani Wawa Akan yarinya karama Ina ta zubar da aji na ai shike Nan Zaki sani ne. Washe gari ma wani sabon wankan yayi tare da saka wani yadi Milk color sharara da shi ya Masa kyau matuka an kashe shi da dinki na haduwa,wani takalmin ya zabo me tsada,waje ya fito ya mikawa Musa takalman yace sauri ka kaiwa Shoe maker ya wanke min yanzu Ina jira,Dan Allah Musa kayi sauri ka kawo min su Suna kyalli,Musa ya fita da gudu ya tafi Bai Dade ba ya dawo,Ahmad ya shirya tsaf kyau ba a magana yace yau barkono da citta Zan tayata siyarwa,yau ma Aamna tana zaune ta Gama sallamar wani ya siyo Singlet sai gashi ya Parker machine,Aamna tayi murmushi Tace Sannu da zuwa,Irin Dan gayun Nan harda wani basarwa Direct ya shige ciki ya zubawa Kansa chin chin yace na Naira Dari biyu yau Zan siya Aamna Tace to,Zama yayi Nan ma Yana kallonta duk kunya ta isheta,Wani magidanci ne yazo yasan Ahmad da irin iya shegensu mamaki ya kamashi ganinsa a Haka da wannan shiga ta Kaya,Bai taba ganinsa da shigar hausawa ba,Kuma Yana Zaune a shago kamarsa me kudi,Shuru yayi yace a bani barkono da citta,Aamna ta Mike zata zuba da sauri Ahmad yace No zauna Bari na tayaki Mana Haba,Tace Kai din? Bai kulata ba yace na nawa? Yace na Hamsim,Aamna tace ga kullin Hamsim can ka saka,ya dauki bakar Leda ya saka Masa ,Citta Kuma Tace gongoni Daya zaka zuba,ya fito ya auna gwangwani Daya ya zuba,mutumin yace babu gyara? Ahmad yace a gindinku kuke so mu kare ne Ina laifi ma duk arahar Nan Baku gani ba,Tsaki Yaja ya dauki citta Daya ya jefa masa a Leda yace gashi Nan anyi gyara,Mutumin ya karba ya tafi shi Kuma ya dawo ya zauna a ciki,Aamna tana ta mamakinsa. Wata Budurwa ce tazo Tace Aamna nazo siyayyar,Aamna Tace to shugo,Budurwar tayi layin bra da panties ai Ahmad Yana ganin Haka sai ya juya baya tare da rufe Idonsa ruf har sai da matar Nan ta Gama zaba ta biya kudin ta tafi sannan ya Bude Idonsa,Dariya ya bawa Aamna Yana jinta tana ta dariya,yau ya Dade sai Yamma lis ya koma gida,sai mamakin Kansa yakeyi Wai Kamar shi shine zai siyar da citta,Yana kwance a palonsa yace gaskiya na Gama fadowa nayi asara wallahi,Kansa ya dungure yace kayi asara kai Kam Ahmad. Wasa Wasa kullum Ahmad sai yaje ya Taya Aamna siyar da Abu har wurin sati Daya,gaba Daya su Mashkoor sun daina ganinsa,idan sun Masa waya ma zasu zo gidansa sai yace Kar suzo baya gida ya tafi Unguwa,yafi so ya zauna shi kadai yayi ta tunanin Aamna Yana Jin dadi,Kwaya da giyar da yake Sha duk ya rage ba sosai ba sabo da tunanin Aamna.

Yau kin zuwa yayi gaba Daya Bata ganshi ba har duba Hanya takeyi ko zata hango shi Amma Shuru duk ta kasa sukuni ta shiga wani Hali,gashi Bata da number dinsa Kuma baza ta iya cewa ya Bata ba.
Sai washe gari yau cikin wata maroon suit ya fito kamar a jikinsa aka dinka yayi kyau matuka 3pm yazo wajen,Aamna ta taso da sauri tana murna a ranta a fili Tace me ya hanaka zuwa jiya? Ya rasa me zaice zuciyarsa tsoro yake ji….yace…ahmm…karya yayi yace kaina ke ciwo jiya,Tace Eyya Sannu ya jikin? Da sauki ya furta tare da tsayawa a gabanta Yana so ya fada Mata me yake ji a ransa Amma ya kasa….yace dama Ina so muyi wata magana ne,akwai abinda nake so na fada Miki,Aamna tace Ina jinka tana ta faman kallonsa,kasa fada yayi ta Masa kwarjini sai ya waske yace kina cin kifi tarwada? Dariya ta kamata Tace sosai ma ai Ina sonsa ya,girgiza Kai yayi Murmushi Wanda ya tafi da Imanin Aamna,yace to gobe Zan kawo Miki da yawa ko yau kike son ci? Aamna Tace goben ma yayi,Yana so ya fada Mata shifa zuciyarsa ta kasa sukuni Amma ya kasa sai yace Zaki Zama kawa ta?Aamna ta kalle shi tace me zai hana,murmushi yayi yace to daga yau mun Zama kawaye ko? Tana Dariya ta Mika Masa Hannu sukayi musabiha Tace na Zama kawarka kaima ka Zama aboki na,yace ae dama Ina so na dinga shawarwari Amma Banda kawa,Aamna Tace Ina abokanka fa?Tsaki Yaja kadan yace ai Bama wani haduwa yanzu sosai,taji Dadi a ranta Tace to shugo ka zauna,no tafiya zanyi Ina da wajen zuwa yau,Aamna Bata so hakan ba Amma Tace to shike Nan sai goben,ya hau machine yayi tafiyarsa gidan Mashkoor.

Yana zuwa ya samu Mashkoor shi kadai, Mashkoor yace Kai me Zan gani yau Kaine da wannan shigar lafiya king? Kafadarsa Ahmad ya buga yace ba lafiya ba yanzu ma taimakonka nazo Nema,ku kawo min agajin gaggawa, ka tashi mu tafi gidana akwai magana,Mashkoor yace to,Giyar da Mashkoor yake kurba ita Ahmad ya tiltila a cup ya Sha ya sake Sha yace muje,a machine suka tafi gidan Ahmad. Aamna tana so ta fada Masa anjima da yamma zata tafi Sokoto ganin Dangin Babanta Amma Bai zauna ba bare ta fada Masa Amma sunyi waya da Mummy ta San da tafiyar. Shi kuwa Mashkoor Yana palon Ahmad suna zaune Ahmad yace kasan Kai abokina na ne Zan fada maka ne Kawai sabo da yanda muke da Kai,Kai kadai Zan fadawa halin da nake ciki,Mashkoor da muryar Yan kwayarsa yace Ina jinka King,Ahmad ya kwashe kaf abinda yake ji a zuciyarsa game da Aamna ya fadawa Mashkoor,Mashkoor tsoro ya kamashi Yaja da baya Yana tangal tangal a zaune yace Sarkin namu Guda ah’ah,Ahmad cikin rada yace Ina fada maka idan na ganta zuciyata sai naji tana wani kida tana rawa tana wani foli..fafo..lifo…fil…fil….dardariya Mashkoor yake Kamar me,yace ah’ah duk Kai kadai?

Ahmad yace Ina fada maka Dan uwarka Yana dukan kafadar Mashkoor kana ganin Wasa ne bafa Wasa nake ba kana wani Yi min Dariya Dan Iska Kawai wallahi zaka bar gidan Nan, Mashkoor yace na daina Ina jinka,Ahmad yace Ina fada maka ba sai naji Ina tsoronta ba,Ah’ah Mashkoor ya furta da karfi yace wannan Yarinyar da ko Nonon kirki babu? Duka Ahmad dirka Masa a baya yace be careful matata ce ba Budurwa ba, Mashkoor yace dalla ba so bane sha’awarta kakeyi Kawai kaje ka dakko ta ka lallabata kaci abinka ka barta,Wani dukan Ahmad ya kaiwa Mashkoor yace Kai dalla Ni ba wannan nake so ba,baka ganewa Ni Kawai nafi so mu zauna tare da ita idan Dan wannan ne zamu iya shekara Nawa da ita sai Sanda take so zanyi wannan fa ba Maganar Wasa bane,Mashkoor yace cab abin Babba ne asiri tayi maka,Haushinka taji daka koreta ta maka asiri.

Ahmad yayi Shuru,Mashkoor yace Zan taimaka maka akwai wani malamin Baban mu zamuje da Kai Nan take zaiyi maka Rukiyya a cire maka tunaninta ka dawo normal asirin data maka ya karye,Ahmad sai ya tuno layoyin Daya taba gani a Kan Aamna,yace Mashkoor kaima kayi magana tashi mu tafi wajen malamin Nan Yarinyar Nan Yar bori ce muje a gwada, Mashkoor yace yawwa kasan yanzu duniya ta canja Wai Yan Mata Dan masifa da bin malamai suna shirka suna tsafi akan maza,Wai mace taje tayi shirka Dan wani ya aure ta ko taci kudin wani,wata ta mallake Miji etc,kawaye sai su cika Mota suyi Kauye Wai an tafi wajen Malam akan wani ya aure su ko taci kudi,ko ayiwa kishiya da yaranta,shi yasa aure yanzu baya Zama Ana ta Yi Ana Sako Mata barkatai,duk macen data auri Namiji da asiri ta sani wallahi idan ya karye sai saki,yanzu shirka Kawai akeyi an ma daina cewa malamai sai bokan Kan dutse,mutane suna ta maida kansu arna Basu Sani ba.

Tafiya sukayi me uban nisa zuwa wani Dan Kauye,Wani dattijo kazami Ahmad ya gani,Mashkoor bayan sun gaisa ya Gabatar da Ahmad da abinda ya samu Ahmad,tsohon yace ku bada dubu biyar kafin alkalami,Ahmad ya zaro ya bawa Malam,Malam yace saura kudin Aiki dubu goma,Ahmad yace Aiki baiyi ba za a baka kudi? Dattijon yace Kai ka cika son kudin tsiya ka bada kudi a rabaka da masifa,ciwon so ai masifa ne,Ahmad yace Nifa ba soyayya nakeyi ba,nace maka tunaninta Kawai nakeyi,Ni nayi love Allah kiyaye, gashi nan yarinyar ta Gama kashe maka zuciya cewar malam,Ahmad ya bada dubu goma shi Sam da gani yasan karya ne wannan cin kudi Kawai zaiyi. Saman Tabarma yasa Ahmad ya zauna,Bayan ya zauna ya Bude Qur’ani ya dinga karatu a Kan Ahmad Yana zaga shi sai da ya Dade sannan yace an Gama Alhmdllh Aiki yayi kyau kuje gida daga yau ka Gama da shafinta, Mashkoor Yana murna ya dinga godiya,Ahmad Baki ya tabe shi baiji canji a ransa ba,Sai dare Suka koma gida,suna dawowa wanka sukayi Suka ci abincin da Suka siyo a hanya,Ahmad ya kalli Mashkoor yace Mashkoor Nifa so nake yanzu Naga Yarinyar Nan,Da mamaki Mashkoor yace ah’ah Kuma dai? Yanzu duk aikin da Malam yayi har kanajin ta a ranka? Ahmad yace tashi ka rakani gidansu Zan haura katanga idan ban ganta bazan iya bacci ba yau dole sai naji muryarta ko na ganta,Mashkoor yace dare fa yayi ka duba lokaci 11pm fa,idan zaka rakani to idan baza kaje zanje Ni Daya,Dan kaga Ina fada maka sirrina zaka wulakanta Ni,Mashkoor yace muje Amma idan munje me zaka ce da su a wannan Daren me zamu ce? Ahmad yace muje Kawai,machine suka hau a daren Suka tafi Kamar mayu. A bakin gate Suka tsaya tare da kwankwasa gidan,Baba ne ya fito Jin bugu yaki karewa Yana budewa tsoro ya kamashi ganin su Ahmad ya tabbatar giya suka Sha shi yasa Suka zo da wannan Daren yasan basa hayyacinsu,lafiya? Baba ya tambaya,soshe soshe Suka Kama Yi, Mashkoor yafi Baki shi yace dama…dama..munzo duba Aamna ne sabo da munji labarin Bata da lafiya,Baba yace sabo da kwaya ta gaya muku karya sai kuzo min gida a wannan daren? Kun firgita mu Ni da matata,to Aamna Bata Nan ta tafi Sokoto tun yamma dazu tace ta sauka tana can Dangin Babanta sai Nan da kwana hudu zata dawo,Kirjin Ahmad ya buga Kamar zaiyi kuka yau bazai iya bacci ba Matukar Bai ji muryarta ba,Baba zai juya yace sai da safe da Sauri Ahmad ya kalli Mashkoor ya Masa rada kace ya Bamu number dinta,Da sauri Mashkoor yace Dan Allah Dan Bamu number dinta Muna so muyi Mata ya jiki,Baba yace Wai uban waye yace muku Bata da lafiya fatan ba takura Mata zakuyi ba,da sauri Ahmad yace a’a Kawai Sannu zamuyi Mata,Baba ya Harare su sabo da Bai so Haka ba Amma sabo da kwarjinin Ahmad yace bani waya na sa maka,da sauri Mashkoor ya Mika wayarsa Baba ya sa Masa number a ciki Yace kuje garam ya rufe gidan,Ahmad ko a jikinsa sai murna Suka hau Machine suka koma gidan Ahmad. A Palo Ahmad yace Kira ta awaryarka muji, Mashkoor ya kalle shi da mamaki yace da wannan tsohon Daren? Ahmad yace Dan Allah ka kirata naji muryarta Ni bazan iya Mata magana ba zuciyata bugawa takeyi,kayi magana da ita kasa a handsfree idan naji muryarta shike Nan Zan samu nayi bacci yau,Amma Matukar banji muryarta ba yau bani ba zaman lafiya, Mashkoor yace abin har ya Kai Haka mun shiga uku?Tsaki Ahmad ya ja, lokacin Aamna ta kwanta ta fara bacci taji Wayarta tana ta Kara,dubawa tayi taga bakuwar Number

AsmaBaffa
10/26/21, 8:53 AM – A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA AAMNA🌵🌵

Page 46-50

FREE PAGE

DUNIYATA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

      NA KUDI NE

MASU SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

RUKEY MUAZ
LEEMAT
~-
MINERH
KHADIJA DANDAWAKI
HUMAIRA MUHAMMAD
AMINA ADAMU USMAN

Tsaki taja tace waye wannan da wannan daren? Kin dagawa tayi har ta katse, Mashkoor ya kalli Ahmad yace King Bata daga ba a kyaleta tayi bacci,da masifa yace ka Kara kiranta Mana,to tana bukatar tayi bacci fa cewar Mashkoor,Bata bacci da wuri na sani ka sake Kira Wai me yasa kake min Haka Zan sa ma poison a lemo ka Sha ka mutu ka kirata again, Mashkoor yace Nifa baza ka Jani cikin haukarka ba,Kawai ka shigar Ni ciki mun haukace yau gaba Daya bansha ko kwalaba Daya ba mun Kare akan kwaila,wata Harara Ahmad ya aika Masa Nan take Mashkoor ya sake Kiranta lokacin wata Budurwa Yar Uwar Aamna Minal ta kwanta a gefen Aamna Tace Wai waye yake ta Kira ne Haka? Aamna Tace ban sani ba,Bari na daga naji cewar minal ta dauki Wayar tare da dagawa, Mashkoor yace an daga….an daga…Ahmad yace ehem Yi magana Mana. Mashkoor yace hello Aunty Balaraba Mashkoor ne? Minal tace ba ita bace Yar uwarta ce Minal ce,Aamna tana ji ance Mashkoor ta Mike zaune,Mashkoor yace ehem Dan Allah Bata kusa me Wayar? Minal Tace gata ma Bari na Bata, Wayar Aamna ta karba,Lokacin Ahmad ya gyara Zama tare da furta ehem a hankali, Mashkoor yace Aunty Balaraba Barka da dare,yawwa Mashkoor ya gida? Lfy Alhmdllh,dama…dama…Ni da King munje gidanku ance bakya Nan kinyi tafiya,Aamna Tace Yana Ina King din,Tsoro ya Kama Ahmad shi Taya zai iya magana me zai ce Mata, Mashkoor yace Bari na Baki shi ya mikowa Ahmad Wayar. Yana karba sai da yayi minti Daya Aamna tana ta faman hello hello sannan yace hello cikin Muryarsa da ya saita me Dadi ta nutsuwa….uhm…ahm…ahhh….munje gidanku dazu ance bakya Nan? Aamna Tace eyya sorry Friend Ina ta so na fada maka Bamu hadu ba Amma jibi Zan dawo Inshaallah,Ahmad yace okay…Allah ya kaimu, Mashkoor da rada yake cewa matarka ce fa ka daina wannan abin taya zaka barta tana tafiya inda taga dama Haka? Ahmad Bai kulashi ba yace Friend sai da safe Bai San me zai ce ba,Tace okay bye ta kashe Wayarta,Ahmad yace Nifa ba Maganar Mata nake maka ba ya za ayi Naga na birgeta shine magana Kawai,Dariya Mashkoor ya dinga yi yanda Ahmad duk yake ta murna akan yaji muryar Aamna,yace to yanzu Zan iya bacci,Mashkoor yace ka haukace Nima ka sani na Zama mahaukaci,Bari naje nayi bacci,Ahmad yace ungo wannan banzar akwakwar Wayar taka tunda nadauki number dinta,Ae ai dole ka zagi Wayar tunda ta Gama biya maka bukatarka. Washe gari da sassafe Ahmad ya farka ya dawo Palo inda Mashkoor yake bacci ya dinga dukan Mashkoor a gadon baya,da kyar Mashkoor ya farka Yana masifa Wai Dan Allah mene Haka jiya ka hanani nayi bacci yanzu ma Haka Mene ne? Baka tashi da wuri mene yanzu abin tashi again,Ahmad yace Yarinyar Nan nake so ka kirata ku gaisa sai ka sa min Wayar a Handsfree naji muryarta,Tsaki Mashkoor Yaja da muryar Yan kwaya yace wai a’ahhh….wannan wanne bala’i ne Haka? Okay kace min kawarka ce Kai ba sonta kakeyi ba wa yace maka Ana Kiran kawa Haka a waya,so kake Yarinyar Nan ta tsaneka sabo da yawan takura Haba su Mata basa son takura,kana nutsuwa fa King,Shuru Ahmad yayi yace okay Bari to bazan kirata ba sai ta neme ni Zan daure,Ehemmmm…Abeg jeka kitchen ka Mana girki King kasan ka iya girki cewar Mashkoor. Ba karamin dauriya Ahmad yayi ba yaki Neman Aamna a waya,Aamna taga Shuru Bai nemeta ba ranar da ta dawo Kaduna yau Ahmad Yana kitchen shi da Mashkoor suna magana Yana girki sai ga Kiran Aamna ya shigo wayarsa,Wata nutsuwa Ahmad yayi tare da cewa yeee…ta Kira ni…daga Wayar yayi yace Hello…..Kawata,Aamna Dariya takeyi Wai Dan rainin hankali ma ba matarsa bace kawarsa ce ma,a Wayar Tace dama fada maka zanyi na dawo dazu,Wata Uwar Zabura Ahmad yayi sai da Mashkoor ya firgita,Ahmad yace Kin dawo lafiya Kamar Yana gabanta har wani zufa yake Yi,Tace lfy Alhmdllh,yace Zan zo gobe,okay Aamna ta furta ta so ace yanzu zai zo Amma Wai wani gobe, Wayar ya kashe ya saki Dan Ihu yace she done come back Yana dukan kafadar Mashkoor, Mashkoor kallon mamaki yake Masa Kawai ganin king dinsu ya haukace. Wanka sukayi Mashkoor ya dauke shi Suka tafi Shopping Wai Ahmad shaddoji zai siyo da yadika masu tsada za Masa dinki sabo da ya birge Aamna.

Ko da Suka shiga inda ake siyar da shaddoji da yadikan maza Ahmad ya kalli me kayan ya zaro Masa Ido yace Guy Kalar birgewa muke bukata masu tsada,Me Shadda yace gasu Nan ku zaba,Ahmad ya dinga zaba Mashkoor ya koma gefe Yana ta kallon ikon Allah har ya Gama sannan Suka wuce wurin tela,Ahmad yace Kai tela fa Wanda yasan me yakeyi yawwa idan kasan tela bana kirki bane karka kaini, Mashkoor Yana ta Dariya yace Wai Ni Kam ko Lilamin Masallaci za’a nada ka ne? Ko kula Mashkoor Ahmad baiyi ba,wani Shagon dinki Suka shiga,Ahmad yace Bari na gwada basirarsa Kai tela nawa zaka min Dinki na karshen tsada? Tela yace dubu bakwai, dubu biyar dubu goma sama da Haka,Ahmad yace wannan dinkin da gani bana arziki bane baka iya komai ba baka San me kakeyi ba Malam ja can dalla, mu bar Nan, Mashkoor ya sake daukansa Suka tafi Wani wajen na masu tsadar dinki Amma da kyau,Ahmad Yana ji an zuga Masa tsada yace yes.. .yanzu nasan Kai telan kirki ne Nan ya bashi kayan,yace auna Ni ko Ina dai dai Ni, wallahi ka min hauka sai na sa an kone shagon dinkinka da kayan ciki sabo da Haka don’t Mess up,tela yace zaka ga Aiki ai bana Wasa,sai da suka Gama komai Suka je ya siyo takalma Designers da agoguna etc.

Sai dare Suka Gama sannan Mashkoor yace Zan tafi gida,da masifa Ahmad yace akan me ai wallahi ba inda zaka je Sai an Gama tsare tsare da Kai, Mashkoor yace Nifa na gaji Haba ka rike Ni na kwana na yini Yar giyar ma ban Sha ba tun jiya Ni bazan iya ba, baza ka saka Ni a wannan haukar ba,Fuska Ahmad ya Bata tare da furta Kai meke damunka ina magana kana magana are you mad? Shuru Mashkoor yayi yace to kayi Hakuri na zauna Amma a kawo min ruwa da kayan aiki,Nan Ahmad ya koma bedroom dinsa ya kwaso kayan shaye shaye ya ajiye musu Suka dinga Kora abinsu,Ahmad Yana murmushi yace yawwa na tuno nasan dole tana yin Facebook babu Wanda baya Facebook a duniya,Nan take ya fara latsa wayarsa Yana duba Facebook Yana Searching sai dai Bai San sunan Baban Aamna ba,Amma sai ya gwada Aamna Hussain,Nan take sunan Aamna ya bayyana da hotonta,Yana murmushi yace Yes….see fine Beb,see Beb….naaa..wow…see her lips…oh…..My God…a’a…kaga kyau Haka,…fuskar Wayar ya shiga nunawa da yatsa Yana shafa gemunsa Yana murmushi yace abinda kike min baya dacewa,bakya kyauta min Sam,ki daina…ki daina Tam…..Mashkoor ya saki Baki Yana kallon ikon Allah, Pictures dinta ya shiga dubawa kala kala can ya hango Aamna da wani saurayinta a pic Wato Affan,Glass din wayarsa ya shiga Rankwashi da karfi a saitin Affan Yana ka…ga…shege…Dan… Iska,me yasa zaka tsaya kusa da ita….mugu….Tsaki Yaja ya fita daga Facebook din gaba daya Yana Fushi yace Taya zai tsaya a kusa da ita aikin banza,Cikin Maye Mashkoor yace Wai…Wai…ba kace kawarka bace?Yeah Ahmad ya furta,yace to Mene na damuwa Haka? Maganar gaskiya King ka fa haukace. Ahmad Yana Zaune yayi Shuru Mashkoor yace ya akayi ne? Yarinyar Nan nake so na gani yau da Daren Nan Amma bana son ta ganni kuma bana so ta San na ganta Kawai na ganta a boye ba tare da ta ganni ba,kaga yanzu 10pm muje ka kaini sai na tsallaka gidan, yau ko bacci takeyi har dakinta sai na ganta,Mashkoor tsoron Ahmad ya shige shi Kamar zaiyi kuka yace Wai Mene yake damunka kafa haukace King,Kaga Idan zaka kaini Malam ka kaini Zan zuba ma guba a abinci ka mutu Tam, Mashkoor yayi Dariya irin ta yan kwaya yace muje,a daren Suka hau machine suka tafi,a nesa da gidan Mashkoor ya sauke Ahmad,Ahmad yace karka tafi Ina ganinta Zan fito mu wuce,ta Kofar gidan Ahmad yabi ganin a bude Basu rufe ba,kamar barawo Haka yake Sanda yace bana so ta San Zan kalle ta,da sauri yabi ta bayan gidan wajen Flowers,Baba ne ya fito Yana masifa Dan Iskanci sai a bar gida a bude tun yaushe nacewa shedaniyar Yarinyar Nan ta rufe gidan Nan Amma dake Aamna ba Yar Albarka bace ta bar gidan Abude,Ahmad Yana ji Baba ya zagi Aamna sai ya kasa jurewa Yana bayan ginin gidan yace karya ne kaina Mara Albarka…..tsorata Baba yayi ya rasa a Ina yaji an ramawa Aamna ya shiga waige waige ko zai ga mutum baiga kowa ba,Tsoro ya kamashi ko aljanun Aamna ne suke tare Mata fada,da sauri ya rufe gidan ya kulle ko Ina ya koma ciki da saurin gaske. Ahmad ta Kofar kitchen yabi Dake kitchen akwai kofa ta waje ta ciki sai yabi ta Nan ya shiga Palo Yana shiga Baba ya shigo da sauri ya fada bayan kujera ya buya,Baba Yana masifa ya kulle Palo ma ya sa key, yace aikin banza kitchen dinma a Bude aka barshi Bari na rufe,kafin ya karaso Ahmad da rarrafe ya koma Bayan Daya kujerar,Baba ya kulle kitchen Yana cewa beraye sun fara addabata a Palo naji Kamar sun shiga cikin kujeru Bari gobe da wuri Zan samo mage tayi maganinsu. Ahmad Yana ji a hankali yanda Baba bazai ji ba yace Baba nine ba bera ba,Baba dai dakin matarsa ya shige,Sai ga Aamna ta fito sanye da wata guntuwar rigar bacci fara silk me siririn Hannu,Ahmad ya baza Ido Yana kallo Nan ma a hankali yanda baza taji ba yace Kai bakya kyautawa Baba fa idan Yana ganin irin wannan abin sai Shedan ya shiga zuciyarsa,wallahi sai ya Ayyana wani Abu gaskiya ki gyara,ba kishi nake ba Amma ki gyara,Aamna Bata San Yana yi ba taje kitchen ta fara dafa Indomie,cikin karfin halin Ahmad ya fito fili ya tsaya a Bayanta tare da Harde hannayensa a kirji Yana Shan kallo,a hankali ya Mika hannayensa biyu tare da wara su yace in Dan tallafooooo……hips Ido ya lumshe,Aamna Bata sani ba harda wakarta tana me so na….me so na….Ahmad Yana amsawa a hankali Yana Nuna Kansa Yana gani…gani….Aamna ji tayi kamar ana magana a Bayanta Matsawa tayi da Niyyar juyowa tuni Ahmad ya koma Bayan jikin bango daga Palo ya labe taga ba kowa,ci gaba tayi da aikinta ya dawo shima Yana ta kallonta har ta Gama ta dauka a plate sai ta tsaya dakko ruwa a fridge ta ebo pure water biyu tare da furta Allah sarki a gidan Mijina kuwa Ruwan Roba nake sha,kafin ta Gama gyara kitchen ta fito Ahmad yayi sauri ya shige Bedroom dinta Wanda yaga ta fito daga ciki. Bayan labule ya buya abinsa Aamna ta shigo tare da dannawa kofarta key tana Waka Tace yawwa Bari na kwashi harka ta zauna a gefen bed tana ci tana latsa waya tana Dariya,shiko Ahmad ta bayan labule yace kalli murmushi Malam Kamar wata flower Haba ai wallahi Babu Wanda ya Isa ya ja da Allah,wata baiwar Allah duk duniya kowa da kamarsa daban da Computer ce ke kera halitta ai da tuni tayi photocopy na Aamna ta yafi mutum dubu,Amma Kuwa Allah kowa hancinsa daban,bakinsa daban,Dariyarsa daban,kukansa daban,girarsa daban,kafa,Hannu,Kai,komai daban Allah kenan. Aamna Bata San da mutum ba Tace zafi Bari na sake wanka ba tunanin komai ta tube rigarta ta jefar,Ahmad ya zaro Ido yace tab gaskiya ban kyauta ba Zan kalle mata tsaraici ba Izni,Idonsa Daya ya leko ta labule yace tab Ni idan kika dawo gida na karya ne ki Haifi wani yaro,Ni da yarona zamu Yi takara kenan akan Abu daya Ni da shi ai karya ne,Yarana kuyi Hakuri Uwarku ta ja muku baza kuzo duniya ba akan wannan yaki zanyi da ku,Juyawa tayi yace lahaula fiii……see Ass uhmm….Ganin ta juya baya sai ya juro hannunsa Daya ta labile yace na taba suuu……da sauri ya janye hannunsa Kamar walkiya ganin zata juyo ta kamashi,Towel ta dauka ta shige toilet,sai da yaji karar ruwa sannan ya fito daga inda ya boye,Indomie ta rage yace Bari naci ragowar ta ko na samu karama da tabarakinta ya dauke ya cinye,ruwan data rage ya shanye tas harda tsotse bakin Ledar pure water Wai ya tsotse bakin Aamna,kafin ta fito ta Bude kofa Ahmad ya dauki Wayarta ya turata bakin kofa sannan ya Bude Kofar ya fice da sauri,ta kitchen yabi ya fita tare da haure katanga,ko Ina ya bar kofofin a bude sabo da dabara ya hada. Aamna da sauri ta fito daga toilet Jin karar key an Bude Mata kofa,mamaki ya kamata taga Wayarta a bakin kofa ita data barta a saman bed,abincinta data rage taga an cinye,da sauri ta fito tana duba gidan sai taga an Bude Kofar kitchen ko Ina,ga handkerchief an jefar,Ihu Aamna ta saki tana Baba barayi,barayin waya Baba,Baba ya fito da Aamna ta nuna musu kitchen,Baba yace abinda nake gudu kenan munafuka ai ke kika jawo kece ba Kya rufe gidan,Baba yace Bari na duba Naga me aka sace min,startime wacce ake Kamo tashar kallo Baba yaga wayam an sace,Hannu ya Dora a Kai ya kurma Ihu yace dubu goma Sha biyar dita,Radio dinsa da yake Jin labarai itama a Palo ya barta yaga an sace ta itama,Baba Takaici yace me yasa Dan Ubanki ba a sace wayarki ba Aamna? Aamna Tace ai Nima an cinye min ragowar abinci na da ruwa,wayata ma Allah ne ya kiyaye barayin suna bude kofa na fito daga Bayi da gudu shi yasa suka jefar da wayata garin gudu Basu sace ba,Baba yace ai tsafi sukeyi da tsafi suke Shiga gidan mutum ko ka kulle da key a banza,Mama Tace matsiyata Allah ya takaita Suka koma tare da kulle ko Ina. Mashkoor Yana Kan machine Yana ta jiran Ahmad har 12am ya fara gyangyadi ma Sai ga Ahmad ya fito ta baya da sauri Hannunsa dauke da Radion Baba da Startime din su Aamna wayo ya hada sabo da a tabbatar barayi ne. Mashkoor ya gano plan din abokinsa ya dinga sheka dariya yace sata har gidan surukai wannan wanne irin Dan Iskan suruki ne? Dariya Ahmad yayi yace yau nayi farin gani,tunda nake a duniya sai yau na kalli Abu mafi kyau a duniya,Duk kasar wajen da kaje? Cewar Mashkoor,Ahmad yace ai wannan duk ba kallo bane,Basu da komai me kyau,ai Country me kyau Yana jikin Aamna,Kansa ya dafe yace kaina Juyawa yake kaini gida Kar na Fadi na sume,Rawar sanyi nake ji da mun sani mun dakko Jibson ko banza ya dafe Ni juwa nake ji, Mashkoor yace me ka gani ne Haka? Cikin muryarsu ta Yan kwaya Yace New worldddd….my man,jiri nake ji….yau idona ya samu Karin karfi gani tarrr nake ganin komai,idona ya washe yau,Yau ko me Shan Carrot juice Bai Kai idona kwari da washewa ba,Fess nake gani,Mashkoor Yana ta Dariya yace barawon Suruki,yace ai dole idan ba Haka ba sai su fara Bincike suna sa Ido Watarana su kamani. Baba da safe cikin Fushi ya tashi an sace Masa startime da Radio yace wallahi kullum nayi Sallah sai na buga Tabbatyada duk Wanda yayi min satar Nan Allah ya bayyana shi,Dubu goma da motsi ai ba Nan take ba Kuma duk sakakinku ne ya nuna Mama yace Mene amfanin mace wacce Bata tattala kayan mijinta Bata kula da dukiyar mijinta komai naki Baki San adani da tattali ba ke Kam Baki Dace da matar aure ba da tsohuwar bazawara kika Yi Kama wacce mijinta ya Dade da rasuwa,Mama ta bude Baki Tace Wai ni na sace maka ne wannan wacce masifa ce akan Dan abinda Bai Kai ya kawo ba,Idan kinji haushi yau ki biyani cewar Baba,Mama Tace Zan biya ka Amma kaje Nima Allah ya isa,Baba yace ae ki biya naji Allah ya Isan. A ranar Mama ta aika aka siyo Mata sabuwar Radio da Startime,Baba yace kin taimakawa kanki. Aamna cikin wata doguwar rigar lace ta shirya sea green and milk ,takalminta,Mayafi da jaka duk milk tayiwa Mama sallama Mama Tace Yau ki dawo karfe biyu sabo da Zaki Mana wanki,to ta furta tare da ficewa zuwa Kantin,tunda taje take jiran Ahmad Amma Bai zo ba har 2pm lokacin ta rufe shagon ta wuce gida,20mnt da tafiyarta lokacin Ahmad ya Sha wanka cikin wata sabuwar Jallabiya me tsada ruwan zuma Kamar yanda ya Saba ta tsangale Masa,Takalminsa ma ruwan zuma yayi kyau tare da daura agogonsa me tsada,Sabuwar kitson calabarsa ya gyara tare da Kama ta yasa Black band ya daure ta a tsakiyar kansa,wani uban kyau ya sake tsulawa, Mashkoor Yana ta zugashi yace ai dole ma ta rude,Kaga Handsome,shi Kuma a Gaban mirror ya tsaya Yana kallon kansa sai da ya Gama yace yau ba sauki bazan kalleta ba karta ce Wani sonta nakeyi, Mashkoor yace Good ka ja ajinka ba yanzu ba kwaila Kar ta Raina mu,da Masifa Ahmad ya furta wace Kwailar dan Uwarka? Ya bi Mashkoor zai ci ubansa Mashkoor ya gudu daga room din Yana dariya. Kwafa ya ja ya fito tare da hayewa machine dinsa ya fita sai shagon Aamna Amma sai ya ganshi a rufe,Wanda ke siyar da takalma a kusa ya tambaya yace Ina me shagon Nan? Yace yanzu ta rufe tafi gida naji tana cewa zata Yi Aiki ne,Okay Kawai Ahmad ya Furta ya hau machine dinsa zuwa gidan su Aamna,har cikin gidan ya shigo da Machine dinsa,Aamna ya hango a jikin tap da tarin uban wanki a gabanta na Mama Dana Baba,Sanye take da Vest fara da Skert din atamfa wata maroon,gashinta har gadon baya Bata daura dankwali ba tana ta fama,Mama zaune take tana hutawa Kawai abinta tana ganin Ahmad ta Bata Fuska,ya manta ko Sallama baiyi ba ya karaso da Izzarsa yace Mama Barka da Rana,Baki Mama ta tabe Bata amsa ba Tace sai ka koyi Sallama sai na amsa maka gaisuwar taka,Baki ya tabe tare da yin Sallama ciki ciki ya kumbura Baki Kamar me shagwaba,Mama ta amsa tana hararsa sabo da bakin ciki,Juyowa Aamna tayi tana ta Kallonsa yanda yayi kyau,Murmushi tayi Tace Kawana Sannu da zuwa,Ahmad yace kawa ya Hanya,Lokacin Baba ya fito yace yau me Zan gani bayan auren da kuke da shi kun sake komawa sababbin kawaye Kuma? Mama Tace tayani jin sabon salon bariki, Ahmad Bai kulasu ba tunda wacce yazo wajenta tana Nan Ina ruwansa. Mikewa tayi tsaye suna facing juna juciyarsa sai bugawa takeyi duk sai ya nemi kwarin gwiwarsa ya rasa,a hankali yace wanki kike Yi me uban yawa duk ke kadai,Aamna Tace ae ya na Iya,Kallonta yayi da azababbun Idonsa masu narkar Mata da zuciya yace Bari na tayaki,Aamna tayi Dariya Tace Kaine ka Iya wani wanki kalle ka fa ko Sabulu ai baka iya wankewa ba,komai fa Yi maka akeyi,Nifa super Man ne Ina da karfi da kike gani na har noma Zan iya zuwa gona nayi,Zan Iya nome Miki gonar data fi girman gidana lokaci Daya,karfa ka Sha wahala,ya nuna Kansa yace Wasa kike Dani,Aamna ta Mika Masa kujera ya kalli kujerar yace ba Aiki kike so ba sai kace wata mace na zauna a kujera Allah kiyaye a tsaye Zan tayaki kawo bucket ki gani,Baba da Mama Suka saki Baki suna kallo suna Jin haushi su Kuma gashi Basu Isa su iya ko Masa Maganar banza ba. Bucket Aamna ta kawo Masa har biyu ya nannade Hannun jallabiyarsa dake me dogon Hannu ce,agogonsa ya cire ya ajiye gefe,Yace Ina kayanki a nan? Aamna ta Tace ka gansu a nan,yace Miko ta kansu Zan fara,ai kuwa ta kwaso ta bashi a gabansa kala hudu sai su Hijab da Vest yace idan an Gama sai kije ki cire na jikinki suma a wanke su yau baza ki kwana da Kaya masu dirty a gidan Nan ba,Baba Yana gefe yace Uhmmm…..Sun kasa magana suna tsoro Dan kwaya ne sai ya birkice musu yanzu. Ahmad wanki ya fara baya wanki Yana wanke kala Daya Hannunsa ya fara Dan fashewa Amma ya maze yaci gaba da abinsa,Kugunsa ne ya fara ciwo sabo da sunkuyo amma idan ya Kalli Aamna sai ya fasa mikewa ya huta sabo Kar ya Gaza,Haka ya wanke kayan Aamna fes ya kwashe kayan Baba da Mama Yana tayata suna wankewa ya kusa wanke na Baba,Mama ganin banza ta Fadi sai tace ke Aamna tashi ki barshi ya karasa wankin ki Shiga kitchen ki Mana girki,Ahmad yace ya Zaki ce ta tafi? Mama Tace Kai kace Super Man ne ai sai ka karasa ita ta Mana girki, to Aamna ta furta ta tafi ta bar Ahmad,tana tafiya ya Mike tare da dauraye hannunsa ya kwashe Takalminsa a Hannu da agogonsa da wayarsa,Mama Tace ya zaka daina aikin,dama yayi masifar gajiya,da masifa yace Ni na gaji bazan iya ba dama na gaji yayi tafiyarsa da sauri,Mama tana Kai…Kai….Amma ko juyowa baiyi ba ya hau machine dinsa ya bar gidan. Mama da masifa ta shiga wurin Aamna Tace to ya gudu sai ki Koma ki karasa yace ya gaji shi,Dariya abin ya ba Aamna dama tasan karfin Hali ne Kawai Haka ta fito ta karasa Mama tana ta masifa taje taci gaba da aikin girkinta. Ahmad kuwa a gajiye ya shiga gida Yana dafe Kugunsa ya Iske Mashkoor Yana kallo,Yana yatsina Fuska ya zare rigarsa daga shi sai Singlet da gajeren wando ya fada saman kujera Yana bawa Mashkoor labari yace yau wanki na tayata wash…bayana…taimaka ka siyo min pain killer a chemist kazo kayi min gashi da ruwan zafi wayyooo bayana My waist Yana magana da kyar yace yatsuna sun fashe ….Ni..Ni…nine nace Super man ne Ni, Mashkoor ya dinga dariya yaje ya siyo Masa ya dawo tare da hado ruwan zafi ya dinga gasa jikin Ahmad,shi Kama sai Kara da wayyo,Kwana Uku Ahmad Yana jinyar jikinsa kafin ya warke ya dawo normal lokacin Aamna Bata ganshi ba. Yau Juma’a cikin sababbin dinkunansa yasa wata farar Shadda kamar ka sace shi yanda ya zuba kyau,calabarsa ya daure ya shirya Yana kamshi, Mashkoor ya kalle shi yace ban taba tunanin zaka ja Ni cikin Harkar Nan taka ba,kwana Uku ko Kofar gida ban leka ba wannan wacce masifa ce Wai,Gemunsa yake tajewa Yana shafe shi da wani turare Mai kamshi yace Ni fa na fara gajiya da Harkar wani Kawa da Abokin Nan ya kamata ta San me nakeji a Raina,Mashkoor yace ka bani dama Ni naje na fada Mata kana sonta,Baka da hankali an ce maka sonta nakeyi Kuma ko sonta nakeyi wani ne zai fada Mata Ina sonta ba Ni ba,ai Ni abinda nakeji a Raina game da ita Zan fada Mata ba Wani love ba. Mashkoor yace to yanzu fada Mata zaka Yi? yace ae direct Zan sameta gaba da gaba na fada duk irin abinda zuciyata takeyi idan na ganta yau yau din nan,Allah ya bada sa’a cewar Mashkoor,Fita yayi abinsa Musa me Gadi Yana a dawo lafiya ranka ya Dade,Ameen ya Furta yiyiwa Machine dinsa key ya fita zuwa Shagon Aamna,tana tsaye tana sallamar wata ta siyi kayan kamshi ta hango shi yayi parking,Murmushi tayi Tace Sannu da zuwa,Kasa magana yayi sai kallonta yake Yi har ya karaso inda take ya tsaya a gabanta daf da ita Kamar zai shige cikinta Kuma ya Bata Rai zuciyarsa ce Kawai take bugawa,kasa fada Mata yayi yace ya gida fuskar Nan a daure,Lfy Alhamdulillah ta furta tare da cewa shigo ka zauna Rana,shiga yayi Yana ta Fushi,Tace fushin me kakeyi yau Haka? Kadan ya kalleta Bayan ya zauna a farar kujera yace da zuciyata nake Fushi ita nake nunawa bacin Raina,Dariya ce ta Kama Aamna Yana ta kallonta a ransa yace kin cuceni zuciyata bazan yafe Miki ba Kuma yau Bari na koma gida sai kinci ubanki,Me ta maka zuciyar Aamna ta tambaya yace Ni kadai na San irin wulakancin da take mini Amma ba komai Yaja kwafa,Aamna ta sake kecewa da dariya Tace kana da abun Dariya wlh,Kawai sai ran Ahmad ya baci shi ga abinda ya dame shi ya fada ya kasa fada duk akan Aamna Dan rainin hankali ta sashi a gaba tana ta dariya,a ransa yace na koma ma abin Dariya na koma Comedian ba komai yayi Shuru. Har ta Gama dariyar ta dakko Gyada soyayya Tace ga Gyada muci,ganin tasa hannnu a Ledar ta Eba tana ci sai shima zai Eba Aamna Tace tsaya na bare maka,bare Masa tayi Guda biyar ta zuba Masa a tafin Hannu Tace to ci,kallonta yayi sannan ya zuba a bakinsa Yana daga zaune Yaja baya yayi wani tangal tangal Kamar zai Fado Aamna ta rike kafadarsa da sauri tana tambaya lafiya???yace Dadi ne ya kwashe Ni sabo da hannunki da ya shafi jikin gyadar nan,Dariya Aamna tayi Tace Kai Ni nayi zaton ma wani Abu ne,wani English novel ta dakko na love tana karantawa Tace ka San littafin Nan? Na Mene ya tambaya? Love Novel ne Baki ya tabe yace sai ku wannan ai,Mayafinta ne ya Dan zame kadan gashin Gaban goshinta ya bayyana wani yala yala,Hannu ya sa tare da jawo mayafin ya gyara Mata Aamna dai mamaki yake Bata kamar ba shi ba,duk irin kiyayyar Daya nuna Mata tana ina ne? A ranta Tace Anya ba Yana da manufa a kaina ba kuwa? Gaskiya Zan nemi shawarar Siyama. Kiran Sallah aka kwala Sallar Juma’a,Aamna ta kalle shi tace yanzu za’a fara khuduba sai muje Sallah ko? Da sauri ya girgiza Kai yace a gida zanyi anjima,Jam’i Yana da Lada fa? Yace na fiki sani ai, kin San kuwa Islamiyya Nawa nayi a duniya? Kin San saukata Nawa? Aamna Tace Dan Allah muje tare,a ransa yace Yarinyar Nan fa zata fara juyani karka sake wannan Yar tatsitsiyar ta juyaka a banza,ai ba sonta kakeyi ba da har zata juyaka,wata zuciyar tace Amma idan kaje Sallar zata ji Dadi zata samu farin ciki,Kumatunsa ya Mara a hankali yace Kar ka Bari ta juyaka ka dawo hankalinka,mikewa yayi yace Zan tafi,Tace Nima tafiya zanyi zanje gidan Zuhra,yace kin fiye yawo to na fasa tafiyar Zama ya koma yayi Dole ta zauna,Lokacin Sallah yayi Yana kallo tayi Alwala tayi Sallah a Nan shagon,tana idarwa yace Sannu da kokari,Fuska ta Bata tace Dan Allah kayi Sallah Kar lokacinta ya wuce,Shuru yayi Kuma yaki tashi sai yaga tayi Fushi ta zauna,Fuskarta ya leka kadan a ransa yace akan Haka har tayi fushi,Bari to na Yi Amma badan fushinta ba,Mikewa yayi tana kallo yayi Alwala ya Tada Sallah murna tayi ta saki ranta ta juya tana kallonsa a nutse yayi sallarsa kasancewar Bai Sha komai ba,Yana idarwa ya Mike ya fice tare da tafiya ko Sallama bai Mata ba. Mashkoor kuwa Yana can a gidan Ahmad tare da su Jibson gaba Daya Yana ta Basu labari yanda Sarkinsu ya lalace,duk sukayi tagumi suna jimami,Jibson yace ai kuwa sai munje har inda yake tayata siyar da citta mun kure shi,yanzu King ne ya lalace Haka abin haushin Akan wannan Yar Yarinyar Aunty Balaraba cewar Bash,Mashkoor yace yanzu idan kaga shigarsa Daya canja kamar Limamin masallaci,Salati suka saki Tawaga yace duk akan Yarinyar nan lallai sai munci ubanta kuwa tunda ta mayar Mana da King Haka, Mashkoor yace Uhm Baku gani ba har wani sharemu yake Yi ba Amma muyi Masa Uzuri ai King ne sai abinda yace,Allah sarki masu shaye shaye da hankalinsu sun San Amana da abokantaka duk abinda dayansu ke so suna so,sannan basa mantawa da Alkhairi da zaman tare,shi yasa sun Shaku da juna sosai. Ko da Ahmad ya shigo ya Iske su tafawa sukayi ya haura sama,Yana shiga wayarsa ya dauka tare da Kiran Sis dinsa Humaira,Humaira Tace Yaya na? Ya kake? Ba lafiya sis Dan Uwanki ya fada cikin bala’i,Humaira ta tsorata sabo da Bata taba Jin yayanta Haka ba,Kamar zata Yi kuka Tace Yaya mene ya sameka? Sis wata ce Nan idan na Ganda zuciyata kamar zata fito ta fado,sai ta dinga Yi min kida me zaki,Humaira Tace Kamar ya? Yace idan fa ban ganta ba bana iya bacci,sai na ganta nake samun nutsuwa,Haka idan naji muryarta sai naji Kamar wani kidan goge sabo da Dadi,gashi tsoronta nakeyi sai naji na kasa fada Mata me nake ji,Yanzu ya zanyi? Humaira tayi zaton zaice Aamna ce Amma yace Mata wata,Amma duk da Haka tayi murna yayanta ya fada soyayya,Tace Yaya kaje ka sameta karka ji tsoro Kawai ka fada Mata me kake ji,ka daure Haba Yaya kamarka wace zata ce baka Mata,Sis Nifa ba sonta nake Yi ba Kawai dai Ni na fada Miki abinda nake ji,Humaira tayi Dariya tare da furta ka fada Mata karka ji wani shayinta kaji,yace to sis Zan gwada ya kashe wayar,lokacin da yayi wanka su Jibson sun tafi sai Mashkoor sai shi. Ahmad dakin Aamna ya Shiga Wanda ta bari,cikin kayanta data Bari ya zabo wani Mayafi Baki ya fito Palo wajen Mashkoor tare da jefa mayafin a jikin Mashkoor yace Man tashi ka yafa mayafin Nan za mu gwada practical akan yanda Zan furtawa Aamna me nake ji game da ita,yanzu ka yafa mayafin Nan Kaine a matsayin Aamna Ni Kuma Zan zo na gwada ya zan bullo Mata idan naje, Mashkoor ya dinga dariya harda buga kafa,ya Mike yayi Rolling da mayafin Aamna ya taho Yana yanga tare da wani shanye Hannu,a Gaban Ahmad ya tsaya tare da Yi Masa fari da Ido ya wani tsotsi lips yace Hey…..harda rike hips da Hannu Daya yanda Mata ke Yi,Ahmad Dariya ta kamashi shima ya kalli Mashkoor yace to ai Ni gemunka ne idan na kalla Taya Zan maka magana Ina ganin gemu dalla jiba Muscle dinka damatsa na maza,jiki Kamar katako, Mashkoor ya sake makale Murya Yana fari da Ido yace Dan Allah kayi mu gwada ai Kawai Kamar shooting Film ne Oya fara Mana nine Aamna gani. Ahmad Yana daga zaune ya fara magana Kamar zaiyi kuka,Baby Idan na ganki zuciyata wani Dancing take min,Idan kika min murmushi kuwa har wani Rawar galala zuciyata take min,Sannan Ni sai naji Ina shakkar Yi Miki magan….da sauri Mashkoor ya dakatar da shi yace dalla Haka zaka Yi lallai zata Raina ka Haka maza ke magana wani gadangatsai Taya zaka burgeta oya canja salo Action…..Ahmad yayi Gyaran Murya tare da gyarawa ya kalli Mashkoor zai fara magana sai ya sheke da dariya yace wallahi idan na kalli Damatsanka hankalina Bai kwanciya bana kallonka a Aamna ga gemu da saje haba,Kayi sauri Dan Allah wannan fa Kamar Film ne gwada Ina jiranka Mashkoor ya furta Yana wani Fari da Ido Yana karairaya Kamar Dan Daudu,Ahmad mikewa yayi tsaye yace Ni bazan iya ba kallonka nakeyi wani Gardin banza dalla bani ya fisge mayafin daga jikin Mashkoor tare da ajiyewa a gefensa, Mashkoor yace kaga matarka ce fa ka daina wannan abin ka fadawa Mummy ta fadawa Aamna ta dawo gidanka kaga shike Nan. Ahmad yace baka da hankali Nifa ba Wai wani mu zauna tare ko wani Sex ba,ya za ayi na birgeta,ya za ayi tasan me nakeji a Raina game da ita shine Kawai dawowarta gidana ba shine mafita ba,Ni ba wannan nake so ba,Dan dawowarta ai ba matsala bane Kawai Ni ka Gane nufi na,idan ta San halin da nake ciki Nan gaba Sanda taga tana so sai ta dawo gidana Ni wannan ba shine damuwa ta, Mashkoor yace Amma sai kayi ta wahalar da kanka kana tsallaka musu gida,Kai banza ne bana so ajina ya zube ta Gane Ina son na kalleta ko wani Abu,ai abin sai da dabara cewar Ahmad. Da dare 9pm Ahmad suka Isa gidan su Aamna Mashkoor Yana jiransa a can bayan gidan,Wai shi lallai Bai so Aamna ta Gane Yana son ganinta sai dai ya kalle ta a boye.

Sharhi

AsmaBaffa
10/26/21, 8:53 AM – A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA AAMNA🌵🌵

Page 51-55

KARSHEN FREE PAGE

DUNIYATA AAMNA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

        NA KUDI NE

MASU SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Kinfi karfin page
NAFEE
Allah ya bar kauna

Page naku ne

MAMU GALADIMA
AYUSHEE
MOM PAPI AND ALAMEEN
OUM ABULKHAIR
HAUWANCY COOL LIFE
S.Y.SAGAGI
RA’AYYS
I HAFSAT
UMMY MANGA
MAMAN ARFAT
MAMAN YASIR
M DEWU
HAUWA A CHINDO
HALIMA

GODIYA TA MUSAMMAN

DIYAR KATIBI
UMMIN HIBBAH
UMMA KHURSUM
ASMAU YUSUF
UMMIN DEEJAT
BESTYNBEELAT

Yau Baba Bai dawo da wuri ba,Aamna Kuma dawowarta kenan daga gidan Zuhra Mama Tace tazo ta tayata dafawa Baba abinci,ko hutawa Bata Yi ba ta shiga wajen Mama a kitchen suna girki,ta Kofar gate Ahmad ya shigo gidan,ta windown kitchen ya leko dai dai lokacin Mama ta dago kanta sama Kawai Harshen Ahmad ta gani ya Mata gwalo ya bace.

Amma Bata San shi bane Tace Kinga kamar Harshen mutum ta window ya min gwalo ya bace Aamna,Aamna ta sheke da dariya Tace wallahi Mama yanar Ido ta Kamaki sai munje asibiti an duba idonki,Mama ta dage ita fa sosai taga Harshen mutum,Aamna ce ta maida abin Dariya shi yasa Mama ta hakura Kawai, shi kuwa ya gansu a kitchen ai ta Kofar Palo ya shigo a hankali ya shige Dakin Aamna,bed din Aamna wani me kyau ne na karfe irin na kasar waje Dan madaidaici Amma kasan bed din Yana da tsayi mutum zai iya Shiga kasan Bed din ya buya gashi ta gyara bed din ta saki bedsheet har Yana taba kasa ma’ana ko mene a kasan Bed din baza a iya gani ba,lekawa Ahmad yayi ya kuwa shige ciki ya kwanta abinsa,Bai Dade ba Aamna ta shigo dakin tare da dannawa kofarta key,Abincinta ta Ajiye a plate da ruwa harda lemo mirinda,ganin ba kowa a dakin ta kulle ko Ina sai ta hau tube kaya,dama dabiarta ce idan ta kulle Kofa ta dinga tubewa daga ita sai pant ba komai a jikinta,Ahmad yace yau ma idona zai samu Karin karfin gani Ni da ciwon Ido haihata haihata ya Dan leko ta kasa,Baki ya bude ganin Aamna da pad a jikinta da Alama period takeyi,Yana kallo ta dakko wata pad din da bakar Leda ta shige toilet sabo da Gadarar ba kowa ga towel a Hannunta Amma Taki daurawa ta tafi da shi a hannu.

Fitowa Ahmad yayi ya Bude plate din yaga rice and stew da Naman rago yanka Uku sai salat a gefe,yace da a gidana ne sai kinci nama kin koshi duk Loma Daya sai kin hada da yankan nama,Sorry My world ya rufe Mata tare da komawa kasan bed,ta Dade tana wanka kafin ta fito tana goge jikinta ta fara shafa lotion ta cire guntun Towel din tana ta shafe jikinta,Ahmad Idonsa Yana waje ya leko yace sunanki me Tinjim daga yau,sai data Gama sannan ta saka Riga da wando na bacci masu laushi ta zauna ta tare da fara cin abincinta da mamaki yaga ta cinye tas ta shanye lemo da ruwa,a hankali yace Allah yasa Ina da kudi Zan iya ci dake Amma da talaka kika aura ai ke Kam shikenan sai dai Gomnati ta kawo dauki, Popcorn yaga ta dakko a wani katon Bowl ta Ajiye a gefen bed ta kwanta tana latsa Wayarta tana ci a hankali,idan ta eba ta cire Hannunta tana can tana Danna waya sai ya zuro Hannu ya eba ya cinye a kasan Bed, suna Haka taga wayam Wai har ya Kare,Aamna ta dinga mamakin kanta Wai har ta cinye popcorn din,ta kashe Wayarta tare da kashe light ta kwanta tana adduoi kafin ta Gama Adduar bacci ya kwashe ta.

Sai da ya tabbatar baccinta yayi nauyi sannan ya fito a hankali da Dan hasken wayarsa yayi amfani tare da Kare Mata kallo,Aamna ta baje a saman Bed,cinyoyinta Suka tafi da hankalinsa Hannu yasa tare da shafa su a hankali yanda baza ta tashi ba,motsi tayi kadan tare da sake wangale su,Ido ya Kura musu yasa Hannun ya janye rigarta sama sosai ya kallesu son ransa, ganin kamar zata farka sai ya daina, Kansa ya duka a saitin kirjinta tare da kwantar da Kansa a Kirjinta yaji wani laushi sai ya lumshe Ido Nan take yaji ya fara Jin bacci,da sauri ya tashi Jin ta hada zufa sosai sabo da Rashin wuta bare a kunna fanka,Mifici ya gani a can gefen bed din nata,Dauka yayi a hankali ya shiga yiwa Aamna fifita ba ji ba gani Kamar me jinya a gadon asibiti,Aamna cikin bacci taji Iska me Dadi tana Ratsata ta sake gyara kwanciya tare da Jan numfashi me Dadi,Murmushi yayi yaci gaba da Mata fifita sai da Hannunsa ya gaji sannan yaga Kamar zata farka sai ya ajiye mificin ya lallaba ya bude Kofar a hankali ya fita Allah yasa Bata farka ba Kuma Bai hadu da kowa ba har ya bar gidan, Mashkoor Yana ta uban jira ya hauro ya fito Suka tafi gida.

Hannu Dayan Wanda ya shafa Cinyar Aamna sai Ahmad ya daga shi sama kada ya daina amfani da shi Kamar Wanda aka yiwa lallen Sallah,Mashkoor yace lafiya Wai me ya samu Hannun rauni kaji ne?yace ai wannan Hannu yau ya Zama special bazan na aiki da shi ba,Kai ko Gaisawa da maza bazai Yi ba sabo da jikin Aamna Yana makale a jikin hannun Nan, Mashkoor yace ka shiga Uku wallahi king. Bayan Kwana uku Siyama ce ta Kira Aamna lokacin Aamna tana shago Tace gani Nan zanzo Miki Ziyara,da murna Aamna Tace to sai kinzo,15mnt da yin wayarsu Ahmad yazo sanye cikin 3qutr da t-shirt hannunsa dauke da wata katuwar leda baka,Murmushi Aamna ta saki tare da Furta Sannu da zuwa,jajayen lips dinsa ya turo gaba da shagwaba,Ledar ya kawo gabanta tare da ajiyewa ta Bude yaga kifi tarwada da yawan gaske,murmushi ta saki tare da Kallonsa Tace yanzu baka manta ba Ashe Kuma ma ai Rannan ka Aiko Mashkoor ya kawo min kifin harda kaji da yawa fa,Ba kince kina sonsa ba? Ae ta furta yace to ai shine na kawo Miki,Kuma kaji ai Naga a gidan Baba bakya cin nama kina koshi shi yasa duk sai ramewa kike Yi,Dariya Aamna tayi Tace Ni bana son sharri duk kibar Dana yi,Kallonta ya tsaya Yana Yi har ta Gama dariyar,ke komai naki Dariya Wai Ina rashin kunyarki tayi ne da surutunki? a baya masifa kike min da Shishigi me yasa yanzu kika daina? Aamna kanta ta danga sama tayi fari da Ido Ahmad a ransa yace Mashaallah ko iya wannan aka barni da shi ya isheni farin ciki na sati Guda idan na tuna shi. Mikewa tayi tsaye tana Masa Murmushi Tace Kaine ka gyara min halaye na,kaci ubana da yawa sai lokacin na Gane Allah Daya,a hankali yanda baza taji ba yace ai Nima yanzu uban Nawa kike ci na Zama wani banza,Bakinsa taga Yana motsi Tace me kace? Cewa nayi Ni ba abinda na Miki kece kike min shishigi,Siyama ce tayi Sallama gabanta ya Fadi ganin Ahmad da Aamna a tsaye daf da juna kamar zasu Rungume juna,Fuska ta Bata tana Hararar Ahmad sabo da kishinsa,ita ba hassada takewa Aamna ba Kawai son Ahmad ne yayi tasiri a ranta taji dama ita ce. Laaa Siyama kinzo cewar Aamna,Ahmad juyowa yayi Amma ko kallo Bata samu daga gare shi ba ya maida hankalinsa cikin Shagon,Nan Siyama ta shige ciki ta zauna tana satar kallon Ahmad,Ledar dake gaban Aamna take ta faman kallo taga kamar Abu na motsi ciki,Ahmad ganin tana ta kallon Ledar ya tabbatar Aamna sai tabawa Siyama kifin Nan itama ko su raba tare sai ya leka Daya shagon ya Kira wani yaro Wanda Ahmad yasan Yaron kusa da gidan su Aamna yake ganinsa shima gidansu makwafta ne,Yaron Yana zuwa Ahmad harda shafa Kansa yace Dan magyatso kasan gidan su Aamna? Yaron da Ahmad ya Masa suna da Dan Magyatso yayi dariyar sunan sabo Yaron Kalar yunwa ne,jikinsa tsilili cikinsa Dan kato sabo da Almajirin gidan Wasu ne a kusa da gidan su Aamna,yace ae nasan gidan Ina shiga ma idan an aikeni,Ahmad yace ka iya machine? Yaron yace sosai ma ai Ni nake yo cefane a machine din gidan Uwar dakina,Good cewar Ahmad yace ungo key din machine Dina jeka gidan su Aamna ka kaiwa Mama sakon Nan kace gashi inji Aamna,Yaron yace to ya karba ya hau machine din Ahmad ya tafi,Siyama ta so ace ta karbi kifin ko Quarter ne itama taje gida sun Sha farfesu Amma tana kallo Ahmad ya dauke Dan mugunta. Tunda Siyama ta Shiga shi ya fito ya tsaya a waje,Aamna Tace ka shigo Mana yace a’a Machine Dina nake jira tafiya zanyi,Siyama ta kalla tace ina zuwa kawata ta fito Wajensa suka tsaya,tana ta Kallonsa a ranta tana ayyana irin kyansa,Shi kuwa ganin tana kallonsa harda Kara gyarawa Kamar za a dauke shi hoto,idan ta kalla ta kalla sai ya sake canja style din tsaiwarsa Haka yake ta Mata ya tafi da hankalinta sai daga baya ta lura da abinda Ahmad ke Yi Yana ta canja style din tsaiwa,Dariya ce ta Kama Aamna ta danne kadan tayi Murmushi Kansa ya shafa tare da mazewa kamar ba shine yayi ba,Hannunsa Aamna ta rike ya Janye hannunsa da sauri,Aamna tace lafiya? Kitsonsa ya Sosa yace ba komai Kawai Ni ba a taba min jiki kin sani ko kin manta ne?

Baki Aamna ta tabe Tace daga an Dan rike maka Hannu sai kace Dan gwal? Yace ai nafi gwal Ni,Harararsa tayi a ranta tace Dan ma na Dan nuna Masa caring shi illarsa Bai San arziki ba,Ganin ta harareshi yace Jaraba tare da miko Hannun yace ungo cinye shi ki huta,Bige Hannun tayi tana Dariya Tace bana so,Suna Haka Yaron ya dawo da Machine din Ahmad ya karba tare da bawa Yaron dubu biyu,ya dinga Murna yana godiya,Ina Handbag dinki? Ahmad ya tambayi Aamna.

Tana ciki yace dakko min ita,me zakayi da ita Fuska ya Bata yace ki dakko Mana Ni ba Mudubi ko powder dinki Zan gani ba nasan ku ba Uwar komai a jaka sai Kuna boyeta,Dakkowa tayi tare da Mika Masa yace Bude abarki ki rufe idonki Kuma,Aamna ta zuge jaka ta rufe ido,ganin Haka Siyama ta leko tana kallo Ahmad ya zaro kudi masu yawa Yan dubu dubu ya zubawa Aamna a jaka yace to Bude,Bude Idonta tayi taga kudi dama Bata da kudi tayi broke Bata da ko sisi gashi tana son siyen abinda ba a rasa ba na bukatar rayuwa,taji Dadi sabo da ya Bata lokacin da take bukata Tace Na gode Allah ya Kara budi Amma sunyi yawa kamar,Kansa ya dauke yace na tafi Mummyta ta aikeni tun dazu wani waje zanje na Mata Abu,Aamna Tace Kai dai kana son Mummy kullum Mummy,ai Mummy ta daban ce,Mummy na tafi Mummyn kowa cewar Ahmad,Aamna Tace Nima tawa tafi ta kowa,Murmushi yayi yace kin nemi Number Abbanki kuwa? Aamna Tace me Zan Masa tunda ya manta da ya auri Uwata ya Kuma haife Ni idan na karba me Zan Masa? You are not Serious Haka aka ce Miki Iyaye suna laifi?Shuru Aamna tayi Watarana tana mamakin Hankalin su Ahmad,gasu dai suna tafka abin tsiya sai Suna Abu Kuma na basira da hankali, a fili tace Suma Yan Uwan nasa Dana je Sokoto nace su bani number dinsa Suka ce wallahi wurin shekara Uku kenan duk sun kasa Samunsa sai dai suna Kiran Yan Uwa na can kasar sunce yana Nan lafiya Kawai dai yanzu yayi retire a aiki Bai da aikin Yi ga Yara da Mata sun Masa yawa wahala ta kamashi,Ahmad ya girgiza Kai yace tab nasan yanzu ya sake kanjamewa Allah Sarki Abbinki,Aamna Dariya ya Bata ta bigeshi a kafada kadan Tace Wai Mene Haka ka dameshi Akan ramarsa, Murmushi yayi yace Bai yuwa ya rasa waya sai kace a Nigeria ai can ba a wannan talaucin, Ni Zan nemo Miki number dinsa,Aamna Tace Okay thanks, Machine dinsa yayiwa key tare da tafiya abinsa. Siyama tana zaune ta kumbura tayi fam kamar ta fashe tace ke dai Aamna kinyi asara,wallahi Baki da hankali to wannan abinda yake nuna Miki ba so bane,Kar ma ki yaudari kanki Ahmad bazai taba shiryuwa ba ko jiya naje wajen Jibson a club Suka kwana suna shaye shaye suna rawa,Aamna Tace karya kikeyi Siyama wallahi Ahmad baya rawa,Yana Jin kida Yana bin Waka Amma in Banda ya Dan kada Kansa ba abinda ya taba Yi na rawa,Da kike cewa bazai shiryu ba kece Allah,Ina ruwana da Club dinsa,Siyama Tace Iyye to Bari kiji idan Baki sani ba Neman Mata suka koma Yi yanzu,kije ki tambaya Ahmad lallabaki yakeyi ki saki jiki da shi ya samu biyan bukata,Aamna Tace karfa ki manta Mijina ne,ko ma me yayi Hakkinsa ne ko ciki ya min akwai me zagina a duniya? Wai me yasa kika tsani Ahmad Haka ne Siyama? Siyama Tace sabo da Ina sonki kawata Ina kaunarki bana so ki fada wani Hali,Aamna tayi shuru….Tace to yanzu me kike so nayi? Karki bashi dama Kawai Kuma karki yarda da shi karki Bari Zuciyarki ta fada sonsa cutarki zaiyi,ki kiyaye Aamna bana so na ganki cikin wani Hali,plan suka hada Miki,Ahmad tun Yana yaro kangararre ne a Haka ya girma a tunaninki dare daya zai shiryu sabo da ke? Kiyi tunani fa,wanne duka da wulakanci ne Baki Sha ba a Wajensa? Ai Ni nake tsokanarsa Aamna ko a lokacin Ni ke shiga harkarsa da ban kulashi ba babu abinda zai min,Siyama tayi Dariya Tace kina Abu kamar yarinya 25yrs Sam Baki da wayo Baki da hankali Ni Naga wani Tsoronsa kike ji ma kina wani biye Masa,Dan giya irin wannan Dan kwaya abin kyama cikin Al’umma mutanen da Basu San darajar kansu ba bare ta wani Nan fa Siyama ta dage ta dinga zuga Aamna tana fada Mata karya,har ta Gama sannan Aamna Tace Ni fa bazan iya wulakanta shi ba,Kuma bazan iya masa komai da zai Bata Masa Rai ba,Kawai dai nasan bazan Bari na fada sonsa ba,ko cewa yayi Yana so na Zan Amince Amma badan so ba Zan Amince Dan nayi kokari na canja shi ya dawo mutum Kamar kowa ya daina wannan shaye shayen shine Kawai abinda Zan iya Dan na taimaki Iyayensa,Siyama tace ya dai fiye Miki Ina Baki shawara karki fada sonsa. Bayan wasu satikai Ahmad Haka yake ta wahala da zuciyarsa ya kasa fadawa Aamna idan yaje da Niyyar fada sai ya kasa babu irin plan din da Basu hada ba da su Mashkoor Amma idan Ahmad yaje Gaban Aamna sai ya kasa furtawa,Yau Suna zaune da Mashkoor suna shaye shayensu Mashkoor yace yau shine Plan na karshe King idan baka iya fada Mata ba wallahi gidan Nan Zan Bari kaje ka karata,Ahmad ya daki Center table yace yau Dole ne na fada ma Dole babu fashi mene plan na gaba?wayarsa ce tayi Kara Yana dubawa yaga Bash ne abokinsu dagawa yayi yace ya akayi ne guy? King ku fito Umman Jibson ce ta rasu a asibiti ciwon Sugar dinta ne ya tashi Ana kaita Hospital ta fece wallahi,Ba ko Salati Ahmad yace yanzu Ummati ta ware itama? Yace kwarai kuwa Kun manta yau Kuma ake Sadakar Arba’in din Baban Tawaga da ya Dier shima ya kamata ku fito fa Jibson Yana wani Hali, Mashkoor ya kashe waya tare da kallon Mashkoor tashi mu tafi Ummati ta arce itama shikenan mijinta yayi asarar matarsa Allah sarki Shan maganin Mata ya Kare Abbin Jibson Kuma karya ta Kare Dadi ya kare Masa ya Gama Shan rabonsa, Mashkoor yace Kai tsohuwar Nan ai ta godewa Allah ai su Kam sunci duniyarsu me zasu ce da Allah mu ware kawai. Machine suka figa Suka tafi Ahmad ya kalli Musa yace Kai Musa ka taho ta’aziyyar Ummatin Jibson kaga ku na kirki ne wala’allan adduarku tafi Shiga,Dariya abin ya Bawa Musa ya danne ya nuna jimaminsa yace gani Nan kuwa Bari na kulle gida,Ahmad yace biki ya same mu sabo da yanzu mutuwa ta koma biki Yan iskan mutane su taru ayi ta kwasar girki, Mashkoor yace Ana kaita kabari muje a agazawa su Jibson da tallafin kayan abinci kasan babansu ba harka Yana Shan wahala,Haka ne fa Guy cewar Ahmad,ai kafin kace me Yan shaye shaye ta ko Ina abokan su Jibson suna ta sauka wasu a mota wasu a machina, da su aka yiwa Ummatin Jibson Sallah aka kaita,Tabarmar su daban a Kofar gida sunyi jungum jungum Ana zaman makoki,Jibson ya dunkule waje daya a tsakiyarsu tare da sunkuyar da Kai kasa Yana Dan Hawaye motsi kadan sai Yace Uhmmmmm……..Uhmmmm…..su Kuma abokan suna Sorry…sorry….Guy,Baban Jibson Yana kusa dasu Yana jinsu da mutanensa shima Ana karbar gaisuwa,duk Wanda yazo yiwa Jibson gaisuwa yace Ashe Ummati ta rasu? Jibson sai yace da Uwata ta mutu gwara Ubana ya mutu wallahi,Kowa yazo sai Jibson ya fada Masa da Uwata ta mutu gwara Ubana ya mutu Abbin Jibson Yana ji Yana ta Jan kwafa,wasu kuwa dariyarsu Kawai suke dannewa. Tawaga ne yazo ya kotse machine tare da bulbule mutanen wajen da hayaki ya sakko wajen su Ahmad ya Bude hannaye da sauri Yana takowa Yana an Kuma…an Kuma Yan Uwa an Kuma jama’a…suka ce cikin jimami an Kuma Guyu……ciki yazo ya zauna yace Yau akayi Sadakar Arba’in ta Abbana Ni fa yanzu gaba daya na koma Wani shege….shegeee ne Ni Kawai bani da uba…kaf mutanen wajen babu Wanda Bai Basu Dariya ba Amma wasu Haka suka danne sabo da wajen Mutuwa ne,wani Wanda ake cewa Gayu yace ai Nima Ina cikin Shegun mu mun Zama ‘yayan shege to ba uba ai Kawai ka Zama Dan shege….wani Ana kiransa Jagu Dan wiwi a cikinsu yace wannan abin idan na tuna ba karamin kuka yake sani ba ya fashe da kuka shima Yana cewa Nima Ina cikin ‘yayan Shegu,Wai su Kawai idan baka da uba ya mutu to ka koma Dan Shege,idan Kuma Uwa ce to ka Zama cikakken Maraya komai girmanka. Ahmad ya dafa Jibson yace ai gwara na Zama Shege akan na Zama Maraya Jibson,Mummy ta Mutu ai Kawai ku kaini kabari da Raina Nima ku binne,Mashkoor yace mu Kuma mu zauna da wa idan mun binneka shike Nan muma Bamu da kai? Ai bazai yuwu ayi biyu babu ko daya ba,Ana ta kallonsu Dariya ta cika mutane Amma an kasa Yi sabo da mutuwa kowa sai ya bar wajen yake Dariya,Wani Dan Majalisa yazo Ta’aziyya,Baban Jibson ya Kira shi yace ga babban Dana can,Jibson ya karaso wajen,Dan Majalisa yace Sannu da Hakuri Allah yaji kanta yaro kayi Rashi,Jibson yace Babban Rashi yau na tabbata Maraya Dan Allah ku bani mukami a Gomnati na shugaban Marayu na Nigeria da Uwata ta mutu wallahi gwara Ubana ya wuce sau dubu dubu,Danmajalisa shima abin Dariya ya bashi gashi da yanda suke Maganar abin Dariya ta Yan maye.

Kudi ya zaro dubu Ashirin ya mikawa Jibson yace gashi ko ruwa a siyawa Mutane Jibson yace Allah kiyaye na karbi bakin kudi,wannan bakin kudi ne tunda baka bani ba sai da Uwata ta mutu zaka bani wanne amfani zasu min,Baban Jibson ya daka Masa Tsawa Amma Jibson yace wallahi bazan karba ba,da karfi ya daga Murya Dan wulakanci sai da aka ga Uwata ta mutu Za’a taimakeni duk an wani cika Mana Kofar gida Ana cinye Mana Dan abincin Daya rage Mana,Dame zamu ji da cinye abinci ko da jimamin,kowa Yana ci Yana wani jimami,Mata Yan Uwa suna kuka suna ta girki Ana Dora tunkunya Ana saukewa wallahi baza mu lamunci wannan ba,Ahmad ya mike shima yace a barmu da abinda ya dame mu na rashin Ummati mun gaji tun safe muke bi layi layi na mutane Muna rabon ruwan Sha da Abinci,Tawaga yace aikin banza Muma Haka Dan kudin Sadakar da aka Tara Mana da abincinmu cikin sati Daya aka cinye shi tas ga tarin Yara an mutu an bar min,Baba ya dinga aure aure ya Tara Yara Ashe duk Haihuwar da akeyi Ni ake haifawa ban sani ba, wallahi da nasan hakane da kaina Zan dauki matan Baba na kaisu asibiti Dan ubansu duk a daure bakin Haifarsu,yanzu ga Yara can sunfi ashirin Ni kadai ne Babba Kuma ba Wani Abu ya mutu ya Bari ba gona ce Kawai a Kauye Guda biyu.

Ina Shiga gida Yara suna zare Ido Yan kanana turagutsa ba Wanda zai iya aikin karfi to wallahi a Nan ma tunda Ummati ta rasu Baba baza ka Kara aure ba wallahi ko wace zata aure ka sai mun farke Mata ciki,Ahmad yace bazai yuwu Iyaye ku dinga aure aure Kuna mutuwa Kuna bar Mana masifa ba,ga yanda kasa take ciki yanzu a mutu a bar maka Yara Kai kanka da kyar kake iya rike cikinka, daga yau mun Zama masu yaki da Aure auren Iyayenmu maza,duk tsohon Daya matsu zai Kara aure to ya Nemo juya wacce Bata Haihuwa ko Kuma aje a cire Mata mahaifa. Jibson yace Iya Ummati Abbi ya aura Amma Haihuwar ta Sha Uku Haba jama’a sai kace macen Zomo, Guda Daya ne ya rasu Sha biyu suna Nan cas da me zanji gasu duk mata,ko wacce na shiga Yaya kudin makaranta,Yaya kudin kitso,Ya..ya..ya…masu auren ma yau Fa’iza mijinta ya hanata abinci ta dawo gida an auno Mata shinkafa ta tafi da ita,gobe Safiya mijinta ya mareta ta kawo Kara,jibi Zakiyya mijinta ya korota to a gaskiya bazai yuwu ba,daga yau kunci abincin karshe gobe ko koko ba me Fitowa da shi wallahi.

Mutane suna ji Ana ta kallo wasu suna zanzarewa Baba shima yasan Yaran sunyi gaskiya tsoro yake ji Kar a cinye Dan abincin nasu su fada wani Hali Amma sun tozarta shi ya zaiyi dole ya kyalesu tunda su suke siyo komai abokan,Ahmad kadai mota guda ya sauke musu ta kayan abinci da safe,Haka duk abokan kowa iya karfinsa sun kawo tallafi daban daban,Kuma ko ba mutuwa sune suke taimakonsu basa kukan rashi.

Ranar da akayi Sadakar Uku suka Kori kowa Suka ce Sunna sak ba zaman makoki ya Kare,Ranar Bash ya tafi gida ya Iske Mamansa tana Aiki yace Mama Yaran naki Mu bakwai kika Haifa Dan Allah Mama karki sake Haihuwa Haka,Mama ta kalle shi tayi murmushi Tace baka da kunya Bashir Ni kake gayawa Haka? Wato ka Sha ta maka yawa zaka zo ka min hauka ko? Bash yace Mama Naga darasi Yaran Nan Ni fa kuke haifawa kina ganin Yayana ba lafiyayye bane yanzu nine kamar Babba gashi Mama da kuruciyarki,Dake ita Maman Bash sai ka rantse ba ita ta haife su ba,Allah ya Bata kyan jiki karamin jiki gareta sai ka rantse Yayarsu ko kanwarsu,Bash yace Mama gobe Monday ki shirya zamu je asibiti ki duba abokina,Mama Tace Allah ya kaimu Bashir.

Washe gari da Sassafe Bash ya dauki Mama zuwa Asibiti,wajen Likita Mama taga sun shiga,Bash yace Likita gata na kawo maka ita akan Maganar da mukayi,yace matarka ce ko me? Kawai Bashir yace Matata ce, Maman Bash Dake akwai saukin Hali ba ruwanta yaranta Kamar abokanta tana kallo Bash yace a Mata Allurar Family planning Haihuwar ta Isa Haka,Likita yayiwa Mama tambayoyin da Suka Dace itama dama ta gaji da Haihuwar,Test aka Mata Bata da ciki Nan Likita yayiwa Maman Bash Allurar wata biyu,yace idan time ya cika ku dawo Karku tsallake,Bash yace an gama,ya figi Mamansa a Machine suka dawo gida,Kuma Mama Bata fadawa mijinta ba sabo da Bash yace karki fada Masa kin San Baba Dan gargajiya ne sai dai yaga Shuru kin daina Haihuwa,daga yau Haihuwa ta Kare a gidan Nan sun Isa Haka, Mama tana ta dariyar su Bash.

Bayan Mutuwa ta lafa anyi Sadakar Bakwai Aamna yau kwana bakwai Bata ga Ahmad ba,duk ta Shiga damuwa ta Kira wayarsa Bata shiga,Bata San mutuwa aka musu ba,Shi kuwa Ahmad da dare Bayan sun Gama shaye shayensu da safe 7am ya koma gida, Mummy ya Kira a waya, yace Mummy Ina cikin wani Hali,danki ya fada soyayya jiya jiya na gano cewar Soyayya na fada,Farin ciki ya Kama Mummy Tace wannan wacce me sa’ar ce? Bata kawo Aamna bace tunda yace wata ce tasan da Aamna ce zai ce Aamna ce,ta so ace Aamna ce,Mummy Tace to itama tasan kana sonta ko me? Ahmad yace Mummy kwarjini take min na kasa fada Mata,zuciyata idan na ganta bugawa takeyi,Mummy Tace karka damu Son ka cire tsoro Kai fa Namiji ne ko wace kaje Ni na baka dama ka fada Mata duk irin son da kake mata,Ni Mummy Umarni na baka ka furta Mata karka ji tsoro,ta dinga zuga Ahmad tana dorashi a Kan hanya,suna Gama Wayar yaji wani kwarin gwiwar da Bai taba ji, yace Mummy ce ta bani Umarni,wannan Umarnin Mummy ne naje na fada Mata. Ai zumbur Ahmad ya mike sanye da 3qutr blue da Riga Armless wata white and sky,ba Wani shiri ko wani wanka da canja Kaya na Kamala,lokacin zuciyarsa ta Gama tunzura, Kansa Kuma ba Wani saiti tunda jiya an cake da yawa,7am da sassaffe ya tsaya a Kofar gidan su Aamna ya Shiga dukan gidan Baji ba gani kamar zai balla musu gate,gaba dayansu a tsorace Suka yo waje Baba,Mama , Aamna tare da Siyama sabo da ranar Siyama a gidan su Aamna ta kwana,Baba Ne ya bude kofa,ko kulashi Ahmad Baiyi ba ya fada gidan a fusace da Masifa hankali a tashe Yana Bala’i ya tsaya a Gaban Aamna Dake tsaye sanye da kayan bacci ya nunata da yatsa da karfi a gigice ba nutsuwa Yana haki yace Kin hanani sukuni…tun Sanda na ganki Bayan kin bar gidana kina shago…zu..zuciyata…ta kasa sukuni…Dora Hannu yayi aka ya sake nuna ta da yatsa da sauri da sauri yake magana ba kakkautawa Yana zaga compound din gidan Yana Wallahi na rantse…..ko idona na rufe bana bacci fuskarki nake gani kina min gizo….kullum idan na ganki zuciyata bugawa takeyi…Ina Jin tsoronki……ko yaushe bani da sukuni….burina kullum na ganki….ko naji muryarki…..bana…Bana Iya motsi sai da tunaninki……komai nakeyi kece a Raina….kece…. kike min gizo….sunanki idan aka ambata sai zuciyata ta buga…..Haka nake tsallakowa gidanku cikin dare in labe inyi ta kallonki…..Rannan ma Dan karku kamani nayi muku basaja na sace muku startime da Radio….Baba ya kurma Ihu tare da nuna Ahmad yace Kaine??……Ahmad Bai kulashi ba yaci gaba da bayani….yace kusan kullum da dare sai na shigo gidan Nan na ganki baki sani ba….har dakinki nake buya na Sha kallonki tsirara kin shiga wanka……da Ni kike rufe kofa a room Dinki duk abinda kike Yi Ina kallo….kunya ta lullube Aamna ta sunkuyar da Kai kasa. Ci gaba yayi da bayani yace duk abinda nake Miki Dan kiji Dadi nakeyi…. komai Danke nakeyi….har zuwa shago Dan na ganki naji Dadi ne…..Yan….yanzu ma….zuciyata bugawa takeyi wallahi Ina sonki….sonki nake Yi…da ban Gane sonki nakeyi ba sai yanzu…..Murya ya canja Kamar me kuka ya hada zufa Yana haki yace Yan….yanzu….ma tunda nazo gabanki zuciyata Bugawa takeyi…..idan Baki yarda ba taba kurjina kiji ya cafko Hannun Aamna ya daura a kirjinsa saitin zuciyarsa yace kinji?…kinji?….Aamna Tace ae naji ta zame Hannunta…..Siyama,Mama,da Baba suna ta tabe Masa Baki sabo da basa son abin,shi kuwa Bata su yake ba ci gaba yayi da cewa Wallahi Allah Sonki nakeyi……idan Baki yarda ba Kira number ta kiga sunan Dana saka Miki a Kan number dinki,Aamna ba musu ta latsa Wayarta ta Kira wayarsa sai ga Sunan Daya sa Mata ya Bayyana MY WORLD. Bai tsaya ba yaci gaba da bayani Yana tonawa Kansa asiri Wai duk cikin bayyana soyayyarsa a gareta ne.

KARSHEN FREE PAGEJoin Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

About Mr Hausa Ebooks 1438 Articles
The Power of pen