860 Views

DUNIYA TA AMNA Page 21 – 40 by Asma Baffa

 DUNIYA TA AMNA Page 21 – 40 by Asma Baffa

Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 16 Dec, 2022
Upload Time 10:21 pm
Author
Writer Group Unknown / NIL
Novel Genre

Comment No Comments

DUNIYA TA AMNA Page 21 – 40 by Asma Baffa

Page 21-25

FREE PAGE

DUNIYATA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.

ACCOUNT NUMBER TA
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

‘YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
08033933642

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

BESTYNBEELAT
UMMU LATEEPHA
M BELLO
SA’ADATU TIJJANI
UMMI DEEJAT
NAFEESAT UMAR MUHAMMAD.

Yana Nishi a ransa yace shegiya karfi ne da ita,Aamna kuwa mikewa tayi Tace Bari muje mu gaida Ubangiji wani kuwa sai dai su gaisa da barasa,a fusace ya Mike sai ta zura da gudu tare da fadawa dakinta ta saka key,Yana huci yace Zaki sani wallahi sai dai idan baza ki fito ba Useless kawai,Key din machine dinsa ya dauka tare da ficewa ya bar gidan gaba Daya,Ita kuwa Aamna wanka tayi tare da Gabatar da Sallar Magriba,tana zaune tana Azkhar har lokacin Sallar Isha yayi ta Gabatar sannan ta Mike tare Shiryawa cikin wasu kayan baccinta doguwar Riga ce red me sililin Hannu ta wuce gwiwa sosai ta Mata kyau,Kayanta ta Shiga Shiryawa sai da ta tsara komai fes sannan ta kwanta saman gadonta yunwa kamar zata mutu,Kitchen dole ta fito ta Nema Amma wayam babu ko Lipton a ciki bare wani Abu na dafawa,Kugu ta rike Tace Kan bala’i Bari ya shigo,Zama tayi tana jiransa Aamna Bata San shi sai safiya ko tsakar dare yake shigowa ba,Yana can Yana shaye shayensa. Bangaren Ahmad kuwa tunda ya fita wajen su Mashkoor ya je Suka zauna Yana cewa Mummy Wai kamata Ni za ayiwa auren dole, aure ban sani ba, Mashkoor da maye Yana karkace Baki yace Mum sunyi fuck up fa,Muguntar Daddy ce Kawai cewar Ahmad,Bash yace karka kyaleta kaci uban Yarinyar ai wallahi zata gani ko mu ka Bawa dama sai munyi maganinta,Ahmad yace Guys the things is Mummy tsinuwa tayi min akanta fa,Yar Iska Wai Dazu Dani zata Yi kokawa,Jibson Yana zuka hayaki yace Eyyyeeee…..hey this girl get heart woooo….but show her you are our king,Sweet Boy just Sample the Beb,Ahmad ya kalle su, su Biyar suna ta korawa ya daga zundumemiyar kwalaba ya kurba yace gata da karfi har Elbow fa tayi min a kirji,La’ilaaaaah….cewar Mashkoor Yana dafe Kai yace aci mamanta Guys,Ahmad cike da Takaici yace Hmmmm me….me…me….Mum tayiwa haka,a bani Auren wata Ina Zan Kai wannan nauyin Kai wallahi ma dole ta karba,she must Collect…am….wayarsa ya zaro ya Shiga Kiran Mummy dinsa,Mummy lokacin tuni suna Lagos ma,ta daga Wayar tace Ya akayi Ango,Kamar zaiyi kuka yace Mummy kizo ki dauke wannan Ajiyar Taki Zan fa Iya kashe ta,Zan kashe ta ne Mum,karfa ki sa nayi mummunan laifi tam,Tsaki Mummy tayi tare da kashe wayar Baki daya. Mikewa yayi Zumbur yace akan wannan trash din Mummy ta juya min baya,dole naci uban Yarinyar Nan,Zaga wajen ya Shiga yi,Ya dauki kwalabar Giya ya tarwatsa ta,kujerar da yake zaune ya dauka tare da yin jifa da ita,Su Kuma sauran sunyi tagumi kamar an musu mutuwa Wai Ana Taya Oga bacin Rai ne,Ahmad Bai koma gida ba sai 4pm ya shigo a make ya wuce palonsa tare da fadawa saman kujera ya kwanta Nan take bacci me nauyi ya kwashe shi,Ita kuwa Aamna da Yunwarta ta kwanta Haka da Asuba yunwa ce ta tasheta,Bayan tayi Sallah da Azkhar ta koma baccin Yunwa,sai 11am ta sake farkawa,Gidan ta hau gyarawa sai da ta Gama da room dinta da toilet sannan ta shiga dayan ta gyara,ta Shiga Dakinsa Nan taga Haduwar furniture gadon Kawai abin kallo ne, a Nan ta lalace tana kallo,sai da ta gaji ta gyara Masa ko Ina Neat Yana kyalli da sheki,Har Toilet duk ta Gama sannan ta dawo kasa a Nan ta ganshi Yana ta bacci hankali kwance,kitson calabarsa ta kalla ta leka Fuskarsa tana kallon Halittar Allah Iya Halitta,Tace tab Allah yayi Kira a Nan,waye zaiyi wannan in ba Allah ba,cikin Creazy Jean dinsa fatarsa duk a waje fara Kar da gashi kwantacce luf luf,Aamna Tace Uhmmmm…..sunanka Dan Zarra daga yau,kayi Zarra wallahi kafin a samu me Kama kafarka a kyau sai an tona,Habarta ta tallafe Tace kaga Dan baiwa….Fresh dashi…karya suke wani sweet Boy…ai wannan ya wuce Sweet Boy sai dai Honey Boy,Aamna tana nuna shi da yatsa Tace See Nose Alqur’an,Juyi yayi tare da Sosa Dan wuyansa,Aamna Tace ga Chest lafiyayye,Lips dinsa ta kalla ta Bude Dan bakinta tare da lumshe Ido Tace kiss mukeyi da shi ita kadai ta cuno Baki gaba tana feeling Wai suna kissing,Wani Iri taji a jikinta,Tace Kai da gaske na fara Jin dadin,Tunaninta ta kautar Tace kalli dalla ya wani kwanta da takalmi a kafarsa,a hankali ta tsuguna a kasa tare da zare Masa takalmin kafarsa a hankali ba tare da ya farka ba,Aikinta taci gaba da Yi sai da ko Ina ya dau kyalli da kamshi sannan ta leka waje taga me kula da Compound ya Gama gyara ko Ina na wajen,da Hijab a jikinta ta karasa wajen me Gadi,ya gaisar da ita Tace Musa ya kakeyi da cin Abinci a Nan gidan? Musa yace ai Hajiya duk wata Bayan Oga ya biyani kudin aikina Yana bani kudin Abinci na wata wata safe,Rana Dana dare,ai Hajiya Oga mutum ne me kyauta,Baki ga yanda yake taimakon na kasa ba,abinda nake so shi nake siya naci,ga kyautar kudi akai akai Yana bani,idan zanje ganin Iyali na Sha Tara ta arziki yake min,wayata ma Tekno dubu Arbain da biyar shi ya Siya min sabuwa dal,Aamna Tace yanzu dai kullum siyo abinci kakeyi? Yace me dadi ma kuwa Hajiya,tafiya Aamna tayi yunwa kamar zata kashe ta,Tace Bari ya tashi wallahi dole Nima ya dinga bani kudin Abinci na,Palo ta koma da Idonta Daya a manne ta Iske ya koma Bedroom Yana ta baccinsa,Bai tashi ba sai 2pm lokacin Yayi wanka ya hada Sallar Asuba da Azahar yayi ya shirya cikin jallabiyya ruwan toka,Yana zuba kamshi ya sakko kasa da Niyyar fita,Aamna wacce yunwa ta Gama cinyeta ta Mike da sauri ta kulle Kofar palon tare da sa key ta datse ta jefa key din cikin bra dinta tana kallonsa da masifa Tace wallahi ba inda zaka je sai ka bani kudin Abinci,matarka ce Ni a gidan Mijina nake sabo da Haka hakkinka ne nauyin ka ne ka sauke,Kai ya girgiza yace kina Neman rigima Dani,bana son Wasa da shirme,Ina da aikin Yi bani key Zan wuce Aamna Tace wallahi bazan baka ba sai ka bani kudin Abinci,Kai ya girgiza yace karki Bari kwakwalwata ta dau chaji Zan Miki Illa,Zan Miki Illa ki bude na fita ban son wasa,Aamna Tace wallahi yau baka Isa ba sai ka bani abinci,ka nakasa min Ido sannan zaka kashe Ni da yunwa,yace Mum ce ta kawoki kije wajenta ta Baki ko Ni Nace kizo gidana,bana sonki na tsaneki Akan me Zan Baki kudi na dalla Bude min kofa ya taso da masifa,Aamna ta rike Kugu sanye da Hijab Tace wallahi bazan bude ba,yace look ni bana taba Nonon Mata jikinsu ma bana tabawa ki dakko key ki Bude min kofa kin San Zan iya kwata a cikin Bra din Taki Kawai ban son tabawa ne ya Furta Yana yatsina Fuska,Tace Bazan Bude ba wallahiiii.. ta karasa da kukan wahalar Yunwa. Sauri yake yi zai fita sai ya koma Sama ya fito da kudi dubu Hamsim Bundle na Yan dari biyar biyar yace gashi Zan Baki badan Ina tsoronki ba badan Kuma tausayinki ba Dan Ina so na fita ne Ina da Abinyi,Kudin ta karba Tace da karka bayar Mana Idan ka Isa,kaji dai tsoro na Yaro woooooo……cikin tsawar data razana ta yace Open the door,Ba shiri jiki na rawa ta zaro key ta Bude Masa ya fice a fusace tare da banko Kofar kamar zai ballata.

Ita kuwa murna da farin ciki ya kamata ta dauki dubu biyu ko wanka Bata Yi ba ta gyara Hijab dinta tayi waje,ko me Gadi Bata aika ba ta fice daga gidan,a Unguwar tana tafiya taga wani Resturant da sauri ta Shiga ciki tayi Order taje Away na Jullof rice with salat and chicken,ta siyo lemuka harda su Icecrewm Yogourt ta dawo gida ta baje abinta a Palo taci ta koshi tayi dam sannan taje tayi wanka tasa wani gajeren Wandonsa ta zabo fari ya Mata yawa Amma ta saka Haka,ta dauki t-shirt dinsa baka ta saka sun Mata yawa Amma abinka da me kyau sai tayi kyau,Haka ta gyara palon ta Karo karfin Ac tare da kunna kallo tana kallo ta wani can saman Hannun kujera baza ma ta zauna a kujerar ba ta tale kafafu tana Shan Iceream dinta tana ta Dariya a Haka ya shigo gidan ya sameta,Kallo ya bita da shi ganin kayansa a jikinta tana Shan Icecream,Wayar charger ya fisgo da sauri yace kayana are you Mad,Da gudu tayi cikin wani daki ya bita da kyar ta samu ta buya a toilet,yace Zaki fito ne,idan kin Isa kina ji ke kece ki fito,Tace kaima idan ka Isa ka shugo,baka kunya fada da mace,Namiji da Kai kaje kayi da maza Mana idan ka Isa a tumurmusa ka,Yace Zaki fito ne sai na Ballaki Kuma wannan kayan da kika sa wallahi sai dai a kone su ban Haka skin da ke Idiot ya juya tare da komawa palo.

Tunda Aamna tasan tayi laifi Bata sake Fitowa ya ganta ba sai washe gari ta fito sanye cikin wani Lace fari Riga da skert daf da ita tayi kyau sosai Sanda ta shigayi tana tafiya a hankali,a main Palo ta Iske shi yayi Order Breakfast ya hada tea lafiyayyen gaske ga chips and Egg da farfensun kaji Yana ci hankali kwance,Aamna ta hadiyi Yawu ta fito a hankali yaji motsinta Amma ko kallonta baiyi ba yaci gaba da cin abinsa,a gabansa ta durkusa Tace Ina kwana Yaya Ahmad,sai lokacin ya kalle ta kadan Yaja uban Tsaki,tace Nima yunwa nake ji,wata Uwar Harara ya aika mata,Dan Allah San min ko na fita na siyo? Dama jiya na fita na siyo Abinci na manta ban nemi Izninka ba ka yafe min,Cikin tsawa yace Ina ruwana da rayuwarki Ni da Zaki tafi ma bangon duniya Ina ruwana,wallahi bazan je bangon duniya ba salon idan tashin kiyama yazo yajuju da majuju su fara ta kaina,Kinga ki daina Shiga harka ta,na fada Miki kiyi rayuwarki Mummy ce ta kawo ki to duk wahalarki sai ki fada Mata,Yar wahala Kawai,Yar walagigi Kawai,Ai kuwa Ni gaskiya Raina ya biya da wannan Abincin naka ka fada min Inda ka siyo naje na siyo ai Ina da kudi sannan ko ka bani naka na ci,Tana Gama fadin haka ta janyo plate din chips din gabanta ta fara ci Tace Dadi,sai ta dauke plate din ta gudu daki ta sa key,Ahmad ya dura wata Ashirya yace yau ba abinda zai Hana ban karyaki a gidan nan,Sa’anki ne ni? Aamna Tace ae daga bedroom,Sai da ta cinye tas ta fito lokacin ya bar gidan ma,ta kalli kwanikan Daya Bata duk abincin ya rage Bai cinye ba duka,ta zauna gaba Daya ta cinye sannan ta hau gyara gidan tana mita mutum sai yawon jaraba kullum Yana waje. Duk wani Aikinta sai da ta Gama sannan ta zaro Yar Wayarta Vivo ta Kira Mama suka gaisa da Baba,ta Kira Zuhra ma Suka Sha Hira,Siyama ta Kira karshe,Siyama Tace Amarya bakya laifi kin tafi kin barmu da Aiki a Resturant,Yaya Mutumin naki ko anyi abin ne? Aamna Tace Allah ya kiyaye na hada jiki da Dan giya,ke Siyama wallahi baya kaunar Mace,wannan ko tsirara Zaki zo gabansa baza ki birge shi ba,Dariya Siyama tayi,wallahi Aamna ga masifa kullum Fuskarsa ba Rahma Abu kadan Kuma sai masifa,wannan bazai shiryu ba,banga abinda za a Masa ya shiryu ba,to Ina ma yake Zama da har zai fahimci wani Abu mutumin da sai ya kwana a waje can ko sai cikin tsakiyar dare zai dawo,ga Dan Ido na Guda Daya a manne,Suna ta surutu har suka Gama ta fara karatun Qur’ani,Jin yanda aka banko kofa tasan Ahmad ne ko Sallama dama bayayi Yana shigowa yace ke koma dakinki kiyi karatunki ko ki koma masallaci ki tare,Ganin yanda ya shigo a buge sai ta tashi tsam tayi bedroom shi Kuma ya kwanta a saman kujera,Ya kunna tv ya kure volume karshe kida ya cika gidan a manyan speakers Yana sani yayi Kuma dole Aamna ta hakura da karatun Qur’anin sabo da yanda kida yake dauke Mata hankali,Fitowa ta sake yi,ai kuwa ya Mike a fusace yace ba nace ki daina matsowa inda nake ba ya dauki Remote ya jefe ta da shi da karfi ji kake kwas a goshinta,sosai taji zafi wajen ya kumbura yayi Mata kulu,Itama ta dauka ta jefa masa a bayansa,ta gudu ya bita cikin zafin nama Amma ta kulle Kofa Haka ya rabu da ita yace Zaki fito ne.

Sai bayan Sallar Isha Aamna ta fito sanye cikin doguwar Riga Yar kasar masar,me shape sosai wata silver,ba karya tayi kyau,Mayafinta tayi Rolling ta dauki kudi ta fito,yau ma tayi sa’a sai ta ganshi a kwance Yana cin green Apple,Aamna cike da tsoro ta karaso inda yake wani kamshi yake na musamman,a gabansa ta tsuguna Tace Sannu da hutawa zanje siyo Abinci,Baki ya tabe sai da ya dauki mintuna yace Ina ruwana,mikewa tayi ganin masifa yake ji kadan yake jira sai tayi tafiyarta kuwa,taje tayi take Away sharp sharp ta dawo,Lokacin Yana Zaune Yana kallon wani American film, Sakwara da miyar kifi, ruwa Eva da fruits salat,tana ci tana kallon Film, .

Wayarta ce ta hau Ringing tana dubawa taga Mama,da sauri ta daga,bayan sun gaisa Mama Tace Aamna ga fa kudin sadakinki Baki karba ba,Aamna Tace Ina sane da abina,suna Rai na,a ciki ki dauki dubu Goma kyauta,ki Bawa Baba dubu Talatin,Zuhra a Bata dubu bakwai,Siyama kawata a Bata dubu Uku Kinga dubu Hamsin ta Kare ko? Mama Tace Haka ne,to dubu Hamsin din a ciri dubu biyar a bayar Sadaka Allah ya Kai ladan kabarin mamata sumayya Allah ya Mata Rahma,a sake cire dubu biyar Abba na Daya gudu ya barni ayi Sadaka nayi tawasili da ita Allah ya shirye shi ya canja Hali,Mama tayi Dariya Tace ai duk kin rabar da kudin ba Haka akeyi ba,Zan dai cire na Bawa kowa abinda ya Dace sauran ai naki ne,Aamna Tace to koma dai mene abinda aka barmin a kaiwa Kawu Isma’il can kauye ya Siya wake da Alkama a ajiye idan sukayi tsada sai na siyar na samu riba,Nan fa Ahmad yace tab Riba kudin riba ai masifa ne, ka siyi Abu ka boye sai yayi tsada kazo ka siyarwa mutane,Wannan ba Business bane,Aamna Tace Kai baka ga laifinka ba barasa kwalaba Nawa kake dirkewa cikinka wlh kayi hankali Kar Hantarka ta tabu tam,Hannu yasa ya murde Mata kunne ta kwalla Kara,Mama ta waya taji Kara Tace lfy? Mama wani kwaro ne ya firgita Ni.

Can Baba ya fisge Wayar yace ke Aamna Dan Ubanki kiwa fa mijinki biyayya,duk abinda yace kiyi bana son sakarci,Kuma ko me Zaki shuka ki shuka gaskiya kiyi gaskiya ato sabo da mu dangwali arziki da kyau,Aamna Tace yo Baba ai Gaskiya Ni a jinjina take da ita aka haife ni,dankwalin Aamna ne ya zame layar ta Guda biyu Dake soke a kanta suka bayyana,Ahmad Yana gani ya girgiza Kai a zuciyarsa yace mashirkiya,Ita dai Aamna abincinta take ci tana Dan juyowa ta kalle shi kadan sabo da faratansa na Hannu Dana kafa Daya Tara sunyi tsayi Kamar Arne Amma da gani suna Shan gyara wani fes da su sai dai ba a Yankewa,Allah yasa kayi bacci sai na yanke wannan uban faratan Aamna ta furta a ranta. Ganin tana ta Kallonsa Yaja Tsaki tare da mikewa ya dauki key din machine dinsa zai fita,Aamna Tace Ina zaka je da daren Nan Haka?Ni tsoro nake ji gaskiya,Kwafa Yaja a ransa ya furta Mummy ta Gama Dani,idan na Mata Illa tsinuwa ta hau kaina,juyowa yayi a fusace yace Allah ya taimakeki Ina son Nonon Mummy Dana yasha yabi lafiyar jikina Amma da kin Gane kurenki,Aamna ta kyalkyale da Dariya Tace au har yanzu Nonon Mummy Bai Gama bi maka jiki ba? Sanda aka haife Ni ko yaye Ni ba ayi ba aka samu cikin Saddeeq shi yasa ya cuce Ni na Sha gubar cikinsa,Aamna sake kecewa da dariya Tace ko shi yasa aka ce ka Dade a tsumbure baka girma ba Dan Mummy Tace har cutar koshokwo kayi Haka Kawai Aamna tayi karya Tace Mummy ce ta fada Mata,ai kuwa shi da saurin Fushi kwaya tana sashi saurin Fushi ai Kan Aamna ta rufe baki yace uwar Koshokwo nayi,Aamna ta Mike zata gudu Suka dinga zaga palon Nan sai ya kamata ya dake ta Itama ta guduwa,ta samu tayi waje Compound da gudu,fita yayi Yana huci ya hau lifan dinsa ya fice sannan Aamna ta dawo ciki abinta. Bayan Sati biyu da Auren Aamna kullum fada sukeyi da Ahmad ba Wani mutunci, Mummy ce ta Kira Aamna Tace,bayan sun gaisa Aamna ta saki kuka Tace Mummy wallahi kullum sai munyi fada ya Duke Ni saurin duka ne da shi Kuma yaki siyo kayan abinci kullum sai dai naje na siyo ko na aiki me Gadi shima Haka Mummy, Dariya Mummy tayi Tace Kuma wallahi Ahmad ya Iya girki sosai a haka,kin San nice na sallami Peter me dafa Masa abinci, Aamna ki Kara Hakuri,bazan turo Miki kudin Abinci ba Yana da kudi,kece Zaki San yanda zakiyi Masa dole ya Baki kudi ki zuba abinci a store kin Gane,ae naji to ta furtawa Mummy,Bayan sun Gama Wayar Aamna ta zauna tayi tagumi tana saka Taya zata sa ya siyo Mata kayan abinci ko ya bada kudin ta siyo tunda kudin hannunta sun kusa karewa. Bayan tayi Shirin bacci cikin wata Riga da wando farare masu laushi ta zuba kyau ciki,a Palo ta zauna tana jiransa ai kuwa taci sa’a yau Ana Sallar Isha ya shigo gidan Yana tafiya da kyar da yanda yake Gadara ya nuna yau baiyi shaye shaye da yawa ba,Sannu da zuwa Aamna ta Furta,ko kulata baiyi ba Direct sama ya haura ya fada toilet,wanka yayi ya fito tare da Gabatar da Sallar Isha ko Addua baiyi ba ya Mike ya saka wasu kayan bacci dark blue me digon fari Riga da wando,fresh milk ya sha sannan ya kwanta a Gadonsa Nan take bacci ya kwashe shi me nauyi,Aamna ta biyo shi dakinsa Wanda Bata shiga sai idan zata gyara,a hankali tayi knocking Shuru taji,tayi Sallama Shuru,sai ta bude Kofar a hankali saman bed ta hangoshi ya wani Yi dai dai Yana baccinsa,Aamna tayi murmushi Tace Allah sarki yayi bacci,a gefen bed din ta zauna a hankali gefen kafafunsa,Nan take ta tuna da taga faratansa ya Tara sun Sha gyara,Room dinta ta koma ta dauko razor blade sabuwa dal ta bare,a tsorace tayi shahada ta Dan rike Yatsansa kadan sannan ta fara yanke Masa farcensa daya Tara Yana gayu da abinsa,ta fara yanke su Daya bayan daya,gashi da nauyin bacci har ta Gama hannaye Bai ko motsa ba Kawai baccinsa yake Sha,ta dawo kafa ma ta yanke Masa tas ta gyara ta kwashe farcen data yanke ta zuba a trash da razo din duka,ganin Bai da Niyyar tashi ta hakura itama ta koma dakinta Bayan ta kashe Masa hasken wuta ta Dan rufa Masa blanket sabo da taji sanyin ac yayi yawa. Itama komawa tayi dakinta ta kwanta abinta,sai 2am Wayarta ta tashe ta sakamakon saita Alarm da tayi, Mikewa tayi tare da Gabatar da Sallah Nafeela raka’a hudu tayi Adduointa sannan ta koma ta kwanta,sai Asuba ta sake tashi tayi raka’atanil fijr tare da Sallar Asuba ta zauna ta Gabatar da Azkhar sannan ta koma bacci,10am ta tashi ta hau gyaran gidan,Compound kuwa me Gadi ya Gama gyara ko Ina har Garden,Dakinsa ta shiga karshe taji karar ruwa alamar ya tashi Yana toilet,bedroom din ta hau gyarawa komai ya koma neat dama shi Sam Bai da kazanta akwai tsafta,ko Ina kamshi ne ke tashi,toilet ya Bude ya fito daure da towel a Kugunsa karami Kuma a hannunsa Yana goge wuyansa ga kitson kalabarsa Nan sabo an canja Masa sabo sai wani sheki yake Yi Bai jika gashinsa ba sabo da Attachment aka saka yellow, red and green,Aamna jikinsa ta kalla lukwi lukwi sumulmul,Fuskarsa a daure ko kulata baiyi ba ya tsaya a jikin Mirror Yana karewa Kansa kallo,Muryarsa taji yace Sexy Guy,gemunsa da Sajensa ya shafa yace Fresh Guy,Aamna ta zaro Ido taga Yana ta yabon Kansa Yana kallon Kansa a mudubi Yana shafa kitson kalabarsa,Toilet din ta shige ta gyara masa a ranta tana jinjinawa tunda take gyara Masa gida Bai taba nuna yaji Dadi ba ko abin ya birge shi ba,harkarsa Kawai yake Yi,Tana wanke toilet taji Muryarsa Yana Kiranta Bush girl…..Bush girl….tsoro taji Kar Taki zuwa ya Mata duka a banza Fitowa tayi da sauri Tace gani,Wani murmushi ya saki me tsada yace Good girl Ashe kin Gane sunanki,da Hargowa yace Ina wani perfume a Nan sabo? Murmushi Aamna tayi tace ai na dauke shi Ni zanyi amfani da shi sabo da Naga na Mata ne Kai Kuma Namiji ne,wani Ashar ya dura yace kin San tsadarsa kuwa? Yo ba gidan mijina bane,Kuma ma kayan Mijina ai Nawa ne ta karasa da shagwaba,Tsaki Yaja yace why are you always looking for my trouble? Idan na balla ki hmmm common dakko min kafin Raina ya baci,Aamna Tace Idan kana son na baka ka bani kudin Abinci ko ka siyo kayan abinci a gidan Nan yanda Zan na girki da kaina. Wani Takaici ya kamashi ji yake kamar ya harbeta yace bana Baki kudin abincin ba uban me Zan Miki,Aamna Tace Ni ka bani Dan Allah yau naje kasuwa na shirya store da kitchen dina,kana min fuck up fa a gidana,kanta yayo Aamna ta fisge towel dinsa ya Fadi kasa ya dawo zigidir, da sauri ya dauki towel din ya daura kunya ta balain kamashi,Abu na farko a rayuwarsa da yake Jin kunya Bai so aga tsaraicinsa Amma wannan Yarinyar ta cuce shi,Aamna takawa tayi zata gudu ya cafko ta ya dakko belt din Wandonsa tana Ihu ya riketa Kam ya dinga tafkarta iya karfinsa,tana ta Ihu tana cewa banga komai naka ba,kayi Hakuri,bazan fadawa kowa,bazan cewa kowa ga Kalar abinka ba,ganin zai Mata Illa a banza Tace Tsinuwar Mummy a kanka,Yana huci Idonsa yayi jajir ya tsaya cak Yana haki,Ita kuwa Aamna da Dan Idonta Daya a manne ta Mike tana kuka Wiwi,ta koma toilet din ta karasa wanke Masa tana kuka ta fito zata fita kenan ya shirya cikin wasu kana Nan Kaya farare tas marasa nauyi wandon pencil irin na shakatawa a gida da Alama ba fita zaiyi ba yau,rafar kudi Yan dubu dubu ya jefo Mata yace gashi Nan ki Siyo Uwar kayan girki,last warning ba ruwana da ke,karki sake Shiga harkata,ke magana ma ban so ki min,Aamna Tace ai wallahi baka Isa ba Mijina Guda ai dole na maka magana,Kwafa Yaja yace to kuwa Zaki ci Ubanki wallahi. Key din machine taga ya dauka Ashe fita zaiyi Ba zato Aamna ta sa key din kofarsa ta kulle ta cire key din ta jefa a bra dinta Tace Yau ma baza ka fita Muna dakin Nan zamu yini sai dai yunwa ta kashe mu,lips dinsa ya tamke tare da rufe Idonsa kam tsabar bacin Rai,yace ban so Tsinuwar Iyaye ta shafe Ni,sannan gwara nayi komai Akan na taba Nonon mace Bude min kofa ko yanzu na karasa Miki idon Daya,Aamna ta tsaya sanye da Atamfa Riga da skert na lefe ne sun kamata sosai,Tace tunda aka auro Ni baka taba ko Dan Rungume Ni ba,Please yau kafin ka fita Ina bukatar warm Hug,just ordinary Hug,Nima yau Ina so na motsa jam’iyata,kina hauka ne? Meke damunki,Ni zanyi Hugging naki? wata Dariya yayi yace Ashe nine ma na ganki nace Ina so,kanki akwai motsi lallai,Aamna Tace to lallai zamu kwana a Nan,tsayawa Suka Yi a Gaban kofa har na tsawon minti biyar ba Wanda yayi magana,nisawa yayi tare da girgiza gashinsa yace open the door,Aamna tace Baby Hug me Mana ka fita abinka,tunani ya tafi idan ya duketa Mummy dinsa,idan yace zai kwace key sai dai ya zura hannunsa a Boobs dinta shi gaskiya Bai son taba Nonon Mata,Baya Yaja kadan yayi Dan tangadi sannan yace Okay ya runtse Idonsa sannan ya Bude hannayensa,Aamna tana murmushi taje ai kuwa ya cakumeta irin bai iya ba Kawai cakumarta yayi ita Kuma tana sani ta kankameshi ya fisge jikinsa da bala’i yace bazan tabaki ba din,kinyi kinji Dadi Bude min kofa,Tace yanzu kuwa ta dakko key ta Bude Masa ya fice a fusace,ya hau machine dinsa kenan sai ga Aamna ta fito da gudu tana wait wait…da masifa ya juyo sai yaga Ashe wayarsa ce ya manta,Tace ka manta wayarka Baby,fisge Wayar yayi tare da Mata wani kallon banza ya Bawa machine dinsa wuta ya fita,Aamna kuwa wanka tayi ta shirya tsaf ta Kira Siyama kawarta suka je kasuwa,duk kayan Abinci na more rayuwa sun siyo dai dai gwargwado,tare suka dawo a taxi Suka shirya kayan a Store tsaf,kitchen kuwa komai na amfani akwai dama,sabo da Haka Jullof rice sukayi da wake taji kayan lambu da nama,Zuhra ce itama tazo ganin Amarya suka zauna suka ci abinda suke so,sannan suka gyara wajen,Palo Suka dawo suna kallo,Zuhra Tace Kan bala’i gaskiya gidan Nan ya hadu ba karya,Siyama ta Mike a saman doguwar kujera Tace har wani bacci nake ji ga ac ta ko Ina,Suna kallon wani Indian Series suna Hira sai ji sukayi an banko kofa,Siyama da Zuhra sai da suka firgita,ita kuwa Aamna ta Saba ko a jikinta tasan shine,ya shigo dauke da Ledar take away a hannunsa,Yana ganin Baki ya sake daure Fuska Kuma ko Sallama baiyi ba Sannan kallo Basu ishe shi ba bare su sa ran zai musu magana,ba Wanda yayi magana yazo har inda Siyama ke kwance a doguwar kujera yace cikin tsawa keee….tashi Zan kwanta a Kan kujerata,ai da sauri ta hantsilo kasa ya haye tare da kwanciya ya wani Mike Yana wata Mika,su Zuhra sai kallon kallo,Suka Yi tsit a palon sannan Suka ce Ina Yini? Banza Iska yayi da su,da Tsawa yace bani remote ya dakawa Zuhra tsawa,ta Mika Masa abinsa Wai Gadara yake gidansa ne. remote ya dauka da Gadara ya canja Chanel suna kallo ya Shiga wata Chanel ta Yan Iska Wanda a tashar Watarana har Xxx suke saka wa,sannan sai tallan Magungunan maza Dana Mata na Kara karfin gaba,da tallan kayan sex,Shi Kansa Bai taba kallon Chanel din ba sabo da su Zuhra ya kunna,ai kuwa sai Suka ga Ana Nuno maza da Mata tsirara,sai aka koma tallan condom na maza,Yana kalla yayi wani murmushi yace mun gode Allah ya Kara basira turawa,ya kamata fa ku yo Mana wanda yafi Haka kauri wannan fashewa yakeyi Bama Jin dadin shiga da fita,Mata aka nuna daga pant sai Bra,Ahmad yace wow see Bebs wannan zata Yi min,Wata kanjamammiya aka nuna,yace ke dalla matsa Jibson ke son irinku, kunya ta lullube su Zuhra Suka Mike tsam tare da yiwa Aamna sallama,Tace tun yanzu zaku tafi Haba Dan Allah? Ai ko kulata basuyi ba suka hada karansu sukayi waje,tuni suka bar gidan. Yana ganin Haka yayi Dariya ya canja Chanel ya koma kallon kwallon kafa,Aamna ce ta dawo daga rakiyar su Zuhra,da kukan shagwaba ta shigo tana dire diren kafafu tana Haba Dan Allah….Haba…Dan… Allah Baby, wani Haushi ta bashi Takaici yasa Ahmad ya zaro Wayar charger ya kifa Aamna da ita ta gudu dakinta ta kulle Kofar ya dawo Palo Yana masifa Ni Zaki yiwa shagwaba,Baki San na tsani wannan haukan ba,aikin banza Kawai,wani Ihu ya saki Yana kallon yatsunsa na kafa Dana hannu,Jin Ihu sa yasa Aamna ta yo waje ba shiri tana cewa lafiya? a tsorace yake lokacin shi yasa yace fingers Dina,farce na Dana Tara Ina ji da su an yanke min,jikinsa ya kalla tsaf yace Aljani ne,Amma wannan ya cuce ni,Dariya Aamna ta dinga Yi Tace nice ta fece da gudu daki. Rasa abinda zai Mata yayi sabo da bacin Rai wuka ya dakko a kitchen ya ajiye a kusa da shi yace yau Zaki ga abinda Zan Miki ba ruwana da wata Tsinuwar Mummy.

AsmaBaffa
10/26/21, 8:52 AM – A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA🌵🌵

DUNIYA TA AMNA complete hausa novel by Asma Baffa

Page 26-30

FREE PAGE

DUNIYATA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

    NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.

ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

‘YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

AGRA
ANEESAH
UMMIN HIBBAH
ASMAU YUSUF
RAHMA
FARHAT MRS MJ
PHAATIMAH

Ranar Aamna Bata sake Fitowa ya ganta ba kullum sai ta tabbatar ya fita take Fitowa tayi abinda ya kamata har kwana Uku sannan yau Bayan tayi Sallar Isha taci abincin data dafa Tace Fitowa zata Yi ai ta San yanzu ya huce,a hankali ta fito sanye cikin wani Bum short sky da Riga t-shirt red ta zuba kyau ciki,tana Fitowa taga shima ya banko glass door din palon ma’ana yanzu ya shigo kenan,Yana ta uban tangadi ya fada saman kujera shirim Yana magana a hankali cikin maye shi kadai,Aamna ta kalleshi taga bacci zaiyi ta lallabo a hankali Tace ka koma bedroom ka kwanta,ya furta barrrr…….niiiii….aaaaa…..aaaa….Nan…..Aamna Tace no Nan bazai maka dadin bacci ba tashi ta Kama hannunsa kenan ya fisge hannunsa,sake rikewa tayi Tace taso ta janyo shi ya Mike da kyar Yana tangal tangal a Haka ta kaishi sama ya fada saman bed dinsa,tsugunawa tayi ta zare Masa takalmansa a hankali,ganin har ya fara bacci ta Karo Masa karfin Ac din ta kashe Masa light ta fita ta barshi tana tunani,Palo ta dawo ta zuba Uban tagumi tana mamakin Ahmad kullum cikin shaye shaye baya Free Sam,Tace wannan wacce kaddara ce Haka ta sameni,da wacce zuciyar Zan iya daukan wannan masifa,gashi na Bari an daura Aure ya zanyi,Sam bana birge shi duk shigar da nayi Bai taba kallona ya nuna na tafi da shi ba duk da Nima ba so nake ya Yana ba.

Taya zai shiryu Haka,Ido ta lumshe ta kwanta a saman kujera tana ta sake sake a ranta.

Dakinta ta Mike zata tafi Bayan ta Gama kashe kayan wuta ta sake leka shi ta gani ta hango shi kuwa Yana ta bacci Amma ya dunkule waje Daya Yana ta Rawar sanyi kamar zazzabi ne a jikinsa,dama taji jikinsa ya dauki zafi dazu,kamar ta wuce sai ta fasa ta shiga bedroom din,a gefen bed din ta zauna tana tunanin me zata Masa,Tsaki ta ja kadan ta shiga zare Masa Riga a hankali,jikinsa ta taba zafi zauuuuu,Toilet ta shiga ta ebo ruwa a Bowl da towel karami ta shiga goge masa jikinsa a hankali,kirar jikinsa ta shiga karewa kallo tana Dan goge Masa jikinsa da Towel,ita mamakinta Sam a face baiyi Kama da me Shan giya ko wani Drugs ba,idan baka sani ba baza ka taba ganewa ba,sai dai acting dinsa yanda yake abu ba tarbiyya kana gani,Ac din ta kashe gaba Daya sannan taji zafin jikinsa ya Dan ragu,a hankali take girgiza shi tana tashinsa Me Burkutu….me Burkutuuu…….Shuru,taceme giyaaaaa…..Shuru,ta girgiza shi shuru, Kuma Yana numfashi sai da ta Dade sannan taga ya dafe Kansa da Alama ciwo yake Masa Yana Nishi kadan yace Ohhh my God,a hankali ya Dan Bude idonsa,ba a wani hayyacinsa yake ba,ya fara Mika Hannu jikin Drower yace i need to take my drugs,Drower din ta Bude da sauri mamaki ya kashe ta ganin kwayoyi iri iri Kamar hauka duk na Maye,Salati Aamna ta saki Hawaye ya shararo Mata ta shanye da kyar,ta Dan duba Drugs din sai taga paracetamol,shi ta ballo ta dakko Masa ruwa da sauri ta Mika Masa Yana daga kwance ya karba ya Sha abinsa a kwance shi ba Wani ganeta yake Yi ba. Zama ta ci gaba da Yi gefen Bed din tana ta faman gyangyadi,so take Yi ta ga ya samu sauki,a ranta Tace ko Ina ruwana oho,Amma tunda dai lalura ce Bari na jira,tana Nan zaune taga ya fara Juyi ya hada uban zufa alamar zazzabin ya sauka,ac ta kunna Masa,cikin mayen baccinsa yace Mummy yunwa Zan Sha ruwa,Aamna ta kalle shi taga bacci ma yake Yi,da sauri tayi kasa ta hau dafa Indomie lokacin 11:30pm, sharp sharp ta Gama ta dakko da kankana wacce ta yanka Nan take,da sauri tayi sama,ta ganshi zaune a gadon ya jingina bayansa a fuskar bed din ya lumshe Ido,still ba Riga a jikinsa. Aamna ita ke shirmenta ba ganeta yakeyi ba ya bugu da yawa dishi dishi yake hango ta shi yasa ya kyaleta da lafiya yake da tuni taci duka,sabo da samun waje saman bed din ta haura ta zauna a gefensa Tace ga abincin,you have to eat something sabo da kafi Jin sauki,a hankali ya juyo ya kalleta ya turo lips dinsa gaba,Tace haba na Mummy ci Mana karka kwana da yunwa akwai Dadi wannan Indomie taji Hadi kaci sai kayi Santi,Kansa ya dauke can gefe,Aamna Bata hakura ba harda rera waka Wai Dan tuzuru….ya dawo mata,…..yanzu….da ba’ayi maka aure….. ba wa zai dafa maka….Oya Fadi kaima tana tafi,Dake a bige yake sai yace shima Nine Tuzuruuu……yawwa to Bude bakin ta furta tare da ebo Indomie a fork,…..ya Bude da kyar Yana kumbura,ta zuba Masa tana murmushi Tace Ehemm….mutumin kirki…maza Kara ci ta sake ebowa ya karba a bakinsa,Tace Good King…oya again….ya karba,yaji tayi Dadi sosai tana ta bashi Yana ci Yana ganinta dishi dishi. sai da ya cinye tas ta dakko kankana Itama Haka ta dinga bashi baya ko magana sai da ya Sha da yawa sannan yayi gefe can da Kansa Nan ta Gane ya koshi,ta Balle ruwa ta tsiyaya a glass cup ta bashi Nan ma a Baki ya shanye ta Kara Masa ya shanye,Tace Inye King din ba,Harara ya Aiko Mata tayi shuru,ta tattara kwanikan ta maida kitchen,shi kuwa Yana Jin karfi a jikinsa wanka yayi sai lokacin Yayi Sallar la’asar ,Magriba da Isha sannan ya kwanta bacci ya sake gaba da shi. Aamna shugowa tayi taga yayi bacci ga sallaya alamar Sallah yayi,baya kashe light sai ta kashe Masa tare da sake feshe room din da wani Room freshner me Arnen kamshi ta rufe Masa kofa taje itama ta kwanta. Washe gari da Ihu ya farka Daya tuna kamar jiya Aamna ce ta shigo,Nan ya tunano me tayi,wani ransa ne ya baci shi kadai ya dinga masifa har yayi wanka ya fito cikin wani gajeren wando ruwan toka da Riga brown t-shirt,Lokacin Aamna ta cakare cikin wani wando legins tight,pencil tayi kyau duk na lefe ne, Yar rigarta yellow me siririn Hannu cibiyarta a waje,a kitchen take tana shirya Breakfast kamshi ya cika gidan,ji tayi kamar ya fito da sauri ta fito ta sawa Kofar palon key Yana kallonta yasan cewa zata Yi bazai fita ba sai ya Bata kudi ko wani Abu,dama da fushinta ya tashi yau,yace tun kafin na Miki duka ki Bude kofa ko ki Fadi abinda kike so na Baki,bani da lokacin shirmenki yau,Aamna Tace Breakfast zaka ci sannan ka fita,kullum Ina matarka baza kaci Abinci na ba yau ba inda zaka fita a gidan Nan,sabo da ma baka da lafiya baka Gama murmurewa ba,Ahmad yace shine jiya kika shiga Zaki min fyade? to ta Allah ba Taki ba,nafi karfinki,Wai harda wani cire min Riga ke Uwata ce ko ubana,ke Wai matata ko?Dariya ya bawa Aamna Tace ae naji zauna ka jira Ni,idan naki fa?,kitchen ta shiga da sauri ta Hado komai a tire ta kawo gabansa a Palo ta Ajiye Tace Bismillah kayi ka ci na Bude maka ka tafi,sai da ya dauki lokaci sannan yace badan Ina tsoronki Zan ci ba,Dan Ina da abin Yi ne kawai yau,Aamna Tace a Haka zaka fita da gajeren wando? Ina ruwanki munafuka Uwar gulma ya Furta,Shuru tayi Tace Enjoy your meal,Bread ya dauka ya gutsira ya kurbi tea sau daya,sai ya dauki chips Guda hudu yaci yace to Bude min na fita,ba musu ta Bude masa,zai fita ya zuba Mata Rankwashi me zafi ya fita abinsa,Ihu ta saki kadan ta zauna ta cinye abincin nasa,shi Kam Machine dinsa ya hau ya fita da shegen kitson calabarsa,Wanda sai dai ayi ta binsa da kallo. Tunda ya fita Bai dawo ba sai cikin tsakiyar dare,yau anci sa’a Bai Sha komai ba,hannunsa dauke da Ledar take away na abinci,a gajiye ya shigo Amma yaga Aamna zaune tana kallon American film,Sannu da zuwa ta furta,Baki ya tabe ya haura sama abinsa ko kallo Bata Kai matsayinsa ba. Bayansa ta bi a hankali Yana jinta Bai kulata ba,Yana Shiga bedroom dinsa Wanda ya Sha gyara kamshi ne Kawai ke tashi,kafin ta Shiga ya kulle kofarsa tare da murda key Yana faman Jan Tsaki,Dariya Aamna tayi tana daga jikin Kofar Tace ya jikin naka? Kai ya girgiza yace Uwaki yake ciki,,ta rasu fa marainiya ce Ni,Yace to tayi ta mutuwa Mana Ina ruwana,Wai ke Baki da zuciya ne? Aamna Tace ae bani da ita My Husband,tana Jin tsakinsa ta juya ta koma dakinta ta kwanta abinta tare da Adduar bacci ta kwanta.

Shi kuwa Abincinsa ya zauna yaci ya shiga toilet yayi wanka tare da brush,cikin kayan baccinsa dogon wando da Riga me dogon Hannu silver color wani yadi Silk sharara,Sallaya ya shimfida ya fara jero sallah ba nutsuwa ba komai da saurin masifa kamar zai tashi sama,idan yayi ruku’u ko Gama dagowa baya Yi zai sabe da sujjada, kafin kace me tuni ya idar tun daga Azahar har Isha,ko Addua babu Ya Mike Yana tunanin ma kamar Sallar Isha raka’a Uku yayi Amma ya fuske tare da furta Ina laifi ma na karasa raka’a dayar a raina Kawai ta cika hudu nayi ya fada saman bed yayi kwanciyar ruf da ciki sai bacci.

Washe gari 9am ya tashi kasancewar baiyi shaye shaye ba,Room din dake cike da kayan Exercise ya shiga Yana ta motsa jikinsa sai da ya Dade sannan ya fito sanye cikin kayan gym dinsa bakake yayi kyau,Yana Fitowa ya Iske Aamna har ta Gama gyara ko Ina na ciki,kamshi yaji a kitchen lekawa yayi ya hangota tana ta soye soye, Shiga yayi fuskar Nan ba Rahma cikin Muryarsa ta Yan kwaya yace bani kasko zanyi girki,Aamna Tace ga wasu Nan ka dauka Mana Kuma ma ai gashi Ina girkin da Kai sai muci wannan,cike da bala’i yace da wannan nake so nayi,gidanki ne ko Ubanki ya Siya min kayan kitchen ne? ai kayan Mijina Kaya nane Kuma wallahi bazan baka ba,baka Isa ba kayi kadan kayi karami da yawa na baka kaskon nan, sabo da Nan gidan Mijina nane Kuma gida na yawwa eheee ….Mari ya dauke ta dashi garin Jin zafin Mari Aamna ta saki ludayi ya Fado saman kafarta gashi yasha Mai na suya me zafi Nan take ya kone Mata wani Dan bangare a kafarta,Ihu ta saki ta durkusa kasa Amma duk da Haka Bai kyaleta ba ya tallafe Mata keya ya dauke kaskon da man Baki Daya da dankalin ciki ya watsa a cikin Sink,har kankon ya Bari cikin Sink,sabon kasko ya dakko ya fara Girkinsa,Aamna ta Mike cikin bacin Rai da Hawaye a fuskarta ta tattaro karfinta ta durma Masa duka a gadon baya ta arce da gudu,shi ko jin zafin dukan ma baiyi ba,ita Tunaninta ta Rama,Zuma ta dakko tare da shafawa a kafarta iya inda ya kone,Palo ya dawo da kwansa soyayye da tea da wani snacks Kamar bread,Aamna Fitowa tayi dama tasan shi Bai zuwa Dining Sam,Yana Palo zaune saman kujera ya wani kishingida a Haka yake cin abinci,Aamna a ranta Tace duk abinda ya shafi Sunnah da dabi’a ta Musulmai baya Yi Sam,abinci a kwance za a ci,a kasan center carpet ta zauna tare da nannade kafafu kamar wacce zatayi karatun Qur’ani ta zuba Masa Ido,Hannu ta zura da sauri ta zari soyayyen kwai fefe Daya,ta fisge snacks ta balli Rabi ta Ajiye Masa,ta Buda tsakiya ta sa kwanta ciki ta rufe,Bai ko kulata ba,tana ta ci yasha tea da yawa saura Rabi ta dauke cup din ta gudu,dama ya koshi shi take uban gudu da tayi zamanta ma shi baida time dinta yanzu. Mama zaune take a Palo tana gyara wake Baba yayi wanka ya Sha Yar shaddarsa zai tafi kasuwa ya daga Hannu sama yayi wata Hamma tare da Mika yace Alhmdllh Aishatu sakayau nake jina,Kamar wani sabon musulunta,ji nake Kamar yau aka Yi min wankan tsarkii,sabo da mun Aurar da Yaran Nan mun huta Kuma Alhmdllh Bamu siyar da akuya ta dawo tana goge Mana danga ba,Mama Tace Bari Kai dai Baban Zuhra ai idan na tuna musamman Zuhra tana can tana zamanta lafiya sai naji Ni kamar Ina cikin watan Ramadana Naga Kuma Daren lailatul qadri,ita kuwa Aamna mun fita ko ba soso ba Sabulu,ta koma bangaren danginta suje can su karata,gashi Dake so suke su Aurawa Dansu Dan Giya har da bani jarin Million Uku cewar Baba shima,Mama Tace yo ai mun gano wayon badan Allah aka Bamu ba,harda wani gida ,Baba yace ai Ina sani na kwantar da Kai na nuna musu mutunci na hada dabara nace su bawa Aamna auren Ahmad zai shiryu.

Hahaha Mama tayi Dariya Tace Dantijara wannan ai bazai taba shiryuwa ba,ita Kuma Aamna nasan kwadinyin tsiyarta shi zai zaunar da ita shi yasa kaji shuru,ko mun Mata waya sai Tace lafiya suke,Munafuka cewar Baba tana can tana Shan wahala,yanzu da zamu je sai Munga ta rame,Kaga yanzu har tayi kusan wata Guda da Aure, kudin Sadakinta data Bamu mun karbe ba ruwanmu sauran Kuma da Tace a siya Mata wake a ajiye a Kauye fa? Baba yac ae gobe fa zamu je gidan Aamna sabo da karta gano cewar Bamu damu da ita ba ko Bamu dauke a matsayin ‘ya ba sai mu tafi Mata da kudinta mu Bata muce Kar tayi wannan sana’ar Kawai ta kashe kudinta,Mama Tace ita a dole me Neman kudi Ubanwa zai barta tayi Sana’a, Dan taga kudin sadakin Zuhra mun siya Mata Saniya a Kauye Ana kiwo shine itama tace a siya Mata wake,Mama Tace ai baza mu Bari ta Gane komai daga wajenmu ba,kamar yanda ta taso a Hannunmu ba yabo ba fallasa ita Bata Isa Tace Bamu sonta ba Kuma Bata Isa Tace muna sonta ba to yanzu ma hakane,musamman yanzu da ta auri jinin kudi,a hankali zamu dinga zararta kudi,so nake Nan gaba ta Bude min katafaren shago na siyar da kayan sawa na Mata cewar Mama,Baba Yana dariya yace ai Ni Kinga na samu jari.

Amma naga Harkar tayi min kadan dole Nan gaba Nima ta Kara min jari,Mama Tace na karbo wasu layu da guru idan munje Zan sa ta Kara daura su so nake sai na mayar da ita Yar bori da wayo sabo da idan Mijin nata ya gani yace malamai take bi kaga bazai taba sonta ba bare ta zauna a daula,lokacin mun yagi rabon mu,idan ya sako ta sai ta dawo ta zauna a shago na Wanda Zan Bude Nan gaba da kudin surukanta ta dinga siyar min da kayan. Baba Yana dariya har da buga kafa yace kin iya planning,tunda Bata auri talaka ba Allah ya canja lamarinsa Kinga muma harka ta Bude sai mubi a Haka mu yagi rabon mu. Siyama kwance take saman tsohuwar katifarta sai faman Juyi takeyi tana murmushi ita kadai tare da matse pillow a hankali Tace Kai idan ban ganshi ba yau bazan samu nutsuwa ba,Wasa Wasa a hankali sonsa ya Shiga Rai na daga ganinsa sau biyu sau uku,wata zuciyar ce ta gargade ta tace to Faisal din naki fa,Kuma Wanda kika haukace akan sonsa Mijin babbar kawarki ne, wata zuciyar Tace so so ne Amma son Kai yafi,a fili Tace duk yanda naso kawata ta samu farin ciki ai Bai Kai ga kaina ba,Kuma ma mene tunda Allah Bai haramta ba,abinda ya Dace na San yanda zanyi ya Gane Ina sonsa,kafin kawata ta rigani gwara Ni na rigata,zumbur ta Mike Tace dole na Kori Faisal na daina sonsa,Sam baya birge Ni yanzu,Akan Ahmad Zan iya koyar Shan barasa Nima Indai zai so ni,ta yanda Zan bullo kenan Nima na nuna Masa Ina Sha nasan zanyi Nasara,Mikewa tayi tsaye tare da jawo Wayarta ta danno Number Aamna. Aamna kuwa daidai wannan lokacin 11am su Mashkoor su Biyar ne Suka zo tare da cike palon suna ta kurbar giya,Ahmad Yana kwance,Aamna ce ta fito sanye da Arabian gown black da Alama fita zata Yi,ta gansu a palo,kallo Suka bita da shi Banda Ahmad da ko kallo Bata ishe shi ba,Mashkoor ne ya galla Mata Harara ya furta anzo an aure Mana Sarkin mu,kina Bata Masa Rai a banza,Jibson ya ja tsaki,Aamna dai Bata ko kulasu ba,wurin Ahmad ta karasa ta Dan dukar da kanta saitin Fuskarsa Tace zanje kasuwa ba kayan Miya da kayan lambu ka bani kudi da Izni,Tsaki Yaja yace dalla Wai Ni na kawo ki ne,ki tafi ko Ina kika ga dama,Kudi ya jaro dubu Ashirin ya jefa Mata a Fuska yace dauki ki bani waje mayya,Su Jibson Suka kyakyace da dariya ba ji ba gani,Aamna ranta ya baci ta Harare su tayi waje abinta. Napep ta shiga har kasuwar kayan Miya,duk abinda take bukata sai da ta siya,ta zuba komai a Napep zasu tafi Kiran Siyama ya shigo Wayarta,Fuskarta dauke da murmushi Tace Yar halak ya kike? Siyama Tace Ina Kofar gidan mijinki kina gida na shigo? Aamna Tace Ina kasuwa wlh Amma bani 10mnt yanzu Zaki ganni,Kawai ki shiga gidan Ahmad Yana Nan da abokansa kije kafin na zo Amma ki kula karki kulasu zasu iya Miki wulakanci,Siyama Tace to tare da kashe wayar Tace dama ba Dan ke nazo ba ai ta shiga taci Uwar gayu cikin lace Riga da skert wani ruwan kunun kanwa,Sallama tayi tare da Bude Kofar ta shiga dauke da Sallama,wani kamshi da sanyi ya daki Siyama, Siyama a ranta Tace shegiya Aamna akwai iya gyara,babu Wanda ya amsa Sallamarta cikinsu,shiga tayi Kawai ta zauna a wata kujera da bakowa,Ahmad ta kalla Suka hada Ido ta bangale Baki da murmushi Tace Ina kwanan ku,Suka kece Mata da dariya banda Ahmad da ya sake hade girar sama data kasa,a ransa yace an kawo min yarinya gida danginta sun dameni da zuwa gidana,Siyama tayi Shuru tana ta kallon Ahmad Kamar zata cinye shi,gefen Bash ta zauna Tace lemo kuke Sha ne? Kallonta Suka Yi Suka sake kwashewa da dariya,Bata hakura ba Tace Kai dama na sanka ma Brown ake ce maka ko ta nuna Mubaraq Brown,Siyama a ranta Tace Kan uba Taya Zan samu ko number Daya daga cikinsu ne? Tana wannan tunanin sai kuwa Jibson Sarkin son Mata yace Yan Mata kin hadu fa,Siyama tayi murmushi hankalinta na Kan Ahmad,Jibson yace da Allah bani number dinki Mana,ai da sauri Siyama Tace to dama abinda take so kenan ta kulla alaka da wani a ciki ko zata samu hanyar Shiga jikin Ahmad ta Haka,ta Bawa Jibson number ya Kira ta Nan take tayi Saving tana cewa ya matar gidan Bata kawo muku girki bane? Abdul Tawaga yace ta fita fa,Cab Miji yayi Baki Amma matar baza ta kawowa abokan Miji abinci ba wannan wacce irin mace ce,Ahmad ne ya kalli Siyama kadan ya dauke kai,Tace Bari ta dawo ai dole ma na tayata ta shirya muku better,Jibson yace da kin kyauta Uwar Kinibabba,Siyama ta kalleshi da sauri Wato itace Kinababba,yace dama yunwa muke ji,suna Haka sai ga Aamna ta dawo da fara’a tayi Sallama.

Siyama ce Kawai ta amsa itama da fara’a Tace kawata kin dawo kenan,Aamna ta mikawa Siyama Hannu Suka tafa tace kinsan Ni jinin Larabawa ce Zan koma na tuno da Dan larabcina na Islamiyya Marhababiki ya Siyama,Kyaifal Ummati? Siyama tana Dariya itama da kalkala Tace Alhamdulillah…Alhamdulillah,Shukran cewar Aamna,Kujera ta nunawa Siyama tare da Furta Ijlis kawata,Siyama ta koma ta zauna tana cewa jalasna ya kawata,duk sai da suka Bawa su Jibson Dariya,Ahmad Kam Kawai Dan Baki ya tabe sabo da shi Yana mugun Jin larabci Dan Basu Sani bane.

Zama Aamna tayi itama,Siyama Tace Hauwa’u kuwa tace tana Gaida ki,Hauwa’u Yar class dinmu,na Gane ai kice Ina Amsawa na gode,Siyama da larabci tace Ma Fi mishkla,ya kamata mu shiga kitchen ayiwa abokan mijinki girki Bai kamata su zauna da yunwa ba,ya kike Abu kamar Baki San darajar mijinki da abokansa ba,Aamna Bata kawo komai a ranta ba Tace Kuma fa Haka ne muje to ki tayani. Kitchen Suka Shiga Siyama tana ta wani kwarkwasa Wanda take Yi Dan shi Bai gani ba su Jibson sune Suka bita da kallo suna Hadiyar yawu. Fried rice suka Yi hadaddiya taji hadi da soyayyar kaji,ga zobo sun hada me Dan Karan dadi,salat ma an hada daban,a Dining suka shirya komai tare da gyara ko Ina sannan Siyama da Shishigi tazo Tace mun Gama guys gashi can a Dining,Ahmad Bai ko motsa ba sai su Jibson ne Suka zagaye abinci suka far Masa,kafin kace me sun cinye komai suna Santi sun shanye komai,Siyama tana zaune a cikinsu Suka ci tare sai taga Aamna ta fito da katon tire da wasu miyagu food flasks na musamman komai ta jera a Gaban Ahmad kasancewar tasan Bai zuwa Dining side. Serving dinsa tayi komai ta zauna a gefen kafafunsa tace tashi kaci Abincin,Siyama ta Bata Rai tana daga can Dining ta tsura musu Ido ranta a bace tana Jin Ina ma itace a wajen Ahmad Haka ba Aamna ba,Abinda Aamna ta fuskanta Kamar Bai da lafiya kwana biyu tunda yayi zazzabin Nan,Bata San tsabar kwayace ba take sashi Yana slow. Ka tashi please tun safe baka ci komai ba,Ahmad yaki tashi,Siyama ta saki murmushin Jin dadi,a hankali Kuma da ya gaji ya Mike tare da Zama ya saki jiki sharaf yayi wani Slow ya tsaya a Haka yaki Kuma magana. Aamna tasa spoon ta ebo abincin Tace to Bismillah,kamar bazai karba ba sai Kuma Yaja Tsaki tare da bude bakin kadan Tace ka Bude Mana ya Dan Kara budewa ta zuba masa,Kamar Yana tauna madaci Haka yake ci,a hankali yace kice waccen Yar Uwar Taki ta bar min gida kallo na take Yi bana son kallo,Dan kar ya fasa cin abincin Aamna Tace to Bari ka Gama cin abincin tana ta bashi a Baki Yana ci sai uban Tsaki yake ja,ya ci da yawa yasha Zobon ya daure Fuska Kuma yace cikin tsawa ta bar gidan Nan,ba Aamna ba Siyama ita kanta sai da ta firgita ta Mike ba shiri,ya kalli su Jibson yace daAllah kuje Ina son Zama Ni Daya Yana magana ya girgiza kitsonsa,gaba Daya Suka ce an Gama sarki Suka kwashe kayan mayensu Suka Yi gaba,Siyama ta kalli Aamna tayi murmushin yaudara Tace kawata na wuce,Aamna ta Mike ta saka Hijab Tace muje na rakaki,har bakin Titi ta raka Siyama,ta Bawa Siyama dubu Uku tace gashi kawata kiyi kudin Napep. Siyama ta karbe Tace na gode kawas,Aamna Tace kiyi Hakuri da korar da ya Miki wallahi banji Dadi ba Amma Kinga ba yanda zanyi da shi idan kin dawo next time sai na Bude Miki kayan lefen Nawa ki zabi abinda kike so ciki,Siyama ta washe Baki Tace na gode kawata ai na matsu na fara daukan wanka zanzo jibi sai na zaba,Aamna Tace ba damuwa Amma me kike ganin Zan bawa Zuhra itama?Siyama ta daure Fuska Tace zuhran data auri me rufin asiri uban me za a bata,irin mu ai mune muke bukatar taimako,Aamna Tace haba Siyama ya Zaki canja Hali Allah ya Hana mutum zaiyi Alheri ka Hana hakan,ko mutum Yana tayar da Kai da million ai Alheri Dadi gareshi Kuma ma ai kamar Yar Uwata ce tare Muka taso itama abinda take so zata zaba,me Napep ja muje dalla cewar Siyama cikin Fushi,Dariya Aamna tayi ta juya gida,tana zuwa ta tura Kofar palon taji Gam an rufe,tasan Ahmad ne ya rufe Wato Bai so ma ta shiga Kar a takura Masa,Murmushi tayi Kawai ta Danna door bell har ta gaji Bai bude ba,a bakin Kofar ta zauna ta zuba tagumi Tace kaddara kenan,Allah ya jarabce ni,Kwalla ce ta cika Idonta taf. Wasa Wasa har Magriba tayi Bai Bude ba sai jikin tap taje Wanda ke Garden tayi Alwala tare da Gabatar da Sallah a Nan tayi har Sallar Isha sannan ta dawo tayi bugun duniya Ahmad Yana can Yana baccinsa yaki budewa Kawai Kuma Yana sani yayi haka.. A bakin Kofar Aamna ta zauna tare da jingina da jikin bango a Haka bacci ya kwashe ta,har 9am lokacin Kuma Mama da Baba sunzo kawo Mata Ziyara,a Nan Suka hango ta,Mama Tace cab ga Alama mun gani Aamna Bata cikin Jin dadi,Baba yace Yar jakar uba gwara duniya ta koya Mata hankali ko ta koyi darasi,gida har gida sai Takaici a ciki,Allah yasa ba Zuhra bace a wannan halin, Mama ce ta taba jikin Aamna da Kalar tausayi Tace tashi Aamna,firgit ta farka taga gari ya waye sai Rana ta gani kwall a kanta,Salati tayi ta Mike tsaye cike da kunya Bata so su Baba suka ganta a wannan halin ba sabo da tasan zasu shiga damuwa. Baba yace Ashe yau za ayi yaki a gidan Nan,yata Dana rike da Hannu na muka Raine ta in dauka in bada ita Amana Amma a wulakanta min ita Haka karya ne wallahi,ba a haifi mutum ba,Baba Yana bala’i ya kaiwa Kofar Naushi zai daki kofa Mama ta kifta Masa Ido tare da yin wuf ta damko hannunsa tana Haba Baban Aamna da Zuhra Haba,gidan suruki ne Bai kamata ba,Abi komai a Sannu,Aamna tana Jin tsoro Ta durkusa a kasa tana rokon Baba tana Dan Allah Baba kayi Hakuri ka rufamin asiri,Kayi min Rai Baba wallahi idan kuka tafi Ni zai duka,dukan tsiya zai min,a hakan ma ya muke karewa kusan kullum sai ya dakeni,Dan Allah Baba ku tafi gida Ni zanzo,Kamar gaske Baba yace Ina ai wallahi yau sai na Kira Uwarsa da ubansa Akan Haka baza mu lamunci wannan ba,Mama tace ai batun tafiya gida Bai taso ba akwai abubuwan da mukazo tattaunawa da yawa sannan Kuma yau a Nan zamu yini muci mu koshi muna Nan har sai ya Bude Kofar,Aamna ta dafe Kai Tace wayyo Allah na Shiga Uku,Baba Kar ya wulakantaku a gabana bazan jure ba sai dai ya kashe Ni a kanku Dan sai na Rama,Ashe akwai hargitsi da balbalin bala’i kuwa yau a gidan Nan cewar Baba ya nemi waje ya zauna daram,Mama ta gyara Mayafinta ta zauna itama,Aamna kuwa Tap ta nufa tayi Alwala tayi Sallah sannan ta dawo wajen,Suna zaune sai Suka ji baram an Bude kofa da karfin tsiya,kamshi ne na daban ya daki hancinsu,Yasha wata jallabiya Brown Yar tsangalalliya Takalminsa flat Brown yayi kyau kace baya Shan komai,Fuska ya sake daurewa ganin Dangin Aamna,Tsaki Yaja da karfi ya furta sai kace Uban tsohonki ne ya Gina min gida,Kun da dameni da wannan tsofaffin Banzan,Aamna Tace wallahi ba sune tsofaffin banza ba sai dai in naka ne na banza na wofi. A fusace ya juyo Yana huci yace Mummy na data auro min ke wacce ta nace tana sonki kika zageta yau? Jikin Aamna ne yayi sanyi Tace ai ba da ita nake ba Ni,ko kaji nace Mummy? Mummy ai na fika kaunarta Aamna ta wayance Kar yaci ubanta,Baba ne yayi karfin Hali yace ae da ita ake din sai me? Aamna Tace Ni bada ita nake ba Baba,Mama Tace Iyyee…..Juyawa Ahmad yayi yace Zan dawo gidan Nan zamu hadu ya Haye machine dinsa ya bashi wuta sannan ya dage kafa Daya sama yazo har Gaban su Baba ya kotse machine din tare da bashi wuta ya bulbulesu da hayaki ya fita a tsiyace.

Aamna ce ta daka tsalle tare da nuna Bayan Ahmad da yatsa Tace sai nayi maganinka zaka dawo ne sai ka sani,sai na cije ka wallahi a gadon baya,Iyayen Nawa zaka yiwa haka,zaka San ni Yar halak ce.

Mama Tace ke dalla rufe Mana Baki, banza matsoraciyar banza kin Gama cika Mana Baki gashi a gabanki ya ci Mana mutunci Baki ce komai ba sai da ya tafi,Baba Kuwa Takaicin Aamna yasa yace tir dake Aamna muje ciki mu kiyi Mana girki muci mu Sha.

AsmaBaffa
10/26/21, 8:52 AM – A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA🌵🌵

Page 31-35

FREE PAGE

DUNIYA TA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

     NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.

ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

MAMAN MURTALA
HAFSATOU
‘YAR BAIWA
INNARO
AISHA
SALIHU UBAIDAT HARUNA

Aamna da sauri ta fada kitchen sabo da so takeyi suyi sauri su tafi,babu Bata lokaci tayi musu farfesun kaji,ta musu jallof din taliya Tasha kifi da kayan lambu sai lemuka da ruwa ta kawo musu,Suka zauna Suka dinga kwasar girki, Baba Yana yin Loma Daya yace Allahu Akbar sai na tuna da Uwar dakina Dake Kano Hajiya Sahura lokacin da aka kaini almajiranta na Zama Yaron gidanta,Haka take dafa Taliya Malam Kamar daga Otel(Hotel),Mama Tace taji tarihu kaga inda tsiya tayi tafiyar dogon zango,ai a Nan gidan Tsiya Balaguro tayi ba tafiya ba cewar Baba,Aamna tana ta dariya Tace ai kudi yake bani da yawa,kwana na Daya na fara fita,ba ruwansa da wani Ni Amaryace inda Naga Dame nake zuwa,Baba ya tsurawa Aamna Ido yace indai akan irin wannan cefanen ne ki dinga ficiwarki daga Nan ki dinga biyowa ta gida kina yaga mana. Sai da suka koshi,Baba yace zuba min wani farfesun a flask na tafi dashi idan munje gida zamu ci da breadi,Aamna cikin sauri ta samo flask karami ta kwashe ta bar kadan ta hada musu harda lemuka,cikin lefenta ta dakko wata atamfa da turaruka ta bawa Mama atamfar turaren Kuma ta bawa Baba,Sai Jin dadi sukeyi,Mama ta zuge Jakarta ta sake zaro wata laya da guru na damtse ta mikawa Aamna Tace ungo Bude Damtsanki ki daura wannan,Aamna ta Bata Fuska kamar zatayi kuka Tace Mama Kinga fa wani a hips Dina kince idan na cire Baku yafe min ba Haka kaina layu ne fa har biyu idan zanyi wanka nake cirewa Ina Yi nake maidawa Kamar yanda kika ce shima Kar na cire,Mama ta Bata Rai Tace saka wannan layar a gashinki itama ki soketa ga pin Nan a jiki Kuma wallahi kika cire Bamu yafe ba,Aamna ta karba ta soke Laya ta Uku cikin gashinta,ta dauki guru ta bude farin damtsenta ta daura,Dake tana da haske sai ya Mata kyau. Mama Tace to Haka ake so,sai magana ta karshe zamu Kira surakanki a waya mu fada musu kina cikin wahala zamu dauke Yar mu idan suna so ki zauna sai sun turo Mana kudi sabo da Haka ko sun kiraki sun tambaya kice Haka magana take wallahi idan kika ce ba Haka ba kinji mun rantse sai kin bar gidan Nan ta karfi sannan sai Kinga matakin da zamu dauka a kanki. Aamna tace Haba Baba Wai me yasa kuke Haka ne,Ni fa ba sonsa nakeyi ba,Kuma ma Ni Nan gaba barin gidan zanyi Akan me zaku karbar Musu kudi,a gidan Ubanwa Zaki bar gida? Sai mun Gama kwasar rabon mu tukun yarinya,Shuru Aamna tayi Tace shike Nan to kuje Allah ya kiyaye Hanya na gode,sauri takeyi su tafi Kar ya dawo gidan,Mikewa sukayi ta rakasu Suka tafi,Suna tafiya ta dawo ta hau gyaran gidan sai da ko Ina ya fito fes sannan taci abinci ta sheka wanka tayi Sallar Azahar,Kwalliya tayi cikin wata English gown silk maroon,me Hannun vest tayi mugun Mata kyau ta fito da shape dinta matuka,Fitowa tayi ta koma kitchen ta duba farfesun data ragewa Ahmad,Sai tayi cabbage soup ta Sha kifi tayi sakwara,me Gadi ta bawa sauran ta Ajiye ta zauna a Palo tana kallo,Bayan tayi Sallar la’asar tana karatun novel a Wayarta taji ya shigo Yana waya yace Daddy Kuma me ya same shi? Yana asibiti? Bazan zo ba Allah ya bashi lafiya ya furta tare da Zama a saman kujera ya rufe Ido tare da dafe Kansa. Duk da baiyi Sallama ba sai tace me ya samu Daddy din? Wani kallon wulakanci ya Mata yace ina ruwanki ko son gulma,na fada Miki ki daina shiga safgata Zan Tara Miki gajiya wallahi tam,Shuru tayi Tace abincin fa? Baza’a ci ba ko dole ne sai naci girkinki? Wai me yasa kike son takura min ne? Sabo da Kai Mijina na ne shi yasa,Baki gaji da duka bane Naga Alama,Kai baka gajiya da fada da mace? Ko kunya baka ji fada da mace,idan kana Jin Kai Namiji ne kaje can waje kuyi da maza Mana kaga yanda zasu maka jina jina,ka zauna a Nan Ni sabo da mace ce sai dukana kake Yi wallahi sai Allah ya tambayeka,ranar lahira sai Allah ya Kamaka da hakki na,Murmushi yayi na rainin hankali yace sai na karasa wannan idon Daya shima a manne shi,Sai lokacin Aamna ta tuna ma Idonta a manne yake,Haka duk inda aka ganta sai dai taji Ana ta Mata Sannu da Allah ya sawwake,tana sani Tace zo na yanke maka farce gasu Nan sun fara taruwa,kwanciya yayi a kujerar tare da juya Mata Baya yace wannan karon wallahi kika kuskura ko da Wasa kika taba min farce saina ballaki a gidan Nan,ka godewa Allah ba sajenka da gemunka na yanke ba,Banza ya mata yana tunanin Daddy da akace Hawan jini ya kamashi saura kadan yayi paralyse. Damuwa ya Shiga a ransa sosai gashi shi bazai iya Addua ba baida time,juyowa yayi Aamna ta kalleshi da sauri,Je kiyi Alwala,tsoro ya Kama Aamna a ranta tace ko hakkinsa zai karba yau na Shiga Uku maybe nafeelar sunna zamuyi daga Nan sai Sex,Idonta ne ya kawo kwalla Tace Alwalar me Kuma? Fuska ya Bata yace Zan fa zaneki wallahi kije nace kiyi Alwala ki zo,Aamna Tace wayyo Uwata na shiga Uku,shi ya manta ma Daren farko Ana Alwala da Nafeela,Aamna tace ka Bari sai dare Dan Allah kayi min Rai,Yace Bari na tashi kiga tsayi na,da sauri ta tafi tayi Alwala ta fito da Hijab a Hannunta tana kuka Hawaye shabe Shabe a fuskarta,Alwalar kikewa kuka duk tsoron Allah naki da kurin Sallah da waye waye,Aamna tayi Shuru tana Hawaye Tace Dan Allah kayi hakuri ance da zafi,zafin me? Alwalar ce da zafi? Ya tambaya Yana zaro Mata Ido,Sallayar Dake Hannunta ta shimfida yace to kalli gabas ki fara Nafeela,Aamna Tace bangane ba,ba tare zamu Yi ba? Yace Kiyi Nafeela nace ki yiwa Daddy Addua Allah ya bashi lafiya a madadi na,Ni bazan iya Yi bane. Baki Aamna ta Bude sai lokacin taji kunyar kukanta na banza na tunanin banzan ta,Tace Bari ayi magrib,tana yin Sallar Magriba ta fara Nafeela. Haka tayi ta Nafeela tana yiwa Daddy Addua Allah ya bashi lafiya,sai da ta idar Tace nayi to,ko magana baiyi ba,Wayarta ta jawo ta Kira Mummy, bugu Daya ta daga Bayan sun gaisa Aamna Tace Mummy ya jikin Daddy din? Mummy tana murmushi tace waye ya fada Miki? Aamna ta saci Kallonsa yace in kika ce Ni na fada Miki sai na karya ki yau,Aamna Tace lokacin da kuke waya Ina wajen,Mummy Tace okay da sauki sosai gobe ma muke sa ran Sallama mu koma gida,yaya fatan dai rigimar Bata Yi yawa ba? Aamna Tace ae Mummy,Baba ya kirani jiya,Gaban Aamna ya fadi,Mummy Tace banji Dadin abinda suka Iske Ahmad ya Miki ba,naga Baba yaji Haushi da yawa yace zai dauke ki daga gidan,Kunya ta Kama Aamna Tace Mummy ki kyale Baba rikicin tsufa yake Yi. Dariya Mummy tayi tace Mama Kuma Ashe Business take so ta fara lokacin Muna cikin damuwa a asibiti abinda ta Nema Bai samu ba sai dubu dari hudu ta samu kacal Amma Inshaallah Zan Kara Mata wasu,Aamna tayi Shuru sabo da Matukar kunya da nauyi data ji, Tace kuyi Hakuri Mummy wallahi Ni ba sa Hannun na ciki,ban San zancen ba ma,Mummy ta fuskanci Aamna ta Kuma Gane su Baba Kawai kyalewa tayi,karki damu Aamna na fihimci lamarin,kici gaba da Hakuri Zama Dan Allah kinji,Aamna Tace Inshaallah ba matsala,kina bukatar kudi ko wani Abu? Aamna tayi murmushi Tace a’a Mummy ba abinda nake bukata komai Yana Yi min idan na tambaya,kin tabbatar? Aamna Tace ae Mummy kiyiwa Daddy Sannu da jiki a gaisar min da Humaira Kuma,Mummy ta dinga yiwa Aamna godiya sannan ta kashe wayar. Ahmad ransa ya tunzura Jin irin godiyar da Mummy ke Mata to uban me tayi ake gode mata,Cikin masifa yace ni baza a gode min ba Dana dauki kaddara nake zama dake cikin kunci sai ke Za’a godewa Ana wani sa Miki Albarka ke ga fitsararriya ko? Harda wani Jin dadi kina to Mummy…ya makale Murya tare da gwada muryar Aamna yanda take magana,Aamna Tace Wai Kai me yasa baka da kirki ne? Yace ke dalla rufe min Baki ke Wato an Baki lasisi ko harda wani Kara siyo waya Vivo sabuwa,wannan ba gata bane, ke ga tsigalalliya ko kina wani girgiza da kafada ya gwada girgizar Aamna Idan tana masifa,Aamna ta kyalkyale da Dariya gashinsa ya girgiza tare da gyara sabon kitson calabarsa,Aamna Tace shike Nan Zan Kai karar ka wajen Mummy,Yace idan kina yiwa bushashen tsohonki kije ki Kai karar tawa ki gani idan akwai Wanda ya Isa ya tankwara Ni ko yasa naji magana,an fada Miki wani Jin Magana nakeyi. Baki Aamna ta Bude Tace ai Ni tsoho na ka ganshi me kiba ne,Ashe Ahmad ba Baba yake nufi ba yasan Baban Aamna na asali Dan Sudan wani mugun bushashen tsoho ne,ramarsa ta baci tunda lokacin da wayonsa Bai manta shi ba,Sai yace kije ki binciki tarihinki yarinya kiji waye tsohonki Dan lukuti ne ko kuwa,Aamna ta Mike tsaye tace Allah ban yafe ba sai na cijeka ta fado Kansa Kamar wata Kura ta Bude Baki da gaske ta Kai Masa cizo a wuya,wuyanta ya cafka da hannunsa ya shaketa sosai ta fara kakari Idonta ya firfito kamar zata sheka lahira ya hankadata gefe ta Fadi a kasa dabar, mikewa yayi zai fita ta jawo rigarsa Iya karfinta,ya juyo ya dauketa gaba Daya ya jefata saman kujera Kamar Yana wrestling,Aamna ta cakumo kafafunsa ya Fado gefenta,Idonsa Wanda ya canja yayi ja sabo da kwaya ta motsa ya watsa Mata wani kallo ai sai ta Mike ta arce da gudu. Key din machine dinsa ya dauka ya fice abinsa ya hau machine kenan yaji an jefo Masa Robar ruwa a Kansa kwas,Kansa ya daga sama yaga Aamna ce ta baya balcony dinta ta sama tana cewa aje a Kai karata wajen human Right idan an isa,ko kazo ka dokeni,Yatsunsa ya wara ya Mata dakuwa Wato ambola Aamna ta Masa gwalo,yace zamu hadu ne da karfi yanda zata ji,mu hadu Mana gani ta matso jikin karfen wajen Dan Allah taho mu hadu tayi girgizarta da kafada,saura kadan yayi Dariya ya matse yace Fuck you….Aamna Tace Dadi ne da shi come and fuck me,Dariyarsa ya guntse yace Yar Iska ce ke ai,nafi karfin Iska sai dai Guguwa,Machine dinsa ya kotse yayi waje abinsa ya barta tana ta dariya. Tunda ya fita Bai dawo ba sai wurin 4am ya shigo a chake yasha da yawa,tunda ya Shiga Dakinsa Bai tashi ba har gari ya waye,12pm Aamna ta Gama komai tana ta duba shi Bai tashi ba,Haka taje ta wanke Masa toilet ta gyara dakin bed din ne Kawai bata gyara ba kasancewar Yana kwance,Fitowa tayi ta zauna sanye cikin doguwar rigar Shadda purple ta Sha kyau,sallamar Siyama ta ji,ta Mike Suka Rungume juna Siyama Tace ba Zama nazo Yi ba maza muje na zabi kayan,Bedroom Suka haura Aamna ta bude Mata akwatuna Tace zabi,da mamaki sai taga Siyama ba hankali duk kayan masu tsadar take zabewa har ta zabi kala biyar ta koma Kan Arabian dress,ta zabi English wear, ta zabi Inners,Aamna gashi ita Tace ta zabi abinda take so tana ji tana gani Siyama ta zuba a katuwar leda,Aamna Kamar ta kwace Amma ta danne zuciyarta Suka fito haka,suna Fitowa Ahmad Yana Fitowa ya Sha wanka cikin kana Nan kayansa kamar kullum 3qtr da t-shirt marasa nauyi ne da Alama ba fita zaiyi ba,Kallo Daya ya musu yace Mene a Nan? Ya dakawa Siyama Tsawa. Da sauri Aamna ta firgita Tace ka…Kaya…kaya ne na lefe kasan Ana Dan bawa kawa wasu abin,Ya Mika Hannu yace bani cikin tsawa….Siyama jiki na rawa ta Mika Masa ledojin ya fisge kuwa tare da budewa yaga Kaya da uban yawa,ya kalli Aamna yace waye ya Siya Miki kayan Answer me,Aamna Tace Mummy ce,yace ke ta siyawa ko wannan jakar ya nuna Siyama da yatsa,Aamna Tace Ni,yace to ba don Mummy tana sonki ba ta siya Miki shine Zaki bayar sabo da ba kudinki bane,Mummy ta me yasa bakya respecting din Mummy ne Wai duk son da take miki,Siyama ya kalla yace last warning duk abinda Zaki ki tsaya a Downstairs main Palo Kar na sake ganinki a sama Nan,sabo da idan na sake ganinki baza kiso abinda Zan Miki ba,baza kiji dadin abinda Zan Miki daga ke har kawar taki,bi hanya….ya furta da karaji,Siyama tayi kasa da gudu,Aamna zata bita yace wait…tafin hannunsa ya Buda kamar zai mareta yace karaso ki Mari kanki da kanki. Aamna da sauri tazo ta Kara kumatunta a hannunsa,yace Baki ji zafi ba da karfi Zaki taho ki taskawa kanki mari,Matsawa tayi baya ta taho da gudu tare da hannunsa da Hannunta ta Kara kumatunta a tafin hannunsa da karfi ta taskawa kanta Mari yace Good tare da murde Mata kunne yace daga yau idan kika sake ebar wa Mummy Kaya kika bayar sai na babbalaki nayi raga raga dake. sannan duk kayan Dana Baki kudi kika siya idan na samu kin bayar zaki ga abinda Zan Miki,Aamna Tace sabo da tsumulmula ko me? Yace yes…son kudi ne Dani…Ina son kudi…kayan ta kwashe ta maida daki sai murna takeyi gwara Daya kwace dama Bata Yi Niyyar bayarwa da yawa Haka ba,kafin ta fito tuni Siyama tana Napep ma sabo da tsoro gashi Kuma tana sonsa a Kansa take ta wulakanta saurayinta ya rasa me yayi mata ya kasa Gane Kan Siyama. Aamna cikin Fushi ta dawo Palo ta zauna kan kujera me kallon wacce Ahmad ke zaune sai harararsa takeyi,Tace abinda kake min Sam bana Jin dadi kawayena da Yan Uwana gaskiya gaskiya bana son abinda kake musu,bana wulakanta naka Nima karka wulakanta min nawa ehe,Nifa akan wannan bazan fa yarda ba,Nima kwayar Nan na Iyata,aikin Yan giya na iya shi nima,Haka Kawai in Banda kaddara ma Dana dorawa kaina,ga maza can suna kauna ta,ga masu kudi na gari masu Addini Wanda zasu kula Dani naki yarda dasu,banga laifinka ba laifi nane,Nan..nan Affan ya dawo daga malaysia ya dawo da kudi da mota Yana rokata naki yarda,Nan su Deeni Dan gidan Dan Majalisar jaha sakakina yasa kawata ta kwace min shi Ina ji Ina gani, ga bushashena Kamalu naci Masa mutunci a banza ya gudu.

Dama ance kamatuddini tudan yanda nace Masa bushashe Haka tun ba ayi nisa ba gashi ka Rama Masa Ni Babana Mahaifi kacewa tsotsatse,tun anan duniya gashi Ina gani Allah na tuba Amma gaskiya Ina cin ubana a kasar nan,Ina karba a jikina wallahi,ta ko Ina duniya ta min daurin Alawa ko Ina ba sauki anyi min kika kaka,na Shiga tsaka me wuya,Baki Gama Shiga masifa ba yanzu kika fara tunda kika yarda kika aureni cewar Ahmad ,Aamna tana huci Tace Ina ma mu Mata aka bawa damar saki ko kishiya wallahi da tuni na maka saki dari da talatin da biyar, ko na auro maka kishiyoyi har Uku,kishiya na farko Mashkoor babban abokinka Zan kashe makudan kudade na auro shi sabo da na huce takaicinka,na biyu na Nemo tsohon saurayina Affan,na Uku nayi manage da Mubaraq Tawaga Kai Kuma Kaine Uwar gida,ai wlh da kaga wulakanci,duk ranar kwananka ba abinda Zan tsinana maka sai dai sha’awa ta kashe ka,Amma a sauran kwanan su Affan kullum asubar fari zaka ga mun fito yin wankar tsarki.

Dariya ce ta Kama Ahmad yace ai ke dakikiya ce shi yasa kike wannan tunanin,Namiji Daya ma wallahi yafi karfinki Indai ya amsa sunansa Namiji Irina bare har maza hudu,,Dariya Aamna tayi Tace a Ina ka amsa sunanka namijin Kai dalla duk kwayoyi da giya sun Gama kashe ka,Kai da tsoron Boobs ma kakeyi,Ahmad yace ae naji ai tsoro halak ne,bana sonsu ne shi yasa,Ni ba birgeni sukeyi ba Mene abin sha’awa a Nan Abu cako cako Haka a kirji ba kyan gani,ka taba Abu kamar wani jikin mage ba dadi Haka yagwalgwal,Dariya Aamna take tayi Tace na fada maka kwayoyi sun kashe ka,ka daina Sha wallahi ka samawa kanka lafiya,wannan abubuwan ka tambaya kaji mu kanmu idan Muka je wanka dadin wanke su muke ji bare Kuma maza,Kama fara sonsu tun yanzu sabo da idan na gaji duk ranar dana je na kalli film jam’iyata ta motsa zanzo ne dole ka koyi sonsu. Fuska ya Bata yace ko da Wasa kika zo Zaki Sha duka ne, tunda ke Baki da kunya Ni Ina da kunya ni Fulani ne ni,Aamna yau tana mamaki Ashe Yana magana Haka,Tace Kaine me kunyar lallai,Shi yasa nace wa Mummy ta Bari na samo yarinya karama Yar secondary wacce Bata San komai ba me hankali da kunya Amma Mummy Taki yarda ta dakko min me Degree wacce ta Gama balaga a waje ta fitsare kafafunta. Aamna Tace kamar ka sani ai idan muka wuce 22yrs to Kar muke ganin kowa,Ahmad yayi Shuru Bai sake magana ba har ta Gama surutunta ta koma kallon Indian film,Yana ta kallon soyayya ya tabe Baki yace bani remote,Mika Masa tayi ya canja Chanel ya Kai Wrestling,yace ga inda ake abin arziki ba love ba,kasa ta lalace komai love,gidan radio love,Yan film love,writers love,matasa love,tsofaffi love,tsoho ya tsufa maimakon ya Bari aci gaba da dama Masa kunu Yana Sha har ya koma lahira a’a sai kaji ya Kara aure ko aji matarsa ta Haihu,tsohuwa sai aga tana Shan maganin Mata abin haushi ta Aiki mutum siyo min Zuma da gumbar Mata zaka ce,Aamna ta kyalkyale da Dariya harda rike ciki ya gwada yanda tsohuwar ke magana tana makyarkyata da Murya,Shi kuwa ko Dariya bayayi kamar ba shine yake Maganar ba.

A Ina kaga tsohuwar ta fada,jajayen lips dinsa ya tsuke, Baki ya turo gaba Yana girgiza Kai kwaya ta motsa yace Maman Jibson ce take Aiken wani Dan yaronta Islamic chemist,Aamna tayi Dariya Tace Sallar Azahar lokaci yayi kaji ana Kira,ba yanzu zanyi ba sai ta nuna luguf,zata sake magana ya daka Mata Tsawa karki dameni Dan Kinga nayi magana dake Ina cikin Good mood ne Daddy ya warke karki kawo min raini ba Dan arziki bane ni yawwa kije kiyi sallarki ba ruwanki Dani,ko ke nake yiwa Sallar? An fada Miki zanyi Abu Dan wani Dan Adam ne eyeee? Aamna Tace a’a,yace to ki daina shiga hurumina,bana Shiga harkarki ko Kinga Ina Shiga rayuwarki? Ina ruwana da rayuwarki,Ina ruwanki da harkata,Tace babu yace to San Inda dare ya Miki ko na zubar Miki da hakora,Sum sum Aamna ta wuce taje tayi Sallah,ko da ta fito sai gani tayi har ya dafa Indomie da kwai ga coffee ya hada Yana sha abinsa,Yana gamawa yayi ficewarsa,Kitchen ta Shiga itama.

Wasa Wasa Har Aamna ta kwashe wata Uku a gidan Ahmad kullum a haka suke ba Wani canji,halinsa ya ishe ta,ta Gama gajiya da zaman gidan gaba Daya,yanda ta sanshi tun farko Bai canja ba,ga Kuma Siyama da ta nacewa gidanta kullum shi Kuma Yana ci musu mutunci Wanda Haka Sam baiwa Aamna Dadi a gabanta Ana ciwa kawarta mutunci sabo da Bata San kudirin Siyama ba,Siyama tuni ta sallami Faisal ta sa an mayar Masa kudin auren da ya kawo,Faisal ya shiga damuwa Amma ba yanda ya iya Haka ya hakura bayan ya Sha fama da zuciyarsa,Siyama kuwa Bata fadawa Aamna ta Kori saurayinta ba sabo da kar a gano ta,gashi kullum Kara son Ahmad takeyi kamar hauka. Bangaren su Mama kuwa tuni kusa da gidansu ta bude katon shago tana siyar da Inner wears na maza da Mata,masu kyau take siya idan anyo order daga kasashen waje,ta gyara ciki komai glass da glass ne Dan karamin shago, Baba ne ya cika Mata kudin Suka Bude abinsu sannan a Kofar shagon daga gefe kayan kamshi take siyarwa citta,barkono,kanunfari da masoro da su Kimba da gyadar curry etc,tana Zama a shagon da kanta sannan ta sa wani yaro a ciki Dan makwaftansu da taga Yana da Dan hankali tana biyansa Dan abinda ba a rasa ba,Zuhra Bata San duk abinda ke faruwa ba sabo da ita Bata Bayan su Baba,duk abinda suke Yi Bata Jin dadi tana Kuma kokarin yi musu Nasiha,ganin Haka sai Suka daina fada Mata komai,gidan Aamna kuwa Bata zuwa sosai sabo da halin Ahmad taga baya son Baki a gidansa. Da Yamma Aamna tana share sharenta tana mopping ko Ina Ahmad Yana kallonta ta gama,sai kunci yakeyi Yana faman huci,duk abinda take Masa baya gani,tana gamawa da ciki ta fita compound kasancewar me Gadi Musa ya tafi Kauye wajen Iyalansa sai Nan da sati biyu ko Uku zai dawo,Duk girman Compound din Haka ta gyara shi,Ahmad ya fito yace sai ta wanke Masa machine Haka ta wanke Masa tas,ta Sha wahala da kyar take mikewa,Yana Fitowa ya kalli Tyre Kawai ya juyo ya kwashe ta da Mari a saman Idonta Wanda yake mata ciwo,Botikin ruwan data wanke Masa Machine ya dauka ya juye Mata ruwan a kanta gaba Daya,Aamna ta fashe da kuka yayo kanta ta matsa gefe sai ga Siyama ta shugo da sauri Tace lafiya Ahmad????….Kafin ta rufe Baki ya fyallawa Siyama nata rabon marin Yana cewa Yan Iska matsiyata,Aamna duk dukan da ya Mata Bata ji haushi ba sai Akan ya Mari Siyama,Machine dinsa ya buga ya fice,Siyama ta fara zuga Aamna Tace wallahi ki bar gidan Nan Aamna Idan ba so kike Watarana a tsinci gawarki ba,Wannan Bai da hankali kwaya da giya sun Gama da kwakwalwarsa,tun dare Bai Miki ba ki bar Masa gida,gwara ki rasa aurenki Akan wannan halin da kike ciki,auren me auren wahala,Iyayensa su na can sun barki idan an kashe ki Basu da asara,Dansu Yana raye suna da kudi abinsu kece a kasa Aamna ki Kama gabanki kinji na fada miki. Aamna Tace Mummy fa ba Haka Mukayi da ita ba,Mummy din banza,wallahi ki farka daga mafarki Aamna ko sonsa kikeyi? Da sauri Aamna Tace Allah ya kiyaye min tir na so wannan mutumin,Siyama taji Dadi a ranta Tace to ki hada kayanki ki tafi gidanku na tabbata Baba bazai Bari ki dawo ba ki fitar da kanki daga wannan masifa,Aamna Tace gaskiya kika fada na gode Siyama ke me kauna tace Inshaallah yau a gidanmu Zan kwana Bari na hada kayana idan ya dawo da wuri Zan tafi yau idan Bai dawo ba gobe da sassafe Zan taho,Siyama Tace yafiye Miki Ni na tafi ta fice abinta,Duk Hirar da sukeyi Ahmad Yana jinsu ashe Daya fita da machine ta Kofar me Gadi ya shigo Dake Kofar me Gadi biyu ce akwai ta ciki akwai ta waje,Dama shi ya gaji da su so yake ta bar Masa gida ya samu Freedom ya gaji da shishingi da take masa,yafi so ta Kori kanta da kanta sabo da Mummy Kar taga laifinsa,farin ciki ya kamashi,sabo da tayi sauri ma ta bar Masa gida sai da 5pm tayi sai gashi ya dawo gidan da fara’a Yana ta rera wakar Bob merly Yana girgiza Kansa Yana lumshe Ido har Palo.

Sharhi Dan Allah

AsmaBaffa
10/26/21, 8:52 AM – A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA AAMNA🌵🌵

Page 36-40

FREE PAGE

DUNIYA TA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

     NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.

ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

ZAHRAH
RAMALURV
JIDDAH
ZEEY SOORAJ
HAJIYA ABOU
SERLMAH
I LOVE MY SAIF

Aamna Tana kitchen kamshi na tashi ta fito tare da furta Sannu da zuwa,Annurin fuskarsa ne ya gushe ransa ya dugunzuma ganin Bata da alamar tafiya,Tsaki Yaja yayi waje abinsa Bai dawo ba sai 9pm zazzabi ya dawo da shi gida,tana kallo a Palo taga ya shigo Yana kankame jiki Yana Rawar sanyi da sauri ya fada saman doguwar kujera ya dunkule,Aamna Tace lafiya? Harara ya watsa Mata tare da furta duk bake kika jawo ba,bakin cikinki ya zuba min zazzabi,Aamna Tace au nice? da wacece idan ba ke ba Kawai kinzo kin tare min fili da Fadin gida,ba dama na samu Freedom na Wala Ni da gida na,Dariya tayi Tace to Yi hakuri,bazan hakura ba sai kin bar gidan Nan cewar Ahmad,Ni kwata kwata ba kaunarki nakeyi ba,Sam Baki min ba tsarin zubinki gaba Daya Bai min ba,Aamna Tace duk kyan Nan nawa? Wani kyau ne Dake an fada Miki kyau nake Nema idan kyau ne naje na kalli kaina Mana har Zaki fada min kyau? Dariya ta Kama Aamna yace ke Baki da kunya ko tsagera ko fitsararriya ko? Idan ba tsaurin Ido ba ki kalle Ni kice me? Ki tafi gidanku na gaji Dake Ni,Ina Nan daram wallahi baka Isa na bar gidan Nan ba. Bargo ta Mike taje ta kawo tare da lulluba Masa Tace ko na shigo ciki na Dan jona maka heater? Wlh idan kika shigo bargon Nan yau Allah ne yasan irin dukan tsiyar da Zan miki,Dauko min magani a dakina paracetamol da ruwa,Aamna taje ta kawo Masa ya Mike ya karba ya Sha,Tace ko a Kira Likita ya maka Allura maybe Malaria ce,Ni ba a min Allura babu Wanda zai sokar min duwawu ko Hannu,Ina ma Likitanci na karanta ko Yar Hygiene din Nan da wallahi sai na tsira ma Allura cewar Aamna ta furta tare da daukan waya ta Kira likitan da Mummy ta hada ta da shi Wanda ke duba Ahmad,Bayan sun gaisa ta fada Masa,a daren yazo ya duba Ahmad ya rubuta magunguna yace malaria ce,Bayan ya tafi Aamna ta Aiki Musa ya siyo Magungunan. Lokacin jikinsa yayi sauki ta hado Masa cous cous da miyar kwai ta kawo ya karba yaci ba laifi ta bashi Magungunan Tace sha,yace sai ki dura min ta karfi bazan Sha ba,Aamna Tace okay sabo da ba kwayar maye bace ko? Yace ae ai Wanda baya shaye shaye ya bar Dadi ya furta da slow, Zan fadawa Mummy Allah gwara ka karba ka Sha, ki fada Mata Mana tsoro nake ji ke Baki ga ba Wanda yake fada min naji bane?na gani Dan Allah ka Sha zaka daina zazzabin,Da kyar ya karba ya Sha yace gobe bazan Sha ba,ya tashi ya koma bedroom dinsa, kwana Uku Aamna tana fama da shi da kyar ta samu ya Gama shanye maganin Kuma ya warke fes. Siyama ce ta kwada Sallama tare da shigowa,ta Iske su Mashkoor a palon lokacin Aamna tana bedroom tana bacci,ko nemanta Bata Yi ba ta zauna wajen Jibson ta kalle su Har Ahmad Wanda ke latsa waya,Ta kalli kayan mayen tace gaskiya Kuna birge Ni wallahi,Musamman idan na kalli giyar Nan Dake cikin dundumemiyar kwalaba,Ina so inga Ana daga Dunduma a duniya,Suka kwashe Dariya banda Ahmad,Jibson yace kaji fa sabo suna Wai Dunduma,Siyama taji Dadi Tace Ni ko Mijina naga Yana daga Dunduma bazan damu ba Zan koma Taya shi Sha ne, Mashkoor yace Baki da hankali mu kanmu so muke mu daina mun kasa Amma ke kina mace kina wani Eh yane Haba Yawa kike,Siyama taji haushi a ranta ganin Bata birge su ba sai ta tashi zata haura sama wajen Aamna Ahmad ya daga Mata Uwar Tsawa yace idan Baki bar gidan Nan ba wallahi na tashi ko ya Mike a zabure Yana cewa Upstairs din na Ubanki ne? Ko da kwandalar Ubanki aka gina gidan da har Zaki kallar min sirrin Dakuna,Shegiya da kanki Kamar butar Shayi, da gudu tayi hanya ta fice. Jin Hayaniya Aamna ta tashi ta fito itama tana murje Ido Tace lafiya naji Hayaniya?Takalminsa ya cire a zuciye ya Wulla mata yace ai duk ke kika jawo Ina Zama na lafiya Yan Iska Kun dameni a gida wallahi ranar lahira sai Allah ya Kamaki da hakki na,sai Mala’iku sun jibge ki da almudun bakin karfe,Su Mashkoor cikin kwaya Suka ce Kuma ta saman kwakwalwarki zasu dirka miki kinzo kin Sa abokinmu a bacin Rai,Dariya ma Suka Bawa Aamna Tace Dani da ku zamuga Wanda za a jibga a lahira kuci gaba da Shan kwaya ku gani,Kana jinta fa King cewar Jibson,Ku kyaleta Bata da hankali ai. Bayan wasu kwanaki Aamna Sam zaman gidan ya ishe ta shi yasa kullum sai ta fita siyo kayan Miya ko kifi ko nama etc Dan kawai ta Dan shakata,yau ma Shiryawa tayi ta tafi kasuwa zata siyo vegetables, Duk da Haka Siyama Bata hakura ba ta dawo gidan Aamna ta Iske Aamna ta tafi kasuwa,yau ba ma Jibson,Ahmad,Mashkoorsu Uku suna gidan suna kallon ball suna shaye shayensu,su Jibson sun turnuke palon da Hayakin Shisha da Wiwi,Ahmad kuwa Giya yake Sha a kwalabar Yana dagawa,Ganin Siyama ransa ya sake baci Amma baiyi magana ba,Jibson yace mayya an dawo ne? Mashkoor Yana tangadi yace Chaiii….Wai ko harda ke aka Daura Auren ne? Ko Mata biyu aka bashi Bamu Sani ba?to wallahi mu dai Iya Aamna muka ji ance an daura Aure mu ita Muka sheda an daura da ita cewar Mashkoor,Jibson ya kalli Siyama yace ke muna wajen fa har mandiri aka kada Ana Waka Ana Ahmad Angon Aamna Gam.. Gam… sannan kizo ki Raina Mana hankali. Siyama tayi banza da su sai ga Aamna ta dawo Siyama ta Mike Tace balarabiya kin dawo? Da murna Aamna ta wani tuno Dan guntun larabcinta Tace Marhababiki ya Siyama ta wani Rungume Siyama har da Yi mata kiss a kumatu Wai ita Balarabiya,Siyama da munafunci Tace Aina tazhab? Wai ina taje, Azhab Ilal suk cewar Aamna wai da larabci taje kasuwa Wanda da kyar suke tuna Dan abinda suka tsinta wani ma ba daidai suke fada ba,kiyi Hakuri na Dade ban San kinzo ba,Siyama Tace Ma Fi mishkla,Mashkoor yace cab da Kun taimakawa kanku Kun daina Sam Baku iya Larabcin ba,bakinku ya dafe da miyar Kuka zaku Raina mana wayo Baku Iya komai ba,Jibson ya nuna Ahmad yace da kun San irin Larabcin da King keyi ai da Sai Kun Mari kanku da kanki sabo da haushin kanku zaku ji.

Aamna Tace Kai ku kiyayeni matar oganku ce Aunty ya kamata Kuna kirana bana Wasa da ku,Dariya sukayi Suka ce Aunty Balaraba daga yau,tun daga wannan Rana kaf abokan Ahmad sai dai sucewa Aamna Aunty Balaraba ita Kuma amsawa takeyi.
Washe gari da dare Aamna ta kawowa Ahmad Abinci ganin baici komai ba tun Rana,Ashe hakan data Yi shi haushinta yaji ya tsaneta ya gaji da takura Masa da take yi Kawai ya dauki abincin ya watsa Mata a jikinta stew din Allah yasa ba zafi ta Bata Mata riga,Taji Matukar haushi har ta fusata Tace barin gidan zata Yi ,da sauri ta dakko mayafinta,Yana ganin Haka sai murna ta kamashi,Aamna sai ta ganshi har murmushi yakeyi sai ta fasa tafiyar ta dawo gabansa Tace ranka ya Dade zanje na siyo Abu a shago tayi waje,ransa yayi bakikirin sabo da bacin rai tashi yayi ya tafi wajen Me Gadi Musa,Musa Yana Zaune a Bench Yana waya da matarsa Ahmad ya zauna a Bench din.

Musa cikin wayarsa yace da matarsa na Baki Ruhina gaba Daya,da sauri Ahmad ya kalli Musa yace baka da hankali idan ka Bata Ruhinka Kai Kuma ya zaka Yi da rayuwarka kenan ka bata Ruhin ka mutu kenan? Musa ya dagawa Ahmad Hannu Wai yayi shuru yaci gaba da cewa Ni gaba Daya na Baki duniyar Nan gaba daya ma Uwar gida na,Baki Ahmad ya bude da bala’i irin na Yan kwaya yace Kai…wai…to nufinka idan ka Bata Duniya mu da sauran mutane da muke ciki mu tafi Ina a Ina zamu zauna?ko sama ta Daya zamu koma,Musa ya kashe wayar yace a’a ikon Allah Oga Ni Matukar zata ji Dadi ku tafi sama ta goma Mana,Ahmad yace Kai Musa wallahi Indai zaka ci gaba da wannan furucin na soyayya wani ka Bata Duniya wallahi sai na koreka a aiki,akan me Dan wulakanci Muna zaman mu lafiya cikin duniya kace wani kayiwa wata banzar matarka kyautar ta,Baki Musa ya Bude sai Kuma ya tuna Ogan nasa Dan giya ne kwakwalwarsa da motsi Kuma Bai taba soyayya ba shi yasa. Musa yayi Dariya yace Allah huci zuciyarka Oga ai duk kalaman soyayya ne ai duk abin karya ce,Kenan duk karya kake mata? Ahmad ya tambaya Musa yace ai Dan aji Dadi ne,yace kenan soyayyar da ake fada duk karya ce? Musa yace duk ita ake zugawa juna,Nima fa Oga cewa tayi ta bani zuciyarta,Baki Ahmad ya bude yace to yau duk sai kunci ubanku wallahi maza tashi ka dakko Cooler dole ta Ciro zuciyarta ta baka ka saka a Cooler,Musa Dariya ta Gama Kama shi,Yace zaka Yi Dariya da kyau yau sai naga ta inda zaka Ciro Ruhinka Dan Ubanka,Kai ba mala’ikan daukan Rai ba komai ba kace wani ka Bata ranka Dan Ubanka gashi kana motsi kana numfashi yau sai ka Bata ka mutu yanzun Nan,Musa ya sake kecewa da dariya shi Ahmad Bai San soyayya ba,yace tsuguna yau sai ka kinkimi duniya a kanka Baki Daya ka Kai mata har kauyenku sannan bayan ka Kai Mata mu Kuma kazo kasan inda zaka Kai mu,Musa yace kayi Hakuri Oga na fasa Bata wallahi bazan Bata ba na Kuma fasa karbar zuciyar Tata,Ahmad yace Yan iskan banza da ka Bata mu gani mana,Kun zauna Kuna biyewa Mata ya Mike ya fice daga gidan. Aamna zaune take suna waya da Mummy,Mummy Tace Aamna me kike so a duniya ki fada min ko mene Zan Baki,Aamna Tace Mummy da gaske ko mene?Mummy Tace kwarai ai tunda kika iya jure Zama da Dana Ahmad a wannan halin ba abinda bazan Miki ba,Aamna Tace dama Ni burina idan na samu kudi naje Hotel na kama daki nayi kwana Uku Ina Shan ac,azo a gyara min room nayi order abinci naci nayi bacci,sannan Buri na na biyu idan samu kudi nayi wanka da ruwa Eva ko Swan,sannan naci abinci na wanke Hannu na da ruwan Roba,Dariya Mummy tayi Tace Anya kuwa Aamna kin Kai 25yrs ko kema kin fara Shan kwayar ne?Dariya Aamna tayi Tace Allah Mummy,to shike Nan ba yanzu ba ki Bari sai Nan gaba cewar Mummy sannan ta kashe wayar. Da dare Ahmad zaune yake a bedroom dinsa Yana Danna System Aamna ta shiga dauke da tiren Abinci ta Ajiye Masa,Tsaki Yaja da masifa yace ce Miki akayi yunwa nake ji? Bazan ci ba ki dauke abinki tun kafin nayi fatali da shi,Wayarsa ce ta shiga Kara yaja tsaki sannan ya dauka yaga Humaira ce kanwarsa dagawa yayi,yace sis ya akayi ne Mene ne Zaki dameni? Yaya dama gobe zanzo na kawo maka Ziyara,Fuska ya Bata yace ke karki zo min Ni Kun dameni kije gidan Saddeeq Mana sai Dole waje na Zaki zo wannan Candy da kika Yi ai ta zame min masifa tunda damuna zakiyi Dan Allah ki fadawa Daddy ya saka ki a University da wuri Haba,Dariya Humaira tayi ta Shiga rokonsa Dan Allah Yaya so nake fa nazo na ganka please…..Shuru yayi mata,Tace Yaya Dan Allah zanzo kaji….ke mayya karki lashe ni ki tsotse min bargo yau she Zaki zo? Kwana biyu ko Uku Kuma Zaki Yi,Tace to Gobe Yaya da wuri zan bi flight sai kazo ka daukeni a Airport,Alright sai kinzo murna Humaira ke Yi harda godiya,Aamna tana jinsu ta dauke Abincin tayi gaba,me Gadi ta kaiwa gaba Daya.

Washe gari 2pm Humaira ta sauka,Aamna gani tayi ya Sha wanka cikin kananan Kaya wasu masu kyau ya fito ya hau wani machine dinsa Irin na Yan achaba Quilin ya tafi Airport,Humaira ta ganshi a machine ita Bata taba Hawa machine ba,ta Rungume shi tana murna ya janye jikinsa Yana dariya yace sis bana son wannan haukan kin girma ku Yan Lagos Baku da tarbiyya,Dariya tayi Tace Kai Yaya Kai fa yanzu muharramina nane fa,ku dai Kawai Kun dauki aladun turawa ya furta tare da rike Mata Hannu yace Oya hau mu tafi,ta kalli machine Tace Yaya kasan fa ban Iya hawa machine ba Kuma ai ya kamata ka aro mota ko ta abokai ce ka dauke Ni,Wanda Basu da motar kuma fa gasu Nan Ni ban Iya aro ba idan Zaki hau ki hau ko wallahi na tafi na barki iskancin banza Kawai ya fara bala’i,Humaira tayi Dariya Tace Kai Yaya ta ja kitson calabarsa tace da a Kano ne da tuni Yan Hisba sun Kamaka,Yace su ma Wanda suka Raina suke wa.

Daukanta yayi tare da daura ta a saman machine din,Jakarta Kuma ya daura a gabansa ya figi machine Kamar zai tashi sama Haka yake fyalla uban gudu da Humaira tana ta dariya ita Dariya yake Bata. Aamna tana cin abinci a Dining suka shugo,Humaira ta taho da gudu zata tafi wajen Aamna Tace laaa Auntynmu…Auntynmu…da sauri Ahmad ya cafke ta yace ke wace Auntynki? Baza kije wajenta ba wajena kika zo ko wajenta? Humaira tayi Shuru yace muje sama,Murmushi Aamna tayi tace Barka da zuwa kanwata,Humaira ta dago Mata Hannu zanzo mu gaisa Aunty…..fisgar Hannunta Ahmad yayi Suka tafi sama Yana Hararar Aamna,Aamna Dariya tayi Kawai duk tayi laushi ta nutsu sabo da Duniya garata takeyi. Hana Humaira Fitowa yayi sai da ya tabbatar ta shiga wanka sannan ya fita ya Mata take Away na abinci Wai baza taci na Aamna ba,Yana dawowa ya Iske Aamna da Humaira suna ta Hira suna dariya,Muzurai ya fara Yi ya karaso tare da fisgo hannun Humaira yace wa yace ki kula min kanwata ko kanwarki ce? Aamna tayi Masa shuru kawai, a palon Suka zauna Humaira gudun masifarsa yasa taci abincin nasa ta koshi,Humaira Tace Yaya yanzu a machine kake yawo?gaskiya Daddy Bai kyauta ba,Ke share wannan zancen Ni nafi Jin dadin ma machine Dina,Aamna ya kalla yace Baban wasu kuwa ko Tyre Bai da ita bare mota,Aamna Dariya Kawai tayi,Humaira tana ta Mata magana da Ido,itama Aamna tana maida Mata da Hannu da ido,Ahmad idonsu Kawai yake gani Yana motsi, tashi yayi Kawai ya fice abinsa,Nan Humaira Suka zauna da Aamna suna ta Hira abinsu. Tunda Humaira tazo Aamna ta samu kawa har fita kasuwa sukeyi da yawo Ahmad ya kyalesu harkarsa yake yi,Haka shima Humaira ta takura Masa Wai sai ya kaita yawo a Machine,da ya fita da ita yawo yau suna ta zagawa duk Wanda ya kalli Humaira sai yayi Masa bala’i. Wani guy ya ga Humaira kyakyawa ta birgeshi suna tsaye da Ahmad a jikin machine Yana ce Mata Sis na fada Miki kina saka Nikaf tunda ku Kuna kula da Addini Kawai ku rungumi Islama hannu biyu kina saka Hijab da Nikaf kin fa girma tam,I’m warning you Sis,Humaira tana ta dariya shima ya kalleta ya dinga dariya a jere a jere irin ta Yan Kwaya ba kakkautawa,Humaira Tace Yaya kaima kana ganin kyanka Mata sai kallonka sukeyi,Ke dalla rabu da su sun kalle Ni a banza ai duk wacce ta Soni to Allah ya jarabce ta sabo da ban Dace da a so ni ba sis,Humaira taji tausayinsa kwalla ta cika Mata Ido Tace Yaya Wai waye ya koya maka shaye shaye ne Wai? Handkerchief din Dake hannunsa ya zabga Mata a Fuska yace muje gida Yana Juyawa yaga saurayin Nan ya kafe Humaira da kallo,a fusace ya nufi wajen saurayin yace zaka lalata min kanwa Dan uwarka me kake kallonta kana ayyanawa a ranka? Kana Nan kana ta kallonta kana ayyana wani Abu ko ya Kai Hannu zai chakumo shi Humaira ta rike shi tana bashi Hakuri Dan Allah Yaya ka barshi mu tafi,Fisgewa yayi ya dauki wani karfe da ya gani a kasa zai buga masa,Humaira tace ka gudu wlh,Matashin Nan ya arce a tamanin Dan yaga Ahmad ya birkice lokaci Daya ya haukace,Masifarsa ya maida Kan Humaira yace gobe Zaki tafi,Kuka ta saki Tace Allah Yaya Ni sai nayi sati Daya,Zan mareki gobe ki shirya ai kinyi 3days tafiya dole hau machine mu koma gida. Tunda suka tafi yake masifa Yar wa na lalata da Za’a lalata min kanwa,Bana kallon Yar kowa shine za a kalli kanwata,ko Wannan Yarinyar da akace matata bana kallonta shine wani zaizo ya fara ayyana wani Abu a ransa a Kan kanwata. Humaira da suka koma gida Bayan ya fita ta Bawa Aamna labari,Aamna Tace kwaya ce fa ke sashi wannan zafin zuciyar,Humaira Tace Aunty kina kokari Allah ya bada ladan Ibada,gashi gobe yace dole Zan koma ya zanyi, kiyi Hakuri ki tafi kawai,ai dole cewar Humaira,Haka kuwa washe gari 11pm ya Kai Humaira Airport ta koma lagos. Yau ma kamar ko yaushe Jibson da sauran abokan Ahmad suna Palo suna kallon ball sai ga Siyama ta shigo,Aamna Tana kitchen tana girki ita tana mamakin yanda Siyama ke sintiri a gidanta,Fitowa tayi suka gaisa ta samu wuri ta zauna Aamna ta koma kitchen abinta,Jibson ne ya Sosa gashinsa me uban yawa Wanda ya Gama kone shi ya dawo fari irin na Yan Ball,yace gashin Nan nawa ya kamata na Dan rage shi naji kaikayi yake min,Ahmad ya kalli Siyama Fuska ba Annuri yace ke Sosa Masa gashinsa Mene amfaninki,Siyama ta Bude Baki kamar zata Yi kuka Tace Ni wallahi ba Yar Iska bace,Tsawa ya daka Mata Sosa Masa karki Bari na tashi,Siyama ta Mike jiki na rawa ta tsaya a Bayan Jibson ta nutsa yatsunta a sumarsa tana Sosa Masa,Ido ya lumshe yace shi yasa nake sonka Sarkin mu,Kaji wani Dadi da taushin Hannu,Aamna ce ta fito mamaki ya kasheta,Siyama ta kalleta Tace mijikin ne yace sai nayi ta karasa da Hawaye,Aamna Tace ke Kuma ga banza ko dalla cire hannunki,Ahmad yace tana cirewa ke Zaki Sosa Masa,wallahi baka Isa ba Kai din banza ta janye Siyama Tace na tafi gida,Siyama ta fice da sauri ta tafi,Jibson yace Aunty Balaraba me yasa kike Mana bakin ciki ne? Respect your self Jibson Ogan naku ma Bai Isa ba bare ku ta ja tsaki ta haura sama. Washe gari Ahmad wani wankan Sugar ya dauka ya fito Yana wani tattala kafafu Yana Bouncing ga Uwar Gadara Mashkoor ne yazo da machine dinsa Quiln ya dauke shi tsabar basa jin Magana Ahmad baya ya juya ya hau machine ta baya sun hada baya da mashkoor Yana kallon baya shima me tukawa ya kalli gaba,Headphone ne a kunnensa Yana Jin wakar Shaggy da Sean Paul reggae music,Wani uban gudu Suka tsinkawa a Machine lokacin Aamna taje gidan Zuhra a Hanya suka hadu Mashkoor yace ai sai Aunty da karfi,Da kallo ta bi Ahmad irin zaman tijarar da yayi,Zaginta yayi da Hannu ganin tana kallonsa,Kanta ta dauke ta shiga Napep abin ma Dariya ya Bata. Su kuwa Basu tsaya ko Ina ba sai a Bank,ya Shiga ciki masu bin layi kowa Matsawa yayi ya Basu waje Ganin rigima suke Nema,Wani Dan matashi waya ya dauka Yana kusa da Ahmad Yana waya da budurwarsa kasa kasa yace Baby zuciyata kullum Dake take bugawa,da ace Ana bude zuciya Dana Bude Miki Kinga tawa yanda sonki yake dankare a ciki,Ahmad Yana ji ya juyo da masifa yace to Dan Uwarka sai kaje Likita ya yanka maka kirnjin a gabanta ta gani,Wai kowa sai karya a gidan Uwar wa zuciyarka take bugawa da ita a ciki mutum ne zai Shiga zuciyar mutum ta buga da shi,Ina zuciya Yar karama zata dauki nauyin mutum zaka wani ce da ita take bugawa a ciki,da karfi yake magana ai kowa hankalinsa ya dawo kansu sai Dariya akeyi wani tsoho yace yaro kayi gaskiya wallahi wannan karyar ce ta shigo yanzu ta kalaman soyayya. Tsaki Ahmad Yaja ya fitar da kudi masu yawa, wani yace bawan Allah ka Adana kudin Nan Kar ka hadu da Yan Iskan gari,Mashkoor Yana gefe yace ai mune da kanmu baka gani bane mune ai Yan iskan da kanmu a Nan,wa ya Isa ya zare Mana ido,aka Yi Shuru matar tana irgawa Ahmad kudi tana ajiyewa ya galla Mata Harara yace ke ni fa bana son Daudu Yar Daudu idan Baki iya aikinki ba wallahi na Kai kararki a koreki banza,Wai ke ma’aikaciyar Bank harda wani sa glass da Suit ke a dole kina samun salary,Yan Yara daku Kuna rainawa mutane wayo kuka sake kwanan bank Dinku tattalin arzikinsa zai durkushe mu daina Ajiyar kudi,Duk ma’aikatan sun San Ahmad Yana zuwa Yana musu tijara shi yasa Yana zuwa suke sallamarsa ya tafi,suna gamawa Mashkoor yayi wani Bouncing Suka juya Ahmad yace My man oya muje… muje….Yana wani Gadara,Wandonsa Daya sabulo ya danja kadan,Zasu fita kenan sai ga Aamna ta shigo itama zata ajiye kudi a bank,Ahmad ya kalleta Kamar ba matarsa zata wuce su ya riko Hannunta tare da sa damtsenta ya sakalo wuyanta yayi masifar kunyatata a mutane sai ayi Mata kallon karuwa,Fisgewa tayi ya dauke cak tare da Sabata a kafada yace Muje kudin cefanen kika taho ajiyewa bank Zaki tara? sabo da kar mutane suyi Mata kallon karuwa Tace Dan Allah ka ajiyeni Ina matarka Wai kullum sai kaci Zali na,kaje gida your food is ready, Ni ka ajiyeni wallahi,Ana kallo tana wutsil wutsil yayi waje da ita,Wasu suna cewa kanwarsa ce sabo da suna yanayin Kama sosai,wasu Kuma suce da gaske matarsa ce,wasu suce ko karuwarsu ce,Wani yace ai kuwa wannan zata Sha wahalar Zama da wannan bakin kadarar,wanne ubane Yana gani ya bawa wannan auren yarsa oho. Wajen Machine suka fito,Kamar Yana da hankali shi ya fara Hawa machine din sannan ya Mata Tsawa yace hau,Haka ta hau bayansa Mashkoor ya fige su kamar zai tashi sama,ya dinga kwanto a titi Yana ratsa motoci sai ihu sukeyi Aamna tsoro ya kamata ta kankame Ahmad yace wallahi idan Baki sake Ni ba sai na jefo ki a tsakiyar kwalta,kin sakinsa tayi har suka kaita bakin gate yace sauka,ta sauka yace kina Wasa da Mummy ta kawoki Nan kina wani yawo anyhow,Aamna tayi banza da shi ta shiga gida,Bai Dade ba ya dawo ya Iske ta baje saman Kujera tana bacci,ruwa ya ebo a kitchen ya sheka Mata a Fuska ta tashi a firgice,Harara ta balla Masa ta Mike ta wuce Bedroom dinta tana saka ranar da zata bar gidansa domin ta gaji. Garin Lagos Unguwar Masu hanu da shuni Mummy tana zaune Tare da Humaira a wani gida na ubansu Wanda idan ka kalli gidan ka kallo gidan Ahmad duk kyansa sai ka ganshi gidan talakawa,Humaira ce ta dauki waya Tace Mummy Bari na Kira Yaya naji,Ahmad ta shiga Kira Yana ganin Sis ya daga da sauri tare da furta sweety,Dariya Humaira tayi Tace Yayana ya kake yace Ina lafiya sis ya school,ai nayi Candy Wai ka manta na fada maka Yaya? congrat…Congrat Sis,Yaya Ina matarka? Zamuyi fada fa Ni nasan wata ne Kawai dai nasan Wacce Mummy ke so karki dameni Zan kashe wayata,Sorry Yaya ke ba Wani Yaya kauyanci ne karki Dora min tsufa da wuri wani Yaya,ki kirani Ahmad Dina sak ko King,Mene wani Yaya,ai girmamawa ne Yaya,bana son wani girmamawar mutane a wajena ke dalla Ware kiit ya kashe wayarsa Yana tsaki,Mummy ta kalli Humaira tace ai halin Ahmad sai shi na rasa inda ya gado halin Nan,Allah ya kyauta. Faratan Ahmad sun Kara tsayi sosai,Aamna tana zaune a Palo Yana kwance ta juyo ta kalle shi,Fuska ya Murtuke,Kallonsa ta sake Yi tana kasa a zaune ta jingina da kujerar da yake kwance,kanta ya dafe tare da Danna kanta kasa,Kara ta saki ya fisge dankwalin Atamfarta ya zabga Mata duka dashi,layun Dake kanta ya kalla ya saki Dariya yace nasan na fiki daraja a wajen Allah duk Iskanci na,ke shirka kikeyi yarinya duk Sallar da kike Yi ba a karba,munafukar banza kullum Sallah da karatun Qur’ani Ashe wurin bokaye kike zuwa,shi yasa Allah ya hadaki aure Dani ya daura Miki kaddarar Zama da me cin ubanki,Allah ne yasan irin Barnar da kike yi,Ni duk Iskanci na bana zuwa wajen boka,bana daura guru da Laya,Yan Iska irinku ne masu yiwa Miji Miya da jinjin Haila,fada min ke wanne kikeyi? Aamna Tace Ni wallahi bana zuwa wajen malam,karya kike munafuka,Ni nasan ba Banza Mummy ta auro min ke ba,kin shiga Uku kuwa ke da Jin dadi sai dai ki gani a makwafta,Aamna tayi Mukus ta Mike tare da cire layun gaba Daya ta yaye Hannunta ta Ware gurunta,ta daga rigarta ta zaro na Hips,Baki Ahmad ya bude yace kin Shiga uku,Uku ma sau dubu kika shiga,Ni ba ruwana da tsafinki ki maida abinki kece Zaki ga ba daidai ba a duniya,Zuciyarki ba Allah oh a Haka Shuru Shuru Dake sai daukan carbi da sallah,Ana karatun Qur’ani Ashe duk bana tsoron Allah bane,asubar fari za a jiyo muryarki har makwafta ya makale Murya tare da gwada Muryar Aamna yanda take karatu Wai Allazikhalakhal samawati wal’ard…..Ashe bana tsoron Allah bane wallahi sai Allah ya tambayeki. Aamna tayi Mukus yace ai dole kiyi Shuru ki kalleni kice me? Watarana sai Allah ya Toni asirinki.

Dariya Aamna take Yi ta fara warware layun a gabansa da gurun,ya kalli takardar me Rubutu yace ga harafin A’lif da Hya’un can Wato Sunana kenan Ahmad gashi can na gani,Aamna ta tattara ta kone komai,yace a banza yarinya Yar bori mutuniyar banza,Harararsa tayi ya Mike ya bita zai daketa tayi daki da gudu Yace ki dake Ni ki hanani kuka ki min asiri in gani da Ido na ki dawo Kuma ki harareni Ni ban harareki ba sai ke,Zaki fito ne.

Washe gari Aamna gajiya tayi ta fito lokacin zai fita tace Yau zaka nemeni ka rasa a gidanka yau Zan tafi gidan ubana,wani farin ciki ya Kama Ahmad yace Dan Allah da gaske kikeyi? Aamna Tace da gaske yau a gidan ubana Zan kwana,wani murmushi ya saki yace gaskiya ban taba sanin kina da kirki ba sai yau,Sabo da Haka yau dole Nima na gwangwaje ki,fada min me kike so? Aamna ta turo Baki ta samu waje,yace ai yau ko me kike so Zan miki,Aamna ta Kama shagwaba Tace koma mene ka bani kyautar Ina so,Ido ya zaro Mata wasu farare tas sai da ta tsorata Yace Gaskiya Zan fada Miki ke Yar Albarka ce babarki ta iya haihuwar Yar halak Haka nake so,yanda kika faranta min yau ace ban Miki kyauta ba nayi asara bani da amfani Kawai na mutu yanzu,Dariya ta Kama Aamna duk akan Tace zata bar Masa gida shine yake wannan murna Haka,wannan kiyayya wacce iri ce,Tunaninta ya katse Mata yace shirya kizo mu tafi na kaiki Shopping ki zabi abinda kike so na ban kwana,Dan Allah Kuma idan kin tafi karki dawo har abada kinji,Aamna Tace to,yace ko Mummy Tace kice a’a ke ba ‘yarta bace ta juya Humaira Yarta data haifa Amma ba ke ba,Aamna Tace to,yace Ina jiranki,Da gudu taje sama ta canja wata Arabian gown Dark green me adon black ta Sha kyau ta fito.

Machine dinsa ya gyara ta hau ya fisgeta Suka tafi sai wani katafaren Mall,tare suka shiga yace Ina jiranki zabi duk abinda ya miki,Aamna Bata zabi komai ba ta wuce Bangaren Gold ta zabi wata sarka me kyau da zobenta da Dankunne,yace shike Nan abinda kike so? Tace ae,Kai ya girgiza yace to dauka,Haka ta dauka yaje ya biya kudin Suka tafi,ya maidata gida zai fita Tace to saka min da Hannunka kaga anjima Zan tafi,yace ai yau ba abinda Zaki ce banyi ba tunda Zaki bar rayuwata na huta kawo,Mika Masa tayi ya saka Mata sarkar da kansa da dankunnen,Yatsanta ta Mika Masa ya sa Mata zoben,yace Nice one, karfe Nawa Zaki tafi? Aamna Tace 6pm yace Good,ya Mike zai fita Yana ta murna yau zai rabu da Kaya ya huta,Aamna Tace Idan ka dawo sai na tafi,yace to ai da wuri kuwa Zan dawo ya fita Yana ta murna Kamar an Masa albishir da Aljanna,Tun kafin 6pm ya dawo gidan ya shigo Yana wakar Bob merly Yana Bappalo Soldier……..Ye…yiye….yiye…..Yee…Yee….yiye…

Sharhi fans Dan Allah.

AsmaBaffa
10/26/21, 8:52 AM – A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA AAMNA🌵🌵Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

About Mr Hausa Ebooks 1438 Articles
The Power of pen