1060 Views

DUNIYA TA AMNA Page 1 – 20 by Asma Baffa

 DUNIYA TA AMNA Page 1 – 20 by Asma Baffa

Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 16 Dec, 2022
Upload Time 10:15 pm
Author

Writer Group Unknown / NIL
Novel Genre

Comment No Comments

DUNIYA TA AMNA Page 1 – 20 by Asma Baffa

Godiya

BISMILLAH

INA MATUKAR GODIYA GA ALLAH DA YA BANI RAI DA LAFIYA DA KUMA IKON RUBUTA SABON NOVEL DIN NAN DUNIYATA.

MAKARANTA NOVELS DINA DA BIBIYATA INA MUKU GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI,ALLAH YASA WANNAN NOVEL YA FADAKAR YA KUMA NISHADANTAR,KAMAR YANDA MUKA FARA LAFIYA ALLAH YASA MU GAMA LAFIYA AMEEN.

KAMAR YANDA KUKA SANI NOVELS DINA NISHADI YAFI YAWA CIKI,INA KUMA GODIYA DA KUKE KARANTAWA HAR MUTUM YA SA KUDI YA SIYA WANNAN YAFI KOMAI DADI,INA GODIYA ALLAH YA BAR KAUNA.

Page 1-5

FREE PAGE

LITTAFAN MARUBUCIYAR

GASKIYA CE
MARAICIN RAHMA
MAAIKACIYAR GOMNATI
CIRANIN AMANA
DUK INDA TA FADI
KAMARSU CE DAYA
KASUWANCI NA
JIN DADI SABO
HADIN KAI
ME MAGANI
TUBABBIYA

NA KUDI DANA RUBUTA

RASHIN SA’A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDUAR KAWA
GIDAN GWAURO/DAN NAZIA
DANGIN RABI
DUNIYA TA…….

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DIN DUNIYATA DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER
0175487861 ASMAU GARBA MUHAMMAD, GTBANK.

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER TA
08033933642

‘YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Page din farko naku ne Fans Dina duk wacce ke cikin groups Dina.

Zaune suke a wani katafaren Palo na Alfarma,Palo Wanda yaji furniture Dan gaske,duk Wanda ya Shiga wannan Palo bazai so Fitowa ba,wani uban kamshi da sanyi ne ke tashi,Family Guda su Shida rakacal sai ta bakwan Yar karamar yarinya tana Wasa a kasa,Kidan Bob merly ne ka tashi a wata katuwar plasma tv kamar ka dakko mutum,gaba Daya sunyi Shuru duk Basu cikin nishadi,Ahmad Dake narke cikin luntsumemeyar kujera shine yake kada Kai cikin maye da kwaya da gani kasan Kansa ba kalau ba,sai bin wakar yakeyi da bakinsa,gashi babu Wanda ya Isa yace ya kashe ko ya daina,baya Jin Maganar kowa,Mummy dattijuya itace ta nisa fuskarta dauke da damuwa Tace Haba Ahmad Kaine fa babban Danmu Amma ka duba yanda ka maida kanka Completely Useless har mun gaji da Dake Hanya tun daga Lagos muna zuwa Nan Kaduna wajenka akan magana Daya kaki ji,tunda hakane yau da Yamma zamu koma,Wani farinciki ne ya bayyana a kyakyawar Fuskarsa,ya Mike tsaye yace wow Mama the Mama,Allah yau zaku tafi?yawwa Haka nake so sabo da na samu freedom,yau kwananku biyu Kun dameni dama,Shut up Daddy ya Furta banzan yaro marar tarbiyya,ai Kai dama Daddy nasan baka so na,Zama ya sake Yi Yana bin wakar Bob merly,sai Chanel din Suka cire wakar aka Sako tallan Wani body lotion. Wata Uwar Tsawa Ahmad ya saki tare da nuna Tv da yatsa cikin mayensa na giya da kwaya ya kalli dalleliyar Budurwar da aka Nuno tana tallan Body lotion a tv yace Kai…dalla ku matsa can Kar ku kawo Mana Harkar Daudu anan,mu ba Daudu Muka zo gani ba Ana Harkar arziki zaku zo Mana da Mata Yan Daudu,ke dalla ja can, Dan uwarki a Nan Nigeria muna da man shafawar mu Habiba yawwa,Muna da Habiba Muna shafawa Muna Kara Baki wuluk abin mu yafi Mana,Dariya ya Bawa duka Yan palon har Daddy ya kalle shi yace Ahmad Kai da kake fari Kal jinin Larabawa Kuma a gidan uban wa kake shafa wannan Man,sannan ce maka aka Yi Habiba karamin company ne? Mummy Tace Allah ya shirya min kai,Baki ya turo tare da gyara Ass down dinsa da yayi da wani Creazy jean. Wata Yar kyakyawar jar mota ce Honda tayi parking a bakin wani Restaurant,Yar kyakyawar Budurwar ta fito Hannunta dauke da Handkerchief tana goge zufa, Hannayenta ta Shiga tafawa tana Waka Sannu da Zuwa…..Sannu….da zuwa kekashashe na,Oyoyo Dan Kedararre na…..Oyoyo Karmashashe na,Barka da dawowa Dan tsomalalle na,My Karmash I miss you,Wani saurayi ne matashi mugun siriri wuyansa kamar murkin laima,Kugunsa Kamar zai tsinke,Baki ne wuluk Kamar Iska zata dauke shi Haka ya fito daga jar motarsa Yana wani basarwa a dole babban yaro,Bakinsa ya Bude da Niyyar magana Yan hakoransa manya na gaba Guda hudu Suka yo waje,Yana kallon Budurwar yace naga Alama Baki da tarbiyya,Kamar Ni saurayinki Ina sonki kina so na Amma kina ci min Fuska,glass dinsa ya zare a Fuskarsa ya kalle ta sama da kasa yace Yar talakawa Dake matsiyaciya ki kalle Ni kina wani ce min Oyoyo Karmashashenki? Baki da Manner? An fada Miki badan so ba Zan iya tsayawa da Yar matsiyata irinki? Ki kalle Ni nafi karfinki ta ko Ina,Yar budurwar kyakyawar gaske fara Tace Kayi Hakuri Wasa nake maka wallahi badan naci fuskarka na fada ba,Tsawa ya daka Mata yace dalla ja can dama iyayenki Basu Miki tarbiyya ba,Baki da hankali dai,Ran Budurwar ya baci tace kaga Malam na maka tauna na maka hadiya baka gani ba,to naji bani da tarbiyyar sai kace Iyayenka suzo su Yi min,daga na maka Wasa Kai baka San wasan masoya ba,wannan ne wasan a gidan uban wa ya Zama Wasa? Nan take Budurwar ta bashi amsa a gidan Ubanka Kamalu,Baki Bude ya kalle ta yace Aamna a gidan wa kika ce? Wacce aka Kira da Aamna ta sake cewa a gidan Ubanka nace Kamalu,Kamalu ransa ya dugunzuma yace it’s over between me and you,bani ba ke,Aamna Tace ae naji Nima bani ba Kai tsotsatsen banza,me zanci da Kai dama idan anyi auren ma Banda kashinka ya dinga suka na me zanyi,Dana kwanta a jikinka gwara na hau katifar fasasun kwalaba,Kuma da na aureka ka min kiss da bakinka me hakora Kamar kacar Keke gwara na tsotsi Kusa me tsatsa,Yace irin na Ubanki ne ai hakoran,naji ta furta tare da koma cikin Restaurant taci gaba da aikinta.

Wajen masu girkin taje ta faki idonsu ta saci yankan nama Uku ta watsa a Jakarta ta fito ta baya can ta cinye Naman sannan ta dawo ciki ta Iske Fried rice an Gama an kaiwa wani yaci ya bar Rabi kadan ma ya ci,Aamna da sauri tazo Wajensa Tace Alhaji ka Gama Zan gyara wajen 2pm yanzu resturant zai cika,kafin yayi magana ta sunkuce abincin ta dauke Masa lemon da ko budewa baiyi ba ta Sha kwana tayi ciki,Alhaji ya saki Baki Yana cewa ke ke ke ban Gama ba Amma Ina Aamna tuni Taki ma kula shi,tana zuwa Tace Alhaji ya koshi ta zauna ta lashe abincin ta Balle lemon ta shanye sannan ta fito fes da ita da mamakinta sai taga Alhajin Bai tafi ba,da sauri ta koma Wajensa Tace Alhaji wani abincin Za’a kawo maka ne? Alhaji ya kalleta yace ke Amma wacce iri ce bance na koshi ba kin dauke abinci lemon ma Dan wulakanci ko Bude shi banyi ba kin dauke Ina ta kiranka bakya ji? Aamna Tace eyya Allah sarki kayi Hakuri matsalar kunne gareni banji ba Kuma gashi na zuba komai cikin shara bare na dawo maka da shi,Harara ya balla Mata tare da zube wani kudin yace kawo min wani abincin,da murna ta dauka dama Bata koshi ba,taje ta hadowa Alhaji duk abinda ya bukata,wata white rice with salat ga kwai da kaza,ga lemo,Aamna tunda taga Haka take ta faman zaga wajen da mopper a Hannunta Wai a dole gyara takeyi,tana ta faman goge goge a saitin Alhaji,Alhaji yace ke kin dameni da goge goge ga customers can sunzo kije Mana Haba wannan wacce irin Maaikaciya aka dauka Haka idan bakya so sai na daina zuwa cin abinci a wajenku aikin banza,Aamna tayi murmushi tare da gyara pcap dinta Tace afwan Alhaji ta juya ta tafi Amma sai ta labe a bayan wani lungu daga ciki tana ta kallon Alhaji tana so yayi ya Gama ta samu rabonta,Siyama ce kawarta taje ta sallami wasu customers din Aamna tana labe tana zalama wajen Alhaji,Siyama tayi Dariya tare da kallon Aamna tana labe labe Tace Allah ya shirye ki,Alhaji kadan yaci ya bar komai ya tafi kafin ya Gama fita tuni Aamna ta kwashe komai tayi ciki,Nan ma ta zauna ta cinye ta koshi sannan Tace saura na dare kafin na tafi gida,dole na dinga kiba Ina yin kyau,Aiki a restaurant ai Dadi gare shi ko ba komai Zan cika tumbi na.

Dattijo ne fari me gemu sosai Wanda shi kanshi gemun ka kalla kasan Dattijon ya tsufa domin yayi fari,da gudu gudu sauri sauri ya shigo gidansa inda yake wani mugun Rubabben gida,Gida ne na Haya Kuma gidan Talauci,da gani ba sai an fada maka ba Dattijon Talauci ya Gama da shi,cikin Gida ya Fado Yana masifa tare da furta me zangani Aishatu?me zangani yau,wacce ya Kira da Aishatu ta kalle shi shekeke tare da balla Masa Harara Tace mene? Gashi can kina karar min da kudi,kina min asarar Duniya da Almubanzanranta,yanzu ki duba sabo da Allah tunda na taho Ina kallon kwalabati kumfar Omo tana ta bin ruwa tana ficewa Ful…ful,Yanzu a zamanin Nan kumfa ka gani a kwata kasan kudinka ake kashewa,kina ta kashe min kudi kina abinda kika ga dama,Ga jarabar karar da Ashana kiyi ta kyastata sai ta Kare,Takaici na yanda kike wanki ko wanke wanke sai asarar Omon bala’i,to wallahi da sake baza ta yuwu ba,kullum Ina fama a hanyar sakateriya wajen Dan aiki na Wanda masinja ne ni nayi retired Ina nemowa Ana wulakantawa bazai yuwu ba,Daga yau ko mangyada ne za a zuba a abinci to kowa cokali Daya Daya babu kari aikin banza,Wata buta yasa kafa tare da yin fatali da ita Yana zare Ido yace Ina Aamna sakarai da Sweety Zuhra?Aishatu banza tayi Masa ta ci gaba da aikinta,yace Aamna har yau ba labarin Mijin Aure?

Aishatu tayi Shuru,Dattijon yace na gaji da yahudanci wallahi da nasan Haka ne Aamna ko secondary baza tayi ba,Dan fa Kawai Ina tunawa Amana ce a wajen mu, Nima ban San ya akayi basirata ta toshe na biya Mata har tayi wani HND sabo da asara,ai karatun mace Bai da amfani,amfanin mace aure da girki tayi ta zazzago Haihuwa,yarinya ta Zama bayahudiya abinda taga Dama shi takeyi,Nima jarabata ce tasa Rana tsaka Ina Kauye tare daku cikin sutura na dawo damu Birni na Kama haya,da Muna Kauye da tuni hankalinmu kwance,da duk wannan karyar Bamu shige ta ba,Aishatu Tace ai sai Dana fada maka kaki ji Aamna tana secondary a Kauye Ss3 ka kwaso mu Muka dawo birni gashi yanzu ta waye Taki aure muna ta ciyar da ita a banza ,wallahi baza ta Sabu ba,gidana ya koma na yahudu bazai yuwu ba,ai Birni na dawo ne Kawai Dan na samu sana’a me kyau to gashi hakan Bata samu ba,Dan pension Nawa ma baya Isa Nawa yake Ina abin,kullum sai talauci ne ke karuwa,birni kwai masifa Ni tunda nazo banga wayewar ba,ban wani waye ba,Aishatu Tace yo shekarar mu Nawa a Birnin kwata kwata shekara hudu fa rak Ina wani wayewa Aamna da Zuhra ne Kawai Suka Dan waye Dake su Yara ne,Dattijon yace ke tafi can Aamna Ina ta waye ai gwara Zuhra,Amma Aamna kina gani magana ma Bata iya ba ta Kauye takeyi duk abinda yazo bakinta dankarawa mutum takeyi Dan tayi makaranta ne ma take Dan canjawa,ni dai na fada Miki a kiyaye asarar Omo yawwa ya furta tare da ficewa falau falau da rigarsa doguwa ta wani tsohon yadi dinkin wani falkeke komai ta Masa yawa

Kuka Aamna ta saki Wiwi tana Hawaye tare da nuna Budurwar da Hannu tana masifa tare da Furta In Allah yayarda Shedan sai ya sumbace ki,Shedan sai yayi kissing dinki,muguwa,Azzaluma, maciya Amana,Baza kiga dai dai a rayuwarki ba Saratu,Saratu anyi asarar Duniya,An Sarai asarar duniya,Shegiya wacce Shedan yayi Mata fitsari a Kai, Wacce ake Kira da Saratu murmushi ta saki tare da karkada key din motarta Tace nafi karfinki Kina talaka kucaka me Deeni zaiyi dake duk kudinsu,ke wawiya ce Baki da hankali da har kina me siyar da Abinci a Restaurant kike tunanin Dangidan Dan Majalisar jaha Deeni zai so ki,ai ko kansila Aamna bazai tayaki ba,ganinki kyakyawa Fara Wai zai sa samari su soki? Kinyi kuskure Aamna,ai yanzu samari sai masu kudi suke Nema gidan da Suka gaji arziki,ai yanzu sai kana da kudi ake rayuwa da kai,ke Dan Dakikiya ce tunaninki kyau Yana sawa a so mutum? Dan kina da kyau har Shishigi kike Yi to ki sani samari sai dai su yaudare ki Amma yanzu duk munin masu kudi Haka ake aure su,Talaka ma Bai son Auren talaka bare irin su Deeni masu kudi,Ina Baki shawara ki fita Harkar Deeni ba ajinki bane. Aamna tana tsaye sanye da Jean skert Blue da rigarta T-shirt fara tas me Rubutu Red a Gaban Rigar An saka A&G Food Joint,ta Sanya pcap Red takalminta ma Red,ba karya Aamna karshe ce a kyau,haskenta me kyau ba fari Kal Kal ba Amma fara Ce dai ba Wanda ya Isa yace wankan tarwada ce,dole dai farar ce,Gashinta har gadon baya Baki wuluk,Ga Zararan gashin Ido tare da kwantaccen Gashinta dake goshinta,Girarta wuluk me yawa,Hancinta me kyau bai cika tsayi ba,Fuskarta ba doguwa ba baza Kuma ace Round face ba,Dan Bakinta gwanin Sha’awa Karami with pink lips,Gata doguwa Amma ba can ba,ga Uban Hips kamar ita tayi kanta komai nata me kyau,hakoranta kanana farare tas,Idonta dara dara, Mashaallah,Aamna baza ta wuce 24years ba,Haka kanwarta ma Zuhra kyakyawa ce Amma ita chocolate ce kamarsu Daya da Baba.

Murmushin takaici Aamna tayi Tace ai gaki Nan da Muni yayi Miki yawa Deeni zai kwasa ki cinye Deeni please ta juya tare da komawa Kan bakin aikinta wurin masu siyen abinci,ita kuwa Saratu Tsaki ta ja tare da Bude dalelleliyar motarta baka ta Shiga sannan ta fisgeta a Tamanin.

Sai 11pm ta tashi a Aiki ta saka After dress dinta me Dan kyau tare da rataya handbag dinta tayiwa abokan aikinta Sallama ta wuce gida,Napep ta Shiga zuwa gida,can cikin wata Unguwa ta masu rangwamen gata aka sauke ta a Kofar gidansu na Bulon siminti Amma ka rantse kango ne baiyi Kalar gida bane,da Sallama ta Shiga da kyar aka samu aka amsa mata,Mama Wato Aishatu ta Iske tana Daura Net a dakin babansu Tace Mama na dawo,Tsaki dattijuwar ta ja Tace to sai me,idan da sabo ta Riga da ta Saba,Baba ta kalla Yana daki Tace Sannu Baba,da kyar ya amsa,Kai Kawai ta girgiza ta wuce kitchen Nan ta Iske abincinta an zuba Mata Amma an barshi a Bude baza a iya rufe Mata ba,ta Saba Kawai ta dauka tare da Fitowa sai ga Daya matar gidan tunda dama gidan Haya ne,mutum Uku ne a ciki ko wacce mata da dakinta biyu da kitchen Amma toilet Guda Daya ce du,Gaisawa Suka Yi Tace Maman Zeenat ya gida,Tace lfy Alhmdllh da fara’a, dakinsu ta wuce ta Iske kanwarta Zuhra tana kwance a saman katifarsu tana chatting da saurayinta Wanda zata aura Nan da wata daya. Murmushi Aamna tayi Tace Zuhra Ana Shan love, Murmushi Zuhra tayi tana juyi Tace Aunty Aamna an barki a baya wallahi,Soyayya tayi a rayuwa,Adam ne ke kashe Ni da zafafan kalamansa masu sweet,Dariya Aamna tayi Tace na tayaki murna kanwata ke kin samu Miji Ni kuwa kin barni nice Kuma yayarki gashi Mama da Baba sun tsaneni akan ban kawo musu Wanda Zan Aura ba,Hawaye ne ya silalowa Aamna Tace why me naaa?why Me Zuhra? What have I done wrong? Tausayin Yayarta ya Kama Zuhra Tace kiyi hakuri Aunty Inshaallah kema Zaki samu miji very soon,Kuma Inshaallah su Mama zasu hakura su daina fushi da ke. Kai Aamna ta girgiza Tace Zuhra Ni bazan iya auren Wanda bana so ba,da Zan Iya Dana fitar da ko ma waye Dan na farantawa Iyayena Rai Amma idan nayi bazan iya yiwa Wanda bana so Biyayya ba,Illar Hausawa kenan Allah Bai kawo maka Miji ba a takura maka karshe har sai ka auri Wanda baka so,baza ka Dade ba za a sakeka,ko Kuma kullum ku Kare a fada da sasanci,bana fata inyi aure na fito Zuhra,Nafi so ko wa Zan Aura ace Ina sonsa sosai sabo da shine kadai Zan iya Masa Biyayya,kin San halina Ina da taurin Kai,Kuma Ni ba a iya tankwara ni,So shi kadai ne zai sa nayi Biyayya,Kin San idan bana son mutum wallahi zanci ubansa ne,Amma su Mama sun kasa fahimtata,Zuhra Tace ai ke matsalarki kenan Aunty akwai saurin fushi ga rashin barin ko ta kwana,aure Kuma sai Hakuri,Hakuri na Kawai na auri Wanda nake so ko jibga ta zai nayi kullum Zan zauna Kuma bazan ji Haushin kowa ba. Mama ce ta fado dakin Tace Ina Jin duk abinda kuke cewa,ke Zuhra ki daina saurarar marar hankali,ai yanzu ba auren kauna akeyi ba dubawa akeyi aikin mutum ake dubawa me yake samu,zai Iya rike ki, ci da Sha shi ake kallo ayi aure,ke soyayya Zaki aura Zaki ci ubanki kuwa a hannun maza,kika sake sai Namiji ya sa Miki ciwon zuciya,Aamna tace kinji ko Mama bakwa duba Iliminsa da Addininsa Kawai kudi kuke dubawa ayi aure,Baba Yana ji ya tsomo Baki daga dakinsa yace Ni ki tambaya Sanda na auri Uwarku ban taba ganinta ba Haka itama Bata taba ganina ba Kuma gashi Muna tare har mun haife ku,wallahi Aamna kika sake Watarana sai na koreki daga gidana,badan ma kece kike rage min nauyin gida ba da tuni nayi Miki auren Sadaka Kuma wallah Matukar Naga dama auren Sadaka Zan bada ke. To Baba kuyi Addua Allah ya kawo min na gari,Kuma da kuke cewa Baku ga juna ba aka muku aure ai ku a zamanin da ne Kuma asiri akeyi Ana kafe matar ta zauna dole,Salati Baba ya saki yace Ni Zaki hada da shirka Ina Dan Izala? Shuru Aamna tayi,Mama Tace mayaudariyar banza,kin Yaudari Affan kin Kore shi kince kin Kama shi da cin Amanarki Yana kula Mata,Hassan Kuma kince Dan karya ne,Deeni ma yaro me kudi yanzu kince ya yaudareki ya koma wajen Saratu kawarki Yar gidan Alhaji Sani Likita, yanzu ga Kamalu kin ci Masa mutunci ya gudu shima,Jollof din shinkafata wacce ta rigada tayi sanyi ta bushe ita Aamna ke ci su Mama suna ta mata fada har ta Gama,ta cire kayan jikinta gaba Daya ta wanke tare da shanya su a daren,Wanka tayi da ruwan zafi tare da Shirin bacci ta kwanta ta bar Zuhra tana chatting da masoyinta . Dalleliyar mota ce ta gaske wacce a kalla ta miliyoyi ce,ta danno cikin wani katafaren gida na Gagara,Gida ne Wanda ya amsa sunansa,Babu abinda babu a ciki,motoci ne zasu Kai takwas a gidan Wanda suka gaji da haduwa ga tsada,farare Guda hudu a jere bangare daban Haka ga wasu kaloli daban,Machine ne Guda Uku kala daban daban masu tsada harda Keke na masu kudi su biyu,Gidan Ya gaji da tsaruwa ga flowers ko ina,idan ka Shiga gidan baza ka so Fitowa ba,Kalar gate din ma na daban ne,ba ko Ina ake ganin Irinsa ba a kasar Haka furniture sai dai ko gidajen Gomnoni, Wani Matashi ne ya Bude motar baka Daya shigo da ita,Fitowa yayi da kyar Wow wani Fari ne tas kamar Balarabe har wani ja yake kamar ka taba shi jini ya fito,dogo ne Amma ba can ba,gashi shi ba Mai kiba ba baza ace Kuma siriri ba,Fuskarsa me dauke da hancinsa zarkadede ba irin me tsayi da yawa ba,Sumar Kansa baka wuluk dauke da wani mayen Aski irin na Yan duniya,an kwashe gefe da gefe an yanki wani waje siriri an Kona shi tare da maida shi Fari tas,Sajensa me kyau luf luf me dauke da Dan gemunsa cas,idanunsa Dara Dara farare tas suna wani lumshewa,kowa ya kalli wannan matashi yasan ya Gama gajiya da haduwa,Naira da Hutu sun zauna a jikinsa,Jikinsa na maza Wanda suka amsa sunansu maza,sanye yake cikin wani Crazy Jean me tsada gaba Daya wandon a farfashe yake ruwan toka,da wata T-shirt me Rabinta Fari Rabi Kuma Blue,Takalminsa da agogonsa masu tsada,Yatsansa sanye da zoben Azurfa,da kyar yake takawa ga takama ga aji Amma Kuma Yana tangadi da Alama yayi shaye shaye ya gaji,Yana dafa bango Yana tangadi AHMAD kenan a Haka har ya Isa katafaren palonsa tare da fadawa saman kujera ko Takalminsa Bai cire ba ya kwanta Haka Yana sambatun maye shi kadai har bacci ya kwashe shi. Tunda ya fara bacci gab da Magriba Bai tashi ba sai da gari ya waye sannan Rana da hasken gari yasa ya Bude lumsassun idanuwansa a hankali,Kara ya saki kadan Jin jikinsa a gajiye,da kyar ya iya tashi a hankali ya haura samansa Direct toilet ya shige ya Dade Yana wanka dake akwai tsafta,Bayan ya fito daure da Towel jikin mudubinsa ya nufa turaruka ne da mayuka na maza masu tsadar gaske,Lotion me kamshi ya shafa tare da fesa Body Spray a jikinsa sannan ya dakko sabuwar jallabiya me tsadar gaske fara sal Amma ta Dan tsangale Masa baya sa wacce zata Kai Masa har kafa sabo da Damunsa takeyi,Turaruka ya fesa sannan ya dauki wayarsa me tsada Yana latsawa,a hankali cikin tafiyarsa ta Isa da takama ya sakko kasa ya Bude kofa ya fito sanye da wani flat shoe fari sal shima Yana tafiya a hankali ya bi ta wani corido gaskiya gidan Nan ya Gama haduwa tiles din kasan gidan na tsakar gida fari da Baki ne ko Ina sheki yake Yi da walwali,Me Gadinsa ya hango Yana karasa gyara gidan Yana kida da bakinsa Yana rawa Yana aikinsa,Ya Dade a tsaye Yana kallonsa,Abin Dariya ya bashi mutum shi kadai Yana kida Yana Waka Kuma Yana rawa duk shi Daya, murmushi ya saki kadan tare da girgiza Kansa ya juya ya koma inda ya fito. Har yayi nisa sai ya dawo ya Kira me Gadi Musa,da sauri Musa ya dago yace Oga tare da takowa da gudu yazo gabansa yace Ina Peter banga ya gyara ciki ba Sannan ba Abinci,Oga ai Peter ya tafi kasuwa yace abincinka Yana kitchen yace sauri yake yi,Ni gaskiya Oga Ina tunanin yafi a dakko mace yar Aiki wacce zata na maka girki da gyara maka ciki tunda Ni Ina kula da Campun,Ogan yace ba Campun ake cewa ba Musa Compound,Kuma Ni bana bukatar mace yar aiki,Ni bana son mace ta rabe ni,duk abinda zai sa na hadu da mace bana kauna,Musa ya zaro Ido yace Oga Mata sune Jin dadin duniya duk wata nutsuwa da Namiji zai samu tana jikin mace,Baki Ogan ya tabe yace Allah ko? A wajen wawaye ba,gwara naci abincin Gardi akan naci na mace,Karka sake furta kalmar Nan mace a gaba na,idan ba Haka ba Kora ce tukucinka,Musa yace an Gama,Kayi Hakuri Ranka ya Dade Namiji gwara nace Namiji,macen banza Banda Mum dinka Oga,Baki ya tabe ya juya da Gadara ya wuce,Abincin Peter ya Bude yaga Bai Masa ba,da Kansa ya shirya Girkinsa da lafiyayyen tea dinsa ya karya sannan ya dauki key din mota yayi waje,Yau da wata mota Ruwan toka ya fita kirar Benz. Washe gari Aamna wanka tayi tare da Shiryawa tsaf cikin kayanta Riga da wando sunsha wanki da guga,After Dress ta Dora a Kai tare da yafa Mayafi,ba Wanda ya kalle ta a cikin Iyayenta Balle Tace Za’a Bata wani abinci dama yanzu basa kulata,ko ta gaishe su basa amsawa,Sallama ta musu ta tafi,Mama Tace yarinyar banza ace tasan Burin mu Bai wuce mu Aurar da su ba Amma Taki fitar da Miji abin kunya kanwa zata Riga Yaya aure duk ta tsufa a gida Allah wadaran Dan Riko,shekara ashirin da Hudu ai ba Wasa bane,mu duk da a cikin birni muke muna Nan da akidar mu ta Iyaye da kakanni na auren wuri Amma kash Yaran namu musamman Aamna ta Gama watsa Mana kasa a Ido,marikinta Bai da Buri sai na Aurar da su,ai mutuncin ya mace gidan Miji Amma ba komai Aamna wahala da azaba ma Sai ta sa kin fito Mana da Miji,kin daina Jin dadin gidan Nan kwata kwata,yanzu Zan canja Taku wajen gana Miki azaba duk da Kamar mahaifiyarki ce Ni dole wahala tasa ki fitar da Miji,Zuhra kuwa Shiryawa tayi tuni tayi Kari me kyau Ana ta nuna Mata gata da kauna ta tafi makarantar Boko Wato Secondary school sabo da sun kusa yin candy. Ahmad Bai tsaya ko Ina ba sai gidan Mashkoor inda Suka Fi Zama suna shaye shaye a gidan,can ya Iske abokansu su Biyar Mashkoor, Abdul Tawaga,Jibril Jibson,Bashir Bash, Mubarak Brown sai shi Oga Mai gayya me Aiki Ahmad King,Yana zuwa ya Iske su a zaune a Garden suna zaune a kujeru ga karamin Table an zube kayan maye na shaye shaye kwayoyi da giya iri iri ga Sigari taba da Wiwi,Kirari suke Masa Suna The King…Our King,shi Kuma Yana uban Gadara Abdul Tawaga ya Daga Masa kujerarsa ta tsakiya Kuma kujerarsa ta mulki ya zauna tare da Balle kwalabar Giya ya Shiga tiltila Kamar ya samu ruwa,Bash ya kunna Wiwi Yana zuka ga wasu kwayoyi Daya hada a cikin wani ruwan giya Yana korawa Yana tiltilo hayaki ta Hanci ta Baki cikin kwarewa,Tawaga Yana Aswaki Yana cijewa Yana karkace Baki yace Our King….Sweet Boy,The Handsome King,Fresh Boy, shi kuwa King ya kalli Kansa yace Na me….Na me My Guy,Look at my skin color….

Mubaraq Brown yace Handsome King,Mashkoor Yana wani tangadi a zaune yace Our King ka huta baka hura hayaki sai ruwa Kawai kake bulbula sai kwaya,King ya wani girgiza Kai alamar ya fara daukan chaji shima yace,Hayaki sai dai na shaki na Titi My Guy, Mashkoor yace Look King akwai wata yarinya tayi Fuck Up,the Girl done Mess up man, Wai Ni Ina sonta Tace Banda hankali wani yaro Rabiu Yana Nan malamin makarantar Islamiyya ya kwace min ita,King Yana lumshe Ido duk ya fita a hayyacinsa ya karkace bakinsa gefe Daya irin na Yan shaye shaye cikin kakkausar da mayen muryarsa yace She must Collect,Dole ta karbi Certificate na abinda ta aikata,Na yarje muku kuci mamanta,shi Kuma Yaron za a tare shi dole mu bashi Sample,Sumarsa me laushi ya yamutsa,yace guys gobe Mommy da Dad zasu shugo garin Nan Karku zo gida na sai bayan sun tafi,Abdul yace Confirm,No wahala,Jibril Jibson ya Mike Yana tangal tangal yace ya za ayi ace baza mu zo gidan King ba,The sweet Boy,Cikin zafi da daga Murya King Ahmad yace hey What’s up man Ina magana kana magana kana hauka ne? I’m sorry cewar Jibson ya Fadi a kasa Yana mayensa,da ganinsu kasan talakawa ne Ahmad shine me kudin shike musu komai,Haka Mashkoor Yana da kudi shima Amma ba Wani da yawa ba,Sai Abinda Ahmad yace shine King dinsu,duk wani rashin mutunci da sukeyi a gari shine yake daure musu gindi sai da sa hannunsa akeyi,Ba Wanda ya Isa ya nuna su da yatsa,Dai Dai ne Basu San da zamansu ba musamman Ahmad King din Wanda ya fita daban sabo da Naira da hutu,suturarsa Kawai abin kallo ce,Dukkansu baza su wuce 30years ba zuwa 34years,Ahmad 34yrs yake cif.

Washe gari da Yamma su Mashkoor da abokansa gaba dayansu har King din nasu Ahmad machine sababbi suka hau kowa da nasa Kuma duk King ne ya Siya musu kowa da nasa King shine a gaba suna binsa a baya sun kure Masa gudu sun biyo Hanya duk Wanda Bai matsa ba sai dai su bige shi ba ruwansu,sabo da an sansu Ana ganinsu ake kaucewa,Can layin da Islamiyayyar take suka tsaya Suka Parker machinansu,King shine kadai ya zauna a saman nasa suna ta Masa Kirari suna Our King,Fresh Boy,Sweet Boy,shi Kuma Yana ji da Kansa,Suna Haka sai ga malamin Islamiyya ya taho zai wuce matashi da shi Yana tafiya cikin nutsuwa Baki da shi,Tare shi Mashkoor yayi tare da cewa Yawwa ga dan Iska ya Furta tare da tallafe Masa keya,King ya Mike cikin maye yace kana gaba na kana tsaye,Robar Lemo Wanda ciki hadin kwaya ne a ciki Yana Sha ya daga ya tsiyaya wa malamin Islamiyya a kansa,Nan suka rufe shi da duka Wai yayiwa Sarkinsu magana a tsaye,Wata Mahaukaciyar mota ce me kyau da tsada ta taho a hankali,Mommy da Yar Autarta Humaira sai Daddy Mijinta a baya gaba Kuma Kanin Ahmad ne Saddiq da matarsa Mufida a Gaban mota suna tafiya, Saddeeq shi ke tuka motar,Daddy yace ai Kinga Ahmad din ma gashi Nan da Yan Iskan abokansa,na gaji da zuwa Kaduna akan Yaron Nan wallahi,Na rasa wannan masifa data sameni,Kinga Ni yanda suke dukan wani,Kanwar su Humaira Tace ga Yaya can da kayan maye a hannunsa, Saddiq ya tabe Baki tare da cewa kalli Askinsa Ana ganinsa anga Dan Iska,Mufida matar yayan Tace kuyi Masa Addua Kawai. A wajen Suka Yi parking sai tsawar Daddy dinsa yaji a Kansa Ahmad Mene Haka? Baka da hankali ne,duk suna mota ba Wanda ya fito sai Mummy da Daddy,Daddy ya tashi malamin makaranta Wanda ya ci duka da gudu ya arce Yaron,Su Mashkoor suka kame a Gaban Daddy tare da Sara Masa kamar suna Gaban wani Soja,Zaga Daddy da Mummy suka shiga Yi suna musu Sannu da zuwa Wai Nan murna ce da girmama Iyayen Ogansu,Bash kuzo mu Basu kariya Guys ba Wanda ya Isa ya daga Musu yatsa a Birnin Kaduna kaf. Tsaki Daddy ya ja Yana Jin yanda suke wa Ahmad Kirari,Wandonsa ya kalla wani shegen crazy an Masa daga daga,Askinsa ya kalla yace kalli yanda ka maida kanka Ahmad, Dariya ya Shiga Yi ta mahaukatan Yan maye,Mommy Tace Ahmad Dina meke damunka muje gidan da kake,Daddy yace shiga mota mu tafi,Wani fareti ya shiga Yi a Gaban Daddy Yana dariya cike da maye Yana karkace Baki yace No…no Ni a bike Dina zanzo kasan Ina Jin dadin bike Dina Kawai kuje zanzo daga baya,Tsawa Daddy ya daka Masa shiga muje,Amma ko a jikinsa sai ma Dariya da ya Shiga kyakyatawa irin ta basawa Yana kallon Daddy din da Mommy,Dole Haka Suka shiga mota Suka tafi shi Kuma shi da Abokansa suka take musu baya a machine suna tukin ganganci Dan Ahmad harda dage kafa Daya ya daura ta can sama Yana tuki da kafa Daya,Har katafaren gidansa Suka shiga sannan abokan daga bakin Gate Suka tafi gida abinsu shi Kuma yayi Horn me Gadi ya Bude Musu Gate,Bayan sun Shiga Suka firfito da akwatunansu,Wani handkerchief ya daura a wuyansa ya tsaya a Gaban Mommy Dinsa Yana zagata cike da maye Yana cewa Mummy…Mummy….Momma….You are looking Good ya furta tare da rungumeta yace Ina sonki Mummy,rokonsa ta fara Tace Dan Allah ka nutsu Ahmad,Da karaji Daddy yace Mene ne kike rokonsa, why are you Begging him,Dan ubansa tunda bashi da hankali sai yayi ai,Why…why…Daddy Ni dama fa ba tun yau ba nasan baka kaunata,musamman idan ka saka wannan farin Glass din naka sai ka dinga kwana idan anyi Nan sai kayi can,Ido Daddy ya zaro Yana kallon rashin kunyar Ahmad,Kaninsa Sadeeq ne yace ka canja wallahi Yaya,Cikin karaji ya tasowa Saddeeq Yana ce Masa Kai dalla gafara Ina yayanka zaka min fada,ko Dan kaga munyi Kai Daya Ina da gemu kana da gemu shine zaka rainani Kai wuyanka ya Isa yanka ko,Ka dai gyara halinka,Tafiya yayi zai Mari Saddeeq Mummy ta rike shi tana rokarsa yayi Hakuri, Humaira ya riko tare da Rungume ta yace kanwata kin girma,ya school? Tana Dariya Tace nayi Candy Yaya,Wow ya Furta tare da dagata sama ya ajiyeta suna Dariya,Matar Kaninsa ya kalla Mufida nutsatsiya kyakyawa yace matar mu ya gida fatan wannan shashashan yana kula Dake? Dariya Mufida tayi Tace sosai ma,yace Good muje ciki matar mu ke kadai ce tawa a gidan Nan,kishi ya Kama Saddeeq ganin Ahmad Yana shaye shaye tunaninsa har Mata yake bi sai kishi ya kamashi yace kaje kayi aure wannan matata ce Ni Daya ka daina cewa matarmu yawwa,Stupid Boy Kawai Ahmad ya furta Suka jera da Mufida suna Hira duk da a maye yake Amma Yama Saba Bai fiye buguwa da yawa ba, Sadeeq da Sauri yazo ya shiga tsakiyarsu ya rike Hannun matarsa ya janye ta da karfi,Baki Ahmad ya tabe ya Rungume Humaira Suka Yi ciki. Bayan sun huta sunci abinci Daddy yace da dare Yana neman kowa za ayi Meeting zasu fadawa Ahmad dalilin zuwansu yanzu ma again, Har dare yayi Ana jiran Ahmad Amma tuni ya bar gidan Yana can suna shaye shaye har 1am Bai dawo ba sai kowa ya hakura yayi bacci,Da safe ma Ana ta jiransa har sun karya Shuru Bai dawo ba,can sai gashi a bige ya Fado palon ya tafi taga taga zai Fadi sai ya cije ya Dage Yana bude Ido da kyar Yana Rufewa ya fada saman kujera shirim kusa da Daddy yace An tashi lfy? Ina….Ji…ji..jinku…..m….me…..yaaaaaa….ya…kawo ku Kuma yanzu Kun wani sake dawo min gida…na tuna ance jiya za ayi meeting yanzu gani Ina da abin Yi ku Fadi meke tafe daku har zuwa gidana? Daddy ya zaro Ido yace au gidan ka ne ma? Gidana kace gidanka? Yace gida nane Mana Kai ai Temporary Owner ne Nan gaba mutuwa zakayi naci gado,Ran Daddy ya baci yace gidan Nawa? ni da gidan gida ka gaje min gida?aikin uban me kake Yi? Kaki nutsuwa,Mummy Tace Ahmad Dan Allah ka tsaya ka nutsu kaji abinda ya kawo mu,Ina jinku Mana ku fada,Kaninsa Sadeeq ya tabe Baki,Humaira Tace Addua zaku Masa please,Ita Mufida ita tunda auro ta akayi Bata cikin wacce zata Shiga matsalar Family tana bedroom. Daddy yace kana ji na Ahmad? Yace Yeah,yace so nake ka bar Nan ka dawo Lagos kazo mu koma inda nake da Zama can Lagos Ina so Zan maka Visa mu tafi London gaba Dayan mu,akwai Company na Dake can kayi Handling dinsa kayi Aiki a can ka dogara da kanka,kullum sai dai na cika maka account da kudi kana kashewa a banza,ya kace?Ahmad yayi Dariya yace kasan amsata Mana Daddy Ni bazan je ba wata kasa da zanje Kuma Ni bana son Lagos a Nan gidana Zan zauna a Nan Zan mutu,Daddy yace to gidanka ne? Ni da gida na,Mummy Tace Dan Allah Ahmad ka bimu mu tafi kaga London ko Turkysh ko Kuma a Nan kasar Nigeria sai kayi Aiki an baka company kyauta ka dogara da kanka Kaine fa babban Danmu Kai ya kamata ace ka nutsu,kalli kaninka ya rike nasa a Lagos Yana aikinsa gashi da Degree da Masters Kai kuwa Degree daya ma da kyar muka samu ka karasa a Russia,Ahmad yace kunga fa Ni ba inda zanje Kawai ku daina Bata bakinku mutanen da basa son bakar fata ku Kun damu da su kuje kuyi harkarku,kuyi rayuwarku nima nayi tawa,yawwa kunji ba inda zanje ya tashi Yana tangadi ya haura sama,ya barsu a Nan cike da Alajabi yafi karfinsu.Daddy bakin ciki ya Kama shi ya juya kalli Mommy tare da galla Mata Harara yace Kinga danki ko kin ga abinda kika haifa ko? Mummy Tace au da nane ma Ni Daya? Daga Nan suka fara cacar Baki. Aamna ce ta fito tsakar gida sanye da wani gajeren wando ko gwiwa Bai ba Milk color,da Yar rigarta t-shirt dark Blue,Hannu biyu ta zuba a cikin aljihunta tana tafiya tana yan ga,Cinyoyi da kafafunta lukutaye,Mama ce ta Bude Baki Tace Yau me Zan gani? Aamna kece yau kika Yi wannan shigar ke da bakya so aga jikinki yau me Zan gani na Shiga Uku Kamar Namiji, Malam fito ka gani,Kuma wandon ma na Yan Ball ta saka wani katon buje,Aamna saman bakin rijiyar tsakar Gidan ta zauna daram tare da Harde kafafu,Baba ne ya fito da sauri shima ya Bude baki,yace kwaya kika Sha? Nan fa gidan haya ne ga maza Wanda da matansu,Aamna Fuska ta bata tare da Furta naga Alama a gidan Nan magauta sun min yawa,Magauta sun sani a gaba Ana so aga baya na,to Zan dauki mataki Mama kirji ta dafe Tace Aljanu ne da ke Aamna? Tace Ni yawwa da ace akwai Sigari a kusa ma yau Zan fara zukawa sai anayi ana feso da hayaki ta Hanci da baki sabo da Naga an tsaneni a gidan Nan so ake na lalace to wallahi Zan bi duniya kowa ya huta Matukar ba a daina uzura min ba.

AsmaBaffa
10/26/21, 8:51 AM – A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA🌵🌵

DUNIYATA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE.

ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK.

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

‘YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Page 6-10

Official

By
AsmaBaffa.

PAGE NAKU NE

SAMEERAN GAYA
FLOWER
AUTA
AIDA MAMAN TASNIM
CHOICE

Aamna ce a Resturant dinsu tana hadowa customers abinci tana bin wakar Dake tashi a ciki da manyan speakers sabo da Jin dadin masu cin abinci a wajen,idan kaji uban kida kamar kana club,ai Aamna Bata San Sanda take kada Kai ba tana bin wakar da Baki tana bi layi layi inda masu jiran order suke zaune tana ajiyewa kowa nasa,duk Wanda ya kalleta sai yayi Dariya yanda Bata ji bata gani bilhakki aikinta takeyi tana rawa da kanta,wani babban mutum Bai San Sanda ya saki Dariya ba Amma Aamna ko a jikinta sai ma data soke Wayarta a jikin aljihun skert dinta,wani kida ya dado ta tayi tafi tare da daura Hannayenta biyu a kanta tare da Furta wayyo Baba…. Ai kuwa wasu duk sunyi tunanin kwaya take Sha Kawai sai Dariya akeyi tana Basu nishadi gata kyakyawa ta karshe. Wata Budurwar da saurayinta Tace wannan Yarinyar ba karamar Yar Iska bace ko a jikinta duk mutanen Nan ko kunya babu,Matashin Yana zuba Dariya yace ai shi yasa nake zuwa resturant din Nan,sabo da ita nake zuwa wlh abin Dariya Zaki gani iri iri tana yi,Budurwar kishi ya turnuketa ta kalle shi ta watsa Masa Harara Tace Ni Kuma fa? Allah ya tona maka asiri ka Fadi gaskiya,shi yasa ko yaushe kace muzo Nan munafuki Ashe Dan ita kake zuwa,sai lokacin matashin ya tuna tabargazar da yayi a Gaban Babynsa. Aamna kuwa wani sufa tayi da takalminta a tiles din tana tafiya a Haka Kamar wacce ta hau takalmin Taya Wai duk cikin saurin Aiki ne,Siyama kawarta itama Haka ta shararo da sufarta Hannunta dauke da tire da kayan Abinci Washe gari da Ahmad ya fita Wata hanya Suka samu tare da tare hanyar mota kowa idan yazo sai dai ya juya Inda ya fito,sai da aka kawo Yan Sanda wajen suka dinga fada da Yan Sanda,Bincike Dpo yayi Dan waye? Ai Yana ji an Fadi waye Baban Ahmad a kasar sai ya tsorata yaje har gidan ya samu Babansa tunda ance yazo Yana Kd ma,Bayan sun gaisa Dpo ya Kai karar Ahmad yace mun kyale shi ne sabo da Kai da irin taimako da kake Yi a kasar nan sabo da Haka Dan Allah Ka Jawa danka kunne,Daddy ya Basu Hakuri tare da sanar musu duk irin kangarewar Dansa,Dpo yace sai dai ku dage da Addua Amma a tsawatar Masa Kar mu dauki mataki aga Bamu kyauta ba,Bayan sun tafi Shuru Ahmad Bai dawo ba sai cikin dare Daddy,Mummy da Saddeeq duk suna jiransa sai kuwa gashi ya dawo a make,Daddy ya lullube shi da fada ba ji ba gani,Kaninsa Sadeeq yasa Baki Nan take Ahmad ya shaki kwalar Sadeeq zai Duke shi,Mommy ta rirrike shi tana kuka tana cewa ka Bari Mana Ahmad wayyo na Shiga Uku Ni,Daddy kuwa Mari ya kwadawa Ahmad,Nan take ya dafe kuncinsa Daya da mamaki sai Kuma ya sheke da Mahaukaciyar Dariya Yana Nuna Daddy da yatsa Yana ka mareni akan wannan kanina shi zai ce zai min fada,Daddy yace banza shashasha sai na sake marinka wallahi,Juyawa Ahmad yayi ya haura samansa a fusace,Humaira kanwarsa da Mommy suka bi bayansa suna ta bashi Hakuri suna lallaba shi,Ahmad yace kina gani Mommy marina fa yayi Akan kanina,Ni dama nasan Daddy Baya kauna ta,Bai so aka haife Ni ba gaba daya,Ba Haka bane Ahmad Yana sonka Nima Ina sonka,Yace ai nasan ke kina so na Amma Daddy Baya kauna ta Ni ku tafi ku bani waje Kawai ya dakko kwalabar barasarsa ya shiga korawa,Mummy suka fita sun San halinsa idan yayi Fushi. Ranar da su Mymmy suka kwana Uku da Yamma Ahmad,Mufida matar Saddeeq da Humaira Autarsu suna Garden suna Hira Ahmad Yana ta musu magana irin ta Niggogi irin ta Yan kwaya suna ta dariya, Sadeeq ta sama ya hango su ta window kishin matarsa ya kamashi ya sakko tare da Fitowa Haka ya dinga zaga garden Yana kunci,ya Shiga ya fita ya dawo ya wuce ya sake dawowa,Mufida ta fuskanci wani Abu Tace lafiya dai Baby? Cike da bala’i yace ba lafiya ba ki taso ki kula da mijinki kin zauna kina wani dariyar banza da wofi,Ahmad yace ya zaka dauke ta muna Hira,Hira mukeyi Kai wanne irin yaro ne? Tsaki Saddeeq Yaja ya Fisgi matarsa Suka tafi,Juyawa yayi Suka ci gaba da Hira da Mufida kanwarsa suna ta dariya abinsu,Wayar Humaira ya karba ya juya yace irin wannan waya Haka sis idan kika hadu da irinmu Yan duniya ai sai mu tare Miki Hanya muyi Miki fashin ta,Dariya Suka sake yi Yana ta Dariya ba ji ba gani irin ta Yan kwaya,yace sis yanzu ma Dan na sanki ce ke kanwata ce da su Jibson Zan turo su kwace ta,Dariya Suka sake Yi a tare Humaira ta daki kafadarsa tare da furta Kai Yaya,Kallon Kanwar tasa yayi sosai yace sis you are cute wooo…see your Nose fine nose,kina sa Nikaf fa Kar ki hadu da irin su Brown abokina I swear Kamaki zasu Yi su Sha harka kina kula fa tam,hope Baki kula samari Kar wani yazo ya taba min kanwa Naga kin fara girma abubuwa sun fito Haka, zanzo har Lagos nayi yaki ne idan wani ya Bata min ke, Humaira harda rike ciki sabo da dariya ga kunyar abinda yace,shi kuwa ko a jikinsa Kwanan su Mummy biyar suka fito cikin Shirin tafiya Ahmad Yana binsu a baya Yana ta murna zasu tafi yanzu ma su barshi ya sakata ya Wala,Mummy ta Rungume shi Tace ka Zama mutumin kirki Dana tunda baza ka bimu ba ka kula da kanka,yace to Mummy na, Saddeeq yace wannan ba Wani shiryuwa da zaiyi Nan take Ahmad yayi Kansa da bala’i,Mufida tazo Tace Yi Hakuri kyale shi Yaya King,yace yawwa matar mu ki kula da kanki,Da sauri Saddeeq ya janye matarsa cike da kishi,Ahmad yace wannan wanne irin Dan Uwa ne Haka? Daddy ne ya Kira Driver su wurin Tara yace ya kwace Motocin Dake Hannun Ahmad kaf,Dama Bai damu ba yace tunda Yana da kudin machine ya ishe shi,Daddy kuwa yace tunda baza ka nutsu ba ai Motocin da kudi na ka siya na karbe,Ko a jikin Ahmad yace kuje da ita,Daddy yace dole ma ko baka fada ba,kudi dai Zan na tura maka na kula da kanka sabo da hakki na ne,gida ma kayi ta Zama Amma ka sani ba gidanka bane Nawa ne. Mummy Tace please Ahmad ka daure nasan kana Sallah Amma baka Yi sai Sanda kaga dama ka gyara Sallah ita ce komai awajen musulmi,Ahmad yace sured Mum Zan gyara ki yarda Dani,Nafa sanka Ahmad tun yaushe kake cewa zaka gyara Amma kaki,Ki yarda Mum Inshaallah,nine fa Ahmad dinki,Sunana fa aka kalla aka yo Guarantee trust Bank,Dariya sukayi har Daddy,Yawwa ehem Dad karka manta na tura maka new accnt number Dina Ina bukatar kudi kudina sunyi low,Daddy yace Zan tura ai Ina sane sakaran banza. Ahmad Yana ji suka shiga mota Gate man ya Bude Musu suka tafi Basu bar mota ko Daya a Hannun Ahmad ba aka su Suka kwashe su,Suna tafiya ya dauki waya tare da Kiran Abokansa su zo Iyayensa sun tafi sai murna sukeyi yau suna gidan King. Me Gadi ya kalle shi kawai ya jinjina Kai Amma Ogansa Yana da Hali me kyau Kawai matsalarsa shaye shaye da Rashin Ibada sosai. Aamna tana cikin Restaurant dinsu tana ta Kai abinci wajen masu ci,sannan Kuma suna Hira da Babbar kawarta Siyama wacce aikinsu Daya,tare suka Yi HND a Poly,Rashin samun Aiki yasa suka nemi Aiki a sabon Restaurant da Maman kawarsu Saratu ta bude sabo da Talaucin da suke fama da shi, Siyama Tace kawata Nima fa Allah ya kusa daga Ni,na manta ban fada Miki ba Nafa fada cikin kogin son Faisal,kwanan nan ma nake so na bashi dama ya turo magabata,Murmushi Aamna tayi Tace wow I’m Happy for you Kawa But Ina ganin Kamar kinyi gaggawa ya kamata ki Bari ku fahimci juna sosai Bai Yi ko 1month da fara zuwa wajenki ba,Karki je garin sauri da matsuwar Aure a samu matsala,Siyama ce ta dakatar da Aamna ta hanyar daga Mata Hannu tare da Bata rai,Tace Ni fa Aamna ban Gane Miki ba,ai sai kisa nayi zargin ko bakya kauna ta kina bakin ciki na samu Miji ke Baki samu, Subhannallahi Siyama Allah ya kiyaye ko wani da musulmi bazan Masa bakin ciki ba bare ke da kike kawata wacce muke kashewa mu rufe tare Allah ya kiyaye min,sabo da Haka Dan Allah gobe a daura aurenki da Faisal ma Bai Dame Ni ba Bai shafe Ni ba,babu abinda Zan tsinta ciki,idan wahala ce ma ke Zaki Sha abarki mu Yan jaje ne. Siyama Tace ai ke dama bakya kaunar Aure bakya so kiyi Kuma bakya kauna wani yayi,gaba kike da Sunnar ma’aiki sabo da ke Kinga Baki da samari idan ma kin samu guduwa suke yi,idan Zaki hakura ki auri kowa kika samu ki hakura yanzu an daina auren Soyayya wa zai Iya rike ka Kawai ake Nema ya zaka ci ka Sha ka rayu inda zaka huta da iyayenka,Faisal Doctor ne matarsa mutuwa tayi wajen haihuwar fari,yaro matashi ga kudi me nake jira ai yanzu ba a jira Yan Secondary ma idan suka samu Miji aure suke Yi,kiwa kanki fada,shekaru tafiya suke Yi mu matane,ko ba komai kar tsufa ba aure har mu zo lokacin Haihuwar mu ya wuce,Aamna Tace Allah Baki Hakuri ayi aure lafiya mu muna Nan daram za muci gaba da Addua Allah Bai manta damu ba Yana sane da mu,Siyama Tace ae aci gaba da Zama lafiya Ana gantali, wanne gantali mu da muka yo rako duniya,gamu an halicce mu a Nigeria babbar jarabawa,ga talauci,wannan duniyar Ina Dadi cikinta, aikinsu Suka ci gaba Yi suna Hira kamar ba sune Suka Yi fada ba,dama sun Saba fada da junansu. Washe gari Bayan ta tafi wajen Aiki Sai ta Iske Siyama Bata karaso ba sai Aamna da sauran ma’aikatan,Siyama kuwa Direct gidan Su Aamna ta wuce,Mama ta tarbe ta,Tayi sa’a Baba ma Yana gida,Bayan sun gaisa Tace Baba wata magana ce ke tafe Dani da Kuma shawara,Baba yace Muna jinki Siyama,Siyama ta Basu labarin yanda sukayi da Aamna Akan Maganar Aurenta da Faisal,Baba yace na rasa dalilin Yarinyar Nan da Bata kaunar Aure,Siyama Tace Ni abinda na fahimta Baba Aljani ne ya auri Aamna Kawai shawara ku kaita gidan malamai a Nema Mata magani shine Kawai,Mama Tace tabbas yarinya kinyi nisan hankali,shi yasa ake son kawa irinku ta gari,Haba biri yayi Kama da mutum cewar Baba,yace Inshaallah gobe zamu dauketa mu tafi da ita kauyenmu can Sokoto mu Nema Mata magani,dama jiya anyi Mana Albashi sai a fasa siyan komai mu tafi neman magani Allah yasa a Dace kafin ayi Auren Zuhra itama ta samu nata Mijin mu hada a Sha rikitiba sosai,Haka Siyama ta fito ta zo wajen Aiki a makare ranar Aamna Bata San dalili ba tana komawa gida taga Baba da fara’a ya amsa Sallamarta,ta Gaida shi Kuma ya amsa,Mama ma Haka,Aamna dai hankalinta Bai kwanta ba tayi mamaki,Zuhra kuwa tana ta karasa miyar Taushe,Mama Tace Aamna Sannu da Aiki zauna na kawo Miki abinci,Aamna mamaki ya kamata sai binsu take da kallo har taga an kawo Mata abincin a flask Wanda a baya ko rufe Mata ba ayi bare wani Flask,ta kalli abincin ta kalli Mama Tace Mama ko dai maganin bera kuka saka min zaku kashe Ni?Mama tana gyara daurin zaninta Tace haba Aamna kin taba ganin Iyaye sun kashe yarsu? Aamna Tace na nawa Kuma,bazan ci ba gaskiya wallahi,Ina so na Kara tsawon Rai,bana so na mutu yanzu sabo da Haka Ni bazan ci ba ko ruwan gidan Nan na daina Sha gaskiya. Babu irin lallabawa da lallashin Aamna da Iyayenta Basu Yi ba Amma Taki cin abinci ko ruwa Bata Sha ba,Baba ya kalle ta yace Ki shirya Aamna gobe zamu je Kauye gaishe da Yan Uwana da abokan arzuka,Aamna Tace Amma ba a fada min da wuri ba na shirya,shike Nan Allah ya kaimu goben Amma kafin mu tafi Zan sanarwa ogar mu sabo da gudun matsala,Ba damuwa Aamna cewar Mama. Aamna kwana tayi Bata ci komai ba duk da cewar taci a Restaurant dinsu,Washe gari da wuri ta nufi gidan su Saratu kawarta,Saratu tana bacci har Aamna ta Shiga aka Mata Sallama da Maman Saratu ta Mata bayani zasu Yi tafiya,Hajiya Tace Baki da matsala Aamna Amma kin San dai Baki da kudin fashin da zakiyi,a cikin Albashinki za a cire na Iya kwanakin da kika Yi bakya zuwa Aiki tunda kin San ba aikin Gomnati bane,Gomnati ce ake cin banza Ni Kuma ba Gomnati bace,Aamna Tace ba damuwa Amma,Hajiya Tace a dawo lfy ta Mike tare da haurawa sama,itama Aamna ta Mike ta tafi,dama sun Gama shiri Kaya Kawai ta canja wani lace ja me adon Golden, me Dan kyau Riga da skert,Ta sa takalminta na Sallah da jaka duka Golden,Zuhra Kawai aka Bari a gida sabo da makaranta suna Exam,Napep muka shiga zuwa Tasha daga can Muka hau Motar Sokoto tana ta Adduointa, sun Dade suna tafiya Amma sai kusan dare muka Isa can kauyen Su Baba da Maman su,Asalin gidan Iyayen Baba muka sauka a bangaren Baba,Dakuna biyu da toilet ne na Bulon Siminti Wanda Baba ne ya Gina ya sumulmule ko Ina da Siminti idan sunje can suke sharewa su zauna a gadon uban su,Ko wanne daki akwai Ledar tsakar daki da katifa katuwa da Bedsheet,sai kwanikan cin Abinci da Tukwane har da Reshio dinsu,komai na bukata akwai dai dai talaka,Mutanen gidan Suka tarbe su dake Babban gida ne a bangaren Kanin Baba wato Kawu Ismail muka sauka.

Sai da suka ci abinci suka huta sannan suka gyara bangaren Baba ita da Mama, Bedsheet din Yana wanke a cikin kayansu suka shimfida abin su,a saman Katifun dakunan Guda biyu,wanka suka Yi tare da Yin Sallar Isha,Baba suna Kofar gida shi da Kaninsa da sauran dangi,suma dakinsu Mata ne Yan Uwa aka taru suna hira sai ga Baba da Kawu Ismail,ba tare da Bata lokaci ba Baba yace ke Aamna taso muje Ina Maman taku ta taso mu tafi muyi abinda ya kawo mu ba dadewa zamuyi ba,Hijab me Hannu Aamna ta Daura saman Riga da skert Dinta na jar Atamfa,Mama kuwa Mayafi ta yafa tare da Fitowa zasu tafi,Baba ya kalli Mama yace wannan tayani gantalin Wato baza ki daina yafawa ba ko? Har yanzu fa da sauranki Baki Gama Expire ba,Dariya Aamna tayi tare da sadda kanta kasa sabo da fadan Baba da Mama ya rigada yabi jininsu,Mama Tace Kai ka sani dai,Baba yace ya kamata ki daina Narka kibar Nan ke ba Wani abinci kike samu me Gina jiki ba Amma kullum Hawa kike kamar ana buga Miki Iska,Mama Tace sai ka fara rage taka kibar tukun,Haka suka tafi Suna ta cacar baki,Kawu Ismail kuwa fada yake ta yiwa Aamna lallai ta fitar da Mijin Aure,yace abokan haihuwarki daga me Yara hudu sai me Yara biyar a Nan kauyen,ita Aamna Bata taba sanin Mama da Baba Basu Suka haife ta ba,tasan dai suna Dan nuna Mata banbanci tsakaninta da Zuhra,Haka Dangin Baba tasan Suma sunfi son Zuhra,Haka ma Dangin Mama,Sai wani gida da ake kaita tun tana karama a cikin Sokoto city wani me kyau gidan mutanen Sudan ance Wai Yan uwane suma

Gidan wani mutum suka je Malam me Almajirai,Bayan sun zauna Aamna sai ji tayi Baba suna ta Masa bayani akan bata samu Mijin Aure ba,Kuma ko zancen Aure akayi Aamna Bata kauna,Malamin Yana tauna goro yace Ashsha Aljan ne namijin dare ne wallahi take fama da shi,Mama Tace biri yayi Kama da mutum,Baki Aamna ta Bude tana kallon Iyayen Nata,Malamin yace yanzu Zan kwana Uku ba bacci Ina wani Aiki Amma dole aikin Nan kullum sai an yanka zakara Guda Uku har na kwana Uku,Baba duk talaucinsa sai yace dama na samu wasu kudi Nan take ya biya kudin zakaru tare da bawa malamin dubu goma kudin Aiki,yace Nan da kwana Uku ku dawo ku karbi wata laya wacce zata soke ta a cikin gashinta,Fuska Aamna ta Bata kamar zata saka kuka,Ace Allah Bai kawo lokacin Abu ba Amma Iyayen nata basa gani. Suna Fitowa Kawu Ismail yace saura wajen Malam Kare Aiki,Wannan malamin sanatoci layi suke Yi a Wajensa,Aamna ta girgiza Kai Tace Baba wallahi ba kyau,Wannan shirka ce baza a fadawa Allah bukata ba sai Malam,Baba ya kalleta cikin duhun dare yace ai ke Aljanu gareki sun aureki Bai ma dace a saurare ki ba sabo da ba a cikin hayyacinki kike ba,Yo ka biyewa sakarai cewar Mama,Kawu Ismail yaci gaba da cewa inshallah Kuna komawa zata samu Miji itama,Wannan malamin da suka je Wajensa Rubutu yayiwa Aamna a tafin Hannu yace lashe ai magauta ne Suka mata asiri kuma makwaftan ku ne,Takaici yasa Aamna Tace Allah ya tona muku asiri masu hada fada tsakanin Musulmai,Rankwashi Mama ta zubawa Aamna tayi Shuru,Lashe Kawu ya furta Yana zaro Mata Ido,Haka ba a sonta ba Tace Allah na tuba bana nufin kowa da sharri sannan ta lashe su Baba suna ganin Aljanu ne ke hanata Sha,Haka Suka je wajen wani malamin shima yayi nasa sannan suka jira Bayan Kwana Uku Suka karbo duk wasu Magungunan da aka hada Suka dawo ,Duk wani Rubutu da magani da Suka bawa Aamna Kan tayi amfani da su sai ta samu jikin katanga ta zubar babu Wanda ya sani,Laya Kuma Haka ta soketa da pin a gashinta sabo da kullum Mama sai ta duba gashin dole ta soke Laya a gashinta. Su Baba Basu Sani ba suna ta jira suga saurayi yazo neman Auren Aamna Amma Shuru,ga Kuma bikin Zuhra yana ta gabatowa,duk sunyi Anko da Dinku Nan su na biki duk wani shiri da za ayi mun Riga sunyi,Baba ya siyar da manyan shanayensa Guda hudu dake Kauye sabo da Haka ba Harkar Talauci sunyi komai cikin rufin asiri,Adam Ango ya hada musu Dinner zazzafa me kyau ranar Saturday,Sunday za a daura Aure a Kai Amarya,daga Aamna sai kawarta Siyama bata gayyaci kowa ba,Amarya dai taci Uban gayyar kawaye wurin Dinner,Biki saura kwana daya a fara Aamna tayi lalle da gyaran gashi,amarya kuwa ta Sha gyara sai sheki take zubawa,dangi na nesa sun zo sai tsiya ake yiwa Aamna kanwa zata Yi aure ta bar Yayarta,Haka suka Sha bikin Zuhra da Angonta Adam anyi an Gama lfy tare da Kai Amarya da gararta,gidan Adam madaidaici ne me kyau harda gate yayi kyau gidan,ga Yar motarsa me kyau Toyota,Itama Zuhra Baba ya Dage ya Mata Kaya masu kyawun gaske. Ahmad Yana kwance a makeken Gadonsa Yana zuba bacci,wayarsa ta dinga ruru gashi ya kasa tashi sai da kyar ya farka ba tare da ya Bude idonsa ba ya jawo wayarsa yaga number Mummynsa dama ta fada Masa zata zo ta ganshi a kaduna ita kadai kasancewar Daddy,Saddeeq da Humaira suna Saudiya Umrah,Cikin Muryar bacci ya Kara Wayar a kunnensa tare da Furta Hello Mummy……Muryar Namiji yaji yace da Allah me wannan Wayar sunyi Mummunan Hatsari Driver ya mutu ita Kuma tana asibiti da Allah ayi sauri azo,Firgigit ya farka Yace what….?cikin gigita yace please fada min Address din Asibitin,Nan take ya fada Masa,Da sauri Ahmad ya figi machine dinsa sanye da wando 3qutr da Riga t-shirt fara tas sai asibiti,a gurguje ya fada ciki Yana tambaya aka kaishi Emergency Nan ya Iske Mummy Rai a hannun Allah. Aamna Yau da matsanancin ciwon Mara ta tafi wurin aikinta gudun kar a hanata kudinta cas sabo da ba aikin Gomnati bane,a Haka take daurewa tun tana aikinta da karfin Hali har abin ya fara gagararta,Siyama ta kalla tana rumtse Ido Tace Siyama dole Zan hakura da aikin yau Hospital Zan wuce a duba min marata ya kamata ayi min scanning a gano min mene a wajen Nan,Siyama da tausayawa Tace Allah ya Baki lafiya kawata a dawo lfy sai munyi waya,Aamna ta daura After Dress a saman Uniform dinta Riga da wando ta fita tana tafiya a hankali ta Isa bakin Titi tare da Shiga Napep zuwa Asibitin da suke ganin Likita idan lalura ta taso,asibiti ne na Gomnati Amma ba laifi akwai kyau. Tana rike da mara hankalinta baya jikinta tana zuba Uban Sauri tabi wani Corridor,Gaf taji tayi Karo da mutum,wani kamshi me jarabar Dadi ya daki Hancinta,da sauri taja baya ko kallon Wanda ta buge Bata Yi ba,shima Bai ko kalleta ba hankalinsa baya jikinsa,Bayan tayi magana da wani Emergency ta nufa tana matse kwallar wahala gashi Bata fadawa kowa a gidansu ba,Karo suka sake Yi da juna kamshin mutumin dazu ta sake ji ya cika Mata Hanci Kamar Kar ta daina Shaka,Tsaki Yaja sosai yayi cikin Emergency Yana ta faman yiwa Doctors masifa,Yana cewa a bani Mummy na dole ne,Ni Nace bana son wannan Hospital din me Araha,a bani Uwata wannan so kuke ku kashe min Mummy a Asibitin Gomnati, Wallahi Mummy na ta mutum sai na daure ku,wani babban Likita ne yace Haba Malam Ahmad kake ko wa? Da masifa yace karka sake ce min Malam,Ni ba Malam bane,a masallaci ka ganni Ina Kiran Sallah ko Tafsiri kaga Ina Yi? Idan zaka iya Call me king,Doctor yayi Murmushi sabo da daga ganin Ahmad kasan inda tarbiyya take ma Bai nufa ba,Cikin tausasawa Doctor yace kayi Hakuri zamuyi Aiki iya yin mu a samu ta farfado wallahi Matukar ba a Bata agaji ba ka dauke ta to kafin kaje da ita wani Asibitin zaka iya rasa ta kayi Hakuri idan aka samo kanta sai ka dauke ta idan kaga dama ma ka tafi da abarka China. Aamna kwance take tana hawayen wahala Ana ta lallaba Ahmad Anki kulata,Cikin masifa Tace da Allah ku rabu dashi azo a duba marata Likita mayu sun kamani sun min Ajiya a marata watakil ma Tukunya ce a wajen ko wani karfen Kun zauna a wajen wannan muma ai ba daga sama muka Fado ba Kuma Nan gaba Aure zamuyi mu haihu,muma Iyayen wasu ne,Wani mugun kallo Ahmad ya aikawa Aamna sannan ya koma gefen Mummy ya zauna Yana cike da tashin hankali,Likita Yana zuwa kanta yace Rannan anyi Miki scanning nace ciwon sanyi ne dake sai kin dage da magani,Aamna Tace to ai har na gaji da maganin, wannan sanyi da naci yake jaraba Kawai,kankara nake Sha ko me?Ni ba Yar Madara ba Bamu da ko fridge ace wani sanyi,Ahmad sai lokacin ya kalli Aamna kadan tana kwance yace Doctor da Allah kazo wajen Mummy na ka rabu da wannan rubabbiyar Sanyi ya Gama kashe ta mijinta shike nan sai asosa Mata asosa,Aamna tunda ta kalli Ahmad Bata sake Kallonsa ba sabo da kyawunsa da wani mugun kwarjini da yake mata,cikin lokaci kadan Doctor ya yiwa Aamna Allurai tare da Bata magunguna,sai gata ta watsake ta warke yayin da Mummy itama ta farfado bayan likitoci sunyi aikinsu,Ahmad sai murna yake Yi,Mummy ta sa Hannunta tare da shafa sumarsa Tace karka fadawa Humaira da Daddy tunda naji sauki yanzu da ace akwai mace wacce zata kula Dani sai ta zauna har a sallame Ni,idan za a samo min Yar Aiki ma Zan biyata kudin jinya cewar Ahmad,Aamna ta dauki Handbag dinta ta wuce kenan taji Ana Neman me Aiki Sai gashi ta dawo baya da sauri tare da tambaya Nawa za a biya Ni? Mummy ta kalli Aamna sama da kasa Tace daga dubu Hamsim zuwa sama,Aamna ta Bude Baki Tace yanzu idan yau na fara jinya aka sallameki gobe dubu Hamsim Zaki bani? Ahmad yace kaji barauniya, Mummy ce ta kalli Aamna ta daga Kai Alamar ae,Aamna Tace Alhmdllh na karba zanyi Bari naje gida nayo Shirin jinya,Mummy Tace a dawo lfy tana rufe Ido sabo da da kyar take magana ba laifi Mummy ta Sha wahala. Agurguje Aamna ta koma gida ko abinci bata ci ba ta sanarwa Mama komai,Baki ta tabe Tace yo tunda kinki aure ai sai kici gaba da neman kudin tunda ke kudi ne a gabanki,Baba kuwa Baki ya tabe yace ba abinda kika sani sai neman kudi to a dawo lfy dama bikin Zuhra ya cinye Mana komai,ita dai Aamna kayanta ta bukata ta hada a karamar Akwati tayi wanka tare da yin Sallar Isha sannan ta wuce Asibitin abinta,tana tafiya kamar Namiji sabo da Tace ta daina Zama ta kirki. Tana Shiga ta Iske Ahmad ya jibgo kayan ci da Sha da duk wani abin bukata,Kallon Aamna yayi tare da galla Mata Harara cikin kallo na wulakanci,Aamna ta kalle shi itama tare da tabe Baki ta shiga rera Waka lalatacce….lalatacce ne ko a gidan su,da sauri ya kalle ta ransa a bace gashi ba damar fada Amma duk da Haka sai da Yaja Tsaki yace Talakar banza barauniya,Aamna tace ae naji da me kudi da talaka ai duk Allah yaga dama ya bawa kowa,You are very stupid….nayi magana dake? Ina wakata Zaki sa min ths your Smelling mouth,Mind your fucking Business ya Furta da karaji Wanda sai da Mummy ta farka tare da dafe kanta,duk abinda sukeyi tana jinsu, Nishi tayi Tace Son gobe a canja min Hospital wannan akwai sauro gashi ba Ac,Ahmad Yana maganarsa ta Yan duniya sai kace wani Me wakar Raps yace comfirm Mum,ki Dade kiyi karko and ki mutu AC Mum,Allah ya ja da nisan kwana,Mummy tayi Dan murmushi Tace Ameen a hankali,Aamna ta kalla tace dauki katin Nan ki Siyo maganin da ba a karasa siya ba,Ga kudi Nan a jaka ta,Aamna ta zuge jakar Mummy zata dauki katin da kudin,Ahmad ya fisge jakar ya dauko katin tare da zaro kudi a aljihunsa ya Watso a jikin Aamna yace Jeki,Aamna tayi murmushin bacin Rai Tace ba komai ta Eba ta fita,wurin siyen maganin taje ta Mika katin wani yaro matashi ne a ciki Yace dubu Uku da dari biyu,Me bada maganin da hantara yace ba canji malama,Dan Rainin hankali baza ki samo canji ba. Aamna ta Bude Baki tana kallon yanda yake masifa,Kai Malam kayi hankali da Ni Kanwar uwarka ce Ni da zaka dinga min magana Anyhow,Uban me kika Isa kiyi,Tas kake ji Aamna ta zuba Masa Mari Tace fito mu Buda wallahi Naga baka da tarbiyya,Wanda suke wajen ne Suka fito tare da raba fadan sannan Aamna ta wuce abinta ta siyo maganin a wani chemist dake wajen Hospital din,tana masifa an fada musu Ina tsoron fada da Namiji,In cakwumi Namiji,inci kwalarsa,muyi dambe ba komai ne a wajena ba,girman Kauye ce Ni,har yanzu da ragowar Tuwon dawa a jikina cewar Aamna har ta Shiga dakin da Mummy take tana fada cewar in Balla Namiji ba komai bane a wajena,In samu mutum in farke Masa makoshi Dan uban mazaje,Ahmad ya bita da kallo sororo Yana mamakin mace da tsaurin Ido Haka,Tsaki Yaja yaci gaba da latsa wayarsa.

Amma ita Aamna ta manta ma da wata marar lafiya take jinya taci gaba da cewa ko wanne Namiji Dan iska,to Billahillazi girman Kauye ce Ni sai na soke mutum da kwalaba,Ahmad ya sake zaro Ido a ransa yace tab Wanda ya auri wannan yayi bye bye da duniya kawai,irinsu ne masu kashe mazaje,Aamna Ta fake da wayo tana zagin Ahmad Tace Dan Iskan mutum Dan Kawai Yana da kyau da kudi ai muma Muna da kyan,ae munji mu talakawa ne sai akayi kaka? Duk kudin mutum Dan ubansa malaikan mutuwa Yana Nan zuwa duk tsayin katanga da katon gate haka zai haura ya zare ruhin mutum,abi duniya a Sannu,Duk wani shiga katuwar mota Haka mala’ika zai zaro ran mutum,Wani mugun razana tayi sakamakon tsawar da Ahmad ya buga Mata,shut up kina min Ihu akan maralafiya Zan fa barar dake,Zan Baki certificate wlh watch your words,Mukus Aamna tayi a ranta Tace wannan shege ne shima.
Babu yanda Mummy Bata yi ba Akan Ahmad ya tafi gida Amma yaki yarda ya tafi Yana Nan ya kafa ya tsare.

AsmaBaffa
10/26/21, 8:51 AM – A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA🌵🌵

Page 11-15

DUNIYATA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER TA
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

‘YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa.

Page naki ne
FANCY HONEY

Yana Zaune a gefen Mummy ita Kuma Aamna tana zaune a wata kujera,Mararta ce ta sake murdawa da sauri ta rike mara tare da kwala Ihu Mummy sai da ta Bude Idonta,Da Sauri Aamna ta samu gadon da ba kowa ta kwanta tana Nishi tare da Kiran Doctor,Likita ya shigo yace to yanzu me jinya ce zata Yi Jinyar wata? Aamna tana cije lebe Tace zanyi Haka Kai Likita ba ruwanka yawwa kayi aikinka Kawai wannan kudi Ina Zan bar shi,Dariya Likita yayi yace Aamna kike ko? Tace no Amy karka sake ce min wani Aamna Aemy(Amy)Baki Ahmad ya tabe tare da Bude wata Leda ya fito da manyan kwalaban giya masu tsada Yana korawa Abinsa Yayin da Mummy take ta bacci,tana kwance ta juyo tana kallonsa bata Gane giya bace tayi tunanin wani lemo ne me Dadi na masu kudi,tana ta Kallonsa tana faman Hadiyar yawu,Aamna Tace Wanda yaci shi kadai shi kadai zai mutu,kafin ta rufe Baki yace da Ubanki za a sani a kabari da? Aamna Tace wakata nayi fa,Nima ai wakar nakeyi ko na kulaki? cewar Ahmad Yana cin magani kamar zaiyi Naushi. Aamna ita kanta Tsoronsa take Yi Amma karfin Hali Irin nata yasa take maida Masa martani,Mummy tana kwance tana numfarfashi tasan me yake Sha sabo da taji warinta,baya kunyar uban kowa,sai da ya Gama Shan wacce zai Sha ya Mike Yana saka wayarsa a cikin wani Crazy 3qurt Jean Kan Mummy ya shafa tare da furta Allah ya Baki lfy Bari naje gida nayi wanka Zan dawo,Mummy Tace baza ka canja ba ko son so kake bakin cikinka ya kashe Ni? Murmushi yayi Kawai sannan yace Zan dawo Mum yanzu 11pm Zan dawo a Nan Zan kwana,aci gaba da Mana Addua Ina so na shiryu Amma Ina,A gabanta ya tsuguna,Mummy ta daura Hannunta a saman sumarsa tare da furta Allah ya shirya min kai Ahmad,Allah ya maka Albarka Allah ya tsare min Kai,Ameen My sweet Mum ya Furta Yana Jin dadi sannan ya Mike ya fita Yana takunsa da wani takama da Isa kamar Dan sarki,Machine dinsa ya hau tare da Bude wuta kamar zai tashi sama,Direct gidansa ya nufa ko da ya Isa gidan Toilet dinsa ya wuce ta Sha gyara ya sakarwa Kansa Shower tare da wanka da wani liquid soap me tsada da kamshi,Bayan ya Gama a gurguje yayi Sallar Magriba da Isha sabo da akwai Wasa da Addini,Yana Idarwa ya daga Hannu sama Yana Adduoi tare da rokar Allah Allah ka Bawa Mummy na lafiya.

Yace cikin adduar Allah duk da ba Adduar Nan nake Yi ba kullum Allah Ni me laifi ne a gareka ya Rabbissamawati Wal ard Allah ka yafe min laifuka na ka shirye Ni,Ina so na shiryu ya Allah Amma na kasa ya Allah ka dafa min na shiryu,Allah kasa mu mutu Muna Musulmai masu Imani,Allah karka Bari muyi maka shirka,Ka rabamu da Wutar Jahannama,Ka Bamu lfy da tsawon Rai,Allah kasa nayi tsawon Rai Allah bana so na mutu da wuri ka ja kwana na,Ka rabani da cuttuttukan zamani, ya Allah ka raba mu da talauci ka Bamu dukiya ta halak me amfani,Haka ma ya yiwa Daddy da Yan Uwa da Musulmai,karshe yace yace Allah duk da ba damuwa nayi da Mata ba Mummy ta tana so nayi aure Ya Rab ka bani mace ta gari me so na tsakani da Allah,me Ilmin Addini Dana zamani,wayayya,ba Yar Kauye ba,Ya Rab zukekiya ko ko fara ko light chocolate wacce idan na kalle ta kawai Zan washe Baki ba tare dana shirya ba,mace Yar dagwas wacce ta Dan dire ta Dan baje daga kasa.
Har zai tashi sai ya koma ya sake daga Hannu sama yace Ya Hayyu ya Qayyum na kawo karar Daddy wajen ka Allah kasa ya daina min fada kasa ya dinga so na,Allah kana gani dai Tsoho Nan nawa ya tsane ni kamar ba a son ransa aka haifo Ni ba,to Allah Kaine ka halicce Ni ya zaiyi Dani Allah kasa ya daina tsanata Yana gamawa ya Mike tare da zare jallabiyar da ya saka domin yin Sallah,ya dakko gajeren wando wani me tsada iya gwiwa ya tsaya Masa me Dan Fadi Yana da Aljihuna kala kala a jiki gashi Kalar ruwan kasa yasa Riga Armless baka me rubuyu a jiki da zanen fari,Pcap ya saka Kalar wandonsa Takalminsa ma na Yan gayu Wanda suka San mene wanka ya saka Kalar wandon,wow ba karamin kyau yayi ba Kamar a sace shi a gudu,damatsan Nan gasu Nan na mazaje mul mul irin na Wanda ke Dan Gym,turare yabi jikinsa sannan ya dauki key din machine dinsa ya fita,time ya duba 12am wani 24hrs shawarma joint ya nufa,Ko da ya Shiga ga mutane Nan Kamar Rana,Ana ta shige da fice,wasu Kuma suna ta Shan Shisha shi baya Harkar Hayaki,Take Away yayi na Abubuwan ci sannan ya nufo Hospital wurin Mummy.

Bayan Tafiyar Ahmad daga Asibitin Mummy ce ta Dan yiwa Aamna magana da kyar Tace ‘ya ta kin iya cire kudi a bank? Nan take tace ae,Tace duba handbag Dina ki dauki Atm card Dina ki ciro min dubu dari,Mamaki tayi lallai masu kudi ne,Haka ta dauka tana mamaki da Bata Santa ba Amma har ta yarda Da ita, Code dinta ta fada mata ta fita da sauri taje ta ciro,Handbag dinta ta sa ta zuba kudin da Atm card din,lokacin Likita yazo yace Hajiya anyi komao dakin da kike bukata ya Zama ready aje a biya kudi sai ku koma ciki.
Yana zuwa ya Iske an canja wa Mummy daki Already Kuma dakin na masu kudi ne Idan kana da kudi sai ka biya kudin daki Guda karami a baka Kai Daya,Gado ne daban na me jinya a dakin da Kuma me cutar nata daban,cikin abubuwan Daya siyo ya Bari masu yawa ciki ta Bude ledoji Aamna taga Naman kaza gasashiya ga tsire daban,ga wata Hanta me ruwa ruwa,sai pounded yam da Miyar Egusi shima a take away daban,Sai Lemuka kamar hauka da fruits ga kayan tea,ga plates da spoons,cups etc,komai an tanada,Ido Aamna ta zaro kenan,Mummy duk jikinta inda taji rauni yayi tsami ko Ina ciwo yake Mata Allah yasa Bata karye ba Sannan Bata Yi Mummunan rauni ba Wanda zai wahalar da ita,Dan Nishi tayi Tace Yar Nan zo ki taimaka min naje bayi,Aamna ta Mike da sauri tare da Rike Mummy ta taimaka Mata tana sannu…Sannu Baiwar Allah Sannu Hajiya me kudi Allah ya tashi kafada,Mummy sai da Aamna ta Bata Dariya yanda take Abu kamar tsohuwa,Mummy tace Yan Mata Kamar tsohuwa,Aamna Tace ai itace Hajiya shekarata ashirin da Hudu Babana yace na tsufa gashi naki aure,kin San Baba a Kauye ya taso shi yasa halinsa Bai canja ba,Mummy Tace Uhm,Bayan ta kaita har Toilet sai ta rufo Mata kofa ta fito,Mummy Tace Miko min brush da toothpaste Zaki gani Dana ya kawo,Aamna ta duba ta dakko ta kawo komai da Mummy ke bukata ta Kai Mata,duk Abinda Mummy zata Yi tayi ta fito,Aamna taje da sauri ta taimaka Mata ta kwanta saman bed,a Haka ta samu tayi sallolin da ake binta tayi Addua sosai,Aamna Tace Abinci fa Hajiya?Mummy Tace bani pounded yam din na Dan ci,Amma ta dakko ta zuba a plate tare da cokali ta Bude Hanta da kaza tare da tsire duk a Gaban Mummy,Fruits ma ta yanka sannan ta hada Mata tea me kauri ta zauna tare da sa Mummy a gaba kamar ta samu Yaron yaye,Tace yawwa mashaallah Bismillah ta yanko sakwara da Miya Tace to Hajiya ayi hankali gashi Naga gefen bakinki kin danji rauni tana ta Bata a Baki sunyi Shuru kamar ba kowa,Mummy tana ta ci Tace Baki magana ne? Me zance Mummy sai dai idan tatsuniya Zan miki,Mummy Tace sai kace wata yarinya bana so,Sai da Mummy taci da yawa sannan Tace na koshi,Aamna Tace to Naman fa? Ta Furta tare da ballo cinyar kaza ta mikawa Mummy.

Mummy Tace Alhmdllh na koshi,Aamna ta zaro Ido Tace Kazar Hajiya?kaza ce fa,Mummy ta girgiza Kai Alamar Bata ci,Aamna Tace inda ake arziki ba a tsiya Ni Bari na aikata,Nan Aamna taci Kazar Nan ta gaji ta ajiye sauran,taci tsiren taci duk sauran,Mummy kuwa kankana ta Sha taci Banana da Red Apple,Aamna Kam yau harka ta samu sai da taji zata yiwa kanta Illa sannan ta hakura,ta Mike kenan Tace Bari na wanke Hannu da kwanikan tana juyowa gabanta ya yanke yayi muguwar Faduwa ganin Ahmad a tsaye a jikin Kofa da Alama ya Dade a wajen,Fuskarsa ba kwayar Rahma a ciki,Idonta ta dauke a Kansa ta rabe ta gefensa zata wuce wani kamshi Wanda ba irin na dazu ba ya daki Hancinta sai da ta lumshe ido ba tare da ta shirya ba Haka ta wuce da sauri tayi waje,sai da ta wanke komai sannan ta dawo da su ciki ta Adana a tsaftace ta Iske Mummy da Ahmad suna magana da,Mummy tana ta Masa fada ya Bata Rai yayi Shuru,Aamna tana dawowa Mummy ta bar zancen,ita kuwa Aamna saman gadon da ba kowa ta kwanta tare da dakko Wayarta wacce take Ringing tana bukatar a kawo Mata dauki. Ganin kanwarta Zuhra ta daga da sauri,Tace Amarya bakya laifi,Zuhra ta zuba murmushi tana kwance jikin Angonta Adam tace nayi missing naki sis yau naji ban Iya bacci sai naji muryarki,Wallahi Aunty Amy Aure Niima ne,sai yanzu nasan Ni mutum ce Ashe a baya gunki ce Kawai,da ace nasan Haka ne da bazan Dade Haka ba zanyi Aure,Aamna Tace to me yasa bakiyi ba Ana Haihuwar ki ba,ai sai kiyi tun kina jaririya,Ke Aunty Aamna ke fa adawa kike da Aure,ki daina min sharri wa zai ki Aure? Kawai Ni abinda nafi so a aure shine na ganni Ina fasa kwai a kitchen Zan soya Ina kwas kwas a kitchen,Dariya Zuhra take yiwa Yayarta Kamar me,Aamna Tace ban San Iskanci Dan na fada Miki Buri na a Aure shine kike wani dariya,To Ni ba abinda nake so a aure face in cakare da kwalliya Ina kitchen Ina fasa kwai,Mummy tana bacci Ahmad Yana jinsu Amma wayarsa Kawai yake dannawa,Zuhra Tace Aunty to babbar Harkar fa ta soyewa? Aamna Baki ta tabe tare da Furta Dan tani a yanke shege na kowa a duniya a jefar,Ahmad Yana jinsu wannan Maganar Bai Gane me suke nufi ba. Zuhra Tace Aunty Amy Allah ya Baki kema Kalar da kike so Wanda zai biya sadakinki da shegen tsada,Aamna Tace ke na rage tsada na zaftare farashi na yanda su Baba suka damu Ina Ni Ina zaben Yawan Sadaki,Adam ne ya kwace wayar dake Hannun Zuhra tare da Furta sai da safe Aunty kitt ya kashe wayar Baki daya sannan ya ja Amaryarsa Suka kwanta ita kuwa Aamna kwanciya tayi itama tana latsa Wayarta gashi ta kasa bacci sabo da Ahmad Yana ciki Ta kasa kwanciya bare tayi bacci,Bacci ne ya dameta Haka ta kwanta tare da rufe jikinta da katon Hijab Nan take bacci yayi gaba da ita sai Ahmad shi Daya baiyi bacci ba,sai wurin 2am sannan ya bar Asibitin ba tare da kowa ya sani ba. Washe gari da Asuba Mummy ta farka da karfi a jikinta sosai kamar ba ita ba,Kawai rauni ne da Bai warke ba Amma jikinta fes taji,Da kanta ta lallaba taje Bayi gaba Daya kyankyamin Asibitin take Yi shi yasa ta kasa wanka,Sallah tayi itama Aamna Haka Bayan sunyi Brush da komai suna Azhkar Sai da suka Gama sannan Mummy Tace Aamna kike ko? Aamna Tace ae Tace Yau Zan sa a sallame Ni naji sauki Zan iya karasawa a gida tunda Ina da masu Aiki masu kula da Ni,Aamna tana murmushi tace mashaallah Alhmdllh Haka ake so Allah Kara lfy,Ameen Mummy ta furta,Biro da takarda Mummy ta mikawa Aamna Tace rubuta min Address dinki full sai accnt number dinki,Aamna ta karba ta rubuta komai,Nan take Mummy ta kunna Wayarta tayiwa Aamna transfer na dubu Hamsim,Farin ciki ya lullube Amy Tace Hajiya naji kararrawa na gode Allah ya Kara budi,Ameen Mummy ta Furta tare da mikawa Aamna katinta gashi ko Watarana Zaki neme Ni,Aamna ta karbe jiki na rawa. suna Haka sai ga Ahmad ya shigo cikin jallabiya fara Kar ta kirki,yayi mugun kyau,Nan take Aamna ta bishi da kallo a ranta Tace wannan Dangin Larabawa ne gaskiya,ko kallon Inda Aamna take baiyi ba ya koma wajen Mummy dinsa suka gaisa Yana ta murna taji sauki,Itama Aamna Bata kula shi ba ko gaisuwa,Kayan breakfast lafiyayye ya musu take Away Suka ci tare da godiya ga Allah,Wasa Wasa Mummy ba a sallame ta ba sai 4pm,Aamna tana gani Wata galleliyar mota tazo tare da tafiya da Mummy,Suka Yi Sallama Aamna ta shiga Napep sai gida,ta samu yan kudinta Bata da matsala abinta. Bayan Aamna ta dawo gaba Daya kayan da taje asibiti da su har na jikinta ta cire ta wanke fes tayi wanka dama a koshe take,Zama tayi a gefen Mama,Lokacin Baba ya fito daga daki yace yanzu Zuhra tana can a dakin mijinta tana zamanta lfy Abinta,abin kunya Yaya Guda Bata da ko saurayi ko me Gadi babu Wanda ke zuwa zance,Mama Tace an Rubuta Hatimin Annabi Yusufa har an gaji Shuru kake ji sai Neman kudi,Iskanci ne Kawai da samun waje shi yasa Taki fitar da mijin,laifinta ne cewar Mama Kuma kudinki kwandala mun daina karba kije da abinki,Aamna tayi Shuru har Suka Gama ta Mike tayi waje zuwa Kofar gida a kasa ta samu ta zauna dirshan tare da kurma Ihu iya karfinta tana wayyooooo…..Allah…..na shiga Uku na lalace…..Ina samari suke ko Dattawa ku fito ku Aure Ni,Dan Allah gani sadaka ga me bukata,,Ko me tallan rake ko Shoe shiner ko me Gadi,me Mata uku ma yazo Zan Shiga a ta hudu. Wasu ma tunaninsu tabin kwakwalwa ne ya kamata,sai Dariya akeyi Amma Aamna ko a jikinta,sai da taji Rana ta ishe ta sannan ta koma gida,tana Shiga Baba ya rike ta ram tare da zaro katuwar Sanda ya samu Aamna Kamar Allah ya Aiko shi ya shiga jibgarta kamar zai kashe ta,Mama tana Kara Mata Yar Iska mu Zaki kunyata a Unguwa,Ihu Aamna takeyi ga Yan hayar gidan ba kowa,Karshe ta tashi da kyar ba Mayafi jikinta duk kulun Sanda ne ko Ina da gudu tayi waje tana ihu,Baba baya gudun Abin kunya Kawai ya bita a million Suka zuba tsere layinsu rigarsa tana tashi Kamar mahaukaci Ana ta kallon ikon Allah,har saman Titi suna falfala gudu Baba Yana na koreki a gidana karki dawo daga Nan kiyi gaba,Aamna tana gudun masifa tana cewa wallahi sai na dawo me yasa aka haife ni,Ni Nace ku haife Ni Ina ruwana,Suna Haka zugar machininan su Ahmad Suka taho gaba Daya Suma sun kure wuta,Ganin Baba da Aamna suna falla gudu,Dariya ta kwacewa su Mashkoor, a wajen Suka ci birki,Ahmad ne ya bi Aamna da machine tare da sa hannunsa me laushi ya cafko Hannunta da karfi ya daga ta Kamar ya dauki tsinke ya cilla ta a bayan machine ta zauna daram,tana Jin dadi har da godiya Amma sai taga Ahmad yayi reverse ya juya da ita wajen Baba,Ta saki Ihu shi kuwa Baba zuciyarsa Dake tafarfasa yace Alhmdllh ya tsaya cak,a gabansa Ahmad ya Zana wani shegen kwabo da machine yaci birki sannan Aamna ta dire zata gudu Ahmad da shishigi ya samu ya yarfawa Aamna Mari ji kake gauuuu…..Nan take fuskarta ta kumbura ta zube a wajen kuwa,Baba yace na gode Dan Albarka,Ahmad ya kalli Baba da tsageranci yace Gata Nan Yi Mata dukan tsiya Ina Nan ba inda zata je,ko Kuma Ni yanzu nayi maka maganinta,Baba ya saki Baki yace Kai Malam Taya zaka marar min yata, Mace Budurwa ka mareta kalli yanda ka kumbura Mata Fuska,baka da hankali ne? Wata Mahaukaciyar Tsawa Ahmad ya yiwa Ba ba,Hey….tsoho,da sauri Baba ya rufe Baki jikinsa na mazari. Da yatsa Ahmad ya nuna Baba yace Kai tsoho baka Sanni ba Zan sa yarana su babbalaka,Baba yayi Mukus,Su Mashkoor suka saki Ihu da sowa,Kallon Aamna Ahmad yayi tana kuka,Tsawa ya buga Mata Dan Uwarki Ina Mayafinki? Irinku ne kuke sawa Ana yiwa Yara fyade a kasar nan,Dan uban Babanki Ina Mayafinki eyeeee yayi kanta da hargowa,Aamna ta Mike tsaye tana kuka Tace baka Gane Ni bane nice fa wacce nayi jinyar mahaifiyarka,wani dariyar hauka yayi yace ke dalla Ware so what Dan kinyi jinya,kyauta kikayi? Bar Nan wajen ko yanzu na Tara Miki gajiya,Aamna Tace wallahi sai dai mu Tarawa juna gajiya,Kai Malam Nifa ba ruwana muyi kokawa ba komai bane,baka Isa kaci min mutunci da Mahaifi na ba,sai mu Buda Nima fa Yar Tasha ce,tashancin Nan na Iya shi ta Furta tana dukan kirjinta,Tace baka San har yankan Aljihu nayi ba a kasuwa,su Mashkoor suka hangame Baki,Suka ga Kuma Ahmad Bai sa sun Mata duka ba,Jibson da Maganar Yan kwaya yace King kana fa jinta kana kallonta ka bamu Dama mu sassarata. Mutane tunda suka ga su Ahmad babu Wanda yayi gigin zuwa kallo Dan sun San halinsu,Baba ne ya cire Rigarsa daga shi sai wando dogo da Singlet ya mikawa Aamna yace lulluba mu tafi gida,Aamna Tace Ni a Haka Zan koma ba Kaine ka kwance min zani a kasuwa ba,ka biyo Ni Muna ta tsere Ana kallo duk da dama ai mun Saba,Baba zuciyarka bata da control Wai? Baba yace ai kece Aamna Yar Iska ce,kiyi aure kinki Ni fa duk na washe ki ma wallahi,shekara ashirin da Hudu zuwa da biyar ba ko saurayi,25yrs shine girma tsoho? Mashkoor ya tambaya,Baba yace ae ,to Jibson Yana tangadi yace to ke kiyi auren Mana,Aamna sai da tayi Dariya yanda ya fada da muryar maye,Baba yace ai Bata iya magana ba,Bata waye ba,kwana Nan Muka dawo birni,shekarar mu hudu kenan a birni,sai cin mutuncin samari takeyi na rasa yanda zanyi da ita tafi karfi na,Ahmad yayi Murmushi tare da da shafa gemunsa Yana wani rangaji ya furta Tsoho Bari na kaji idan tayi laifi Kawai ka kirani ka fada min har gida zanzo na kera maka ita,Baba yace na gode Dama ta ishe ni,ta gagareni,Aamna mamaki ya kamata,Tsawar data razana ta taji ance yafa rigar tsoho,jiki na Bari ta karba tare da yin Mayafi da ita,Tace wallahi sai na Rama Nima na iya tashancin,Baba yace kuce Mata ta taho mu tafi gida,da yatsa Ahmad ya nuna Mata Hanya ta juya salin alin tabi Baba suka tafi. Su Aamna suna tafiya wata Budurwa ta taho da gudu wajen Ahmad Tace Dan Allah kaga wani can Haka Kawai ya dameni da naci sai Maganar Batsa yake min nace bana sonsa yaki hakura Wai sai na bashi kaina ko yayi min fyade Dan yaga Kawai Ina tallan gyada tunaninsa Yar Iska ce Ni ta karasa da kuka,Ahmad Fuska a Murtuke yace Yana Ina guy din? Da yatsa ta nuna musu,Ahmad yace Boys kuje ku min maganinsa,ai kuwa Suka tafi Kamar an Aiko su Suka hau jibgarsa,sai da suka Masa ligi ligi sannan Ahmad ya karasa wajen tare da yarinyar,yace Kai Dan uwarka wannan kake so?Kai Dan Iska ne?zaka lalata Yar wasu Tace Bata sonka dole ne? Matashi Yana Nishi jikinsa duk jini Ahmad yace daga yau idan kaga wannan yarinyar hanyar da take idan kabi wallahi sai na yankaka,Matashin yace bazan sake ba,Zan gyara halayena,ayi Hakuri Oga,Ahmad ya Shure shi da kafa yace bace a Nan,ya tashi ya fece da gudu,Yace wa Yarinyar ki dinga saka Hijab idan Zaki talla,Tace to na gode yanlabai,ki daina talla ki Shiga makaranta ko kiyi aure,Tace to ai an kusa biki na Kuma Ina Islamuyya yace Good Ware ke ban son surutu,da sauri ta tafi tana murna. Tafiya sukayi sunyi nisa Suka samu wani yaro ya fisge Wayar wani a Hanya,Ashe Ahmad yaga abinda Yaron yayi ya arce,Sai da ya Bari Yaron yasha kwana sannan yabi bayansa,ya sauka a machine ya cafke Yaron a nutse ya dinga kashe Yaron da Mari yafi a irga tun Yana gani sai da Yaron ya sume,Wayar da Yaron ya fisge Ahmad ya karba tare da kwarawa Yaron ruwa ya farfado yace Kai barawo ko Nan take ya Kira police Suka Yi gaba da Yaron shi Kuma ya maidawa Babban mutumin da aka satar Masa,mutumin ya dinga godiya,yace yaro daga an kirani na dakko waya Kawai naji ya fisge,Ahmad Bai kulashi ba ya wuce gidansa Kawai su Mashkoor suka rufa Masa baya. Tunda suke tafiya Aamna kuka takeyi jikinta duk rauni,Baba yace kece dai kika jawo Kuma kin San Halina wallahi Sai in Miki jina jina,Aamna taci gaba da kukanta tana tafiya,Baba yace Jeki ki Siyo kayan Miya da Salat ki Shiga da shi gida,Aamna Tace bani kudin tana kuka,yace a aljihunki Ni Ina da kudi ne an fada Miki,Nima yau bazan ciyar da kowa ba wallahi tunda aka Dake Ni ta furta tana shesheka,Zan tsine Miki wallahi Aamna Naga kin rainani,Aamna tayi banza da mahaifinta,kwafa Yaja ya juya ya tafiyarsa inda zai je yace yunwa ta kashe ku, Zaki sani Zan dawo gidan ne,Aamna tayi tafiyarta da rigarta a kanta har Gaban me kayan miyar kusa da gidansu tana goge Hawaye tana sheshekar kuka Tace Dan…tala….Dantala… ba….bani kayan Miya na dari hudu…..Salat na na … Naira dariiiiiiiiiiiii……sai ta karasa da sakin Kuka me karfi a Gaban Dantala,Dantala ya saba da halin Aamna yasan Kuma yanda dama suke fada da Babanta,Yace kiyi Hakuri,ita rayuwa ko da wa zaka zauna sai kayi Hakuri Aamna,da girmanki da shekarunki haba Haba,Aamna ta sake fashewa da kuka Tace Wal….wallahi….wallahi tallahi yau bazan ci abinci ba da yunwa Zan kwana,Kuma na rantse bazan Taya Mama Aiki ba,Dantala Ina da zuciya,Kawai duk an bi an tsaneni akan ban samu Miji ba,a kauyen mu kowa sai ya fada min bakar magana bana Iya Shiga cikin dangi na sakata na Wala,Haka a gida ace Iyaye sun tsaneka,Dantala yayi Dariya yace sai hakuri Aamna,Tace wallahi Watarana za a ga na mutu a tsinci gawata Kawai,kiyi Hakuri cewar Dan tala ya zuba Mata kayan Miya ta bashi kudin ta tafi gida. Tana yin Sallama Mama ko kallonta Bata Yi ba,kayan miyar ta Ajiye zata juya Mama ta rike Hannunta caraf,Tace wa kike wa raini Wai? Waye sa’anki a gidan Nan Dan Kan uwarki,Aamna tayi Mukus Mama ta shiga zuba Mata Rankwashi ba adadi sannan ta saketa Tace tashi ko na nayi ball da ke, Aamna ta Mike ta fada daki tare da sake fashewa da kuka,Ita kuwa Mama girkinta ta shirya shinkafa da Miya da salat. Wato Islamiyyar Asabar da lahadin ma kin daina zuwa ko Aamna cewar Mama,Aamna Dake kwance a katifa ta fito Fuska a kumbure Tace na girmi Islamiyya Ni,Duk abinda ya kamata na sani na sani na addini sabo da Haka zanci gaba da saurarar wa’azi Kawai a gidan Radio ya isheni zaman duniya,a kyale Ni inji da matsalata,Ni yanzu ba karatu ne a gaba na ba,Alhadisissani,salisu duk na Iya ya ishe Ni,Sira da Ishmawi na haddace quarter,Zikiri na iya,Qurani saura Izu goma nayi sauka to me Kuma zanyi,gishirin zaman duniya na sani ya ishe Ni,Mama ta rike Baki Tace tab ke Baki ji kunya ba 25yrs Baki sauka ba,to ai da a sauke ba a Aiki da shi gwara ka samu Izu goma kayi Aiki da shi,Bulala Mama ta dakko Aamna ta jawo kujera ta zauna daram Tace a tafke Ni ai na Saba,kamata kullum a Duke Ni to a Dake Ni,Mama kuwa itama akwai zuciya Nan ta dinga tsulawa Aamna Bulala iya karfinta,har ta Gama Aamna ko motsi Bata Yi ba ta tashi a nutse ta shige dakinta,Haka Baba da dare bala’i yakeyi Kamar me,Ita kuwa Aamna washe gari sai da taje chemist aka Bata magunguna,tana dawowa ta Hado kayan sawarta a Akwati ta fito sanye da Hijab Tace Zan bar muku gidanku gwara na shiga duniya. Baba ko a jikinsa yace a gaisar da Yan bariki maza Kar dare yayi a dawo lafiya,Mama ta tabe Baki Tace sakarai,Aamna tana ta jira a lallashe ta ko ace Kar ta tafi Amma taji Shuru,Tace Zan tafi fa bazan dawo ba,Baba yace to,Duniya fa Zan shiga Mama,Mama Tace madalla,Juyawa Aamna tayi ta fara tafiya ba Wanda ya kulata har taje bakin kofa,Tace baza ku kirani ba Wai? Tsaki Baba ya ja,Aamna tayi waje kenan taga wata dalleliyar mota me tsada,Wata Dattijuwa ce ta fito a motar,da wani Dattijo shima fari ya fito,Aamna taji an kirata,Matar ta kalla sai taga Mummyn Ahmad ce cikin shiga ta Alfarma,Aamna fara’arta ta karu har kasa ta zube tare da Gaida su,Mummy Tace ga Baban Ahmad,Aamna ta sake Gaida shi tare da rike Hannun Mummy Suka Shiga gidan. Baba da Mama sunga masu kudi Nan Suka rude,Baba yace laaaaaa Alhaji Ja’afar Kaine a gidan Nawa? Wanda aka Kira da Alhaji Ja’afar yace ikon Allah Malam Hussaini Umar dama a Nan kake yanzu? Baba yace ae wallahi,me ya kawo ku?Aamna dai da Mummy suna mamaki aka shimfida musu Tabarma,Aamna ta kawo musu pure water da lemo,Nan ta ebo musu shinkafa da Miya da salat ta Ajiye,Tace Baba kasan su ne? Baba yace kwarai kuwa zauna kiji labari. Labari

AsmaBaffa
10/26/21, 8:51 AM – A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA🌵🌵

Page 16-20

FREE PAGE

DUNIYA TA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

         NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER TA
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

‘YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39

Official

By
AsmaBaffa

Page naku ne

MAMAN SAMHA
ZAINAB SABO
BK
UMMEEN SADEEQ
BASMAM GLAM
ALHUSNA(MRS IDRIS)

Ni Hussaini Umar kamar yanda kika sani mu Uku Mahaifiyar Hajiya Maryam ta haifa,Kuma mu kadai ne a wajen Mahaifinmu Malam Umaru,Ni Yan biyu aka haife mu Ni Hussaini da Hassan,Hassan tun Muna jarirai Allah ya Masa Rasuwa sai Ni,daga Ni aka Haifo Kawunki Isma’il sai Kanwar mu Kursum wacce kika Sani a kauyenmu Sokoto take aure,Munyi karatun Muhammadiyya har muka girma Noma da kiwo muka gado, tun baya dama mu Bamu taso a cikin kudi ba sai rufin asiri,sai da muka girma lokacin aka hadani aure da Aishatu Yar Uwa ce itama auren zumunci ne,daga Nan Bamu samu Haihuwa ba har Ismail yayi Aure shima a can kauye,sai da ya haifi Yara uku sannan aka yiwa Kursum Aure a kauyenmu itama ta Haihu Daya,duk Ni Allah Bai bani Haihuwa ba har Iyayenmu Suka rasu sai Yan Uwa da dangi,wannan da kike gani Shine Alhaji Ja’afar Wanda shima a Sokoto na sanshi Amma Asalinsu Yan Yemen ne kasashen Larabawa,kasuwanci ya kawo su Nigeria Sokoto suna da company Wanda a lokacin suna da Company na Yogourt da Kuma kamfanin Dake sarrafa Fulawa,sabo da Haka suna bi kauyuka suna siyen madarar shanu da Alkama Wanda a lokacin sana’ar mu kenan a wajen mu suke siya,mun Saba sosai muna mutunci da Alhaji Ja’afar lokacin ya Dade da Auren Mummy har da yaronsu Ahmad Yana shekara bakwai lokacin,su dama masu kudi ne da danginsu duk suna zuwa,ita Mum Yar Sokoto ce,bafulatana ce ya ganta ya aure ta sabo da sonta da yake Yi,Tun Bai Jin hausa har ya koya ya Zama Kamar bahaushe shima ga matarsa bahausa,Tunda yayi Aure ya dawo Nigeria gaba Daya da Zama Amma yanayin Lagos ya fiye Masa Dadi shi yasa yayi gida a can komai nasu a can,Ni Kuma mun Saba mun Shaku,Ja’afar yana tausaya min rashin haihuwa,lokacin akwai wata Yar Uwarsa Hajiya Sumayya,Sumayya marainiya ce gaba da baya sai Dangi Su Ja’afar kenan, Danginsa ce Amma Iyayenta sun rasu,a cikin Dangin Summayya Ja’afar shi ya taho da ita Nigeria ta Dan zauna a Wajensa na Dan watanni, a Nan ta samu wani Wanda shi a Nan Nigeria yake shima Kuma a Sokoto Amma shima asalinsa Dan Sudan ne,ganin balarabiya fara sai ya zauce sabo shi Yana da duhu ma bakin Balarabe ne,aka hada su Aure da Sumayya,Dan Sudan dai yayi Aure Bayan shekara Uku Sumayya ta Haifi Yarta mace kyakyawar gaske aka sa mata suna Aamna,Idan baza ki manta ba Aamna Ina zuwa dake wani gidan Yan Sudan a Cikin garin Sokoto birni,duk Hutu Ina kaiki wajen wasu Dattijai,Aamna Tace ae,Baba yace to kakanninki ne na wajen Uba Aamna,Wannan Ja’afar da kike gani Shine Dangin mahaifiyarki Sumayya wacce ta Dade da rasuwa,Katsam Bayan ta haife ki da shekara Biyu Babanki Rahil menk ya gudu ya bar kasar,aka Neme shi aka rasa,sabo da taurin Kaine da shi,bashi da tausayi, Jaafar ya Shiga Bincike Ashe karya yayi ya auri Sumayya matansa Uku a Sudan da yaransa manya,Ashe Auren sha’awa yayi ya gudu ya barta,lokacin Jaafar ya bani Amana Kan na kula da Sumayya,Muna Haka ciwon Hawan jini ya kamata daga Nan sai ta kamu da ciwon sugar Bata Dade ba sai ta rasu,Ja’afar yayi kuka dangi suka zo suka tafi da gawar mamanki aka binne ta a can kasar su,ke Kuma kina Yar shekara Biyu Ja’afar yace tunda bani da Yara Allah Bai bani ba Kawai na dauke ki ya bani ke halak na kula da ke. Ni da Aishatu munyi murna muka dinga kula dake sosai sabo da Alkawarin Dana dauka shi yasa kika ga na barki kinyi har HND na dage na biya Miki sabo da bana so kiyi kukan Rashi,sannan takurar Aure da kika ga mun dage sai mun Aurar dake muna gudun kar wata masifar ta afka Miki ya Zama kin lalace a Hannun mu,shi yasa muke so mu rabu lafiya,Aamna Hawaye ya shararo Mata Tace Amma Baba ita Zuhra fa Kuma me yasa kuka fifita a kaina? Baba yace Zuhra Bayan kin shekara Hudu a Hannun mu Allah ya bawa matata ciki ta Haifo min Zuhra,kin San zuciya da Kuma son Kai da son da na daban ne,wallahi bazan boye Miki ba,muna haifar Zuhra gaba Daya Muka ji tafi shiga ranmu,a Haka ma kokari mukeyi muna danne zuciyarmu Dan kar ace kin lalace a Hannun mu Amma har ga Allah Aamna munfi son Zuhra da ke,shi yasa Baba Ni ka Bari nayi school Wato na lalace ita Zuhra iya secondary tayi aure,sannan har Sweety Zuhra kake ce Mata fa.

Mama Tace ae ai munyi kokari ma duk abinda kike Mana ke rike kin ma ai munyi kokari bazan ji tsoron ki ba,Aamna Tace tunda na taso nasan Kuna duka na ku hantare Ni Ashe duk fakewa kukeyi da naki aure Ashe dama tsana ce?Mama Tace ke dalla fitsararriya lokacin da Danginki suka Yi watsi da ke shi Kansa Alhaji Ja’afar din gashi Nan ya sake zuwa ko duba ki,in Banda Dangin Babanki da muke kaiki kaf Dangin Uwarki ba Wanda ya sanki domin tunda Ja’afar ya Bamu ke ya tafi sai labari muka samu sun bar kasar ba a San Ina suke ba,sai dai Hana rantsuwa Muna Jin sunansa a Radio Yana tallafi iri iri a kasar nan.

DUNIYA TA AMNA complete hausa novel by Asma Baffa

Alhaji Ja’afar dattijon kirki me Kamala yace Bari Nima nayi magana,lokacin Dana Baku Aamna yarda da aminci tare da tausayawa yasa na Baku ita Amana,ku kanku Kun San Ina da arzikin rike ta,Kuma Dana Baku ita sai Dana Baku makudan kudade Wanda Aamna zatayi karatu har matsayin Degree,Kuma Ni bazan ce ba kuyi kokari ba koma Mene kunyi kokari Kuma mun gode Allah ya saka,Amma Kun San dai Aamna na bada gudunmuwa na kudin daukan nauyinta,Baba yace kwarai muma min Sha wahala da ita,Bata da kunya Bata da tarbiyya gata Nan,Aamna Tace ai tarbiyyar kuce Ni Kuma wallahi Ina da tarbiyya, Haka tunda na taso nayi wayo nasan Kuna nuna banbanci tsakanin Ni da Zuhra,Ni za ayi ta dukana har girma na,Ja’afar ne yayi murmushi yace ya Isa Haka,ke Aamna Har abada Iyayenki ne ban son sakarci,Mummy Tace ikon Allah Ashe Aamna ce Yar Sumayya shi yasa na rasa Ina na santa mashaallah,Ja’afar yace lokacin da Muka Baku Aamna bayan mun koma lagos Arziki na ya bunkasa,daga Nan Kuma Mummy ta Haifo Kanin Ahmad Saddeeq,na tattara Muka koma Colombia da rayuwa,a Nan aka haifar min Auta Humaira Wanda Candy zata Yi kwana Nan,Haka Saddeeq shi nutsatse ne yayi aure da matarsa harda yarsa,Zaman da Muka Yi a Colombia shi ya jawo Babban Dana Ahmad ya lalace da shaye shaye,na rasa yanda zanyi da shi wallahi,mun rasa ya zamuyi ya shiryu,abin ya dame mu,Alhaji Ja’afar ya nisa tare da cewa yaki aure bare yayi wani Aiki Sai dai kashe kudi ya sani Kawai da shaye shaye. Baba yace tab Ahmad din?Aamna Tace Baba shine fa Wanda ya mare Ni ranar Nan da ka bini Titi zaka Duke Ni ka tuna,Wanda ka karbi number dinsa Wai zai koya min tarbiyya? Baba ya daura hannaye a Kai yace lailahaillallahu wannan kwallon shegen Yaron Dan giya? Ai yayi suna kaf gari an San da zamansu,sai dai Kuma Yana da Dan Hali me kyau ta wani bangaren,Daddy ya kwashe duk abinda Ahmad keyi ya fada musu yace wani abin ma Sai Kun gani da idonku wallahi na rasa yanda zanyi,Ashe Aamna ke kika Yi Jinyar Mummy? Dariya Aamna tayi Tace ae Daddy,Baba yace ja’ira Ashe ma Dan uwanki ne,Baba ya kalli Daddy yace game da matsalar Danka Ahmad Kawai a bashi Auren Yar Uwarsa Aamna a daura musu Aure ku Kai wa shege ita gidansa,Ni Kuma nasan Aamna itama irinsa ce Dan ba mutuncin gareta ba suje can suyi ta fadansu har a samu ko Allah zai shiriyarsu sabo da itama Aamna ba wata ta kirki bace Tace ta daina Zama ta gari,Nan take Daddy yace Kuma fa Haka ne Ahmad Yana bukatar jajirtacciyar mace marar tsoro,Mummy Tace hmm ai Ni Naga Drama a Hospital suka dinga fada da juna ba Wanda ke barin wani idan Haka ta faru zanfi kowa murna,Aamna kuwa Hankalinta ya tashi matuka sabo da tasan ma Ahmad kashe ta Kawai zai yi,Kuka ta saki Tace yanzu Dan shaye shaye za a bani? Sabo da anga Uwata ta mutu ubana ya gudu ya barni shine za a min Haka,Mama Baki Bude Tace Aamna mene Haka? Dan Uwanki ne fa,ai Hannunka baya rubewa ka yanke ya Yar, yo tun yaushe da azaba ta ishi mutum Nawa aka Yi Hannu da kafa mutum da Kansa zai kai Kansa Asibiti yace wayyo Allah Likita yanke min na huta cewar Aamna,Mummy Hannun Aamna ta riko tare da mikewa ta ja Aamna gefe tana Mata magana a kunne cikin Rada,Aamna ta washe Baki Tace to na yarda. Baba ya tabe Baki yace Alhmdllh Allah ya yanke Mana zaman Yahudanci,Daddy kuwa Dariya yayi kawai sannan yace akwai wani gidana Babba ne Dana Gina a Nan Kaduna ba nisa da Nan Unguwar Taku na mallaka maka shi halak malak,sannan Zan baka Million Uku ka ja jari,Baba Hanci ya rike kamar mace ya rangada Guda Ayyiriririri….,Dariya Aka dinga yi,Ranar dai sai da suka Gama shirya komai Har dangi an Kira a waya cewar Nan da sati Daya za a daurawa Aamna Aure, kowa yayi mamaki,ikon Allah Wato aure idan yazo wani shi kanshi a shekarar Bai San zaiyi auren ba,Aamna dai ko a jikinta sabo da sun Gama shirya sirrinsu da Mummy ba Wanda ya sani,Gidan da aka bawa Baba Suka tafi har furniture an zuba a gidan, flat madaidaici me dauke da part biyu,ko Ina yasha tiles ga flowers da komai,gidan a kalla zaici mota Hudu a ciki iya wurin parking,Aamna da Mama sai Murna,ranar Abba ya bada kudin auren Ahmad dubu dari biyu Suka tafi cike da murna,Zuhra Suka sanarwa komai murna Kamar me Ita kanta Zuhra dama ta Dade da sanin basu da Alaka da Aamna ko a kamanni Aamna da Larabawa take Kama,Ita kuwa Zuhra Ana ganinta anga Yar Mama da Baba,Yan Uwa da abokan azirki Suka dinga zuwa ganin sabon gidan su Baba,Aamna a waya ta Kira Kawarta Siyama ta fada Mata komai,ai Siyama Murna Kamar tayi hauka ga Kuma mamaki Aamna ba Yar su Baba bace Ashe Shuru akayi,Amma duk da Haka Aamna ta Sha Jin zancen a Kauye,idan ta tambayi Mama ko Baba sai suce karyar mutane ce,,Aamna zata ma riga siyama Auren ma Ashe,Washe gari tare da Siyama aka maida kayan su Aamna na bukata sabon gidansu,Faisal saurayinta shine ya dinga jigila da motarsa har Suka tare,Baba Kuwa Ya samu ya fara Harkar Sana’arsa ta siyar da kayan masarufi jari ya samu. Tunda an San Auren da za ayi ba Wani shiri aka Yi ba,Saura kwana biyu daurin Aure Mummy,Daddy,Mufida matar Saddeeq da Yarta,sai Humaira Auta da Sadeeq Suka taho Kaduna gaba Daya a gidan Ahmad Suka sauka,Yana ta Fushi shi fa an takura Masa da zuwa Masa gida,Bai San Aurensa za ayi ba. Ranar cikin dare Mummy ta haura sama Bedroom dinsa, Yana kwance Yana latsa wayarsa me tsada ga barasarsa a gefe Yana korawa,Mummy ta kalle shi tare da Zama saman Bed din,Yana ganinta cike da shagwaba ya dawo da Kansa saman cinyarta,Yana kallon Fuskarta Idonsa sai wani lumshewa sukeyi sunji kayan maye,Wata kwaya ya dakko a kasan Pillow ya watsa a cikin kwalabar giyar ya jijjiga,Nan take kwayar ta narke a ciki Yace Mummy Dan Sha kiji Zaki samu nutsuwa yanda na ganki nasan akwai damuwa,Murmushi Mummy tayi Tace please ban son hauka Ahmad,Ni zaka kalla ka Bawa kayan Maye?Dariya yayi yace to Mene ciki Dan kin Dan caake kema,Tsaki ta ja,Tace Magana nake so muyi,Ahmad yace Ina jinki Beautiful Mum,Harara ta watsa Masa Tace gobe ka shirya zamuje gidan Wasu Yan Uwan mu a gaisa,Nazo maka da manyan Kaya su zaka sa muje kaji?Baki ya turo yace kin San dai Ni bana gaisar da mutane,idan so kike kiji kunya Kuma to kije Dani Dan wallahi babu Wanda ya Isa nace Ina kwana ko Ina Yini bani da wannan lokacin,Mum Tace ae naji muje Haka,Yace sannan Kuma zanje da Giyata ne kin San bana Free karki ce ban fada Miki ba. Mummy ta jinjina Kai Tace Ahmad me yasa baka da tarbiyya da biyayya ne Haka? Ina mahaifiyarka duk abinda kaga dama fada min kakeyi,Baki ya tabe yace kin San dai bana karya gwara na fada Miki gaskiya,Kansa ta zame Dake kwance a cinyarta da sauri ya rike Mum yace please Mum zauna ki Sosa min Kai nayi bacci,sai kayi aure idan Haka kake so ai, Dariyar Yan giya ya shiga Yi ba ji ba gani yace Aure….Tab ai kuwa sai dai a dauki gawar matar,Mummy ta tsorata Tace Idan Muka daura maka fa Auren da ita sai me? Yace kisa ne hukuncinta,kasheta zanyi,Ni na tsani mata bare wani Aure Dan Allah Jeki Good Night ya furta, Tsaki taja Tace wannan Drugs din da kake Sha sune suke kashe maka sha’awar Mata fa,zaka yiwa kanka Illa,Murmushi yayi yace ai gwara Haka akan nayi Zina,Tsaki ta jasannan tayi ficewarta. Washe gari da Yamma Mummy ta kulle Ahmad a bedroom ta hanashi fita,Yana ta dukan kofa a bude shi Amma Mum Taki,yace aski zanyi fa yanzu I promise you wallahi Zan biki muje can,Sai lokacin Mummy ta Bude shi ya Sha ya bugu Yana tangadi ya fito ya fice,Machine ya Haye sai wurin Aski,Ai wani gashi Attach ya Siya Red and green yace ayi Masa calaba kitso me kyau,Gefe da gefe an kwashe gashin kadan,daga sama Kuma gashi Nan da yawa,Ai kuwa aka Masa calaba me Dan tsayi Suka zubo a kafada kadan,gemunsa ma Haka aka Masa Yar karamar calaba daga tsakiya da red attach,Kyawun da yayi ba a magana ka rantse daga England ya dawo,Kowa ya kalle shi zai rantse wani mugun arnen bature ne ba musulmi ba,Amma Fadin irin kyan da yayi Bata Baki ne sai dai ba tarbiyya idan an gani,duk inda ya gifta da machine sai Kallonsa akeyi,Mum suna Palo Suka ga ya dawo,Su kansu sunga kyan da yayi Amma Kuma bana Tarbiyya bane,Mummy tasan Halinsa Tace Kayi kyau,yace naga gidan da zamuje kin dauke shi da muhimmanci shi yasa nayi gyara na musamman. Sadeeq ya tabe Baki yace Amma ba tarbiyya ba,Zan ci Uwarka yayi Kansa Mummy ta rike shi,Mufida Tace Kayi kyau,yace yawwa matar mu,Humaira ma Tace Yaya Allah ya bani Miji me irin kyanka,Hannu ya Mika Mata Suka tafa yace Ameen,Ai Ni Handsome King ne,Daddy ya tabe Baki yace Kai dalla sakarai je ka shirya mu wuce, Ahmad Daddy yayiwa wani kallo ya Haura samansa Yana cewa azo gidan mutum a Dame shi,Gidanka ne Dan Ubanka gida na kace gidanka cewar Daddy shima,Mummy Tace Dan Allah karka jawo ya fasa zuwa ta bi bayan Ahmad tana lallashinsa Kar ya biyewa Daddy. Toilet ya Shiga tare da banko Kofar kamar zai ballata,Wanka ya sheka ya fito,Mummy tana gefen bed,ya shafa lotion ,Fuska ya Bata yace Mummy Zan cire Towel ki fita,Mummy tayi Dariya Tace to Babban mutum,Sai da ya Gama kalailaitarsa sannan ya kwalawa Mummy Kira,ta shigo da sauri da wata Arniyar farar Shadda me tsadar gaske Gezna,Harda Hula yace ohhhhh…..wannan Zan saka?….na shiga Uku wayyoooo ya Furta Yana zaga dakin kamar zai saka wuta a jikinsa. Ohhhh Mum….Mummy… Mummy….Mummy yake furtawa Yana zagata a dakin,Tace Ahmad Ni din ko? Fuska ya Bata yace na fasa zuwa akan na saka wannan kayan,Tace Dan Ni fa zaka saka,Ohhhhh…..ya sake furtawa Yana girgiza kafadunsa kamar Yaron yaye, Dariya Mummy tayi tare da fisgo Hannunsa ya zille Yana ta Bata wahala sai da kyar ya tsaya ya saka Boxers Kamar zaiyi Ihu Haka ya saka wandon Shaddar wani dai dai shi cif kamar an gwada dinkin zamani fitted na matasa,Singlet Mummy ta bashi ya saka sannan ya saka Rigar Shaddar me Hannu dogo links cif cif shi,ba karamin Arnen kyau yayi ba,Hula kuwa Mummy sai hakura tayi yace bazai saka ba,Haka ta barshi,tana kallo ya dakko farar sarkar Azurfa ta maza wata Yar siririya karama ya saka,Mummy Tace Kayi kyau kuwa Amma sai dai a hausawa ba tarbiyya bace,Yace Mum ku ai local ne Baku San wanka ba Sam,takalmi fari half shoe ya saka,wayarsa kuma Silver color,Glass Brown and white ya saka,Kowa ya kalli Ahmad yasan ba karya Allah yayi halitta a Nan,Mummy tana murna ta fesa Masa turaruka ya tsaya a gabanta yace ya kika gani,Babban yatsa ta daga Masa,Murmushi yayi Suka fito,Ai duka su Daddy sakin Baki Suka Yi suna kallon yanda yayi azabar kyau,Daddy farin ciki ya kamashi Allah sarki mahaifa,yace da ace Haka kake Yi duk da dai kitson da sarkar ba tarbiyyar hausawa bace ai da yafi sauki sauki, Sadeeq yace the Handsome King,Humaira Tace wow I’m proud of you Yaya King,Comfirm…Confirm ya Furta Yana wani basarwa yace Ina Mufida? Da sauri ta fito dauke da Yarta sun Sha gayu Suma,yace kinyi kyau matar mu, Sadeeq yace Kanin miji ne ke wannan wasan ba yayan Miji ba,Baki Ahmad ya tabe yace ku kuka San wani Kani da Yaya. Ko da aka zo shiga mota Ahmad yace Bayan anyi min gorin mota harda kwace motoci na a machine Dina zanzo,Daddy ne ya balbale shi da masifa Kai wanne irin banza ne Wai? Ana gabas kana Yamma dalla je ka shiga waccen motar,Ahmad yace wancan bakar Haba ai sai dai ku ku koma cikin bakar Ni da Mum mu Shiga fara ko na fasa tafiyar wallahi ku baku san wanka ba,Dole Haka Daddy ya kwashe sauran a Daya motar baka Sadeeq ya tuka su,Mummy kuwa suna fara ita da Ahmad sun hakimce a Bayan mota Driver Yaja Suka wuce sai sabon gidan su Aamna. Aamna kuwa dama Mummy ta sanar musu da zuwansu sabo da Haka ita da Siyama Suka shirya abinci iri iri sannan suka Yi wanka,Aamna ta shirya cikin wata sabuwar bakar Truskysh gown me adon Golden,tayi masifar kyau sai ta fito Kamar wata balarabiya,Baba ma Tasha shaddarsa,Mama tasa Atamfarta maroon,Siyama kuwa an zuba lace dark Green,Mama ce ta ja Aamna Bedroom ta zaro wata laya ta makale Mata a kanta cikin gashinta,Aamna Kamar tayi kuka Tace Mama har yau Kuna wannan shirkar ga ta Rannan a kaina kin hanani cirewa layu har biyu,Mama Tace ke dalla ta farin jini ce,Haka aka sawa Aamna dole ta yafa mayafinta Wanda ta Sha acuci,Wani guru Mama ta sake dakkowa tace lallai sai Aamna ta Daura a Hips dinta, Aamna zata Yi kuka Tace wallahi kin San naci kashinki da fitsari idan na tsine Miki sai ta Kamaki,Zan tsine Miki idan Baki daura ba,Aamna tana gani ta dage Riga har wandon ciki aka daura guru sannan ta maida kayan ta fito palonsu hadadde Kamar zata Yi kuka ta zauna tana Danna Yar Wayarta Vivo. Suna Haka Suka ji shigowar motoci,Aamna gabanta ya fadi,Siyama kuwa tuni ta leka ta window har Sanda Ahmad ya fito ta haukace gaba Daya tana lallai Aamna wallahi ku Larabawa ne da gaske gashi na gani,kalli danginki Kan uba kaga wani tantirin Dan Iska Amma duk yafi kowa kyau da iya wanka,Aamna ta Mike ta leka itama tace ai shine Angon,Siyama Tace Yau mun Shiga Uku kashinki ya bushe da gani Zaki ci Ubanki,Aamna Idonta ya kawo kwalla Tace wallah bazan taba sonsa ba,Dan giya ne,idan Kuma ya shiryu fa cewar Mama,Aamna Tace Idan ta dalili na ne sai na yarda Ina sonsa idan ya shiryu sai na gudu na barshi Kinga na taimaki Iyayensa,ko Dan Iyayensa Zanyi sabo da yanda suke mutanen kirki masu taimakon musulmai Bai ci ace suna da Dansu irin wannan ba,Siyama Tace bafa a Wasa da so,karki Bari ya kamu da sonki kice Zaki Wasa da zuciyarsa idan ya Gane ba sonsa Zaki ba kin Gama yawo,na Baki shawara idan Zaki so abinki ki soshi karki ce ban fada Miki ba Aamna ba a Wasa da zuciyar mutum a so,Aamna Baki ta tabe Tace wannan Zan so? Zan dai je da yanda Mukayi magana da Mum,ba ruwanku. Sallama sukayi aka amsa kowa ya shigo a nutse,Baba Yana musu Sannu da zuwa,Nan da Nan Su Siyama suka cika gabansu da Abinci sai lokacin Ahmad ya shigo ya tsaya Yana waya a waje,Ganin Aamna ya bashi mamaki yace Kai keeee……Aamna ma Tace kaiiiii……Ran Ahmad ya baci yace Wai Mum dama gidan wannan zamu wani zo? Daddy yace zauna Malam,Ahmad yace Ni bazan zauna ba Ku Gama mu tafi Ina da abin Yi,Siyama Tace tab a ranta,Zuhra ce ta shigo Amarya taci gayu Adam ya sauke ta,Itama gaisawa akayi ta zauna,Ahmad fafur kin Zama yayi ya zuba Hannu biyu a Aljihu ya tsaya kerere Kuma ba Wanda ya gaisar ko kallon arziki Bai musu ba,Baba shi Kam murna yakeyi Aamna ta samu Miji sai ya kalli Ahmad yace Sannu Sarkin matasa,na baka Sarautar Sarkin matasan Nigeria,Ahmad wani murmushi ya saki ba shiri,Aamna ta wani washe Baki itama ganin irin kyan da yayi,a Haka Daddy ya bada tarihin Aamna da dangantakarsu da Ita,Tsaki Ahmad ya ja tare da zaro Yar karamar kwalabar giyarsa a Aljihu ya kwararawa makoshinsa,Aamna ya kalla ya galla Mata Harara tare da cewa daina kallo na,Tace na kalleka din Kai da wanne idon ka kalleni,ransa ya sake tunzura ya kwada Mata Mari a saitin Idonta Nan take ta durkushe ta saki kuka,Da sauri taro ya watse aka dauki Aamna zuwa Asibiti,shi kuwa Ahmad a waya ya Kira Mashkoor ya dauke shi a machine suka Yi tafiyarsu. Daddy kamar bakin ciki ya kashe shi ransa ya baci ganin yanda aka mannewa Aamna Ido Daya da auduga da plasta Kuma akace Nan gaba sai an Mata aikin Ido,Tunda suka koma gida Basu ga Ahmad ba har kwana biyu ta cika Wanda itace Ranar daurin Aurensa Bai Sani ba.

ASMAU complete hausa novel by Fatima Rabiu

Mummy a waya ta Kira Ahmad ta sanar Masa da Aurensa,ya zaci Wasa ne ya dinga dariya yace Mummy kina da abin Dariya to idan hakane a daura Auren na Amince, Mummy tayi Dariya Tace ka yarda kace? Yace Yeah..Yana dariya Wai Wasa ne, Daddy kuwa ya tattara mutanensa Dana Baba a masallacin Unguwar har Mashkoor ya sa aka Nemo su duka sabo da Suma su Zama Shedu,Ahmad Yana can gidan Mashkoor Yana ta sheka bacci, Ranar Juma’a Ana Idar da Sallar Juma’a da Shedu walliyan Amarya da wakilin Ango suka karbi Aure Nan aka Daura Auren Aamna Rahil Menk da Ahmad Ja’afar Yabalash, Kan sadaki dubu dari,Su Mummy lefe suka yiwa Aamna na gaske Akwati goma Sha biyar,Ahmad ranar ya dawo gida sai gani yayi su Baba duk sun Hada kayansu zasu tafi ba Wanda ya kulashi,Mummy ce ta shigo Bayanta Aamna Amarya ce sanye cikin wani material Brown yasha kyau,idon Aamna Daya yasha plasta a manne da Daya take gani,Yana ganin Aamna ya Mike yace me wannan takeyi a Nan Mum?Mummy ta Bata Rai matuka Tace matarka ce Ahmad,Daddy ya shigo yace yau Shedu sun sheda an daura maka Aure da Aamna Yar uwarka Kuma marainiya sannan da Amincewar aka daura, ta Zama Amana a wajenka,ka sani Aure ba Wasa bane,idan kayi shirme Allah bazai Barka ba,Kuma wallahi ka koreta ko ka Mata Illa ban yafe maka ba Ahmad.
Mummy Tace gata Nan wallahi kaji bazan rantse a banza ba babu Wasa yau aka Daura muku Aure shi yasa nace Rannan ka bimu muje na kaika ne Dan kaga surukanka,Nima kaji na rantse Idan ka koreta ko kayi gigin sakinta bani ba Kai ban yafe maka ba,Kuma Matukar ka saketa Allah ya Isa Nono na daka Sha,sabo da Haka gata Nan Amana da kayanta,Nan Ahmad yaga me Gadi Yana ta shigowa da kayan lefe Yana kaiwa sama Daya dakin da ba kowa Wanda Mummy ta zabawa Aamna a matsayin nata,duk abin bukatar Aamna an kawo Mata abinta,daga Nan Mummy Tace Mashkoor ku shigo,Suka shigo suna tangadi,Mummy ta kalle su Tace gwara da kuka zo yau nasan ku shaida ne a gabanku aka Daura Auren Ahmad sabo da Daddy da Kansa ya gayyace ku Kuma Kun gani,Mashkoor yace kwarai King a gabanmu aka Daura muna ta so mu fada maka Amma wayarka Taki Shiga gaskiya ba a kyauta Mana ba,anci Amanarka King a gabanmu muna gani aka Daura Sadaki dubu Dari Daddy ya bada cewar Jibson.

Bash yace Kuma Daddy yace kayi aure yanzu mu rage zuwar maka gida wannan fa ba Adalci bane King,Ahmad da yayi mutuwar tsaye yace shima cikin kwaya me yasa Baku Hana an daura Auren ba,me yasa Baku rotsewa liman Kansa ba,Daddy ya kawo securities ko Ina King,Ahmad yace Good za aga abinda ba a so kuwa,Mummy Tace kaji dai gargadi Kai ka sani,ta kalli su Mashkoor tace lalatattun banza ku fita muje marasa tarbiyya,Haka Suka fito ransu a bace,Ahmad Yana kwalawa Mummy Kira kizo Mummy ki tafi da Yar mutane,Zan Mata Illa,Zan kashe ta ne,kizo ki tafi da ita,Mum….Mummyyy…..Ahmad ya dafe Kansa kwaya ta motsa Nan ya Shiga hauka da tangal tangal a palon,Aamna tana kallonsa a ranta Tace kaddara ta hau kaina na shiga Uku,me yasa na yarda aka Daura Auren,Wayar Hannunsa ya tarwatsa da kasa,Wandonsa Kamar zai Fado zabar Ass down na iya shege,Ya kalli Aamna yace ke bi Mummy ki tafi kafin na kashe ki yanzu,Aamna Tace wace zata bi Mummy? Ai wallahi Zama daram sai dai mu mutu tare,Zan Miki Illa fa,Illa ai ka rigada kayi min ita tunda ka nakasa Ni ka maida Ni me Ido Daya,waye zai aure Ni a Haka,ai Ina Nan a matarka Zama daram wallahi yaro baka Isa ba kayi kadan Aamna ta Furta da karaji tana dukan Table,yace ke Ni Zaki nunawa hauka,Kai din wa Kai din me,me ka Isa kayi,Ai ransa ya Gama baci ya bita da gudu Suka tafi tare,ta haura Sama da gudu zuwa dakinta tana shiga ya damko gashinta,Tace wallahi ai dambe ne Nima na Iya Suka rukuma kokawa. Kici kici suna Nishi Kamar zakaru,ya dauketa ya makata a saman Bed,ya bita zai jibgeta ta samu tare da makalkale shi ta cikwikwiye shi,Taki bashi damar dukanta,gata da karfi itama Suka dinga kokawa Baji ba gani,sai da suka gajiyar da kansu sannan ya saketa ya dawo Palo ya zauna a kujera Yana maida numfashi kamar Wanda yayi tsere Itama palon ta dawo gashinta ya watse ta zauna tana Nishi itama taji jiki. Yana Nishi yace kin gaji kenan?,Tace na gaji a Ina ai ban gaji ba sai dai mu mutu wallahi,yace to Bari na huta na samo power kiga yanda zanyi da ke,Aamna Tace Nima Bari tawa power din ta dawo ka gani idan Zan kyaleka.

FANSA 2022 complete hausa novel by Sa’adatu Kilishi ceJoin Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

About Mr Hausa Ebooks 1438 Articles
The Power of pen