50 Views

Ba za’a cire rubutun Ajami a kudin Nigeria ba cewar Khalifa Sunusi Lamido

 Ba za’a cire rubutun Ajami a kudin Nigeria ba cewar Khalifa Sunusi Lamido

Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category News
Uploaded On 01 Nov, 2022
Upload Time 9:30 am
Last Modified Date November 7th, 2022
Last Modified Time 12:09 am
Hits 50 Views
Comment No Comments

Ba za’a cire rubutun Ajami a kudin Nigeria ba cewar Khalifa Sunusi Lamido

Khalifan darikar Tijjaniya na Najeriya, malam Muhammadu Sunusi II, ya magantu akan maganar sauya fasalin kudin Nageriya.

a cikin wani jawabi daya gudanar a zaman karatun littafin addinin musulunci na madarijul Salikeen da yake gabatarwa duk mako- mako, Malam Muhammadu Sunusi II, yace “yayi magana da gwamnan babban bankin kasa Najeriya kuma ya tabbatar masa babu batun cire rubutun ajami a daga jikin kudin Najeriya.”

Malam Muhammadu Sunusi II, wanda shine sarkin Kano na 14 ya kara da cewa “tun da aka fara yada maganar cire rubutun ajamin yayiwa ma’aikatan Babban bankin magana kuma suka bashi tabbacin babu tsarin cire rubutun sai dai da maganar tayi kamari ya tuntubi gwamnan bankin kan batun, saboda cewa yadda yaga hankalin al’ummar musulmi dama malaman addinin musulunci kan batun inda Shima ya tabbatar masa cewa baza acire rubutun ajamin daga kudin Nageriyar ba “.

Khalipan, yaja hankalin malaman addinin musulunci kan su daina yada jita- jita wajan yanke hukunci kasar, cewar yadda suka ringa maganganu daban daban akan batun .

Ba za’a cire rubutun Ajami a kudin Nigeria ba cewar Khalifa Sunusi Lamido

Maganar sauya fasalin kudi da gwamatin taraiyya zatayi taja hankalin al’umma inda kowa yake baiyyana ra’ayinsa gami da lamarin, yadda wasu ke Ganin Kara ruguza tattalin arzikin kasar ne zata Kara rugujewa talakar kasa yasha wuya, wasu kuma na Ganin hanyace ta yin ram da barayin gwamnati.
Allah ya tabbatar ma kasarmu nijeriya da Alkhairi.Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

About Mr Hausa Ebooks 2222 Articles
The Power of pen

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*