1029 Views

ASMA’U Chapter 03 End – Hausa Novel

 ASMA’U Chapter 03 End – Hausa Novel

Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 18 Dec, 2022
Upload Time 6:47 pm
Author

Writer Group Unknown / NIL
Novel Genre

Comment No Comments

ASMA’U Chapter 03 End – Hausa Novel

By Fateemah

Kashi na daya 01

BISSIMILLAHI

MANZON ALLAH (SAW), YA CE: (IDAN BAWA YANA SALLAH SAI AZO DA ZUNUBANSA A SAN’YASU A KANSA DA KAFA’DUNSA, DUK LOKACIN DA YAYI RUKU’U KO SUJADA SAI WA’YANNAN ZUNUBAN SU FA’DI DAGA GARESHI.)

Washe gari

Ma’u ce zaune a flour tana kallo Mamee ta fito tace yauwa diya ta xakiyi ma yayanku Abdallah abinci zaiyi bako abokinshi xaizo Ma’u tace to Mamee saiga kairat suka shiga tare kicin suka fara aiki suna cikin aiki kairat tace ya Muhammad ne xaizo, wllhy yana da mutumci yafi yaya Abdallah mutumci, Ma’u tace hmmm nidai ba ruwa na bari yajiki wllhy ai kairat najin haka tace wai rufamin asiri, nan suka gama abincin suka je suka kai shashin ya Abdallah nan sana sauka dawo.

Ma’u kuwa hawa sama tai ta shiga toilet tayi wanka tasa riga da siket batayi wata kwalliya ba amma tayi kyau sosai kayan sun amsheta kamar dan ita akayi su.

Tana zaune bakin gado tana dan daddane wayarta kairat ta shigo d’akin itamah har tayi wanka tace yauwa Ma’u taso muje friend din ya Abdallah ya iso ya Muhammad Ma’u ta d’auki gyralenta ta yafa tace muje suka sauka kasa.

Mamee na zaune tace ai kuwa yanxu suka fita yaxo ya gaida ni suna shashin yayan naku sai kuje ku gaida shi saiku dawo tohm suka ce suka wuce.

Suna kan hanyar shiga shashin yayan nasu kirat tace kinga gobe Monday akwai school kuma ni da wuri xan shiga school Ma’u tace nima da wuri xan shiga ina da, text ne.

A haka dai har suka shiga da sallama suna zaune duka har sun gama cin abinci suna zaune suna fira, Muhammad ne kadae ya amsa musu shi kuwa Abdallah tunda suka shigo yake aikin kallon Ma’u ranshi ya baci wai saboda mi xata sa gyale, wani irin kishi ke taso masa, sun gaida su suka fice.

Shi kuwa Muhammad yace abokina dan Allah wannan yarinyar wacece gsky tayi min, ai Abdallah cikin wani irin kishi yace to kai kuma baka da aiki sai kallon ‘ya’yan mutane to wllhy an mata miji, Muhammad cikin wasa yace kai abokina ko dae kai ke sonta ne naga fa kishi cikin idanka, Abdallah yace kadai jida shi Muhammad yace kai dae za’ace ma kadai jida shi amma intayi tsami maji, Muhammad ya qara cewa tunda an hanani wannan to ina son kanwarmu kairat, Abdallah bako kunya yace tohm in wannan ce an baka Muhammad ya yayi murmushi yace to godiya nake.

Karanta : GIDAN DADI complete hausa novel by Oum Aphnan

Bayan kwana biyu

Ma’u na zaune a d’akinta tana karatun jarabawa (EXAM) dan exam din qarshe suke ta gama school kairat ta shigo tace Ma’u wai ya Abdallah yace kije ki gyara mai d’aki, Ma’u cikin takaici tace tohm Ma’u a cikin zuciyarta kuwa bata san zuwa shashin shi kwata-kwata dan idan taje duk wata kalar wahala saiya sata haka yake mata inta gyara mai d’aki daya shigo saiya ce baiba saita sake duk wata kalar wahala ya iya sata kuma ita kad’ai yake ma wannan abun ta rasa mita mai, wani lokacin ta zauna taita kuka shin dama ita kad’ai ke sonshi ita kadai ke aikin banza gashi wani irin so take mai duk abinda xai mata bajin haushinshi take ba amma kullum addu’a take Allah ya sassauta mata sonshi a ranta.

Haka nandai ta tashi taje ta gyara mai d’akin Allah yasuta baya nan bayan ta gama ta na zaune a flour, Mamee tace yauwa kairat yau zaku fita sayayyar ne kairat tace eh Mamee tace to ga kudin duk abinda kuke so saiku saya, suka amsa sukayi godiya.

Bayan sallar la’asar suka shirya zasu fita Ma’u kuwa tasa wata atanfa mai shegen kyau dogowar riga ce saita yafa mayafi tayi rolling dinshi tayi kyau sosai sun fito sukayi ma Mamee sallama da yake yanxu dukansu sun iya mota to yau kairat xata tuqasu, sun fito kenan ya Abdallah ya shigo gidan ya hangi yadda Ma’u tayi kyau a cikin zuciyarshi yace badae fita xasuyi ba ai danda nan ya nufi gunsu, yace kai ina zaku kairat ta bashi amsa tace fita zamuyi sayayya, ai danda nan ranshi ya baci ya nuna Ma’u ke kuma a haka xaki fita Ma’u kuwa ta kalli jikinta taga dai ba wani aibu a shigar datai a zuciyarta tace inba dai bakin ciki kake minba karna fita, shi kuwa Abdallah yace to wllhy kika fita haka bakije kika sa hijabi ba saidai ki fasa fita maxa kije ki canxa wannan shigar.

Ma’u kuwa har ta fara hawaye cikin takaici tace mah kairat kije ki sayo duk abinda ya kamata ni na fasa zuwa tana gama fadar wannan ta shiga ciki da gudu tana kuka ta rasa mita tsare mah ya Abdallah a rayuwa shidai inbai quntata mata ba, baijin dadi, kairat kuwa ita ma cikin takaicin yayan nata ta shiga mota tana mai cewa shi kuma yaya haka akeyin soyayyar sai girman kan tsiya baxai je ya fad’a mata cewa yana sonta ba amma inya ji uwar bari ya fad’a ne haka dai kairat taita mita harta isa tayo sayayya ta d’akko hanyar dawowa gida.

Ma’u kuwa tana shiga flour ta tadda Mamee zaune ai saita fad’a kanta tana mai fashewa da kuka Mamee tace Subhallahi minene d’iyata Ma’u cikin kuka tace Mamee wai ya Abdallah ne yace wai saina sa hijabi zan fita Mamee tace jiki kira manshi a’a Mamee karki mai magana Mamee tace to ya haka xai dinga matsamiki ne tashi kije ki kiran minshi nace koh, Mamee ki rabu dashi na hakura Mamee kuwa cikin murmushi tace to shikenan amma inya sake zai gane kuranshi ne a cikin zuciyarta kuwa tace ooh kukumah haka soyayyar taku take, Ma’u kuwa tashi tayi ta haura sama ta shiga d’akinta.

Shima a nashi bangaran Abdallah yaji ba dadi abinda yayi mah Ma’u amma wllhy duk kishinta ne yake ja indai akanta ne bai iya saita kanshi.

Bayan kwana 2

Ma’u ce fitowar ta kenan daga EXAM tana jiran kairat su wace gida, kawai tana tsaye saiga wani saurayi yazo kusa da ita yayi sallama yace yan mata ta amsa sallamar sa can saita hango Abdallah cikin mota tasan su yaxo d’auka dan yau basu zo da mota ba ai tana ganinsa saita qara biye ma wannan saurayi taga shin yaya Abdallah zaiyi shin yana sonta da gaske koko.

Karanta FANSA 2022 complete hausa novel by Sa’adatu Kilishi ce

Shi kuwa Abdallah yana hango su ai wani irin kishin da bai taba ji ba shike taso mashi ai cikin bacin rai ya fito daga motar ya nufo su, Ma’u kuwa tsoro ya dirar mata yarda taga ya nufo su idon nan nashi ya kad’a yayi jawur da bacin rai.

Ai kuwa yana zuwa bai xaya wata-wata ba ya daga hannu ya wanka mata mari ya juyo wajan saurayin yace kai kuma na qara ganinka da matata wllhy saika gane kuranka, ai saurayin cikin firgici yace dan Allah yi hakuri bansan matar aure bace.

Kunji masu maratu Abdallah ya shararo qarya wai matarshi har ta xama malol.

Ma’u kuwa ta dafe kumatunta tana mai zubar da hawaye tasan dama hakan saita faro, Abdallah kuwa jan hannun ta yayi ya sata a mota sai gida ko tsayawa baiba d’aukar kairat.

Suna isa ya jata sai shashin shi ai Ma’u sai cikinta ya qara dorar ruwa sai aikin hawaye take suna shiga ya jata kan kujera ya zaunar da ita ita kuwa mutaniyar taku hawaye kamar an bud’e famfo, shi kuwa so yake ya lallashe ta kukan nan da take har cikin ranshi yake jinshi.

Ya xauna kusa da ita yace dan Allah my kiyi hakuri wllhy duk sonki ne da kishin ki ne ya jawo, ai Ma’u cikin farin-ciki a zuciyarta ta danne farin-cikin tace, ni baka sona duk wahalar dani da kake yi wllhy baka sona cikin tashin hankali Abdallah yace wllhy ina sonki ki yarda dani, nan dai Ma’u saida ta bashi wahala da tabara iri-iri, hada cewa wani saiya rera mata wakar soyayya lol.

Ai kuwa Abdallah yace ai kuwa bari na rera miki wakar nan ta mawakin nan wato (TASI’U TK), ai kuwa masu karatu Abdallah ya fara rera waka, bari muji xan iya rera muku wakar kamar haka ( INAMA INAMA ACE IN NUNA WANAKE SO AMINI AURE INAMA INAMA  ABANI DAMA DAGA YAU ZUWA GOBE NA TURO INAMA INAMA NAGANMU NIDA KE MUNA MURNAR AUREINAMA INAMA NAZAMA ANGO KE KUMA AMARYA KONA HAU SAMA DOMINKI ZANA SAUKOKIN TUNA RANAR DANA HADU. DAKE KO KINA TA DARIYA KIN SAKA ANKO ASSALAMU ALAIKUM NACE MIKI KOH KAMAR DAKE DA ITA KONAMUKU HUTO KOH INAGA NA TUNA KOH BABY YAHYAH KINA DA KAYA KINA DA KYAU IN KIKA SA BAKIN ABAYA GAKI DA HANKALI SANNAN AKWAI BIYAYYA SABODA KINA DA KYAU.), Wai masu karatu a nan zan tsaya da wannan wakar ta masoya.

Ai Ma’u cikin jin dadin wakar tace kai mawakin nan ya kamata abashi kyautar mota wllhy wakar tayi dadi so sweet, Abdallah yace ai TASI’U TK ya iya waka sosai nima ina son waqoqinshi, nan dai wannan waka daya rero mata ita ta shirya su, ai kuwa suka fara zuba soyayya, cikin sanyin murya yace Ma’u shin kina sona kuwa, Ma’u cikin kunya ta d’aga mai kai ai kuwa da sauri ta tashi ta ruga da gudu sai shashinsu.

Tana shiga ta tadda har kairat ta dawo Mamee kuma tana sama kairat tace ah Ma’u wannan farin ciki haka kodai an fada soyayya da yayan nawa ne Ma’u cikin murmushi tace ke yanxu fa na xama Auntyn ki ah ah lallai kinkau xama qara da kika gyara man ai karna kira sunanki a gaban yaya yaman rashin mutumci nan dai su kaita fira cike da son yan uwan su.

Abdallah kuwa tana fita cikin farin-ciki harda yar rawar shilol yau ji yake kamar an sashi aljannah wadda yake so kamar ranshi ita mah tana sonshi ai yau ji yake ba wadda ya kaishi sa’a a rayuwa.

To a nan xan daka ta masu karatu.

Ngd sosai da irin qaunar da kuke nuna min

Kashi na Biyu 2

BISSIMILLAHI

FATEEMAH RABI’U

BISSIMILLAHI

MANZON ALLAH (SAW), YA CE: (WANDA YA FARKA DAGA BACCI KUMA YA FARKAR DA MATARSA SUKA YI SALLAH RAKA’A BIYU, ALLAH ZAI RUBUTA SU A CIKIN JERIN MASU AMBATONSA DA YAWA MAZA DA MATA.)

Bayan wata daya

Abubuwa da yawa sun faro, a inda su Ma’u sun kammala school dinsu, cikin nasara, a inda kuma ansa ranar Ma’u da Abdallah kairat mah sun daidaeta da Muhammad duk a tare za’ai bikin nanda, wata biyu.

Mamee ce zaune a flour dasu Ma’u ta tasasu a gaba suna shan kayan gyaran jiki, Ma’u tace wllhy Mamee wannan abubuwan duk ba dad’i Mamee tace ai zasuyi muku amfani ne ita kuwa kairat sai zunburu baki take wai bata sha Mamee tace wllhy zan bata miki rai saikin shanye shi, maxa ku shanye kuban kofinan, haka badan sunso ba suka shanye tas.

Ma’u ce zaune a d’akinta can taji wayarta na qara d’auka tayi Abdallah ta gani mai kiran cikin farin-ciki ta dauki wayar tare da, shagwobe murya cikin sanyin muryarta tace my ykk yace lpyl amma fa wllhy ina kewarki Mamee ta hanani shigowa shashinku wai har sai an kawo minke, xan iya jurewa kuwa, Ma’u tace xaka iya mana duka saura y’an kwana ki fah my nan dai taita kwantar mai da hankili sukayi sallama cike da so da qauna.

Rayuwa nata tafiya lokaci na qaratowa bikin su Ma’u yau saura kwanah biyu yau, alhamis zasuyi wa’axi.

Anyi wa’azi mai ratsa jiki, Ma’u ce zaune dawowarsu kenan daka wajan wa’azi kairat tace wash Aunty Ma’u wllhy duk na gaji, Ma’u tace nima wllhy nan dai suka zauna cikin abokan airxiqi, sai jansu ake anah amare-amare.

Washe gari

Ranar juma’a duban jama’a suka sheda d’aurin auran, Abdallah Abubakar and Asma’u mudi, sai Muhammad Rabi’u and Kairat Abubakar, auran ya samu halartar manyan mutane, cannah hango angwoye bakin nan yaqi rufuwa, sai gaisawa suke da jama’a ana musu Allah yasa alkhairi bare mah Abdallah ji yake yau ba wanda yakai shi barin, ciki.

Ma’u ce da kairat zaune, a gaban dady da Mamee suna musu nasiha su kuwa sun rungume juna sai kuka sukeyi, nah rabuwa da juna, Mamee tace kunga dai bautar Allah zaku yi nayi bari na bari, komai d’an hakuri ne, aure komai cikinshi hakuri akeyi, dady ma ya dora da tashi nasihar.

Kairat aka fara d’auka sana Ma’u da yake itamah ba’a cikin gidan su Abdallah xai ajeta ba yayi gidanshi daban.

Bayan kowa ya watse, Ma’u ce zaune da akan gadonta har yanxu kaku takeyi, Abdallah kowa sauran friend dinshi ya raka, sai tsiya suke mai.

Gaskiya gidan Ma’u ya hadu sosai ba abinda dady bai musu ba duk iri daya da kairat ba abinda ya banbanta musu.

Abdallah ne ya shigo ya tarar da ita har yanxu kaku take ya matsa kusa da ita ya jawota a jikinshi yace haba dan Allah my ki daina kukannan haka ya isa kar kisa min kanki ciwo, ya share mata hawaye yace tashi kici kaxarki, tace na qoshi dan itafa wllhy mah tsoran shi take ji, cikin rarrashi Abdallah yaita bata a baki har taci ta koshi yace to ki shiga wanka daga nan kiyo alwala xamuyi sallar godiya da Allah, cikin sanyin jiki tace to, shima fita yayi dan yayi wanka shima, Ma’u kowa yana fita itama ta shiga wanka.

Bayan ta fito tah shafa mai da turare saida ta shafa ako ina lungu da sako na jikinta sana ta d’akko miski ta shafa a kasanta, saita sa wata riqar bacci mai laushi, mai kyan gaske iya karta guwa, sana tasa hijab har qasa ta zauna tana jiran Abdallah, shima bai dad’e ba ya shigo ya jasu sallah raka’a biyu kamar yarda addini ya koyar bayan sun sallame ya kama kanta yana karanto addu’ar da Annabi ya koyar yayi mata tanbayoyi tana bashi amsa daidae da yarda ake wankan tsarki ta bashi amsa daidae kamar yadda addini ya koyar.

Karanta NIDA QANINA SUDDES

Bayan sun gama Ma’u ta tashi ta cire hijab dinta ai Abdallah yana toxali da kyakkyawar surarta ai saiya tasu ya rungume ta, Ma’u kuwa duk tsoro ya cika ta, qarfin hali kawai take dan tayi alqawarin bazata hanashi hakkinshi ba amma wllhy duk tsoronshi take yarda yake rawar qafar nan tasan baxai raga mata ba ai bata mah gama tunani ba taji ya daga ta samah bai sauketa a ko inaba sai a kan gado, ai bata ankara ba taji bakinshi cikin nata yana yima ta wani shu’umin kiss to a nan na jawo musu qofa.

Bayan sati biyu

Mamee ce ta kira Ma’u a waya take ce mata gobe xasuje qauyen su Asma’un Ma’u kuwa sana tana jikin Abdallah a kwance cikin sanyin murya tace tohm Mamee Allah ya kaimu sukayi sallama Abdallah yace maganar tafiyar gariku ne Ma’u tace eh to Allah ya kaimu Ma’u tace amin.

Washe gari

Tunda asuba suka tashi suka shirya, Abdallah ya shiga mota Ma’u ta bud’e gaba ta shiga, suka wuce gidan Mamee, suna isa suka tadda kairat itama da mijinta har sun iso bayan sun gaggaisa dady yace tohm yanxu zamu iya tafiya, duk suka fiffito Mamee mota daya da dady sai kairat da mijinta ma haka Ma’u mijinta Abdallah ma daban.

Suka d’au hanyar qauyen su Asma’u Ma’u kuwa farin-ciki duk ya cikata yau zata ga qawarta khadija, sun isa lpy tunda suka shigo garin yara da manya sai kallon motocin suke duk da, gari ansamu sauyi ba laifi amma hakan baisa Ma’u kasa gane gidansu ba, haka tai musu jagora har gidansu Ma’u ta fara shiga gidan ba kowa ciki duk ya lalace, Ma’u kuwa harta fara hawaye Abdallah ya rungume ta yace yanxu ina kika sani, tace mai gidan su qawarta khadija nan mah tayi qoqarin gane gidan su khadija suna isa su Mamee dasu Ma’u suka shiga gidan sunyi sallama mamar khadija tana tsakar gida ta amsa tayi musu iso ta shinfida musu tabarma suka zazzauna tace sannunku da zuwa, Ma’u cikin sanyin murya tace mama baki ganeni bako mama tace gaskiya kam Ma’u tace ASMA’U ce ai mama cikin al’ajabi tace Ma’u kece kika komah haka Allah mai ikoh nan Ma’u tace muna tare da mijina wannan kuma yayar mamata ce ta nuna Mamee nan dai tayi mata baya nin su mama tace Allah sarki tohm Ma’u tashi ki shigo dasu, bayan sun shigo ta kawo musu abinci ba nuna wani abu suka ci mama taji dadi da babu ruwansu ba girman kai, nan Ma’u tace mama ina khadija ne mama tace khadija tayi aure ai tuni amma a cikin garin nan tayi harda d’a daya, Ma’u tace Allah sarki tohm bari muje gidanta nan mama tasa wani yaro ya rakasu har gidan khadija, ba laifi tayi aure gidan hali itamah, nan ma dai su Ma’u suka shiga da sallama khadija kuwa fitowarta kenan daga d’aki taji ana sallama ta amsa su Ma’u suka shigo ai duk da canzawar da Ma’u tayi bai hana khadija gane Ma’u ba, cikin tsantsar farin-ciki khadija tace wanake gani kamar Ma’u, Ma’u tace nice qawata ai da gudu suka rungume juna suna kukan farin-ciki, bayan komai ya lafa tayi musu iso har su dady suka shigo tayi musu shinfida suka xauna, ta kawo masu ruwa, bayan sunsha.

Ma’u tace khadija wannan yayar mamana ce ta nuna Mamee wannan kuma mijina ne nan dai ta bata labarin komai tunda ga zuwanta birni cikin al’ajabi da jinjina ikon Allah tace kai amma na miki murna wllhy, Ma’u tace wai khadija naje gidanmu naga ba kowa duk ya lalace ina Innah take, khadija tah sauke numfashi tace, bayan tafiyarki da safe Innah taita nemanki gidanku ba inda bata dubaba amma bata ganki ba ga kudin Ilu tace na aurenki gashi Ilu baida imani akan kudi Innah fah tabi ta rude, ai nan gari ya rud’e wai kin gudu ai Ilu labari na zuwa wajanshi ya tattara mashaya abokanshi na shashanci suka nufi gidanku, yana zuwa bako sallama suka fad’a gidanku ai Innah na ganinsu ta kama karma Ilu yace inah matata Innah cikin matsanancin tsoro tace ta nemeki ta rasa gashi ta cinye mishi kudi, ai nan yasa mashaya suka taru sukayi mah Innah dukan kawo wuqa, saida suka karya mata kafa daya da hannu daya, sukayi tafiyarsu suka barta yashe tsakar gida, tunda ga nan ta fara nadamar abinda tai miki, sai dai mahaifiyarta sa’ade tazo cikin kuka itamah da dana sani ta maida Innah wajanta tana jinya bata iya komai kullum cikin kuka take tana a nemuki ki yafe mata yanxu tana nan an yanke kafa daya da hannu daya saboda ba’a kaita asibiti da wuri ba, ba kudi sadda za’a kaita duk sun rube, sai dae aka yanke su, har yanxu tana can tana jinya cike da nadamar abinda tai miki, to kinji abinda ya faro da Innah bayan tafiyarki.

Ai Ma’u cikin kuka da tausayi tace Allah sarki Innah wllhy nah yafe miki duk wanda ke wajan saida ya d’an tausaya mata, Ma’u tace yanzu to muje wajanta inganta khadija tace lallai Ma’u wllhy samun irinki sai an tuna, gaskiya kina da zuciya mai kyau kinsan tunda abin nan ya sameta garin nan wasu suce Allah ya qara wasu kuma suce ai hakan shiya dace da ita dan alhakinki ne ya kamata, Ma’u tace ni badan wannan xanyi ba Annabinmu yace wadda ya saka ma da sharri kai ka saka mishi da alkhairi, khadija tace hakane to muje duk suka fito suka nufi gidansu Innah.

Karanta BAKAR INUWA…!!!

Sun shiga da sallama aka amsa musu mamar Innar ce zaune a tsakar gida ga Innar a gefe xaune ba kafa daya ba hannu daya duk ta rame ta fita hayyacinta, ba wadda ya gane ASMA’U daga cikin su bayan sun zauna Ma’u kuwa kusa da Innah ta zauna tana ta kallon yarda Allah ya mayar da ita dama Ma’u ga tausayi ai kuwa sai aikin hawaye take, sa’ade mamar Innah tace amma bayin Allah bamu shaida kuba, cikin sanyi murya Ma’u tace ASMA’U ce Ma’u nan ta basu labarin duk abinda ya faro da ita tunda ta bar qauyen, ai Innah tun kamin taji qarshan lbrn ta fara kuka, tana cewa Ma’u kece kika komah haka harda mijinki wa’innan duk danginki ne Allah mai iko dan Allah Ma’u ki yafe min abinda nai miki Ma’u itamah cikin kuka tace Innah na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe manah baki daya, ai Innah cikin jinjina alkairi irin nah Ma’u tace ngd ngd kinji nan Ma’u daxasu baro gidan taba Innah kudi masu yawa da ita da mahaifiyarta ai kuwa cikin jinjina kirki irin nah Ma’u sai godiya suke suna mata fatan gamawa da duniya lpy, kwanan su biyu a qauyen su Ma’u sadda zasu tafi taba qawarta khadija kudi tace taja jari masu yawa Abdallah mah yaba mijin khadijar kudi shimah masu kauri, ai ko sunsha godiya suka rabu cikin kewar juna inda khadija tace xata zo har inda Ma’u take insha Allahu, sai kuma suka nufi garin su mahaifiyarta garin su Mamee kenan.

Bayan sun isa an musu tarba taban mamaki bayan sun huta Mamee ta gabatar musu da Ma’u duk tai musu bayani akanta ai rannan Ma’u taga gata yan uwa sai nuna fata so sukeyi a inda suka nemi yafiyarta na cewa wllhy suma bayin kansu bane suka manta da ita a inda Ma’u tace na yafe muku wllhy, kwanan su uku suka dawo kano cike da tsaraba ta yan uwa bayan dawowar su da sati daya khadija taxo gidan Ma’u ai taga duniya tayi mamaki Ma’u ce zaune a wannan gida taje gidan Mamee harda na kairat mah satinta daya ta komah cike da abin arziqi.

Bayan kwana biyu

Ma’u ce zaune a flour kan cinyar Abdallah sai zuba mai shagwoba take yace my kin hada min ruwan wankan cikin wata irin murya data kashe mai jiki tace na had’a mah yace to ki taya ni wanka manah ai Ma’u najin haka ta tashi ta shige kicin tana mai gwolo yayi murmushi yace xan kamaki ne ai, Ma’u kuwa tana gani ya shige daki ta dawo kan kujera ta zauna , wayar Abdallah ta hanga kawai saita d’auketa ta shiga cikin wayar ba ki cikinta, saita shiga wajan picture tana kallan hotonan shi yayi bala’in yin kyau a zuciyarta kuwa wani son mijinta take qara ji yana shigarata da kishinshi can kawai taga wani pic dashi da wata mace ta riqe mai hannu, ai cikin gigicewa da wani irin kishi da bata taba jin irinshi ba taji hawaye nah zubu mata, aje wayar tayi ta shige d’akinta da kulle ai saita fad’a kan gado tana mai rushewa da kuka ji take kamar tai hauka wllhy wani irin kishin mijinta ke taso mata ta fara magana a fili tana cewa, ashe haka kishin yake ashe haka mata suke ji Ya Allah ka sansauta mun wannan kishi kaku take iya qarfinta, shi kuwa Abdallah yana fitowa yaga bata flour ya dauki wayarshi yaga pic dinda Ma’u ta gani ai cikin tashin hankali shi wllhy ya manta da wannan pic din ya dad’e yaje dakin Ma’u yaji ta kulle ya bubuga amma inah can kuma yaji sautin kukanta, Yah salam yace nan ya zauna yana magiya ta bude amma tayi kunnan uwar shigu dashi dan wllhy haushinshi ma take ji, ga lokacin sallah ya kusa inata kiran magari ba, sai kawai ya tashi ya wuce masallaci.

Ita kuwa Ma’u tana jin ya fita sai taje ta bud’e dakin ta je tayi alwalla taxo ta tada sallah tana rokon Allah ya sassauta mata wannan abin da take ji a ranta, kuma Allah ya qare mata mijinta daga sharrin duk wata mace, hartai sallar ishsha’i tana mai qara hawaye har yanxu ta kasa tsaida hawayenta, haka har bacci ya d’an figeta, can saiga Abdallah ya shiga gidan dakinta ya qara hawa ya taba kofar sai ya jita a bud’e, yai hamdala ya shiga d’akin ya hango ta, kan sallaya tana bacci a hankali ya matsa kusa da ita, ya tallafo ta, ya rungume ta yaga harda yan hawayen da tasha kuka a fuskarta, Ma’u kuwa cikin bacci taji kamar an rungume ta saita bude idonta taga Abdallah cikin sauri zata tashi daga jikin shi ya qara rungume ta yana mai cewa wllhy pic dinda kika gani wllhy na murnar gama school dinmu ne kuma ni bansan ta riqe min hannu ba saida aka dau hoton nah lura kuma karki so kiga abinda ne mata kuma wllhy wadda kika ganta a hoton tamayi aure, Ma’u cikin sauke ajiyar zuciya ta qara rungume shi kamar xa’a amshe mata shi tana mai qara fashe mai da kuka, tace dan Allah mijina karka juya min baya wllhy ina sonka, baxan iya jure ganinka da wata y’a mace ba dan Allah mijina wllhy ina sonka ina qaunarka ta qarashe maganar da wani kukan, cikin sanyin jiki Abdallah ya qara rungume ta yace nimah ke kadai kin isheni rayuwar duniya nima ina matukar qaunarki kinji matata, Ma’u zata qara wata maganar yai saurin hade bakinsu yana kiss dinta cikin lokaci kadan ya fita hayyacin shi ya d’auke ta, sai kan gado, to nan nah jawo masu qofah.

BAYAN SHEKARA HUDU

Wani tangameman gida na shiga cannah hango wata Hajiya tana zaune a daya daga cikin kujeron flour tana dannah waya dagowar da xatayi wai masu karatu kunsan wacece Ma’u ce ta qara kyau ta qara zama babbar mace hutu ya zauna cikinta, can saiga wasu yara guda biyu mace da namiji kyawawa dasu sun rugo sun fad’a jikinta suna mai cewa mommy kinga Abby suka nuna Abdallah shimah ya qara kyau da zama babban mutum, wai baxai kaimu islamiya ba yau sai dai dire ba ya kaimu, Ma’u tace yau Abbyn ku ya kaji ne kuje dire ban yakai ku kunji yan albarka ta basu alawa cikin murna suka amsa sukayi waje.

Abdallah kuwa matsowa yayi kusa da Ma’u yace ina alfahari dake a matsayi mata ta gari kuma uwar yara nah ta gari, Ma’u ma tace nima haka mijinah ta mai rungume shi.

ALHMDLLHI

Anan nah kawo karshen wannan littafi kuskuren dai a ciki Allah ka yafe min darasin dake ciki kuma Allah ya bada ikon amfani dashi.

Ngd sosai da irin qaunar da kuke nuna man sai mun hadu a sabon littafina mai suna, WATA RANA SAI LABARI, yana nan tafe insha Allah.

Nice taku HAR KULLUM FATEEMAH RABI’U CE ðŸ˜

Ngd sosai aminan kirki irinsu

Hauwa’u Ballo
Ameenatu
Fateemah yunu
Aisha sani adam
Hauwa jos
Khadija salisu
Fateemah I b
Sa’adatu R
Minasanuabd.

Da duk wanda baiji sunan shi ba ina godiya a gareku sosai yan uwa

Love you all

Phone number 08130479973

Chapters na BayaJoin Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

About Mr Hausa Ebooks 1438 Articles
The Power of pen