954 Views

ASMA’U Chapter 02 – Hausa Novels

 ASMA’U Chapter 02 – Hausa Novels

Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 18 Dec, 2022
Upload Time 6:38 pm
Author

Writer Group Unknown / NIL
Novel Genre

Comment No Comments

ASMA’U Chapter 02 – Hausa Novels

By Fateemah Rabiu

Kashi Na Daya 1

Bismillah

Asma’u ce zaune tana ta uban wanki Innah ta fito tana cewa wllhy idan baki wanke su suka fita ba saikin maimaeta su, kuma ki gama ki debo min ruwa a rafi,

Ita dai Asma’u to kawai tace mata haka ta dirji uban wanki ga shi ta gaji matuqa, amma ya zatai.

Haka ta tashi ta nufi rafi saida tae sahu uku na dibar ruwa, haka ta dawo gida nan ma bata huta ba saida tai sanwa Innah ta bata wani dan abin ci haka tai hakuri ta ci,

Ke Asma’u zoki daukar min tallar goro cewar innah kuma wllhy idan kudi na suka bace hmm ki kuka da kanki.

Ku Karanta BAGIDAJIYA CE complete hausa novel by Hassenart Mohammed

Haka Asma’u ta dauki tallar goro tana hawaye ita dai wllhy bata son tallar nan amma yaxa tayi dole tai hakuri, haka taita zagawa a garin amma ba wani ciniki,

Ta gaji ga rana da akeyi haka ta samu wata yar bishiya ta zauna ta buga tagumi Ma’u taji ankira ta tasan bame kiranta da wannan sunan sai, qawarta Khadija, ta sauke mata tagumi tace haba Ma’u lpy kike tagumi dan Allah ki qara hakuri, komai mai wuce wane, Ma’u tace nasani amma khadija wllhy na gaji ne Allah ka kawo min mafita, Amin cewar khadija, amma dan Allah ki qara hakuri kinji Ma’u insha Allah, haka khadija taita ba Asma’u shawara mai kyau dama khadija ita ke ba Asma’u baki da shawara mai kyau, qawarta ce tare suka tashi, khadija nada kirki gata da sanin yakamata tana son qawarta Asma’u sosai kuma tana tausaya mata rayuwar da take ciki.

Wannan kenan

Haka Ma’u ta koma gida jiki ba qarfi tana shiga Inna na zaune dama ita take jira ai tana ganinta tace bani kudi na Ma’u ta miqa mata cikin tsoro ai Innah na ganin batayi ciniki sosae ba, ta kamata ta hau bugu baji ba gani, har wata mata ta shigo tana cewa haba dan Allah waike Zainabu baki da imani ne yar marainiyar Allah kina ta cutar da ita duk garin nan ansan abinda kike mata, ai Innah najin haka ta gama basifa ke kuma miye naki a ciki dallah ni fitar min daga gida, matar tace zan fita masu gida, amma kisani kiji tsoron haduwarki da Allah tana gama fadar wannan ta fice daga gidan, ita dae Ma’u tunda ta samu aka saketa ta shige daki ta aikin kuka, Inna kuwa sae masifa take kamar an ara mata baki.

Haka rayuwa Ma’u taeta tafiya cikin wahalar rayuwa ba wani canji, bayan kwana biyu Ma’u ce tafe daga gani talla ta dawo xata gida, kawai tana cikin tafiya, taji ansha gabanta, dagowar da zatai taga Ilu tsaki taja tace dallah mlm kawuce min daga hanya.

Ilu kuwa ya sheke da wata dariya irinta mashaya yace ke wllhy ko kinki ko kinso saena aure ki, Ma’u taimae kallon sama da kasa tace wllhy da in aure ka gara na mutu ba aure, tai tsaki ta wuce.

Shi kuwa Ilu binta yayi har gida ita batama san ya biyu ta ba saida ta shiga gida sana taga wani yaro ya shigo yace wai Ma’u tazo inji Ilu, ai Innah najin haka ke Ma’u wuce kije Ma’u tace nifa Innah baxani ba, Innah tace iye lallai yarinyar nan kin raina ni, wllhy kuma nanda sati biyu za’ai auranki da Ilun sae dai ki mutu, ai Ma’u najin haka ta wuce daki tana kuka, itafa wllhy duk yarda za’ai bazata auri Ilu ba.

Haka qawar ta khadija ta shigo gidan Innah na bakin murhu tana sanwa taji sallamar khadija ai ko amsawa batayi ba, bare ta kalli inda take, khadija bata damu ba danta san hali duk wani wadda yake son Ma’u tsakani da Allah Innah ta tsane shi,

Haka ta wuce dakin Ma’u ta iske ta tanata aikin kuka, khadija tace Subahallahi miya faro kuma Ma’u ta fada jikin khadija tana mae kara fashewa da kuka mai cin rai tace wllhy khadija bazan iya auran Ilu ba koda zan mutu ne, khadija tace nifa ban gane ba iman bayani yarda zan gane, nan Ma’u ta bata labarin duk abinda ke wakana.

MIJIN NOVEL complete hausa novel written by Lubna

Khadija tai shuru can tace aiko ni bazan bari ki auri mashayin giya ba kamar Ilu insha Allahu nasan mixanyi Ma’u tace khadija tohm miza kiyi, khadija tace kedai ba sunce nanda y’an kwanaki za’ayi auran ba tohm ana saura kwana biyu auran da suke ikirari za’ayi zanzo in gaya miki mina shirya kinji daena kuka, haka khadija taita kwantar mata da hankali.

Tohm masu karatu a nan zan daka ta.

Shin mi khadija ta shirya ne masu karatu ko biyo ni duk zaku samu amsarku, a babi na gaba.

Ngd nice taku har kullum FATEEMAH RABI’U CE
[3/4, 4:09 PM] Fateemah R🥰: ASMA’U (MA’U)

Kashi Na Biyu 2

BISSIMILLAHI

MANZON ALLAH (SAW), YACE: DUK WANDA YAKE SON ALLAH YA AMSA MASA ADDU’ARSA A LOKACIN KUNCI DA DAMUWA, TO LALLAI YA YAWAITA YIN ADDU’A A LOKACIN DA YAKE CIKIN AMINCI.

Asma’u ce zaune tayi tagumi tana tunin wane shiri ne khadija takeyi akan wannan auran daza ai mata can kuma ta girgixa kai duk ita kad’ai take magana, tace yanxu gashi har saura kwanah biyu kuma banga khadija ba, ai saita fashe da kuka , yanxu in khadija batayi komai ba yaxanyi ne,

Ma’u ke Asma’u ai bata masan kiran da Innah ke yimata tayi zurfi cikin tunani, ai kuwa Innah ta shigo d’akin tana faman masifa wai kina jina kikayi min shuru dan ubanki turus tayi au tunani mah kikeyi lallai ai kuwa Innah ta buga mata wani aban bugu, Ma’u cikin gigicewa ta tashi zaune tace Innah magana kikeyi a’a dan ubanki ba magana nakeyi ba, shegiya me bakin halin tsiya kuma tunani yanxu kika fara, kuma yau saura kwana biyu auranki wllhy bazan sai maki komai ba haka xaki tai gidan auren naki, dallah ni tashi ki d’aibu min ruwa a rafi saura ki dade jikin kine zai gaya miki, ta fice.

Ma’u kuwa kaku kawai take wannan wace irin rayuwa ce nake ciki haka ni Asma’u yah Allah ka kawo min dauki, tana kaku tana sambatu,

Haka ta tashi ta nufi rafi bayan ta d’ebu ruwa tana kan hanyar dawowa, kawai saiga Ilu yasha gabanta yana cewa ke matata daga ina haka, Ma’u ta zabga mai wata uwar harara, tace ban sani ba kuma wacece matar taka, ke mana Allah ya kiyaye nah aure ka wllhy aure mah kamar anyi shi cewar Ilu ita dai Ma’u raba shi taita wuce tana maiyin tsaki.

Ta shiga gidan da sallama ta tadda Innah ta cika tayi fam wai ai ta dad’e ko sallama bata amsa ba gidan ubanwa kika tsaya ai Ma’u cikin tsoro tace bako ina wllhy ai Innah ta jawo ta ta kama bugu da zagi Ma’u sai kuka take, dallah can ni tashi ki bani guri, ai Ma’u da sauri ta tashi ta shiga d’akinta tana me kara fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi.

Washe gari

Ma’u na zaune a d’akinta tayi shuru tana tunanin infa bata ga khadija ba gobe shikenan za’a aura mata Ilu ta girgiza kai tana hawaye tana mai cewa haba khadija ina kikaje ne kinsan Innah bazata barni nazo gunki ba, ina kike ne khadija tana fada tana qara fashewa da kuka.

Ma’u taga fah har dare yayi amma babu khadija babu labarinta, tana zaune a kod’ad’an d’akinta ta gasa bacci yo ina taga bacci ana shirin aura mata Ilu dan shaye-shaye gobe, taga har shad’aya da rabi amma ba khadija ai saita fara hawaye.

Tana cikin tunanin mafita sai kawai taji khadija tayi sallama a hankali kamar mai rad’a ta shigo d’akin, ai Ma’u bata san sadda ta rungume khadija ba tana kuka wllhy qawa na zata baki zuwa ne har ina shirin neman wata mafitar, khadija tace a’a wllhy zanzo ina can ina miki shiri ne kuma nafi so saida dare kowa yayi bacci, Ma’u tace tohm mikika shirya min.

Karanta Karshen Zalunci book compelet by Mansur Usman Sufi

Khadija tace Ma’u barin garin nan zakiyi, wai kina nufin in gudu kenan cewar Ma’u khadija tace haka nake nufi, ai Ma’u saita fara girgiza kai tana hawaye khadija zan iya kuwa to in tafi ina, khadija tace zaki iya Ma’u Allah na tare dake wllhy daki zauna a aura miki Ilu qara ki gudu saboda wllhy rayuwarki za’a lalata, nan dai khadija taita nuna mata illar inta zauna an aura mata Ilu bashi da wata riba illah a lalata mata rayuwa.

Ma’u ta gamsu tace to na yarda khadija tace yauwa kokefa yanzu zan rakaki bakin gari saiki ta gudu har ki fita daga garin nan kinji Ma’u cikin hawaye tace yanxu kuma ko wacce irin rayuwa xan fad’a khadija ta kama hannun ta samata kudi tace kinga wannan kudin tara miki nayi kiya amfani dasu tana me shire mata hawaye, ai Ma’u sai kawai ta rungume khadija tana mai cewa qawata ngd sosai bansan irin godiyar daxan miki ba, khadija tace ba godiya tsakanin mu dan Allah nayi miki kuma Allah yasan dake kinji tashi muje guri na qurewa.

Haka Ma’u ta tashi tana me kara share hawaye ba abinda ta dauka haka suka fitu cikin sand’a tana mai waiwayan gidansu, yanzu qaddara zata fitar da ita a gidansu ta share hawaye ta d’aga kanta sama tana mai cewa ya Allah ka kawo min d’auki.

Haka khadija ta rakata har karshan gari sana ta tsaya Ma’u ta rungume khadija tana mai cewa qawata zanyi kewarki khadija tace nima haka Ma’u itama tana mai share hawaye.

Haka suka rabu suna me kukan rabuwa da juna, haka Ma’u ta miqe hanya ta kama gudu, gudu take sosai ga duhun daji amma haka Ma’u taita gudu kwata-kwata ba tsoro a tare da ita gani take kamar wani zai ganta burinta ta fita daga garin kwata-kwata.

Ma’u har sanyin safiya tana gudu tayi nisa daga garin amma har yanzu bata iso bakin hanya ba tah gaji sosai ga qishir ruwa ga yanwa amma Ma’u bama tajin su ita dai burinta ta iso bakin hanya.

Gudu take harta iso bakin hanya motoci sai wucewa sukeyi Ma’u tad’an tsaya tana kallo tace lallai in kana qauye bazaka ji mi duniya take ciki ba, tana cikin tunani ta hange mai ruwa ta tsallaken titin wajan ta tsallaka ta siya da kudin da khadija ta bata daidae wata rantsatsiyar mota zata wuce kenan ai kuwa tayi gaba da Ma’u ai mai motar cikin gigicewa ya fito daga motar mutu nan magidanci ne ya fara tsufa amma daga gani kudi na kuka a jikin mutunan dan baka taba gane yayi shekaru da yawa a duniya ba,

Ai cikin tashin hankali ya ratsa muta nan da suka baibaye ta Ma’u ce kwance ko mutsi batayi yace dan Allah ku taimaka man insata a mota muje asibiti, ai kuwa nanda nan aka sata a mota sai KANO dake ba nisa da kano gudu kawai yake sun shiga kano bai zarce ko inaba sai asibiti ai kuwa likitoci suka taru a kanta, sunsamu ta farfad’o a inda aka kara mata ruwa sai bacci take.

Likita yace ma wadda ya kawo ta jikinta da sauki nanda awa uku zata iya tashi zamu iya sallamarku yau mah mutu nan da ban san sunanshi ba yace tohm Masha Allah.

Yaje ya biya kudin magani ya dawo d’akin da aka kwantar da ita har yanzu bacci take, sai mah yanzu ya qare mata kallo ai cikin rud’ewa yace kai wannan yarinya kina man kama da matata ikon Allah shikad’ai yake wannan maganar sai kuma ya girgiza kai yace kai kama ce kawai, nan ya zauna yana jira ta farfad’o.

Tohm masu karatu a nan zan tsaya.

Nice taku har kullum FATEEMAH RABI’U CE.

Ngd da irin soyayyar da kuke nunawa wannan littafi nah ASMA’U

Kashi Na Uku 3

BISSIMILLAHI

MANZON ALLAH (SAW), YA CE : (MAFIFICIYAR SALLAH A WAJEN ALLAH ITACE SALLAR ASUBA A CIKIN JAM’I RANAR JUMA’A.)

Nan ya zauna yana jira ta farfad’o fara motsi tai ya matso kusa da ita, ta bud’e idanu ta tashi zaune ta kalli mutu nan tace dan Allah ina nake nan miya faro dani, mutu nan yace bige ki ne da mota kinzo tsallake titi ne abisa rashin sani shine na kawo ki asibiti.

Yanxu za’a sallame mu inane gidanku koh garin ko saina meda ke, ai Ma’u saita fashe da kuka tace ni bani da kowa sai Allah kuma bana so na kuma gida, mutu nan da har yanxu ban san sunanshi ba yace ban gane ba ni baxan cutar dake ba gaya man miya fiddo ki gida, Ma’u cikin kuka ta bashi labarinta kawai ita taji ya kwanta mata a rai, cikin tausayawa mutu nan yace lallai kinsha wuyar rayuwa amma yanxu xantai dake gida na xan riqeki amanah zaki zauna damu a gida na, ai Ma’u najin haka tace ngd Allah ya saka da alkhairi yace sunana Alhaji Abubakar amma zaki iya kirana da dady kamar yarda yara nah ke kira na, Ma’u tace tohm dady ngd yayi murmushi shidai yarinyar ta kwanta mai a rai, likita yazo ya basu sallama suka fito yace shiga mota tace to ta shiga suka fara tafiya Ma’u kuwa sai kallon garin kano takeyi cike da birgewa da sha’awa a cikin zuciyarta tace lallai birni tayi.

WANENE ALHAJI ABUBAKAR

Alhaji Abubakar dan kano ne a nan aka haifeshi, alhaji abubakar mai kudine sosai, yana da kanfanuni a cikin garin kano harda kewaye, yana da mata d’aya wato, Hajiya Aisha mace mai hakuri da sanin yakamata, tana da kirki sosai suna da yara buya mace da namiji wato Abdallah da Kairat, Abdallah yana karatu a kasar waje a India saura shekara biyu ya kammala ya dawo gida Nigeria.

Back to labari

Ai Ma’u bata qara tsinkewa ba saida aka shiga wani uban gida mai shegen kyau Ma’u kuwa a zuciyar ta tsoro ne kawai tace ni Ma’u ba gidan yankan kai na kawo kaina ba duk a cikin zuciyarta take tunani sai kuma ta girgiza kai tace ba kyau munana zato, bama tasan mutar ta tsaya ba saida yace fito min iso tace to ta fito Ma’u kuwa kallon gidan kawai take.

Karanta Abban Sojoji Hausa Novel

Ai bata qara tsinkewa ba saida suka shiga falourn gidan wai an narka dukiya a gidan mah baki d’aya hmm masu karatu gidan nanfa ya hadu tako ta ina, sun shiga da sallama ba kowa falourn dady yace zauna bari na hau sama nagani ina Mameen taku take ne, Ma’u tace to ta zauna kasa.

Shi kuwa hawa sama yayi ya shiga d’akin matar tashi da sallama ya taddata tana tunani ya girgixa kai ya matsa kusa da ita ya taba ta tai firgigit ta dawo hayyacinta tace harka dawo ne, yace na dawo wai yaushe xaki daina wannan tunanin ne ta sauke numfashi tace dadyn su Abdallah wllhy kullum sai nayi tunanin qanwata Maryama wai dana je qauyan namu sai aka ce ai ta mutu kuma a gidan mijinta ta mutu kasan muna India duk wannan abin suka faru kuma innah tanbayi y’an uwa ko ta taba haihuwa sai dai suyi shiru na rasa mi yasa ta qarashe maganar cikin kuka, ya share mata hawaye yace dan Allah matata ki daina wannan kukan kinji komai xaiyi daidae insha Allah.

Ya qara cewa kinga nazo miki da wata baiwar Allah tana falour ko ince kin qara d’iya nan dai ya bata labarin da Ma’u ta bashi ai Mamee cikin tausayi tace to muje falour inganta wllhy har naji ina son yarinyar.

Suka sakko falour ita kuwa Ma’u tana nan inda take tana ta aikin kalle-kalle, ai Mamee na hada ido da Ma’u cikin firgici da rud’ani tace wah nake gani kamar fuskar Maryama qanwata dady yace nima wllhy naga wannan kamar, ai Mamee ta jawo Ma’u tace d’iyata dan Allah bani labarin rayuwarki duka Allah yasa abinda nake hasashe gaskiya ne, ita dai Ma’u sai taji matar ta kwanta mata a rai sosai ai kuwa ta bata labarin duka rayuwarta.

Ai nan take Mamee tace ya sunan mahaifiyarki Ma’u tace Maryama ai Mamee taba ma san sadda ta rungume Ma’u ba tana kuka tana mai cewa wllhy d’iyar qanwata ce dady shima cikin jin dadi yace kai Alhmdllhi nan dai Mamee taba Ma’u labarin ai ita yayar mamar tace, Mamee tace mun tasu da Maryama d’aki d’aya muke uwa daya uba daya na riga ta yin aure ninayi aure a birni na aure mai hali naji ciwan rabuwa da yar uwata to bayan nayi aure mijina sai wani aiki ya kaishi India to muka koma zama can to duk can muka haifi yaranmu d’anmu Abdallah can ya fara karatu sadda muka haifi qanwarshi shi sana yayi nisa cikin karatu yace mubarshi a can inya idashe karatu zai dawo daga baya sai muka dawo gida Nigeria da qanwarshi muka barshi yana cigaba da karatunshi amma inya samu hutu yana zuwa akai-akai, to sadda muka dawo naje garin namu neman qanwata sai aka ce ai tayi aure harma wai ta rasu wajan haihuwa nayi kuka sosai na rashin kanwa ta na tanbaya ko ina abinda ta haifa sai suyi shuru nayi-nayi su fad’an gaskiya basu cewa komai kamar an rufe musu baki to haka nan dai na hakura na dawo gidana.

Tohm d’iya ta kinji abinda ya raba ni da qanwata mahaifiyarki kenan amma diya ta ya sunanki Ma’u tace sunana ASMA’U ina kira na Ma’u Mamee tace Allah sarki Ma’u kinsha wuyar rayuwa amma daga yanzu ta wuce kuma baxan sanar da kowa kina waje na ba zakiyi karatu kuma sai kinyi aure zaki koma garin naku, ai Ma’u cikin jin dadi tace ngd Mamee tace ba komai diyata ki rinqa kira na da Mamee kamar yarda yara na ke kira na kinji Ma’u tace to Mamee dady yace wai ina kairat ne Mamee tace tana islamiya amma yanxu zasu taso, ai kuwa tana rufe baki sae gata da sallama ta shigo Mamee na dawo to ta xauna Mamee tace ga qawa na miki kuma yar uwarki ce d’iyar qanwata ce nan dai Mamee ta bata labarin Ma’u ai kairat hada hawaye ta tashi ta rungume Ma’u tace yar uwa ya sunanki Ma’u tace ASMA’U ana ceman Ma’u kairat tace Allah sarki yar uwa.

Mamee tace kairat kaita dakin dake kusa dana ki haka kairat ta kama hanun Ma’u suka hau sama sun shiga daki kairat tace yauwa yar uwa ga d’akinki nan nan kairat ta nuna mata duk wani abun amfani tace yau Ma’u saiki shiga kiyi wanka bari naje daki na na d’ako miki kaya, Ma’u tace to ta shiga wanka bayan ta fito ta zauna kan gado tana kallon dakin Ma’u tace gaskiya d’akin yayi kyau.

Shin ka/kin kasance marubuci ko marubuciya dama ta samu da zaku rika samun kudi ta hanyar saida rubutukanku marmaza kuyi register da ArewaBooks don samun damar siyar da littatafanku ta online

Kairat ta shigo tace yauwa Ma’u ga kayan Ma’u tace ngd kai haba yar uwa ai ba komai cewar kairat,

Bayan sun sakko suka ci abinci bayan sun gama Mamee ke tanbayar Ma’u cewar ta gama secondary school Ma’u tace eh Mamee na gama, Mamee tace yauwa daidai kenan dama kairat itama ta gama sai a samar muku da ta gaba tare saiku tafi ai Ma’u wani irin farin-ciki take ji yau gata ga yan uwanta.

Bayan kwanah biyu

Ma’u ta saba da su kairat sosai har an sata islamiyar su kairat ta fara xuwa a inda dady ya nemar musu school suna ta shirye-shiyen fara zuwa school.

Yau Ma’u tana ta shiri da sauri dan yau zasu fara zuwa school masu karatu kunga yarda Ma’u ta canza kuwa ta kara kyau sun fito xasu tafi Mamee tace yara nah yau zasu fara zuwa school to Allah ya tsare kunji amin Mamee suka amsa a tare suka wuce suka hau mota direba ya kaisu time din tashi yayi yaje ya dakko su haka rayuwa taita tafiya a inda Ma’u dad’a wayewa take komai nata na kara cikowa kyanta na qara fitowa karatunsu yayi nisa ita da kairat saura shekara daya su gama a inda kuma yau suna ta shirye-shiryen dawowar Abdallah.

Gidan ko ina yana ta kamshin girki Ma’u ce a kicin sai ita da kairat suna ta girke-girke kala-kala Mamee ta shigo tace yauwa yan mata na bari muje nida dadyn ku mu taro Abdallah dan Allah kuyi sauri ku shirya Mamee ta qara cewa kairat ki tabbatar kinma Ma’u shiri mai kyau kairat cikin murmushi tace to Mamee ta wuce su kuma suka harhad’a kayan abin cin bayan sun gama suka shiga daki sukayi wanka kairat ta zaba ma Ma’u kaya masu kyan gaske.

Ita dai Ma’u tana kallon ikon Allah bata son mi suke nufi ba kairat kuwa murmushi kawai take a cikin zuciyarta tace Allah yasa yaya Abdallah yace yanah son Ma’u dan nasan Mamee da dady haka suke taku Allah ysa tarkon su ya fada.

Haka ta gama shirya Ma’u tayi kyau kamar a sace ta a gudu kairat ta matso da ita saitin madubi Ma’u ta kalli kanta a madubi ai ko ita tasan tayi kyau na fitar hankali, amma yau tunda ta tashi take jin faduwar gaba bata san mi yasa hakan ba.

Can suka ji qarar motoci kairat tace lah gasu nan ai Ma’u sai taji qirjinta na bugawa har saida ta dafe wajan, kairat tace tasu muje mu taro su Ma’u tace dan Allah kije xanzo daga baya kairat tace tohm, Ma’u kuwa window ta leqa ba abinda bata gani can ta hangi Mamee sun fito daga mota wata mota ta hanka an bud’e ta an sako qafa daya Ma’u tace wow amma dai ya Abdallah xaiyi kyau haka har ya gama fituwa ai Ma’u saita saki baki da hanci tunda take bata taba ganin kykkyawa irin ya Abdallah ba.

Abdallah dogo ne amma ba sosai ba, yana da qirar qarfi fari ne amma ba canba idon shi shanyayyu kamar maijin bacci haka suke Abdallah matashi ne baifi shekara talatin ba ga hanci sai lip dinsa pink yana da sanyin hali da son mutane baida sun magana sosai baida son yan mata saida mace tace tana sonshi badai yace yana sonta ba gashi da farin jini.

Wannan kenan

Ma’u sai dai taji kairat na cewa Ma’u tasu to muje sun shigo Ma’u tace to tabi bayan ta suka sauka flour Abdallah kuwa yana zaune yana cin abinci sai santi yake yana cewa wai Mamee wayayi wannan girkin amma dai ba kairat bace dady ya amsa mai yace qanwarka ce nan dai suka bashi labarin Ma’u cikin tausayawa rayuwar datayi baya a cikin zuciyarshi kuwa so kawai yake yaga yar uwarshi ya take amma saboda miskilanci baka taba gane wane hali yake ciki ai bai gama tunani ba sai gasu sun iso flour da sallama jiyai wata zazzaqar murya tace ina wuni ya Abdallah an iso lpy ai ji yayi ba wadda ta iya kiran sunanshi kamar ita ai bai san sadda ya juya ba suka had’a ido ai a tare suka ji zuciyar su ta buga a tare kallon juna kawai suke saida dady yayi magana yace to ga qanwar taka nan ya nuna ASMA’U sai sana ya amsa gaisuwar da ta mai yace lpyl ya gida tace lpyl nan yana gama cin abinci yace Mamee zantai bangare na nad’an watsa ruwa Mamee tace to.

Mamee kuwa addu’a take Allah ysa Abdallah yaso Ma’u dan shine fatanta dady a gurinshi mah haka ne

Abdallah kuwa bayan ya watsa ruwa ya fito yana xaune tunanin Ma’u kawai yake gani na farko yaji yana sonta amma bai san yaxaiyi ba tunda shi bai taba so ba sai a kanta shin ya zaiyi ne amma zaibi komai a hankali.

To Ma’u ma a gun ta haka abin yake ita ma tunanin yayanta Abdallah take lallai tasan ganin farko ta fada soyayya da ya Abdallah wani irin so take mai wadda lokaci guda ya shigeta, tana xaune a zuciyar ta tace ooh rayuwa koya qawata khadija take yanzu in Allah ya yarda na kusa zuwa gareki aminiya.

To masu karatu a nan xan dakata.

Chapters na BayaJoin Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

About Mr Hausa Ebooks 1438 Articles
The Power of pen