1035 Views

ASMA’U Chapter 01 – hausa novel by Fateemah Rabiu

 ASMA’U Chapter 01 – hausa novel by Fateemah Rabiu

Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 18 Dec, 2022
Upload Time 6:25 pm
Author

Writer Group Unknown / NIL
Novel Genre

Comment 1 Comment

ASMA’U Chapter 01 – hausa novel by Fateemah Rabiu

FATEEMAH RABI’U CE

BISSIMILLAHI

Ban zarce ko ina ba sae a wani kauye gsky qauye ne ba irin sosae din nan ba wani gidan qasa ne na hanga katangar gidan duk ta zube shiga ne gidan wae daga ganin wannan gida ana fama da talauci, cannah hango wata yarinya a dakin qasa ko tabar ma babu kwance tana bacci daga gani baccin ma ba dadinshi take ji ba, can saiga wata mata ta fito tana kiran ASMA’U, Asma’u ke Asma’u daga gani wannan yariyar take kira mae bacci ai cikin gigicewa Asma’u ta tashi ta fito tace INNAH, gani dan ubanki wazai je yayi min karan dora sanwa dan uwarki maza zo ki yomin karan sanwa,

Asma’u tace Innah wllhy ban da lpy zazzabi ke damuna ai Innah najin haka ta fara masifa ae koh mutuwa zaki sai kinyo shi shegiya mai bakin halin tsiya da bakin jini, duk qawayanki na kauyen nan duk sunyi aure amma ke kin kasa aurowa saboda bakin jini shekaronki shabiyar amma gaki nan zaune a gida, ita dai Asma’u tai shiru tana aikin hawaye˜­ danta saba da wannan fadan nah Innah amma in akae mata wannan gorin nata kasa auruwa kasa jurewa take sata zubar da hawaye duka ma nawa take.

Inna tace au tsayawa kikai kina kuka ai kuwa Innah ta kama Asma’u saida tai mata bugun tsiya sana ta sake ta dan mah karta kasa yima ta karanne shi yasa, kuma wllhy in baki tashi kika yimin karan nan ba wllhy kika dawo gidan nan nida ke ne cewar Innah,

Haka Asma’u ta tashi jiki ba qarfi ga bugun data sha jikinta duk ciwu yake mata amma haka Innah dan rashin imani ta tasa ta gaba saeda taga ta fita yin kara.

Haka Asma’u ta nufi daji tana kuka haka tayo kara ta dauko hanyar gida tana tafiya tana tunanin iyayanta da suna nan da duk wannan abun bai faro da ita ba, ta share hawayen da ke zubo mata harta isa gida .

Innah na zaune bakin murhu tana cika tana batsewa wai Asma’u ta dadi bata kawo mata kara ba ai tana ganin Asma’u ta shigo gidan haka ta kama ta kara lakada mata na jaki saida taga ta kasa koda daga hannu sana ta rabu da ita, haka Asma’u ta rarrafa ta shiga kodandan dakinta wadda koh arzikin tabarma babu ta samu tadan kwanta tana kuka mai taba zuciyar mai sauraro.

WACECE ASMA’U

Malam mudi shine mahaifin Asma’u ya tasu cikin talauci da wahalar rayuwa yana saeda kayan miya ne a qauyen su yana bin kasuwanni a haka yaje wani kauye ya hadu da Maryama mahaifiyar Asma’u tunda ya hadu da ita yaji yana sonta haka baiyi sanyi ba ya nemi auranta an bashi auran maryama inda suka tare maryama macece mai hakuri da juriya da sanin ya kamata macece kyakkyawar gaske bafullatana ce duk abin da mijin ta malam mudi ya samu tana hakuri dashi su rufa ma kansu asiri shi yasa mlm mudi ke kara sonta suna zama na fahimtar juna, haka har suka shafe shekara biyar Allah bae basu haihuwa ba, tohm nan fa dangin mlm mudi suka tasusu gaba akan sai ya kara aure shine bai da niyar kara wani aure ai haihuwa ta Allah ce.

Karanta Littafin Babu So na Bilyn Abdul daga ArewaBooks

Haka wata rana yaxo wucewa ya gamu da wata zainabu wato Innah kenan shi bai mah lura da ita ba zata wuce ta gaida shi ya amsa ai zainabu tunda ta hada ido da mlm mudi taji itafa yayi mata kuma ko ta halin yaya saeta aure shi.

Wacece zainabu

Zainabu diya ce ga mlm mahmuda ya rasu tun tana karama ta tasu a hannun mahaifiyar ta wato sa’ade macece mafadaciyar gaske duk ita ta lalata tarbiyar zainabu ta tasu cikin sangarta duk abin da tae ba’a ganin laefinta haka rayuwarta ta tashi ga bin maza haka ta zubar da mutumcita da bin malamai.

Wannan kenan,

To a haka dai zainabu saeda ta kai sunan mlm mudi wajan bokan ta, saida ta san yarda tae ta shiga cikin gidan shi tunda ta auri mlm mudi komae nashi ya fara lalacewa tabi ta mallake komae to ita ma dae tunda ta shigo gidan ko batan wata bata taba yiba har gashi sunkai shekara uku to duk wani rashin mutumci daza tai a cikin gidan maryama bata taba daga kae ta kalle ta ba, ta kasance tana hakuri da ita.

Ana haka Allah yaba maryama ciki zuku ga baqin ciki wajan zainabu ai sai wajan bokanta tayi asirin amma ina Allah yace wannan ciki saiya zo duniya.

Haka rayuwa taita tafiya a inda cikin maryama yakae watan haihuwa yau koh gobe wata rana maryama ta tashi da nakuda gashi mlm baya nan tana ta juyi a daki ga azabar cuwu amma zainabu tana shigowa taga halinda da baiwar Allah nan take ciki haka tae kunnan uwar shegu da ita tama barma ta gidan dan rashin imani, haka maryama taita fama da nakuda sanda mlm zai dawo ta riga ta wahala matuqa mlm cikin tashin hankali maryama yana ta kiran sunanta, haka Allah ya sauke ta lafiya ta haifi diyarta mace mai kyau da ita bata wani dade ba Allah yai mata rasuwa.

download ASMAU complete hausa novel by Fatima Rabiu

Ai mlm ya shiga tashin hankali badan kadan ba haka dangin ta mah zainabu kuwa kamar ta zuba ruwa kasa tasha,

Ranar suna aka sama yarinya ASMA’U , dangin maryama sunsu su amshe Asma’u amma da zainabu( Innah ) taga haka saita je wajan boka ya rufe musu baki basu iya cewa komae, Asma’u ta tasu cikin wahalar rayuwa zainabu wadda Asma’u ke cewa INNAH tana azabamtar da Asma’u mlm kuwa bae iya magana saboda shima an gama dashi,

Haka rayuwar Asma’u ta tasu cikin wahala tun tana qarama ta gane Innah ba mahaifiyar ta bace inta tanbayi mlm saidai yace tai mata addu’a ta rasu Asma’u kuwa sai dae taita kuka,

Baqin cikin abinda ake ma Asma’u shiyai ajalin mlm mlm mudi ya rasu ya bar Asma’u cikin kuncin rayuwa ai ace yana kallo amma bazai iya magana ba ana azabamtar da marainiyar Allah wannan abu shi yai sana diyar rasuwar mlm.

Bayan rasuwar mlm dangin maryama sunsu su amshi Asma’u amma Innah tai duk yadda zatai ta hana tasa suka mah manta da ita a rayuwa,

Asma’u na da jiki amma ba sosae ba fara ce kuma tana da dugun hanci yadan baje daga qasa amma ba, sosae ba tana da cikar halitta ta ko ina wadda d’a namiji yake so ga y’a mace Asma’u na da kyau masha Allah.

Karanta Littafin Kishi Da Aljan Chapter 12 Complete Hausa daga shafin AihausaNovels

Innah tunda taga Asma’u nada farin jini duk samarin qauyan tunda ta fara girma suke son ta da yawa ai duk wadda zaizo inda taga yana da halin kirki saeta kore shi haka harta korar mata samari ba mae zuwa yace yana son ta saboda masifar Innah ba wadda bae santa ba a qauyen,

Amma wani Ilu na nan dan shayeye bai da kyan hali duk gari an sanshi bai ji shi kuma yace yana son Asma’u amma Asma’u in akwai wadda ta tsana to ilu ne Innah kuwa tace shi xata aura

Download RAYUWA complete hausa novel by Fatima Rabiu

Tohm masu karatu yaya zata kaya ne Innah burinta zae cika na Asma’u saeta auri ilu ne, yaya rayuwar Asma’u zata kaya nan gaba koh

Karanta Jaruman Duniya book compelet by mansur usman sufi

Masu karatu ku biyu ni duk zaku samu amsar ku, cikin wannan littafi nawa.

Nice taku har kullum Fateemah Rabi’u ce

Back to labari,
Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

About Mr Hausa Ebooks 1438 Articles
The Power of pen

1 Trackback / Pingback

  1. ASMA'U Chapter 03 End - Hausa Novel - DL HAUSA NOVELS

Comments are closed.