Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

Yar Shekara 19 Ta Kashe Mijinta Har Lahira, Makonni 3 da Aurensu A Adamawa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Yar Shekara 19 Ta Kashe Mijinta Har Lahira, Makonni 3 da Aurensu A Adamawa
Yar Shekara 19 Ta Kashe Mijinta Har Lahira, Makonni 3 da Aurensu A Adamawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, a ranar 7/9/2021 ta cafke wata budurwa mai shekaru 19 saboda ta daba wa mijinta dan shekara 35 wuka har lahira.

Wanda ake zargin, Rumasau Muhammed mazaunin Kauyen Wuro Yanka, karamar hukumar Shelleng, ta dabawa mijinta marigayi Muhammed Adamu wuka bayan ya nemi saki kuma marigayin ya ki furta kalmar sakin da take bukata.

Wanda ta fusata da kin sakin ta bayan bukatar ta da yawa, wacce ake zargin ta yi amfani da wuka ta caka masa a ciki, sakamakon haka ya fadi a sume sannan aka garzaya da shi Asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Also Read An Tsinci Gawar Mace Mai Ciki A Motan Mai Sarautar Gargajiya

Rundunar ‘Yan sanda a hedikwatar Shelleng ta cafke wanda ake zargin, bayan rahoton da Jophas Johnsley abokin mamacin ya samu.

Bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa, marigayin ya daura auren ne ba tare da son ran ta ba a ranar 6/8/2021 kuma auren ya dauki makonni uku kacal kafin faruwar lamarin.

Kwamishinan ‘yan sanda CP Aliyu Adamu Alhaji, ya ba da umarnin yin bincike na hankali kan lamarin ya kuma shawarci jama’a da su guji tilastawa yayansu su yin aure da wuri.

Haka zalika, ‘yan sanda sun ba da umurnin gaggauta gurfanar da wacce ake zargin domin ya zama izina mutane yin hakan.

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.