Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun Allah yayiwa babban Jarumin Kannywood Rasuwa

 Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun Allah yayiwa babban Jarumin Kannywood Rasuwa
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category News
Uploaded On 14 Sep, 2021
Upload Time 8:04 am
Hits 475 Hits
Comment No Comments

Description

Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun Allah yayiwa babban Jarumin Kannywood Rasuwa.

Malam Ahmad Aliyu Tage, dadadden jarumin barkwanci ne a masana’antar kannywood kuma mai daukan hoto ne masana’antar a jiya Allah yai masa rasuwa.

da yawa daga cikin manyan kannywood sun girgiza matuka da rasuwar nashi inda Abikan aikinsa suka ruga wallafawa shafukansu na sada zumunta.

Also Read Kalli Hotunan Kannywood Ta Gabatar Da Sabuwar Jaruma, Yaseerah Babangida

Shafin Mujallar fim ta ruwaito cewa kafin mamacin ya cika yaiwa iyalinsa nasihia inda yake ce da su tabbas yana ji a jikinsa wannan ciwo na shi bana tashi bane.

Shugaban MOPPAN na kasa Dakta Ahmad Sarari ya bayyana matukar alhininsa ga rasuwar jarumin ya kuma bayyana rashin nasa a matsayin babban asara ga Masana’antar ta kannywood.

Mamacin ya rasu ne a asibitin koyarwa na muhammad Abdullahi wase, da akafi sani da asibitin nasarawa a jiya, ranar Litinin 13/9/2021

hallau dai mujallar fim ta ruwaito cewa ta samu labari daga wata majiya cewa mamacin ya rasune sanadiyar bugun zuciya.

Dakta Sarari, ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Hakika Kannywood ta yi babban rashi.

“Allah ya jiƙan Ahmad Tage. Allah ya yi masa rahama. Allah ya duba masa bayan sa, mu kuma in tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani.”

Shi ma tsohon shugaban MOPPAN na ƙasa kuma fitaccen jarumi, Alhaji Sani Mu’azu, ya ce mutane da dama za su ji wannan mutuwa da aka yi.

Ya ce ya na fatan ba za a taɓa mantawa da kyakkyawar rayuwar Tage ba da kuma gudunmawar da ya bayar ga cigaban Kannywood.

“Allah ya sa rashi da mu ke samu ya dinga zama wa’azi ga tamu rayuwar,” inji Sani Mu’azu.

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: