Hukumar Hisbah ta kwace Katan din giya 5,760 a Kano

 Hukumar Hisbah ta kwace Katan din giya 5,760 a Kano
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category News
Uploaded On 09 Sep, 2021
Upload Time 2:29 pm
Hits 205 Hits
Comment No Comments

Description

hoto daga FACEBOOK

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kwace motocin tanka biyu dauke da katan 5,760 na giya iri-iri a kan hanyar Kano zuwa Madobi.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Lawan Ibrahim-Fagge, ya fitar a Kano ranar Laraba.

Sanarwar ta ambato Kwamandan Janar na hukumar, Harun Ibn-Sina yana cewa, yayin da yake duba motocin a hedikwatar hukumar, cewa jami’an Hisbah ne suka damke su da misalin karfe 4:00 na safe, ranar laraba.

Also Read Kalli Kyawawan Hotunan Tsofaffin Matan Jarumi Adam A Zango

“Hukumar Hisbah ta hana sayar da giya a jihar don gujewa maye,” in ji shi.

Ibn-Sina ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da yaki da miyagun kwayoyi da sauran abubuwan maye a tsakanin matasa a jihar.

Kuma Ya yaba da kokarin hukumar Hisbah, masu sa kai da masu ruwa da tsaki kan jajircewar su, ya kara da cewa rashin kyawun dabi’a tsakanin matasa ya kasance abin damuwa ga al’umma.

Kwamandan-janar din ya ce za a ci gaba da kokarin kawar da al’umma daga barazanar miyagun kwayoyi da sauran abubuwan maye.

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: