download TAKOBIN IZZA littafi na daya 1 complet hausa novel document


Awani zamani maitsawo wanda aahude kimanin shekaru dubiyar dari biyar baya lokacin duniya tanafama dadahun jahilci inda zalunci yayawaita mugunta dakyeta yaxamo ruwandare aduniya awannan xamanin duniya takasancene kashin dankali babba yadanne karami akasa awannan xamani mai karfi shine kemulki domin dazaran kanaji da izza da jarumta saika dibi dakaru ka afkama wata al umma insuna karfi sukare kansu inkobasuda karfi tofa synxama bayi ababan walakantawa tabbas awannan zamani babu wani mai yanci saimai karfi sai attajirai saikuma hatsabiban bokaye sanna awannan
xaamani Sarakuna nagasan tara dakarune gamida fadin kasa domin indai baka dakarfin runduna tarin yammaxa madauka rayukan mutunda aljan tofa baxaka iya tsare kasarka da jama arkaba sannan dukiyarka da ahliinkama ako yaushe xaka iya rasasu rasawa na har avada wannan dalili yasa sarakunan duniya sumiketsaye wajan kare kasashensu inda surika tara mazaje runduna runduna sanna suhimmatu wajan kai farmaki ga sauran kasashe domin kara fadin kasa dakuma tara dukiya wannan al amari kuma shine yahaifadda yake yake aduniya inda xubdajini yayawaita kisan kai yaxamo ruwandare hakan yasanya sarakunan du.niya yunkurin mulkan duniya takowani hali awannan karnin kasashe biyarne suke cara babu kamarsu afadin duniya domin sunada karfin runduna sunada yawan
 sadaukai da jaruman fama sannan sunada tarin dukiya kamar kasa kasashen sune Farisa, Kisraa, Missiraa sakuma kasan Rum dakuma Kasar Siriyaa, wadannan kasashe biyar suntunbatsa kuma sunshahara aduniya sunxama dodanni sungallabi sarakunan duniya domin cikinsu duk wanda yasama watakasa ido tofa saisummallake wannan kasa
kasar Farisa kasace hamshakiya maidaukeda tarin jama a kimanin miliya dari biyar maxajen kasan sunaji da tsantsar sadaukanta dakuma takife domun basajada bayya afilin daga sune akema lakabida makara yakii suna karkashin ikon wani hamshakin sarkine hatsabibi kuma
shaidani maisuna Kumairu yakasance mahandami kuma maibaba kere yatsani gasa bashida wani buri aduniya face ace shine sarkin sarakai ma ana yazamo shine sarkin Duniya saboda hakane yasanya bokayansa dari da goma shadaya suimar binkice suganomar hanyar daxai mallaki wannan Duniya shikadai, Kasar Kisra kuwa wata hatsabibiyar sarauniyace kemulkin kasan takasance shaidaniyace kuma iblishiya sannan basadaukiyace
gagarabadau domin tarihi yanunacewa itakadai tana tunkaran alkarya koma yawan jama ar alkarya tafasata tamallake karagan mulkin alkaryan sunanta Suraida tanada karfin runduna kumatanada girman ixxa domin cikin kasashennan biyar babu sarkin dabaya shakkanta domin takara dakowannensu kuma sunji badadiii to itama Sarauniya Suraida batada wani buri da yawuce Mulkan duniya asabila dawannan burinnatane tashiga dakin halwanta takudurci binkicen hanyarda
xatabi tamallaki wannan duniya wani abin ta ajibi tsawon kwanaki dari tadauka amma babu abinda yabayyana agareta face Wata shafceciyar takobi dakuma taswiran wani karamin binni mai bansha awa to yanxutadukufane wajan gano wace takobine wannan kuma mene alakar takobin dawannan birniii Kasar Rum wani shararren sarkine maidumbintarihi yanaji datsantsan jarumta dasadaukantaka sannan yanada sa a alamarinsa domin tarihi yanuna baitaba burin mallakan wani abu aduniya yarasaba indai yadurfafi abu tofa sai yagabayansa anakiransa sarki
Maridu dan sa a shima burinshi dayane yamamaye duniya kowa dakomai yakoma karkashi ikonsa shima yatunkari bokansa dawannan bukat inda boka Yaibinkice aduniyar tsatsuba natsawo kwanaki casa in daidai baci basha karke wannan takobin da taswiran wannan birni sune subayyana agareshi ganin hakannne bokan yakwarara ihu gamida fadi kasa sumamme akasar misraa kuwa kasa maitarin sadaukai
miliyan dubu gomma kasace maicikeda alfari dakuma dauwamemmen tarihi domin tarihi yanuna samada shekaru dubu hudu baya ba ataba cinsu da yakiba sannan kuma babu wani yaki dasufita sudawo batareda nasaraba wata shahararriyar matsafiyace maisuna Maxarya kemulkin kasan shadanitace kuma iblishiyace domin bata fa abokan mu amala face dodanni da aljannu darafanai itama burinta dayane tamallaki duniya atafin hannunta kuma tayi wani mafarki wata Takobi da taswuran wani binni sunbayya mata takobin
yaimutukan burgeta dimin yanada mutukar kyau shaukin ganin takobinne yasa tamika hannu domin ta dauki takobi ammna sai wani matashin jarumi maitsananin kyau dakwarjin yafuto daga cikin wannan taswiran binnin yashekamata sara ahannu kil yakille hannunta afurgice sarauniya tafarka tareda kwarara ihu takwalama sarkun yakinta kira tace kashiryamin dawakai xan xiyarci Uwar aljannu domin taimin bayani akan Wannan Takibi dakuma taswiran wannan birniii sai kasar Siriya wata hamsgakiyar
daulace wacce awannan karnin babu wata kasa datakaita yawan jama a dakuma karfi arxiki sarkin dake mulkin kasar siriya ba sadaukibane kuma ba jarumibane sannan bayaya tsafu saidai hamshakin attajirine domin duniya tasallamamasa cewa babu wani sarki ko attajiri da yaikusa dashi atari dukiya afadin duniya toshima yana burin mallakan duniya atafin hannunsa sabodahaka kullun yanatareda manyan bokaye domun gonomar hanya toshima yayi wani mafarki da yafurgitashi kuma yatashi hankalin bokayansa dubu goma
dadari biyar domin watarana yanutsa aduniyar barci yainisa ashanin barcinsa sai yatsunduma aduniyar mafarki inda yaganshi awata hamshakiyar kasuwa kasuwace wacce takecike da mutane kai harma da iblisai kasuwan tacika tatun batsa dimin kaitsaye xaka iyakiran wannan kasuwa kasuwan duniya kwatsam sarki Uddairu yashiga wata rumfa domin siyan Zinare sai yaitoxali dawata kyakkyawan takobi anratayeta abango sannan gawan tawiran karamin birni maibansha awa kusada takobin shima ankafe abango sarki Uddairu yatambaye maiwannan rumfa kowannan takobin nasiyarwane maiksnti yace aa banasayarwa bane sarki Uddairu yace to imbanasiyarwa bane akamme xa a kawoshi kasuwa lallai dole asiyarmin da wannan takobi kukuma ikwata dakarfi
maikanti yace una aiwannan takobi tagagari yammaza balle mata sarki yadakama maikantin tsawa kai wawa mekake nufi maikanti yace abinnufi manyan sarakunan duniya masuji dakarfin dantse datakana dasihiri tsafi da iya sarrafa takobi wannan takobin tagagaresu jinhaka sarki Uddairu yafusata yakwarara ihu gamida tsawa take dakarunsa sama miliyan biyu sumamaye gurin sarki Uddairu yakalli maikantin yadakamai tsawa yace kaiwawa mekace takobin yagagari sadaukai jarumai da hamshakan matsafako toninan yauxammalakeshi koda xa ai bolan gawawwaki dakoramar jini sarki yaceda dawani dakare kasa takobinka kasars kamaukantinnan sannan kadaukomin Takobin inga Izzarta jar uba take dakaren yadatse kan maikantin sannan yamika
hannu danufin yadauko takobin kwatsam wata matashiyar Jaruma tafuto dagacikin wannan taswira tasare kan dakaren jini yaitartsatsi yawanke fuskan sarki Uraid tuni matashiyar takoma cikin taswiran kar uba Sarki Uddairu yakwarara ihu yai umurni gadaukacin dakarunsa miliyan biyar dasu daukomar takobinnan sannan su yayyaga wannan taswira jar uba bakidaya su antaya domin cikin kantin afusace domin cika umurnin sarki kar
ubaaa kwatsam sai wasu matasan jarumai masu kiran sadaukai dacikar kwarjiniii su biyar sufoto ajikin wannan taswira uku mazane biyu mata sunarike dawasu miyagun takubba dankari su afkama dakarun sarki Uddairu dasara dasuka sukarika fatali damaxaje kisa suke irinna daukan fansa tamkar iblisai kamar aljannu haka sadaukan yarannan suke ragargazan maxaje babu sassauci surika sarewa sokewa gamida karya kasusuwan maxajee cikin sa adaya tak sutarwatsa gayyan dakarun sarki uddairu inda alokaci guda
sukewaye sarki Uddairu sukaimar rufdugu alokacinne yafarka daga barcinsa yakwarara ihu aguje dakarunsa sufada dakinsa suna muxurai sarkin yakinsa yace ranka yadade meke farywa sarku yace akuramin sarkin bokaye ayyana jar uba koda boka yaxo Sarki Yddairu yalabartamai mafarkin dayayi sai Boka ayyana yamike sannan ykwarara ihu yakama girgixakai yanajada baya KAI WAI wannan wani tikobine kuma menene alakan taswiran bunnin da wannan takobi
TAKOBIN IZZAlittafi na daya 1
NameTAKOBIN IZZA
Size124kb
Authorismail Abdullahi
File Typetxt
uploaderMr Dlhausanovels
ebook compilerShuraih 99%
date modified12 September, 2020
descriptionhausa FICTION
Subscribe to our newsletter

Leave A Reply

Your email address will not be published.