Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

download NI DA PRINCE complete hausa novel document

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

 SHIMFIDA

Mikewa tai azabure tare da kallan agoggon bango na dakin dasauri tamike ganin takusa makara, mamaki take yanda bacci yadauketa akan sallayar datai sallar asuba,kaya ta cire tai saurin fitowa tsakargida taja ruwa a rijiya tafada toilet, wankan minti 5 tai tafito tafada daki tazura doguwar riga baka tasa hijab fari tare da daukar nikaf dinta da jakar makarantarta, dama ita sam kwalliya bata dameta ba.

Dakin ummanta tashiga azaune taganta tana ninke kaya tashiga da sallama tare da gaidata ta amsa cikin daure fuska Salmah kam tasaba da wannan hali na ummanta dan yanzu abin baya damunta, mikewa tai tare da cewa umma banga Abba ba koya fita ne? Kara hade rai umma tai tace ki wuce kigaida Goggo dan shikam ya fita tadan tabe karamin bakinta tare da karasawa dakin goggon ranta duk ba dadi, sam batasan matar.

Sallama tai Goggo dake kwance ta amsa mata cikin gadara salmah tashiga tare da gaida ta goggo ta amsa tare da cewa yawan banzan za’a tafi? Salma tadaure tace goggo nidai makaranta zani😞.. Goggo tai tsaki tace oho dai tunda ke da kamal kunfi karfin iyayenku ai sai kuyi tayi tace goggo yaza’aikifadi haka? cikin zafin rai goggo ta mike zaune tace karya aka muku?

Wayasani ma ko kamal din yamanta dake yayi auransa acan kasar dayake ke ya barki nan kina yawon nuna jiki😏? Idanun salma? Idanun salma suka ciciko da kwalla tadaure ta mike tace natafi makaranta goggo tace ke kika sani munafuka mudai kika kuskura kika dauko mana abun kunya sai kinsha mamaki, Salmah tai saurin yin waje tana share kwalla umma tagani a tsakar gida alamar duk zancen dasukai taji dasauri ta wuce dan tasan umma baxata taba sa baki a wannan maganar ba, nikaf ta daura takarasa waje.

Titi ta fita tasamu bus din dazatai Buk tahau, acikin mota kanta kawai ta jingina a kujera tana tunanin wannan al’amari wai ace tsakanin ta da mahaifiyarta bawata shakuwa? Wai ‘yar fari😟? Ita atunaninta tin? Ita atunaninta tin yaushe aka dena wannan abun? Intayi magana sai Abba yace mata uwarta ai bafullatanace tai wata ajiyar zuciya tare da dauko hoton kamal cikin jakarta takuramai ido aranta tace yaya yaushe zaka dawo? I really miss you, lissafin kwanan wata tashigayi yaci ace yaya kamal yadawo dan ayanda yafada mata randa sukai waya saura 3wks su taho to yanzu gashi taga harda durin kwana 5 😞. lalai yaya kamar bai matsu yaganta ba? Rabonsu da juna tun shekara 3 dasuka wuce, maida hoton tai ganin sun iso tafito daga motar ta shiga makaranta.

Lalai yau tayi late cikin hanzari tafara tafiya

sam bataji motsin mota a bayanta ba sai da

motar tazo daf da ita dasauri ta juyo cikin

razana tare dayin gefe amma ina motar

gudu takeyi gashi kamar dan koyo ne ke

tuka motar sam ba’a seti take tafiya ba

motar sai data gogi jikinta hakan yasa tafadi

kasa tim🙆🏻

Tabi motar dakallo idanta taf da kwalla dan

mutane sun taru suna kallanta abin haushi

bawanda yataimaka mata, ahankali motar

tafara yowa baya sai alokacin takalli

number motar Prince 1 ne rubuce a jiki.

Sai da motar tazo daf da ita dan harta

runtse ido tadauka murkusheta za’ayi jin

shiru yasa ta bude idanta ahankali kafar

mutane uku tagani ahankali tafara dago

idanta har ta dure su akan nagaban wanda

tasani shine Prince Salman dan tanaganin

rashin mutincin dayake yi a school din wani

wahalalen yawo ta hadiya.

Salman yakashe mata ido sannan yace

limamiya bakya gani ne? Aranta tace

limamiya? Yacigaba kosai muntaimaka miki

da glass ne? Salmah tamakamai harara

sannan tadaure tace ku bugeni maimakon

kubani hakuri sai kuce me? Amir dake baya

yai wata dariya yace hakuri? Oh prince

kagane metake nufi ai😆? Salman yace ohh ai? Salman yace ohh ai

kaji halin talakawa sannan yaciro bandir din

dari biyar yacilla mata yace sune matsalarki

I know😏? Idanun salma

Najib dayai shiru abaya dan shi yake koyon

tukin motar azahiri shikam baijin dadin

abinda ke faruwa amma yazaiyi?

Salma tai wani murmushi tare da daukan

kudin sannan takaraso kusa da Salman ta

mikamai ganin yaki amsa ta daura akan

motar sannan ta matso kusa da salman tace

maza irinku masu daukan mutane banza

sannan suke tunanin kudi na maganin

komai suna matukar bani tausayi😏? Idanun salma tana

gama fad’ar haka ta juya tafara tafiya,

mutanen dake gun suka shiga gulma, ran

salman yagama baci yamaimaita afili

Tausayi? Sannan yakalli kayan jikinta yaga

gaba daya kayan datasa basu wuce kayan

2000 ba amma takalleshi tace yanabata

tausayi?

 


Dasauri yakara kusa da ita ta baya ya fizgo

hijab dinta, jikintane yafara rawa ganin bata

taba shigowa makarantar ba nikaf bama

bare hijab ahankali hawaye yafara gudu a

idanta salma yadawo ta gabanta dasauri ta

tsugunna tare da kankame jikinta, ya firgita

ganin yanda Allah yamata kyau amma

rashin mutuncin dake idananunsa sun

rinjayeshi yatsugunno kusa da ita sannan

yace tausayi? Nidake yanzu waye mai kalar

tausayi? Hawaye kawai takeyi yai wata

dariyar mugunta sannan yace banza ‘yar

tallakawa ya mike yafara tafiya tace kai da

kake d’an masu kud’i fin wasu kai? Tsayawa

yai chak sannan ya juyo yace ke kinsan niko

waye ma? Tace why should I know? Yace be

careful dan zan iya ruguza miki rayuwarki

mark my word ya juya ya tafi.

Amir yashiga tafamai yace woo Man kana

burgeni, salman yai tsaki yafada mota yace

najib zokaja cikin sanyin jiki najib ya shiga.

Salma kam suna tafiya tadau hijab dinta

tasa da nikaf dinta tamike tare da kallan

agogon hannunta shikenan tayi missing

lectures dan kusan 40mins kenan dashiga

class ahanakali take tafiya tana jin wata

muguwar tsanar salman jitake daza’a bata

wuka ace anmata uzuri takashe mutun daya

data tsana a duniyarnan to lalai ba shakka

salman zata lumawa wannan wukar😡..

Salma kam yaci alwashin sai ya nunamata

shi basa’an yinta bane dan tunda aka

haifeshi bawanda yataba fadamai maganar

banza irin wannan banzar yariyar dabai

masan ta ba, Amir yakalla yace adubomin

ko ita wacece, Amir yace wannan yarinyar?

Salman yace yes I can’t live her like this.

Amir yace angama prince….


DOCUMENT INFONI DA PRINCE complete
Name NI DA PRINCE
Size 211 KB
Author Ayusher Muhammad
File Type doc
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modiied 17 September, 2020
description hausa FICTION

DOWNLOAD DOCUMENT

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.