download MURMUSHIN ALKAWARI complet hausa novel document

DANDANO

Nas acikin duk kyawawan matan dana taba baka labarinsu abaya irin su tani da kyakkyawa ummi kawar mabaruka gurguwa babu wacce takai koda rabin kyawun FALMATA. Sidi mai jaka yace dani yana dubana.

Wacece kuma Falmata?

Itace mace ta farko da nake son saka maka zaren labarinta yanzun nan idan Allah yaso. Sidi mai jaka ya amsa min kai tsaye. Nikuwa sai na girgiza kai cikin tsananin shakkar jin abinda yace kana nace dashi a tausashe.

Yanzu ashe baba sidi har akwai wata mace wai ita falmata da za’ace wai tafi ummin nan kawar mabaruka kyawu? Haba baba jifa sunanta wai falmata saikace wata hula. Ni sunanta ma baiyi kama da sunayen kyawawa ba. Baba sidi ya kalleni cikin murmushi kana ya dada karyar goro ya jefa bakinsa yace.

Nas kenan to ai abinda nake so ka gane shine kyawun fuska daban kyawun suna daban kuma abinda nake so ka sani shine falmata tana daya daga cikin kyawawan mata na wannan zamani. Ayadda na sami labari ita kanta falmata tana kiran kanta da kyakkyaw haka nan alokacin da take budurwa kafin ta auri SAIFULLAHI wani saurayinta ya taba cewa da ita.

Kai falmata wallahi kyawunki yafi kyawun kudi akan doron kasa. Gashi idan kika bata rai sainaga kin kara kyawu idan ko kikayi murmushi Wallahi numfashina har daukewa yakeyi saboda shauki…

Kana nufin kasa dani ita falmatan matar aure ce? Na katse shi da wannan tambayar. Baba sidi ya gyara zama akan tsohuwar kujerar kana yayi gyaran murya yace.

Haba Nas me kake ci na baka na zuba kaidai bani aron kunnuwanka kasha labari.

Na gyara zama nace Naba Ka.

Yauwa to kamar yadda nace dakai tun farko inason ka dauki zuciyarka cancak ka mayar da ita cikin wani kayataccen dakin shakatawa wanda ke dauke da kayan alatu acikin garin Borno.

Na mayar da zuciyar tawa. Nace dashi ina mai tunanin irin zaren da wannan tsoho zai saka min awannan rana. Sidi mai jaka ya dada gyara zama sannan yafara cewa.

.

Karfe biyar da biyar na yammacin wannan lahadi wata farar kofa ta bude sannan wata kyakkyawar halitta tafito daga cikin bandaki sannu ahankali tana rausaya kamar bishiyar turare ta ratso kan tattausan kilishin dake lullube da dandasheshen dakin shakatawar tana tafe tana wakar wani fitaccen fim na hausa. Alokacin data kawo tsakiyar dakin shakatawar tana wake tana rausaya ji takeyi kamar itace ainihin yarinyar dake wannan waka acikin fim din data Gani.

Wannan kyakykyawar halittar sunanta Falmata fadin kyawunta kauyanci ne kokuma bata lokaci domin za’a iya asarar takardu da ruwan alkamali masu yawan gaske kafin a zayyane surar wannan kyakkyawa.

Kamar yadda ta saba yau ma falmata daga ita sai daurin kirji da wani tattausan shudin kyalle mai taushi haka ta shigo falon in ka dauke wannan daurin kirjin jikinta tik take kamar dankali. Kanta babu dan kwali sai gashin kana yalo yalo baki sidik yana sheki ya kwanto mata har gadon baya. Tun da take ba’a tabayi mata kitso ba domin koda anyi ma anyi a abanza don ko rabin sa’a bayayi zai warware saboda tsabar santsin gashinta.

Sannu ahankali falmata ta nufi jikin katon madubin sannan ta janyo wata yar kujera mai doron baya ta zauna sannan ta dubi kyakkyawar halittarta ajikin madubin tayi murmushi.

Sannunki yarinya falmata… Kyawu dai kam Allah yabaki…. Saidai kuma bakiyi dacen miji ba. Tace da kanta lokaci guda kuma tana kokarin goge ruwan dake diga daga cikin lallausan gashinta falmata ta dubi fararen idanunta sannan sai jajajaja bakake bakaken lebben bakinta suka fadada da murmushin alkawari ga wanda yayi dace take kaunarsa sannan saitaci gaba da rera wakar fim dinta tana kwalliya abinta. Alokacin babu wani mahaluki aduniya daya isa yace wai acikin bakin ciki mara misaltuwa take domin na farko dai fuskarta a washe take lebbanta dauke da murmushi gashi kuma tana rera waka abinda harda rausayawa.

Tsahon kusan sa’a guda ta share tana shafe shafe da goge goge daga karshe dai ta dubi kanta duba na karshe ajikin madubi saitayiwa kanta murmushi domin tayi farin ciki da abindata gani takuma riga tasan cewa ko iblishi ne shi bai isa yaganta ya dauke kai ba. Dole ne hankalinsa ya kwanta da ita. Dolene ya amince da ita ayammacin wannan rana mai kunshe da manufarta ta aiwatar da boyayyen sirrin dake zuciyarta yana ci ganga-ganga kamar wutar makera.

Falmata ta shige wani dan daki ba’a dade ba sai gata ta fito da wasu shudayen kaya riga da wando dinkin fakistan wadanda sukayi matukar matse jikinta gamgam. Suka kuma fito da boyayyiyar halittar da Allah yayi mata afili wannan shiyasa falmata kurawa jikin katon madubin idanu akaro na biyu ta sake nazarin kanta.

Falmata tariga tasan ita kyakkyawa ce domin tun tana yar kankanuwa mahaifinta ke kiranta da kyakkyawa uwarta ma kyakykyawa Take kiranta dashi yan ajinsu ma yan uwanta mata a fimare sun sha cewa da ita kyakykyawa ce amma a fakaice. Domin wata sa’ar sai daya daga cikin daliban mata ta dubi falmata tace kai Allah yaban gashi irin na falmata wata babbar kawar falmata ta taba cewaWata babbar kawar falmata ta taba cewa ba abinda take son falmata dashi sai tsayinta.

Irin wadannan batutuwa su saka sa tun falmata bata kula har dai ta ankara da cewa ashe dai itama kyakkyawa ce.

Dan haka ayanzu data dada kallon kanta jikin madubin saita dauki turare ta fesa ta dada daukar wata kalar daban ta fesa sannu ahankali saida ta fesa sama da kala bakwai sannan saita wuce kai tsaye ta zauna akujerar dake kallon kofar katon dakin shakatawar ta fara zaman jiran maigidanta saifullahi.

Karfe shida saura kwata na yamma saifullahi ya karaso gida tun kafin ya shigo dakin shakatawar yaji kamshin turare ye bugi hancinsa abin yabashi mamaki domin ya riga yasan ayadda matar tasa ta tsane shi batayin kwalliya don shi sai in zata fita unguwa wannan duk bata dame shi ba domin ya riga yasan ko matarsa tayi wanka ko kada tayi ko tayi kwalliya ko kada tayi ko tayi direshin ko kada tayi kai aduk halin datake ciki kyawunya bai taba gushewa ba kamar yadda kaunarta bata gushewa cikin zuciyarsa ada…. Dacan kafin idanunsa su kai kan babbar aminiyarta INYAMI.

Cikin tsananin mamaki saifullahi ya shigo cikin dakin sanye da babbar riga da yar ciki da wandonta kansa matse da rantsatstsiyar hula tangaran hannun na dauke da bakar jaka wacce awani lokaci daya wuce babban direbansa MUDI ne ke rako shi da jakar har cikin dakin amma tun daga ranar daya auri falmata sai ya haramtawa direban shigowa musamman ma dayake direban ya fishi dan kyawun gani. Afuska nesa ba kusa ba. Saifullahi baki ne dogo kakkaura yana sheki kamar an shafa masa shuni saboda baki yanada tarin gashin baki kamar tsohon soja hakanan yanada tarin gashin kai duguzunzum kamar shekar ungulu adan sa’ar dayake saurayi sosai ashekarun alif tari tara da tamanin cinyewar kenan da burgewa ka ajiye suma duguzunzum babu ko tajewa wannan tsohuwar al’ada ita ke biye da saifullahi har zuwa wannan lokaci dayake dan shekara arba’in da biyu kaida ka dube shi ka dubi falmata saika ga kamar hasken fitilar kwai ne da na hasken rana. Dayawa daga cikin mutane sunyi ittafakin cewa in banda al’amari na masu gidan rana saifullahi bai isa debowo falmata ruwa wanka ba ballantana na sha.

.

Falmata ta mike tsaye cikin fara’a tana rausaya ta tare shi.

Sannu da zuwa Saifu. Tace dashi kana ta karbi jakar dake hannunsa. Saifullahi yayi tsaye sororo cikin tsananin kaduwa da wannan sauyin yanayi na bazata domin shi a tunaninsa bayan abinda yafaru a yammacin jiya yau idan suka fara rikici sai makwabta sunzo rabiya. Amma abin mamaki sai gashi ta karbe shi da murmushi harda ce masa SAIFU.

Rabon dayaji ta kira shi da sunansa tun ran daren amarcinsu na farko awannan ma sunansa ta kira ta zaga.

Yaya naga ka zuba min idanu. Cire rigar mana kasha iska. Tace dashi kana ta kashe masa idanu cikin rausaya ta dora jakar akan kujera kana ta matso kusa dashi ta cire babbar rigarsa da hularsa ta jefa kan kujera sannan ta kama hannunsa ta janyo shi daf da kirjinsa tace a tausashe.

Ko kaifa. Yanzu bakafi jin iska ba?

Saifullahi ya gyada kai kamar jangwalangwadan kadangare, domin yana cikin tsananin kaduwa falmata ta kama hannunsa shikuma yana biye da ita kamar tunkiya lokaci lokaci yana satar kallon jikinta wanda ke ta faman rawa acikin matsatstsun kayan kamar roba. Ga mamakinsa saiyaji kwarjininta da kamshin dake tashi daga jikinta duk sun ruda shi rabon da hannunsa ya taba hannunta anfi wata biyu.

Sannu ahankali har takaishi dakin kwanansu ma’abocin kawa da wani fankadeden gadon alfarma mai kamar filin wasan kwallon kafa. Gadon dauke yake da wata jijjigegiyar katifa mai numfashi wacce ko kobo ka jefa akanta sai yayi tsalle ya fadi kasa. Suna zuwa daf da gadon sai falmata ta kama kafadarsa a tausashe ta zaunar dashi sannan ta dube shi da tattausan MURMUSHIN ALKAWARI tace… Ina zuwa saifu. Cikin sauri ta fice daga dakin saifu yabita da kallo sannan iya kumshe idanu yana Allah Allah tayi sauri ta dawo azuciyarsa yana cewa da ace kullum haka takeyi min me zai hadani da kawarta Inyami? Ba’a dade ba saigata dauke da wani farin faranti mai dan fadi wanda ke dauke yankakkun tufa dakuma kofi mai dauke da sassanyar tataccen ruwan ya’yan itatuwa dangin zaki. Falmata ta ajiye farantin agefen gadon sannan ta matsu kuda da mijinta ta dora cinyarta akan tasa tace a tausashe.

Duk ka gaji dubi idanunka yadda sukayi jajur da alama barci kakeji?

Akaro na farko sai saifullahi ya jefeta da murmushi sannan yace. Wallahi kuwa kamar kin sani murmushin falmata yafadada lokaci kuma ta dauko tataccen ruwan ya’yan itatuwa ta mika kusa da bakinsa. Jikinsa na rawa ya karbi lemon wani farin ciki da bege gamida kunyar cin amanar da yayi mata suka taru suka narkar da zuciyarsa ko daya dubi kyakkyawar matar dake zaune ajikinsa tana bashi ruwan zaki abaki kamar wani karamin yaro sai zuciyarsa ta karye nan da nan wani zazzafan hawaye ya fara sartu akan fuskarsa idan har falmata taga hawayen to bata nuna alama ba.

.

Falmata ya kira sunanta a sanyaye.

Meyasa ki sauya irin halayyarki agareni? Falmata ta dubeshi da murmushi tace.

Gani nayi lokaci yayi daya kamata na rungumi mijina hannu bibbiyu na shayar dashi ruwan kauna. Saifullahi ya dubeta cikin shakka.

Yanzu duk bayan cin amanar danayi miki jiya bakiyi fushi dani ba saikika kara kaunata? Falmata ta lumshe idanu cikin murmushi sannan saita langwabe kai ta kwanta akan kafadarsa kamshin mai da turaren dake jikin gashinta ya bugi hancinsa.

Kwanta ka huta saifuna. Kabar wani tone tone abinda yafaru ya riga ya wuce saidai kawai a kori gaba. Falmata tace dashi a sanyaye sannan saita tura shi ahankali da kyawawan hannunta saifullahi ya kwanta akan gadon idanunsa akan kyakkyawar fuskarta.

Tun da nake aduniya falmata ban taba sanin abinda ake kira da SO kulawa da kuma dadin aure ba. Sai yanzu da kika sadaukar da kanki agareni. Falmata ta matsa daf dashi ta kwanta agefen jikinsa akusa dashi sannan ta dora hannunta akansa tafara shafa gashin kansa mai taurin tsiya kamar ciyawar kan iyaka. Tana cewa dashi a tausashe.

Kada ka dami zuciyarka da tunanin shudadden al’amari ka kwanta ka huta idan ka tashi ma tattauna… Kaji saifuna. Saifullahi yaji tamkar amafarki yake ganin wannan al’amari dan haka sa’ar da ya lumshe idanunsa sai ya sake bude idanunsa domin a tunaninsa tabbas mafarki yakeyi. Koda ya bude idanun sai yayi ido biyu da falmata har yanzu tana nan kwance akusa dashi ta kura masa idanu cikin murmushi, hannunta akan kirjinsa.

Ina matukar son murmushin nan naki falmata. Falmata ta saki wata tattausar dariya mai kamar busar sarewa sa’ar dataji abinda ya ce. Sannan saita dada matsawa jikinsa kana ta kara bakinta agefen kunnensa tace.

MURMUSHIN ALKAWARI ne nakeyi ma. Saifullahi ya lumshe idanu yace. Murmushin alkawarin me? Falmata ta shafi fuskarsa tace.

Murmushin alkawarin daga yau din nan har abada bazamu sake fada ba da juna. Wannan batu shi ya dada tausasa zuciyar saifullahi ga mamakinsa saiyaji duk gabobin jikinsa sunyi lakwas ba’a dade ba sai ya fara wani kwakkwaran munshari kamar rago barci ya daukeshi.

Tsahon mintuna goma falmata na jikinsa tana kallon fuskarsa azahiri amma abadini bashi take kallo ba.

Can saita fara janye jikinta a hankali har saida tabar jikinsa sannan saita tashi zaune akan gadon akwai sauyin yanayi na lokaci guda akan kyakkyawar fuskar ma’abociyar murmushin alkawari. Cikin sanda saita dage rigarta sannan ta tura siraran yan yatsunta kamar budar idanu saita zaro wata sharbebiyar wuka mai baki biyu kamar bakin damo ta juya wukar ahannunta ahankali kamar mai wasa da yar tsanar kashi kana saita dubi Saifullahi ta kuma dubi katon dumbinsa tayi murmushi sannan saita runtse idanu ta rike wukar da karfi da hannu biyu ta daga sama sannan ta soka wukar da karfi atsakiyar tumbinsa Cus! Saifullahi ya farka a gigice adaidai lokacin da falmata ta zare wukar sannan ta sake caba masa aciki saifullahi ya kwalla kara sannan yafara haure haure falmata tayi tsalle daga kan gadon ta diro kasa sannan ta dubi Saifullahi wanda tuni har ya daina motsi harshensa ya zaro waje tace cikin murmushi.

Ai na fada ma daga yau bazamu sakeyin fada ba. Tana gama fadin haka saita juya cikin sauri ta fice daga dakin sannan ta rufe kofar da karfi ta nufi cikin falo jikinta na rawa.

.

Sidi mai jaka yayi shiru sa’ar dayazo nan ya dubeni da murmushi yace.

Nas kaji me kyan dan maciji ko? Bakina na rawa na dube shi nace.

Kada dai kace dani har zaren labarin wannan ya kare? Sidi mai jaka ya fashe da dariya yace.

Kaida kace bazaiyi dadi ba? Menene kuma na damuwa da ya kare ko bai kare ba?

Haba baba sidi don Allah kaci gaba….wai kana nufin wannan marar imanin mayaudariya kashe shi tayi da gaske? Sidi mai jaka ya furzar da duddugar goron data taru abakinsa kana yace.

Tun daka fara jin dadin labarin bari mu koma cikin falon muga abinda falmata keyi ai baka ma ji komai ba awannan labarin me akayi da maza inji karya? Abin ma da yanzu muka fara ai labari saima tubanina ya karaso tukunna. Ya danyi shiru sannan sai yace.

.

Nas sa’ar da falmata ta shigo dakin shakatawar jikinta na rawa saita wuce kai tsaye zuwa bandakin datayi wanka dazu aciki tana zuwa saita kalli mudubi. Tsoro da fargaba suka damki zuciyarta sa’ar data ga duk kammninta sun sauya kwalliyarta ta baci fuskarta tayi fari fat. Kamar taga fatalwa. Cikin sauri ta dauke kanta daga kan madubin sannan ta nufi inda komin wanka na tangaran yake jikinta na rawa ta cire kyawawan kayan dake jikinta ta watsar gefe guda domin amfaninsu agareta ya wuce. Jikinta na rawa tsirara saita shiga cikin komin wankan sannan ta kunna shawa.

Sassanyan ruwan ya fara wanke kanta sannan sai gangar jikin.

Wannan shi yafara dakushe kaduwar dake jikinta domin kaduwa ce kawai amma ko kusa ko alama bata nadamar abinda tayiwa mijin nata domin maci amana ne… Maci amana wanda yaci amanata duk kuwa da aurensa danayi alhali bana kaunarsa falmata.

Koda sassanyar ruwan shawar yaci gaba da kwaranya atsakiyar

Koda sassanyar ruwan shawar yaci gaba da kwaranya atsakiyar kanta da bayanta sai zuciyarta ta tafi dofon tunanin wani shudadden lokaci shekara kusan guda kenan kafin ta auri Saifulahi.

.

Tun sa’ar da wannan kyakkyawar mata tafara kaiwa munzalin ‘ya mace nas sai Allah ya jarabce ta da kaunar wani saurayi wanda bata taba ganinsa azahiri ba sai acikin akwatin talabijin.

Wannan saurayi shi Falmata ta fara kauna aduniya kuma akanta ta kare kauna haka nan har zuwa lokacin data soke mijinta Saifullahi da wuka babu wanda wutar begensa ke ruruwa akullum kwanan duniya sai wannan saurayi.

INFO

 

MURMUSHIN ALKAWARIcomplete
NameMURMUSHIN ALKAWARI
Size85kb
AuthorNazir Adam Salih
File Typedoc
uploaderMr Dlhausanovels
ebook compilerShuraih 99%
date modified15 September, 2020
descriptionhausa FICTION
Subscribe to our newsletter

Leave A Reply

Your email address will not be published.