download KUYANGA complete Hausa Novel document

SHIMFIDA

Sarki Abdallah Adalin Sarki ne mutum me kamala da Son talakawansa Wanda yake da mata Uku sai yara biyu matarsa ta farko uwar gidan itace Hauwa,u Anace mata *UMMAH*
Mebi mata itace Saratu *MAMAH* sai ta Uku amaryar sarki itace Fatima Amma *FATU* akece mata
UMMAH macece me tsananin kishin gaske Tanada gadara da iko ita din yar gidan Sarautace tana buga ikonta agidan sarki domin sarki Abdallah yanaji da ita don haka take buga sha,aninta ackn gidan kowa shakkarta yakeyi tundaga fadawa,Bayi maxa da Kuyangin gidan da duk wanda ke cin gidan har kishiyoyinta D’anta Daya jal Yarima Anwar Wanda aka shagwaba shi da Gata Awaje yayi karatunsa Tundaga Sakandare har tagaba da Sakandaren wanda ba karamar tabarbarewar tarbiyya zamansa acan yaja masa ba don tun daya gama karatunsa yaki dawowa Yasamu guri xan babu kwaba babu harara 
Har saida labarin abinda yakeyi yadawo kunnan me martaba yai masa aike takakkiya aka taho dashi
Yayi masa fada sosai har kurari yaimasa yace inhar baidaina ba zai yi masa Aure ackn dangi zai laluba yadaura masa Aure da koma wacece
Aikin Anwar acan neman matan banza turawan nan sun sassanshi haka abokan banza yake mu,amula dasu basu da aikin komai saibin club club ana lolewa da mata anashan Giya ana raye raye 
Amma yafi Ronce da wata baturiya data nace masa mesuna RIHANNA wacce duk wulakancinsa takan shanye Abu daya yasa yake d’anshan mintinta tasan takan iya kulawa da d’a namiji duk luggar yaudara da iya Romance ta kware
Inda tayi musu zarra kenan gata da kishin tsiya tasha zane mata masu kawo masa hari Amma ahakan yake yakiceta yaje yashana da wacce yakeso danma tana shakkarsa da bazata bari yasakeba
Anwar yanada isa da jinkai jinsa yake tamkar sarkin wani zubin to kullum azuciyarsa yana jin kome zaiyi babu wanda ya isa yakawo masa cikas tunda shi din dan sarkine me jiran gado
Mahaifiyarsa ke kara sakawa yaji izxa aransa akullum takan nusarsa cewar shine sarkin gobe duk da shi bawani son yazama sarki yakeyiba tunda yasan inya zama sarki dole yazauna guri guda kuma yabar duk abinda yakeyi knn.
Sarki Abdallah akullum cikin bakin cikin Abinda dansa Anwar yakeyi yakeji aransa wanda yarasa yadda zaiyi dashi don yakintsu tunda shine babban dansa wanda wataran dole shine sarki agarin
Yasan da cewar Mahaifiyarsa ke xugashi tunda yahaneshi da zaman turai tace abarshi yahuta acan kafin wani lokaci bata son abinda zai bata masa rai
Sauran matan Sarki su idone nasu domin ta tsakiya MAMAH bata taba haihuwa ba itako Amaryar sarki FATU ta haifi Danta namiji tsiransu shekara biyar da Anwar yaron sunansa LAMIDO
Ummah bata kaunar FATU da D’anta sbd Fatun bata dade da zuwa gidanba ta samu ciki 
Ko MAMAH data rigata xuwa bata qullaci fatun ba domin MAMAH macece me tawakkali duniya bata dametaba
Kowane d’a  daga cikinsu tadaukeshi tamkar ita ta haifeshi
Amma tun tasowarsu da suka girma sai tafi kaunar Lamido domin shi yarone me hankali magana ma bata dameshiba a Nigeria yayi karatunsa
Lokacin daya isa shiga jami,a alokacin Sarki yaso turashi Turai shima Amma sai FATU taki amincewa sbd a ganinnta xaman turai ga yaro ba uwa ba uba na bata yaro da canza masa halinsa mekyau zuwa mara kyau tunda shima Anwar dayaje ba haka yakeba ada daga baya yakoyo wasu dabi’un
Sarki bai bata rai akn hknba domin takawo masa kwararan hujjojinta akan rashin son zuwan nata Turai yakuma gamsu
MAMAH ma bataga laifin taba domin tasan komai kuma kansu ahade yake su biyun
Sautari UMMAH takance wai sun hade mata kai 
Sukuwa shakkarta da sukeyine yasa basa shiga Sabgarta
******
Tun Dawowar da Anwar yayi Nigeria kusan wata biyar yaji yagaji da zaman atakure yake baya futa club balle korawa da neman mata sbd babu dama duk inda yayi ido akansa suke inma yayi awajen gari Sarki zai iyaji azo ace yabatawa gidan suna shiyasa yafison yafita away
Rihanna tayi ta damunsa akan inhar bai dawo Turai ba zata hado kayanta ta biyoshi ta nemi inda yake 
Hankalinsa yadaga dan yasan zata iya shiko yasan inhar tazo kashinsa yagama bushewa ackn gidan
Ba shiri yahau hada kayan dazai tafi dasu domin yai mata Alqawarin zaitaho cikin Satin domin ma kwana biyu yabata zaitafin
Da tunanin yanda zaishawo kan Sarki yabarshi yatafin yashiga cikin gidan Bangaren Mahaifiyarsa domin yafara kai mata zancen su samo mafita tukun
Yana tafe afarfajiyar gidan yana tafiyar Jinkai da wani shankamshi da Rangaji ackn Shigar Alfarma ta sarauta
Bayi maza Da kuyangu mata nata aiyuka suna wuceshi tareda durkusawa suna kai gaisuwarsu ga Yarima sarkin gobe
Wata *KUYANGA* Yakurawa idanu dayaga tanata sharar gurin ajiye dawakai kanta ba dankwali dan gyalen data yane kanta ya xame bata saniba
Farace shar gata da hips ga nashanu suncika  mata kirji
Ta dago zata bar gurin yakwalla mata kira
Aguje takaraso gareshi da biyayya ta durkusa tana gaidashi
Yakara kallonta na sakanni kana yace ckn shanqamshi “me kikeyi acan?
Da rawar murya tace “ina..,ina yin..,Shara nakeyi…
Yace “Dama Sharar gurin Dawakai nakune mata kona Bayi Maza?
Tayi kasa da kai tace ckn rage murya “Allah yataimaki Yarima tuba nakeyi ba aikina bane MAHBUB nake tayawa yatafi wani uzurin.
Yace “MAHBUB!wanene kuma *MAHBUB?* 
Tahau kame kame tazaci ko laifi tayi
Tace “Abokin shawaratane tamu tazo daya.shima yana tayani Aiki shiyasa nake tayashi
Ayanda take maganar yabashi Sha,awa bakinta me kama da anzana heart yatsurawa idanu yaga tana motsashi ahankali
Koda tayi shiru shima shirun yayi yana kallonta kawai
Wani abu yaringa ayyanawa aransa
Dataji shi shiru saita dago kanta dasauri tayi tsammanin yatafine saitaga ashe yana gun 
Tayi saurin yin kas da kanta don gudun kada suhada idanu
Yace mata “meye sunanki?
Tace ” sunana *KUYANGA* !!
Yace “ke Sunanki nace zaki fadamin na gaskiy KUYANGA ba suna bane aguna wannan kalmar larabcine abangaren hausa kuma ace Baiwa.
Tace “Sunana *ZEENATU* 
Ya gyada kai kawai yawuceta yana kara ayyana abubuwa ackn ransa
Koda yashiga cikin Dakin Mahaifiyar tasa tararta yayi hadimanta na mata hidima daga me matsa mata kafa ana mata tausa sai meyi mata furfita saikuma masu bare mata ayaba tana karba tanaci
Yana shiga hadiman suka miko tasu gaisuwar xuwa gareshi 
Ya amsa da ka
Ta nuna musu kofa tareda alamun sufuta subasu guri
Saida suka futa kana yagyara zama yace “UMMAH Barkanki da warhaka
Tayi murmushi ” Yawwa barkanka Abin faharina yarima Mejiran gado sarkin gobe da yardar Allah.
Yayi murmushi yace “Uwata maganin kukana yauma gani gabanki nakawo kukana nasan banda matsala tabangarenki zaki sharen hawaye Mai martaba kawai nakeji 
Tace “fadi ko meyeshi zanmaka zankuma saka ayi maka 
Yace “Ummah inaso inkoma Turai nagaji da zaman Nigeria niba aiki nake futaba kusan kullum nake gida bana motsa jiki kewa ta dameni kitaimakamin kisa baki me martaba yabarni intafi.
Tayi murmushi “Angama Yarima yaushe kake son katafin?
Yace “Jibi nashirya tafiyar
Tace “Jibi jibin nan? Amma baiyi kusaba kuwa nikaina bason kayi nesa dani nakeba gashi kaida akeso kahaye karaga wataran yaxa,ayi aga baka xama abaka.
Yace “kada kidamu da Wannan Ummah na wataran ai dole inxauna din nidai yanzu kiyimin kokari intafi
Tace “kada kadamu kamar katafi kagama zanyiwa TAKAWA maganar ayau.
Yayi murmushi yace “Yawwa nagode Ummah saidai kuma.……
yai shiru yana sosa keya
Tace “ehe!fadi mana yakai shiru kafadi komeye in akwai bazai gagara ba zanmaka.
Yace ckn rage murya “Saidai naga wata yarinya awaje ackn KUYANGU  zanso mutafi da ita tayimin Rakiya domin ta hidimta mini acan.
Murmushi tayi tace “bakada wannan matsalar kowannensu akarkashinka suke kanada ikon kowanne bawa agidannan ko kuyangu dan haka kasa aranka kamar ka tafi da ita kagama yatake yarinyar?
Take yahau kwatantata
Tagano ko wa yake nufi domin KUYANGA Zeenatu tafi kaf kuyangun gidan Nutsuwa  dakyawun yanayi tanada kyau nagani afurta 
Jin mahaifiyar tasa ta Amince masa yasa yaita xuba mata godiya
Shiyasa yake matuqar son mahaifiyar tasa baitaba neman abu ta bangarenta yarasaba tana son akullum tafaranta masa bata son laifinsa
Koda yafuto farfajiyar gidan baza ido yaitayi ko zai sake ganinta
Amma baiyi sa.ar ganin kome kamartaba
Tsaki yaja Aransa yace “to meye nawa nadamuwa da son ganinta Alhalin ita zata zamo gadon baccina ita xata xamo jin dadina ita zata zamo komai nawa sai yadda nayi da ita

KUYANGAcomplete
NameKUYANGA
Size179kb
AuthorNabilancy
File Typedoc
uploaderMr Dlhausanovels
ebook compilerShuraih 99%
date modiied17 September, 2020
descriptionhausa FICTION

Subscribe to our newsletter

Leave A Reply

Your email address will not be published.