download A’INDO TANTAGARARRIYAR YAR AIKI complet Hausa novel document

 SHIMFIDA

Tinkim  wani  kauye ne dake wajen jihar Zinder ,a kasar Niger ,kauye ne wanda kusan zan iya cewa tsaka tsakiya yake tsakanin Nijeria da Niger. 
  Kauyen yanada kyau da dadin zama,mutanen garin akoy karamci da son bako,gidan Ado Mai saida kifi kowa yasan sa a kauyen,tunda ya taso yake sana’a saida kifi,har ya zama samari ,ya hadu da kuluwa mai bakin masifa,kowa yasan kuluwa da masifar ta,hakan yasa duk wanda yake son ta da aure yanzu ne zakaji an zuge shi.ace Masa ai batada da’a bata san darajan yan Adam ba,masifafa ce,sai kaji an fasa auren. kauyen auren wuri ake ma yarinya daga kin kai shekaru sha uku sha hudu yanzu za’a aurar dake,yayyin da kuluwa saida takai shekaru goma sha takwas kafin  Ado mai  saida kifi ya gani yace yana so kuma yana iyawa Saida akasha duru kafin  a bari ya aureta.
   Bayan anyi Aure kuluwa tana masa ladabi da biyaya da duk wani abinda ya danganci sauke hakki ne na mijin ta ,saide fa ko kadan batada hakuri ,idan ya mata abinda bashi ba,yanzu ne zata juye masa buhun bala’i…..
   A haka suke zaune,yau dadi gobe ba dadi,Ado yanada daidai abin rufin asirin  sa,domin dai abinci bai gagaresa ba,sanan sutura batafi k’arfin su ba,da sauran abinda ba’a rasa ba,saida sukayi shekara daya kafin Allah ya Albarkace su da samun yan tagwaye duka mata,masu matukar kama da juna,kyawawa dasu bazaka taba gane su ba,ranar suna za’a sa musu sunan su na hassana da husseina  anma Kuluwa ta zuba masifa dole fa sai ansa ma daya sunan mahaifiyar ta da ta rasu,Allah ya jikan Mahaifiyar ta itama masifafa ce ta bugawa a jarida,dan kuluwa dai gado tayi……
   ba yanda Ado ya iya yace”tayi hakuri asa musu hassana da husseina sai a dinga Kiran Hassanar da sunan A’indo ,anan kawai ta yarda,aiko akasa ma hassana sunan A’indo.
    Tunda suka taso halinsu yadan banbanta,a halayen su kadai zaka iya banbanta su,dan ko mahaifin su saide ya Kira  da sunan su tukon yake ganewa, mahaifiyar su kadai take ganesu,watarana, anma ranar da suke jin iskancin sai suyi kicin kicin ko kai waye bazaka ganesu ba.
  ,,,,,,,,,, Husseina mafadaciya ce ta gidan gaske,yanzu ne ta zage ku danbata da ita,bata wargi kai ko fada taga anayi idan taga ba’a danbata ba yanzu zata saye fadan ayi da ita,gata tantiriya .yayyin da Hassana A’indo ta hada kusan duka A’indo dai  itama tana masifar ,saide akway ta da wauwta irin ta yan fari,ga tsiwa,ga karambani,kome ita ta iya,ga karambani yi ba’a sa ta ba,ga keta,uwa uba kauyenci saide matsoraciya ce ta gidan gaba, tunda suka taso kowace da burin ta ,A’indo batada buri sai taje birni aikatau,ita duk yanda take ganin yan mata daidai ita na kauyen in sunje aikatau wasu har a wuleliyar mota ake kawo su,to sai ta d’auki wanan tasa a ranta cewar Yar aiki baban matsayi ne da ita ,wanda ko a birinin da wuya a samu mai matsayin Yar aiki.
   Sun adabi mutanen gari,kowa fata yake suyi auren nesa,saboda duk kyansu ba Mai zuwa wurin su saboda masifa irin tasu da ta uwar su,a yanzu haka sunada kusan shekaru goma sha bakway anma ba mijin aure Mahaifin su har ya gaji ya zuba ma sarautar Allah ido,A’indo kuwa a kauye ba Wanda baisan sunan ta ba,da ta biyo guri kace  sai kinyi A’indo sai tace Tantagariyar Yar Aiki ba.”
   Ana cikin haka kanwar Mahaifin ta tazo daga birni wada take a birnin zinder tana zuwa ta samu yara ta d’auke su ta kaisu Aikatau a birini duk wata ana biyan iyayen su,itama tana samu.
   A wani zuwa ne da tayi A’indo ta aza bala’i itama fa sai taje aikatau dinnan,ba yanda Mahaifin ta ya iya yace suje ,wata kila ta samu miji ita in ta fita daga kauyen tunda dai wanan kauyen ba Wanda ke son su da aure,suna kuka haka suka rabu ita da yar uwarta Husseina,tun daga lokacin da A’indo ta tafi  husseina   ta Kara zama masifafiya,ta adabi mutanen gari tace ai ta dalilin su yar uwarta ta tafi,saide fa tace itama dan lokaci take jira,anma in lokacin yayi duk inda yar uwarta ta tafi a birni itama sai ta bita. 
      Ranar da aka shigo birni da A’indo duk Wanda ke cik’in motar Saida ta cika cikin sa da dariya,ana tsakar tafiya ta fido kanta ta window mota tana ihu wai ga bishiyoyi can na gudu,akayita dariya.       
       kusan gidan biyar  aka kaita aikatau anma duk inda taje sai tayi ta’asa,su korota.
  A karo na shida ne aka kaita gidan wani dattijo Alhajin Sanmani Hamshak’kin Dan kasuwa ne Mai kudi,yayan sa biyar Mata biyu Maza uku.
   Alhassan shine da na farko dan kimanin shekaru talatin da biyar a duniya (35years) Yan biyu ne yar uwar tagwaitakar sa bata  zo da rai ba sai shi,a yanzu haka yana kasar waje aiki yake sodja ne baba na kasa da kasa Wanda duniya keji dashi kuma take takama dashi,saboda ilimin sa kwazo ,basirar sa,uwa uba yasan kan aikin sa .baya dariya ko kadan,babu Wanda zaice ya taba ganin dariyar sa,saide murmushi , murmushin ma iyakar sa lebo . Mai bi masa shine idrissa dan kimanin shekaru ashrin da biyar,sai khalipha dan kimanin shekaru ashrin da uku suna karatu,sai halissa Yar shekara ashrin da biyu tayi aure a Niamey shekara biyu da ta huce,sai auta   khalissa, yar kimanin shekaru goma sha bakway su suna karatu ne.
  Sai mahaifiyar su Hajiya saude datijuwa Yar kimanin shekaru arba’in da biyar.
    Katon gida ne sosai tsarare ,Wanda aka kashe masa naira wajen tsara sa ,ginin ma ginin   turai ne, yan aiki gidan kusan ma’aikata goma sha tara ne,kowace da ranar aikin ta, bayan masu gadin gidan da masu tsaron lfy masu gidan su ba’a sasu a lisafi ba,Hajiya saude duk masu gyaran falon da ake kawo mata Sam bata wani ganin kyan akin su ita tafi so in ta fito falo taga ko Ina kal kal yana walkiya,hakan yasa tasa a Nemo  mata Yar aiki ta kauye a cewar ta su suka fi aiki domin basa Wasa da aiki suna sakin jikin su suyi aiki basa gajiya.
   Hakance yasa Anty najin irin Yan aikin da Hajiya keso ta kawo A’INDO gidan yau ai tun a k’ofa ta tatare siket zata arta a guje Saida Antyn tata da ta gane nufin ta ta rike hanun ta kam,tayita lalaba ta sanan suka shigo..

DOCUMENT INFO

A’INDO TANTAGARARRIYAR YAR AIKIcomplete
NameA’INDO TANTAGARARRIYAR YAR AIKI
Size483kb
AuthorMaimuna AbdullahI
File Typedoc
uploaderMr Dlhausanovels
ebook compilerShuraih 99%
date modiied17 September, 2020
descriptionhausa FICTION

DOWNLOAD DOCUMENT

Subscribe to our newsletter

Leave A Reply

Your email address will not be published.