KULU – na Bala Anas Babin Lata

Posted by | Mr Hausa Ebooks |
Price | GPL |
Category | Hausa Ebooks |
Uploaded On | 03 Dec, 2019 |
Upload Time | 12:01 am |
Last Modified Date | February 16th, 2022 |
Last Modified Time | 10:44 pm |
Hits | 538 Hits |
Author | |
Writer Group | Unknown / NIL |
Novel Genre | No genre attached |
Comment | No Comments |
Description
KULU – na Bala Anas Babin Lata
KULU – na Bala Anas Babin Lata
littafin gwarzon marubuci Bala Anas Babin Lata
An buga littafin a shekarar 1991
Farashi 200 naira
Published at okadabooks
About book
Sankon mai gidana Abba shi ne ya soma gaishe ni a daidai lokacin da na shigo garejin akan Kawasakina maras salansa. Na je na kafe babur din a karshen gini daura da ofishin Abba. Sannan na nufi wajen da yake yana ta fama da wata tsohuwar lada. Kwanansa biyu yana aiki akanta. Amma har yau bai yi dace ya kammala gyaranta ba.
Mai gida Abba gajere ne mai kaurin jiki yana da sanko, ban taba ganin mai dogon sanko kamar nasa ba, tun daga goshi har keya, in rana ta haska shi daukar ido yake yi kamar madubi. Amma bai damu yasa masa hula ba.
Yana saye da shudiyar rigar kaki watau rigar aiki, ta yi bakikkirin da maikon mota.
“Barka da aiki Maigida.” Na gaishe shi a dai dai lokacin da na karasa wajensa. Na leka cikin injin ladar.
“Barka kadai.” Ya amsa ba tare da ya dago kai ya dube ni ba. Ya samu rabin minti yana aiki bai dago kai ya dube ni ba, sannan ya dan juyo. Da ya ganni a cikin kayan gida sai kamaninsa suka sauya.
“Lafiya dai ince ko?” ya tambaye ni. Na ce lafiya kalau. “To yaya na ga haka? Ka makara amma kake bata lokaci. ‘Ya dubeni sosai da ruwan kasar idanunsa sannan ya ce “Dahiru ‘yan kwanakin nan ban san abin dake damunka ba. Baka son aiki ko kadan. Bayan shekaru biyu baya ban sanka da lalaci ba amma duk ka sauya. In ce ko ba shawarar Bimo kake dauka ba.”
Na ce. “Ko daya babu wata shawara da Bimo ya ke bani. Bana jin dadin jikina ne kurum tun daga lokacin da aka taso mu daga titin jami’ar Bayero.”
“To mene ne ke damunka, mutuwar zuciya.”
Na yi ajiyar zuciya. Sannan na sunkuyar da kaina. Don bani da abin cewa. Da ya ji ban ce komai ba sai ya ci gaba. “Dahiru gaskiya zan gaya maka in ba zaka zage ka yi aiki ba to zamu rabu.
“Ba wai ina nufin na kore ka ba, saboda mun dade tare da kai na kuma san matsayin da kake na maraici, amma bana son lalaci. Na san yanzu kasuwa ta lafa mana tun tasowarmu daga titin Bayero. Saboda haka ya kamata ka lura ka gane a matsayin da nake ciki. babu ciniki, amma wannan bai hana ni baka abin da na saba baka ba, ka san a maimakon abin da nake baka ba wani abu nake so ba face aiki tukuru.”
Ya sunkuya ya dauki sufana da ke yashe a kasa a gabansa. “Bimo kanina ne, amma saboda rashin aikinsa da yawan makararsa dole ne mu rabu, nan ba da dadewa ba, saboda haka ka mayar da hankali, na kara jaddada maka ka mayar da hankali ga aikin nan, don kuwa da aikinka na dogara. Ya kamata mu sake fito da sunan garejin nan” Ya koma ga aikinsa. “Jeka ka shirya ka fito aiki.”….
DOMIN CIGABA DA KARANTAWA SAI KU SIYA LITTAFIN AKAN 200 A OKADABOOKS TA HANYAR DANNA MABALLIN PURCHASE AT OKADABOOKS DAKE ANAN KASA
Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel
Leave a Reply
Related Files
-
Rai biyu written by Khadija Candy
11 months ago
1101 Hits -
download NIDA FATALWA complete Hausa Novel
2 years ago
992 Hits -
Jaruma yazila book 3 complete hausa novel document
1 year ago
314 Hits -
A dalilin gata hausa novel complete document
1 year ago
586 Hits -
Gudu a jeji hausa novel complete document
1 year ago
881 Hits -
BAKAR GABA 6
3 years ago
505 Hits -
IZZAR SARAUTA complete document hausa novels
1 year ago
5787 Hits -
Dan sarkin sauban hausa novel complete document
1 year ago
1299 Hits -
BIYU BABU complete hausa novel document
2 years ago
566 Hits -
Tsantsar butulci hausa novel complete document
1 year ago
892 Hits
Hausa Ebooks
-
BAKAR INUWA complete hausa novel written by Bilyn Abdul
1 day ago
334 Hits -
DAMUWATA complete hausa novel written by Mrs J Moon
1 day ago
135 Hits -
RASHIN JITTUWA complete hausa novel written by Mrs J Moon
1 day ago
191 Hits -
RUMASA’U complete hausa novel written by Mrs J Moon
4 days ago
313 Hits -
MUTUNCI MADARANE complete hausa novel written by Mrs J Moon
4 days ago
446 Hits -
ZEENATU complete hausa novel written by Queen Meemi
1 week ago
368 Hits -
KOFAR AJALI return complete hausa novel written by Abdul Alhaji Musa 10k
1 week ago
506 Hits -
SAIFUDDEEN complete hausa novel written by Billy Giro
2 weeks ago
1133 Hits -
NAGARTACCE complete hausa novel written by Oum Hanan
2 weeks ago
1125 Hits -
SHIN SO DAYA NE complete hausa novel written by Hafnancy
2 weeks ago
599 Hits
Movies and Films
-
Download Kalubale indian hausa fassarar Algaita
2 days ago
134 Hits -
Download Jaruman Kasa indian hausa fassarar algaita
2 days ago
102 Hits -
Download Inuwa Indian Hausa Fassarar Algaita
2 days ago
77 Hits -
Download Hatsabibi Indian hausa fassarar Algaita
2 days ago
121 Hits -
Download Fusataccen Dan Sanda indian hausa fassarar algaita
2 days ago
102 Hits -
Download Gadar zare indian hausa fassarar Algaita
2 days ago
68 Hits -
Download Barkonu Indian Hausa Fassarar Algaita
2 days ago
72 Hits -
Download Fuska Biyu indian hausa fassarar Algaita
2 days ago
106 Hits -
Download Dan Baiwa indian hausa fassarar algaita
2 days ago
82 Hits -
Download Farcen Gumurzu indian hausa fassarar algaita
2 days ago
73 Hits
Musics
-
Download Music: Adam Zango – Amarya
4 days ago
95 Hits -
Download Music: Adam Zango – Diana
4 days ago
91 Hits -
Download Music: Adam Zango – Allah ya gyara
4 days ago
71 Hits -
Download Music: Adam Zango – Manyan Mata
4 days ago
62 Hits -
Download Music : Adam Zango – Matan Aure
4 days ago
67 Hits -
Download Music Auta Mg Boy – Amana da amana mp3
1 week ago
130 Hits -
Download Music Farfesan Waka – Damfara Mp3
1 week ago
120 Hits -
Download Na Baki Soyayya – Adam A Zango Ft. Sals Fateetee Mp3
3 weeks ago
198 Hits -
Download Soja Boy – Nishadi Mp3
3 weeks ago
155 Hits -
Download Music: Sarkin Waka – Sai mun bata wuta Atiku
4 weeks ago
438 Hits