GOYON KAKA complete PDF

 GOYON KAKA complete PDF

Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Hausa Ebooks, Love
Uploaded On 27 Sep, 2019
Upload Time 12:20 am
Hits 1949 Hits
Author

Comment No Comments

DANDANO

Yarinya ce da baxata haura shekara takwas ba ta sheko da gudu cikin gdan nasu ko sallama babu,direct bandaki ta nufa abin data debo acikin rigarta ta xubesu a bakin ban dakin mangaro nagani da alama tsinkosu tayi ba wani excuse ta tura kofar bandakin saboda matsanancin fitsatin daya korota,
suman tsaye tayi sakamakon wanda ta gani a bandakin saboda tsabar tsoro a wando ta sako fitsarin,a 360 ta juya kotakan mangwaron batabi ba dakin kakarta ta shige gurin buya ta shiga nema can Allah y bata sa’a ta fada karkashin gado a lokacin kakar kuwa tana baccinta batasan mai yake faruwa ba.
Wanda ta bude a bandaki kuwa ransa duk y baci saboda bakin cikin yarinyar ta ganshi ba kaya a dalilin wankan da yake a gaggauce y karasa wankan y futo ransa duk a jagule matashine da baxai wuce 22 years ba ko daki bai shiga ba y wuce dakin kakar,masifa yakeyi tun daga tsakar gda yake kwalawa kakar kira danyasan xata iya boyeta kaka!kaka!!kaka!!!wlh yau saina kusa balla yarinyar nan kowa ma y huta ayi yarinya sai hatsabibanci,dannaga iskancinnaki gaba yakeyi tinda harkin kai ki leka mutum a bandaki yana wanka lokacin y karasa shiga dan duk babatun da yake a tsakar gidane kaka kuwa bata jishi ba saboda tana wata sabuwar duniyar cikin bacci.
Kaka!kaka!!kaka!!! ya kwala mata kira da karfi a firgice ta farka a baccin tana haba mai gdan wannan tashin hankalin kira kamar an kawo farmaki,tsaki yayi mtsss yace ni ina shegiyar jikarnan taki mai siffar aljanu,bata fuska tayi tace wlh Aslam ka kiyayeni,ubanme tayi maka xaka fara xaginta yarinyar ma da bata gidannan,tsaki yadanyi yace yace ai baxaki gane ba,tace eh mai xan gane,yace yarinya bakyason laifinta nidai kawai ki futomin da ita danyau saina babballata,islam cikinta ne yace kuwwwww tana xaxxaro ido tana addu’ar yasa karya ganta,dan tasan laifin datayi masa inya kamata xai iya kasheta,dan wlh yaya Aslam mugu ne,kaka ce ta juya tayi kwanciyarta tana kayi ka gama nidai a gidannan ko mai kama da islam ban ganiba tun rana data futa.
Juyawa yayi yace wlh nafasa yin satin yau xan koma dan aljanar jikarnan taki xata iya sakamin hawan jini,kaka tace kafi ruwa gudu umma tagaida aysha kuma karka kara kiran islam da aljana in baxata kirata da sunanta ba ka bashshi ba dole bane,islam sai data tabbatar da yaya aslam y futa sannan ta fara kokarin futowa.
Kokarin futowa takeyi daga maboyar tata kakace tajiyo mutsu-mutsu a karkashin gado tace au Ashe shegen berannan bai mutu ba aikuwa yau xan saka maka maga..bata karasa magana ba taga islam ta fito tana xaxxaro ido ,kaka ta kama baki tace lah ga ja’irar kaya yaushe kika shigo,xumbura baki islam tayi tace daxu nashigo.
Kaka tace to menene y hadaki da wancan mai bakar xuciyar yadda y xuciya daya kamaki dako makota baxasu iya kwatarki ba,karamin bakinta ta cuno gaba tace to ai daga gonar malam tanimu muke shine fa fitsari y matsoni tofa bansan fa yana bandakin yana wanka ba shine nashiga duk cikin dangarta take maganar,kaka ce ta tuntsire da dariya tace kaji yar nema daman nasan laifi kikayi masa,islam itama dariyar take tace Allah bada gangan nayi ba,kaka tace toh naji,islam tace yanxu ina yaya aslam din saboda futa xanyi xamu tafi rafi yau ana kamun kifi,
kaka ta karkatar da baki tace kinsan bakar xuciyarsa yace gda xai tafi,islam tace gwandama dama duk y takuramin y koramin abokanaina y hanasu shigowa gidannan sannan y hanani futa wasan dare,tashi tayi tace kaka saina dawo,kaka tace to amma baxaki hutaba naga yanxu kika dawo,tace au bari nadauko mangwaro na ki boyemin dan sai da mukayi dambe da hanne na kwato mangwaron nataho nasan intaxo tagan shi xata dauka,ta futa ta dauko ta kawowa kaka ta dauki daya tana wlh kuma kaka karki shamin kinjiko,kaka tace xancen banxa mai xanyi da kayan tsami xoki dauki abinki,dariya islam tayi tace Allah y baki hakuri kakata ta kaina ta fuce,a kofar shigowa dakin kaka sukayi kicibis da yaya aslam rangwashi y sakar mata a tsakiyar ka,
wani gigitacciyar kara ta saki sanadiyyar wani masifaffen xafi da taji y ratsata,a kuje ta fuce waje taci gaba da ihu,da gudu kaka ta taho har tana tuntube xani na faduwa tana daukaᗒ da aslam suka hadu xai shigo dakin hade girar sama da kasa kaka tayi tace me kayi mata,murmushi yayi yace haba ta wajena me kuwa xanyi mata tsorata dai tayi data ganni shine fa ta fice da gudu taxata xan daketa,dariya kaka tayi tace yauwa aina xata dukanta kayi narama mata,xaro ido yayi yace yanxu saiki dakeni tace ras ma kuwa,sallama sukaji anayi kaka ta xari mayafi aslam y mara mata baya malam tanimu suka gani y kawo karar islam da kawayenta da abokananta irin barnar da sukayi masa acikin gona,kaka tace karka yiwa jikata sharri yaushe taje gonarka,kana da wannan shegen saka idon da bakar rowa ta yaya har xasu dauki mangwaronka ka bassu,
yace ai katanga suka haura,kaka tace ni islam bataxo da mangwaro ba Aslam ne y dinga bawa malam tanimu hakuri dan yace mai gari xaije y fadawa,tsaki kaka tayi tace kaje birni ka fadawa sarki ba mai gariba,dakyar Aslam y shawo kan malam tanimu dan sai da y bashi 2k y hakura dan tanimu akwau san abin duniya lol,bayan sun shigo gida dan karamin tsaki
 
Aslam yayi yace wlh ke kika dada bata yarinyar nan in ba haka ba yaushe har tasan ta haura katangar mutum ta sato masa mangwaro dududu nawa take,kaka tace karyane fa sharri yakeyi mata,Aslam y nuna mangwaro akan gadon ta yace wancan fa,kaka tahau borin kunya tace to ayi mutum sai bakar rowar jaraba y shuka mangwaro mai warin gawasa kanshi y ishi yara y hanasu mai xai hanasu tsinkowa,Aslam yace wlh da inada iko da mayar da ita gurin aunty amarya xanyi tunda ba tarbiyya kikeyi mata ba,
harararsa kaka tayi tace to ko ubanka nina raineshi kuma nabashi tarbiyya,xaro ido yayi y kama baki yace Allah y baki hakuri,kaka tace naji,yace ai yayana wlh baxan kaisu riko ba balle kuma
*GOYON* *KAKA* xaki tayi tace wanema xai rikema yaya,yace eh naji kinsa ina bata lokaci sallama naxo miyi xan tafi,kaka tace haba Aslam au da gaske kake baxaka cika satin ba,yace gwanda natafi tunkan kikai ga duka tunda kin fara xagi tace nayi dukan ma indai kan islam ne sainayi maka,y futa yana kinjiko tace ga daddawa nasiya musu ka tafi da ita yace baxan dauki kayan wari ba yaja trolly bag dinsa yai gaba.

DOWNLOAD EBOOK

GOYON KAKA Complete
Name GOYON KAKA
Size 124kb
Author Umma Yahaya
File Type pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 14 September, 2020
description hausa FICTION

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files