GANGAR JIKINSA NA AURA

GANGAR JIKINSA NA AURA

complet
Na Jameela Umar Tanko

Domin downloading na littafin sai ku danna hoton kasannan 👇👇👇👇

[post_ads]

[post_ads]

KADAN DAGA CIKI

Wata kwarababbiyar mota kirar bus mai
kararfatattakekkiyar salansa ce ta tsaya a bakin
get dinmakarantar ‘yan mata ta gwamnatin
tarayya dakegarin Kazaure, wato F.G.G.C.
Kazaure. Tana tsayawakondastan motar ya ja
kofar ya bude “Barararaa”saboda kwankwatsewar
da kofar motar ta yi sakamakon cin ruwa da
gafje-gafje da tsabar tsufa.Wani dattijo mai
kimanin shekaru saba’in da doriyane ya fito, da
wata *yar yarinya tana biye dashiwacce
shekarunta basu wuce shekaru goma shadaya ba,
Bayan sun furfito kondastan motar yazagaya baya
wato but ya fefer wata katuwar akwatin karfe
irin ta *yan makarantar wacce akadafka sunan
mai akwatin garza-garza da fenti bakiHANNE
HABU IMAMU. Ya ajiye gefe ya sake janyowata
karamar katifa wacce take daure ya doraakan
akwatin, sannan ya dauko wani bokitin karfesabo
dal yana sheki shima an fenteshi da sunan mai
bokitin wato HANNE HABU IMAMU. Daga karsheya
mayar da kofar but din ya rufe ya juyo ya
kallidattijon wato Malam Habu ya ce “Baba baka
fa cikamana kudin motarmu bafa, gashi har kun
sauka”Malam Habu ya sake marairaicewa ya ce
“Dana daAllah fa nake hadaka kuyi hakuri kudin
da yayi saura a aljihuna ko gida bazai mayar dani
ba, sai nanemi ciko kayi hakuri dan Allah, dan
haka nemanace ta zauna a maleji yanzu baza ka
tausayawatsoho ba, karbi arba’in din?” Kondasta
ya sakefusata ya ce “Dalla Baba kana bata mana
lokaci gafasinjoji har sun fara tsaki sun kagu
suma a kaisu inda zasu. Ka zauna kana mana
magiya tun dazumuma fa ba’a bati muke shan
man motar da mukejigilar nan bafa, da kasan
kudin motar taka bai cikaba me yasa ka hau? Har
zaka ce wai yarinyar amaleji ta zauna, maleji ba
cikin mota bane? Bakasan har a sittin muke
daukar na maleji ba daga inda muka dauko ku
zuwa nan nayi maka ragi nace kakawo hamsin
dinma gashi kaki biya sai wataarba’in ka bani, kai
wallahi Baba saika ciko managomarmu kaji ko?
Direban motar dake zaune awajen tuki wanda
yake jin duk abinda suke yi, saiyanzu ya waigo
inda suke yayi magana ya ce “K.b wai yane? K.b
ya ce “Har yanzu wannan tsohon baidaina magiya
ba wai shi ayi masa ragin goma kudinyarinyar
nan data zauna a maleji, Hamsin nace yabiya, ya
wani bani arba’in. Kuma ma dan raininhankali
harda cewa kudin aljihunsa bazai mayardashi gida
ba, wato yana da kudin, cikawa ne bazai yi
ba.din aljihunsa bazai mayar dashi gida ba,
watoyana da kudin, cikawa ne bazai yi ba. Malam
Habuya danji dadi ganin direban yayi magana ko
zaice abar masa amma sai yaji kalamansa
sabanintunaninsa gara ma abinda kondastan ya
fada masa,cewa yayi in har bazai biya ta dadin
rai ba to zasu farka aljihunsa su dauki gomarsu,
Malam Habu yarike baki don mamakin irin
wannan rashinmutunci, can ya nisa ya ce “Allah
Ya kyauta, bari nabaku kudinku abin duk bai kai
ga haka ba, yasahannu a alhihunsa na dama ya
dauko watacukurkudaddiyar naira biyar ya sake
saka hannu a aljihunsa na bangaren hagu ya
dauko gudar nairaashirin da kwandaloli guda
biyar, ya hadakwandalolin nan guda biyar da
cukurkudaddiyarnaira biyar din nan ya mikawa
kondosta ya ce”Gashi dana Allah Ya kiyaye. Ba
kunya ba tausayintsohon nan yasa hannu ya
karbe yana gunani “Daman kana dashi ka tsaya
kana bata mana lokaciduk fasinjoji sun kagu,
direba ya juyo ya ce “YayaK.b ya baka, sun cika?
K.b ya ce “Eh sun cika jamujeJ.J.C. Malam Habu
da *yarsa Hanne suka bi motar dakallo har ta
hau titi ta kure sannan hankalinsu yadawo kan
kayansu. Malam Habu ya kalli *yarsa Hanne
wacce hawaye ya gauraye idanuwanta
dakumatunta, abin ya bashi mamaki ganin Hanne
nakuka alhali kuma ita take son karatu take
murna dazasu taho, ya sake juyowa sosai ya
kalleta yagahawaye ne ke zubowa daga
idanuwanta dayanabin daya, ya ce “*Yar Baba,
kukan me kike yi? Karki cemin yanzu bakya son
makaranta bayan keaka kira fadar mai gari aka
tambayeki kika ce kinaso. Ba’a son raina ba nima
na kawo ki makarantarnan ke kika amsa musu.
Shine kuma yanzu kikekuka? Idan kinsan bakya
so to ni a wajena tafinono fari sai mu juya kafin
mu shiga ciki. Kansila da mai gari su suka
tilastamin in kawo ki amma badanhaka ba nima
bazan rabu dake ba na kawo ki nanuwa duniya,
babu wanda kika sani. Hanne tagirgiza kai cikin
shesshekar kuka ta ce “Baba bamakarantar bace
bana so, rashin kunyar da masumotar can suke yi
maka shine ya sani kuka. Malam Habu yaji
hawaye ya cika masa ido amma sai yajure yayi
murmushin karfin hali ya ce “Allah Sarki*yar
Baba, babu komai duniya ce. Duk wanda
yagagirman tsohon wani, za’a ga girman nasa.
Hakakuma duk wanda ya raina tsohon wani sai
an rainanasa, zamani ne ya canja babu sanin
girman Allah, ko an hada mutum da Allah kamar
an hadashi dasa’ansa, wani cewa zaiyi daina
hadani da Allahkarka cuceni Wa’iyazubillah. Ya ci
gaba da cewa”goge hawayenki ‘yar Baba kizo in
dora mikiakwatin mu shiga ciki kada dare yayi
min kinga harla’asar tayi. Tasa gefen gyalen da
taci damara dashi ta goge idanuwanta kana ta
matso ya ciccibiakwatin karfen nan ya dora mata
a kai shi kuma yadauki bokiti da katifa a daya
hannun sa’annansuka juya suka doshi cikin
babbar kofar shigamakarantar, yaci gaba da yi
mata nasihohi masuratsa jiki yana nuna mata
wannan abin da aka yi masa a gabanta ya zama
darasi a wajenta duklalacewar tsoho koma ba
tsoho bane na gaba da itakada tayi masa fitsara.
Ta zamana ko a ina takekuma kome ta zama ta
girmama na gaba da ita.Ta zama mai taimakawa
mabukata, kasancewartasan talauci ta kuma
dandanashi tana kandandanashi. Masu gadi uku
suka iske a bakin kofarshiga cikin makarantar,
suna zazzaune, 

Domin cigaba da karantawa sai ku danna hoton kasannan don downloading littafin zuwa kan wayoyinku 👇👇👇👇👇


[post_ads]

[post_ads]

ga duk wayanda suke samun matsala ta wurin downloading ebooks namu kuma suke da bukatar mu rubuta masu copy din littafin mu turo masu ta whatssap ko profile nasu
SAI KU TUNTUBI mamallakin shafin Shuraih Usman
Ta facebook profile nashi
Kota nambar waya 08140419490
Kota adireshin Email
shuraihusman@gmail.com
Sai de ku sani wa hakan zamu cajeku wasu kananan kudade
its Shuraih Usman 99% 
Subscribe to our newsletter
Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Leave A Reply

Your email address will not be published.