BAKANDAMIYAR GUMURZU kashi na shida 6

BAKANDAMIYAR GUMURZU 

Kashi na shida 6
Na Umar Abdulhadi Mati
Karshe
DOMIN DOWNLOAD NA LITTAFIN ZUWA KAN WAYOYINKU SAI KU DANNA RUBUTUN KASANNAN 👇👇👇👇👇

[post_ads]

[post_ads]

Kai!! dakata sarki nawwar ya dakawa boka nazara tsawa cikin murya mai cike da fushi, kafiya, haɗe taurin zuciya ya fara magana “shin ka manta da ko wanene sarki nawwar kada fa ka manta nine ƙi gudu mai sanya maza gudu, bazan karya tarihin jarumtakar ahlinmu ba in gudu in bar ƙasata da alummata ba.
Yayinda su sarki nawwar ke wanan tattaunawa shikuwa aljani fargam juyawa yayi ya dakawa sauran mayaƙansa tsawa yana mai cewa” me kuje jira da sauran waɗanan “yan tsakin ku karasa su mana”, nan take aljana zarma ruwan bala’i, sadauki saljam, sadauki salka, aljana zabariyya, dodo zalƙim, da sauran sadaukan da sukayi saura na daga jinsin aljannu ,dodanni, mutane sukayi kururuwa haɗe da afakawa rundunar sarki nawwar nan take masifaffen yaƙi ya ƙara kaure a tsakanin mai taken a mutu ko ayi rai domin kowani ɓangare yaƙi yake da zuciya ɗaya da niyyar akashe shi ko ya kashe nan take kura ta tashi tayi sama wutar yaƙi ta fara ruruwa tana toroƙo.
Saidai wanan karon lissafin ya canza domin mummunar ɓarna akeyiwa rundunar sarki nawwa domin wanan karo aljana zarma wasu baƙaƙen takubbane take yaƙi dasu wanda lokaci ɗaya take kai sara hagu da damarta duk sara idan takai takan sare kan mutum ukku ko biyu, itakuwa aljana zabariyya wani baƙin mashine a hannunta wanda da takai suka ko duka saidai kaga mazaje na zuba kamar gobara a gonar auduga, ɓangaren sadauki saljam ma babu kyau duk da cewa ƙafarsa guda akwai ɗori na karaya hakan baisa ya gaza ba domin duk sadaukin da ya raɓeshi sunansa gawa , haka sadauki salka shikuwa babu makami a hannunsa saidai duk sadaukin da ya tunkaro sa na take zai watso masa koriyar wuta ta ƙoneshi ƙurmus, ɓangaren su dodo zalƙim da kalkus kuwa abin yafi na ko ina muni domin kowannesu da yakai jimƙa ko raruma saidai kaga ya damƙo mazaje ukku ko huɗu ya ruɓurɓushesu ya watsar da karyayyun sassan jikinsu kokuwa kaga yadda kasan takar da sun kama mutum yana ihu haka zasu yagashi biyu.
Haƙiƙa kisan da ake yiwa dakarun sarki nawwar abin ya munana, saidai suma fa suna yiwa rundunar aljani fargam ɓarna musamman ma sarkin yaƙi farha wanda ya haukace idanunsa sun rufe ragar gazar maƙiya kawai yake ba aljani, ba dodo ko mutum duk wanda ya shigo gabanshi sunansa gawa domin lokaci ɗaya yake kai sara da duka da ƙafa da mangara da hannu, itama ɓangaren basadauki haka abin yake, sai kuma dakarunan guda shidda masu sanye da jajayen kaya wanda suke tsaron lafiyar sarki nawwar wanda tuni sun jima da saukowa ƙasa….. Ebook created by Shuraih Usman 99%

DOMIN CIGABA DA KARANTAWA SAI KU DANNA RUBUTUN KASANNAN 👇👇👇👇👇

[post_ads]

[post_ads]

ga duk wayanda suke samun matsala ta wurin downloading ebooks namu kuma suke da bukatar mu rubuta masu copy din littafin mu turo masu ta whatssap ko profile nasu
SAI KU TUNTUBI mamallakin shafin Shuraih Usman
Ta facebook profile nashi
Kota nambar waya 08140419490
Kota adireshin Email
shuraihusman@gmail.com
Sai de ku sani wa hakan zamu cajeku wasu kananan kudade
its Shuraih Usman 99%

Subscribe to our newsletter

Leave A Reply

Your email address will not be published.