BAKANDAMIYAR GUMURZU kashi na hudu 4

BAKANDAMIYAR GUMURZU
kashi na hudu 4
Na Umar Abdulhadi mati

Kadan daga ciki

[post_ads] Tungar da Basadaukiya taja a gaban sadauki salka shine yayi sanadiyyar tashin wata matashiyar ƙura tsayuwa tayi irin ta sadaukai mata hannunta na dama na riƙe da zabgegiyar takobi ta ɗorata akan kafaɗarta yayin da hannunta na hagu ke riƙe da faffadan madaidaicin ƙugunta ta zubawa sadauki salka daradaran fararen idanuwanta tana mai masa wani irin murmushi mai nuna tsantsar yadda dakai, haɗe da raina abokin gaba. Karon farko da ta buɗe baki ta fara magana cikin wata zazzaƙar murya sadauki salka baƙin dutse ko? To yau ko baƙin ƙarfe kake ni basadaukiya naci alwashin sai na ladabtar dakai ayaune watan jin kunyarka ya kama, ayau sai ka amshi hukunci na zaluntar ba’yin Allah da ƙwace musu dukiyoyi da kakeyi tabbas kai gagarabadau ne a wanan nahiya tunda ka gagari sarkuna, attajirai, matsafa, da sadaukai, ka maida dayawa daga cikinsu marayu wasu kayi sanadiyyar karyewar tattalin arziƙinsu dan haƙa ayau ni Basadaukiya sai na ɗaukar musu fansa saina sa zuƙatansu farin ciki saina sa ka zama abin dariya ga alummatai dake wanan nahiya saina… Tsawar da sadauki salka ya dakawa basadaukiya ce tasa ta dakata da maganar da takeyi, haƙiƙa sadauki salka ya gama fusata domin saboda tsananin fusata har wani baƙin hayaƙine ke fita daga hancinsa kamar ba ɗan adamba cikin wata kakkausar murya marar daɗin ji ya fara magana ke yarinya idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi sadauki salkan da kika sani a da bashiine ba a yanxu a gabanki azatonki bani bibiyar duk wani motsi naki, kina ”yar shekara goma yarana sun haɗu dake a dajin dake iyakar wanan ƙasa taku yayin da kika fita farauta kece mutum ta farko da kika mani ɓarnar da ba zan taɓa mantawa ba domin kin kashe mani ɗan’uwa yayin da kukayi arba har sukayi ƙoƙarin yi maki fashi tare da ƙoƙarin cire maki kyallen da kika rufe fuskarki tun daga nan na fara bibiyar alamuranki, bayan nan mun ƙara haɗuwa dake karo na biyu lokacin kina “yar shekara shabiyar a daji inda muka fafata ƙazamin yaƙi a tsakaninmu amma babu wanda yayi nasara daganan bamu ƙara haduwa ba sai yanzu da muka haɗu a filin wanan gasar kisani kamar yadda kikayi mummunan tanadi a kaina nima haka nai miki mummunan tanadi dan haka idan baki shirya ba ma ki shirya dan ga maza nan bisa kanki nan take sadauki salka ya zare wasu adduna guda biyu haɗe da kawarara wata uwar kururuwa wadda saida tasa “yan kallo suka rufe kunnuwansu batare da ɓata lokaciba ya fallo da zababbben gudu

DOMIN DOWNLOAD NA LITTAFIN SAI KU DANNA 👇👇👇👇👇👇👇👇

[post_ads]

[post_ads]

Subscribe to our newsletter

Leave A Reply

Your email address will not be published.