TSOHON ALKAWARI complet

 TSOHON ALKAWARI complet
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 09 Apr, 2019
Upload Time 11:00 pm
Hits 2179 Hits
Comment No Comments

Description

TSOHON ALKAWARI NAZIR ADAM SALIH Ebook creator:- Shuraih Usman Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521 Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha’Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha’ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya Hakkin mallaka (m) Nazir Adam Salih TSOHON ALKAWARI 1 . Nazir Adam Salih (Nas) . A ranar ashirin da takwas ga watan Afrilu na shekarar Milladiyya ta dubu biyu da guda hudu wacce ta yi daidai da ranar Laraba na tashi a rude, kwakwalwata a cunkushe domin sama ko kasa na nemi sabuwar basirar da zan yi rubutu na rasa. Tun misalin karfe goma nake zaune na sa littafin a gaba ina kallo har zuwa karfe goma sha biyu na rana kwakwalwata ba ta zo min da komai ba sai tunane- tunane marasa amfani. Ina nan dai zaune cikin akurkin dakina ni kadai da biro a hannu sai jujjuyashi nake yi kamar sigari daga karshe dai na tabbata ta kare min dan haka sai na ajiye biron na mike tsaye gami da mika kuma cikin damuwa. “Me ke damuna ne?” Na tambayi kaina ko da idanuna suka kai ga shafin littafi na ga ko alif ban rubuta ba sai na yiwa kaina murmushi, maganar makaranta littattafaina ta fado min sa’ar da suke cewa wai ta qare min, lokacin da na kasa fito musu da cigaban ALJANI YA TAKA WUTA da kuma BINDIGAR KWALI NA BIYU lallai ga dukkan alamu suma da gaskiyarsu tabbas ta kare min tunda dai gashi na sa littafi a gaba na kasa rubuta komai tsawon sa’o’i biyu. . Na gama hakura, na fito kofar gida kenan sai na hango wata yarinya dauke da fanteka da kwanuka a samanta abin tsautsayi ta zo tsallaka kwata kenan sai kafarta ta zame, fantekar a cike take da danwake, wannan shi ne ya yi sanadiyyar barkowar wani zazzafan gumi a kan goshina, zuciyata ta fara harbawa, sakamakon abin da na tuna, tabbas na san inda zan je na samo labari. Na sake duban dunkule-dunkulen dan wake burjuk a kasa sai ta tuno min da TUBANI ina tuno da tubani sai na tuno da dattijo SIDI MAI JAKA A cikin sauri na nufi gidan wata kakata, na yi sa’a kuwa na sameta a gida. Bayan mun gaisa sai na ce da ita. “Tubani nake son ki yi min.” Ta dubeni cikin dariya ta ce “Ka ci gidanku ja’iri dan nema, kai a zamaninku ana yin tubani ne? Sai dai jefi-jefi.” Na dubeta gami da sa alamun nutsuwa a fuskata na ce. “Dan Allah ki yi min wallahi da gaske na ke yi, fada min duk abubuwan da za a saya sai na baki kudin…” . Bata sami damar suturta tubanin nan ba sai bayan karfe biyu. Bayan na gama sallar Azuhur sai na ga ta bade tubanin da yaji sosai, domin na riga na san Sidi Mai Jaka zai yi matukar farin ciki da hakan, na sa ta dada kwarara masa mai, sannan aka zuba min shi a cikin kwano. Karfe biyu da kwata na isa gidan Sidi Mai Jaka dake bakin kasuwa. Abin da ya fi damuna shi ne tun sa’ar da muka rabu da shi shekara biyu da suka wuce ban kara zuwa wurinsa ba. . Ina isa kofar gidan sai na leka zauren cikin doki, gabana na ta faduwa domin kada na yi zuwan banza ko baya nan. Ga mamakina Sidi Mai Jaka na nan zaune akan kujerar katakonsa, carbi a hannunsa, haka nan akwai lofe a gefensa a ajiye bisa wani farin buzu. Sidi Mai Jaka ya dago kai muka yi ido biyu, ko dakika biyu ba a yi ba ya shaida ni. . “A’aha, yaushe a gari inji ma ki bako Nas, ashe daman kuna duniya?” Na dubeshi da dariya. “Baba Sidi kuma tsofaffi ba ku bar duniya ba ballantana mu.” Sidi Mai jaka ya fashe da wata shakakkiyar dariya. Na dubi Sidi Mai jaka kallon tsaf, kana idanuna suka yo nazarin zauren. Ko kusa ko alama babu wani canji a kamannin Sidi Mai jaka ko kuma zauren gidan. Wani abin dadin mamaki kuma shi ne, tsohuwar rigar nan dake jikinsa mai kamar rariya, ita ce dai har yanzu bai sake wata ba, na yi mamakin karfin hali irin na wannan rigar, domin sa’ar da na fara ganinta shekaru biyu da suka wuce ban taba tsammanin zata sake wata guda a duniya ba ta fatattake ba. Har yanzu katon farin tabaron nan nasa na nan daraf akan hancinsa. . Jikinsa kuwa sa’ar da na dubeshi sai na fara tunanin me yiwuwa tun bayan rabuwata dashi a shekara biyu wankansa bai fi sau uku ba, me yiwuwa ma sai dai ko alwala. Amma fa duk da wannan al’amari na Sidi Mai jaka ina matukar girmamashi. Shekaru biyu da suka wuce, wannan tsoho Sidi mai jaka dogo fari yankwanannen tsoho, kansa fari fat, da furfura, farin gemu da fuska ma’abociyar fadin goshi ya taba bani labarin wata malamar asibiti TANI da wasu yan fashi. . Sidi mai jaka ya dubi kwanon dake hannuna cikin farin ciki yace. “Ko shakka ba na yi wannan alkawarina ne na TUBANI ko?” Na ajiye kwanon a gabansa lokaci guda kuma na matsar da lofen dake kan farin buzun na zauna na dubeshi cikin murmushi. “Tabbas ka canka tubaninka ne.” . Fuskar Sidi Mai jaka ta washe, cikin nutsuwa ya mika hannu ya dauko wata butar roba, ya guntsi ruwa a bakinsa ya kuskure bakinsa ya fesar a jikin bango. Kana ya janyo kwanon tubanin nan ya bude ya fara kallonsa cikin nutsuwa. “Nas, ina me yi maka albishir da cewa wannan kyauta ta tubani da ka kawo mini tamkar wani dan mukullin labari ne da na dade ina son na baka to sai dai kuma shekaru biyu kenan yau rabonka da nan sai yau Allah a kawoka.” “Haka ne.” Na ce dashi, sannan na dada gyara zama domin na san sabon labari ya riga ya zo…Shekaru biyu kenan yau rabonka da nan sai yau Allah a kawoka.” “Haka ne.” Na ce dashi, sannan na dada gyara zama domin na san sabon labari ya riga ya zo…. Sidi Mai jaka ya birkita manya- manyan tubanin, sannan ya dauki tsinke, ya tsiraki wani kato ya tura a baki, nan da nan idanunsa suka fara zubar da hawaye saboda yaji.Ko wace ce ta yi ma tubanin nan, ba karamin kwarewa ta yi ba Nas.” Sidi mai jaka ya ce dani. Na gyada kai. Sidi mai jaka ya cire farin tabaron dake idanunsa ya sa hannun rigarsa ya goge idanunsa sannan ya dubeni ya ce.”Nas kune samari yanzu idan aka ce ka yi auren jari za ka yi?” Na dubeshi cikin mamaki na girgiza kai na ce.”Ya danganta da irin macen…koda yake dai ni a gaskiya baya bani sha’awa, ni na fi son auren da muke kaunar juna don Allah.” Sidi mai jaka ya dubeni ya kyalkyale da dariya ya ce.Abin da Anas mijin Mabaruka gurguwa kenan ya kasa fahimta.” Na dubeshi a karo na biyu “Wa yekuma Anas mijin Mabaruka gurguwa?” Sidi mai jaka ya tsikari katon tubani ya jefa a bakinsa.”Shi ne labarin da nake son na baka Nas ban saniba ko kana da sha’awar irin wadannan labarai na irin wadannan mata masu matukar son kansu a duniya fiye da kowa?” Na yi shiru na dan lokaci ina juya, abin da ya ce cikin zuciyata. A gaskiya ni a son zuciyata na fi son a bani labarin yan ta’adda irin wanda ya bani shekaru biyu da suka wuce, to amma da yake ni yanzu ta riga ta kare min dole ne na saurari komai domin bani da zabi. Wa ya sani ma ko wannan ma ya fi wancan labarin dadi.”Zan so kuwa na ji labarin wannan gurguwa, wace ce ita'” Na tambayeshi, Sidi mai jaka ya yi dariya ce.”Bi ni a hankali Nas dadina da kai gaggawa sannu a hankali zan fara saka ma zararrukan labarin ina kulla maka su kamar yanda gizo-gizo ke sakar gidansa” Sidi mai jaka ya dan yi shiru sannan ya ci gaba.”Ita wannan gurguwa mai suna Mabaruka ba a taba samun wata mace a zamanin ta mai arzikinta ba, miloniya ce a fagen kudi, to sai dai kuma wani ragin jin dadi da ta samu shi ne gurguwa aka haife ta” Sidi mai jaka ya juyo ya dubeni.”Nas, domin ka fahimci zaren labarin nan da kyau, dole ne na ajiyar zaren labarin gurguwa mabaruka, na koma na dauko ma hoton Anas” Na dago kai a kagauce na kalle shi.”Ka ce kuma da labarin gurguwa za ka ba ni.” Sidi Mai jaka ya gyara tabaronsa kana ya tsikari tubani guda ya jefa a bakin salatinsa.”Dole ne mu fara da zaren labarin Anas, in kuwaba haka ba Nas, ba za ka taba fahimtar labarin nan ba” Na gyada kai cikin fahimta.”Yauwa Nas, ina son ka dauki zuciyarka ka mayarda ita cikin wata mashahuriyar otal.” Na dubi Sidi mai jaka cikin kaguwa na ce dashi “Na mayar””Yauwa” Ya ce dani sannan ya fara.**** “To Nas ga Anas nan a cikin dakin karbar baki na otal din yana zagayawa cikin farin ciki da annashuwa domin aljihunsa a cike yake da albashinsa na wannan watan”Sidi mai jaka ya yi yar atishawa sannan ya ce.”Kafin na ci gaba bari na baka hoton Anas. Ka ga Nas Anas dogo ne wankan tarwada mai kyawun fuska na ban mamaki. Domin an ce ba mata kawai ba hatta maza idan Anas ya zo wucewa sai sun kalleshi sun yaba da halittar Ubangiji. Wani karin abin burgewa kuma gareshi shi ne duk irinsuturar da ya sa sai ta karbeshi cif-cif kamar daman da ita aka haifeshi. Wannan da kuma iya zancensa da tarairaya shi ya sa dimbin mata suke kaunar Anas kamar su hadiyeshi. Wani abu da zai baka mamaki Nas, shi ne Anan ba wai yan mata bane kawai ke son sa, hatta dattijan mata ma suna kaunarsa sau da yawa masu budurwar zuciya daga cikinsu kan yi kokarin su kaiwa Anas cafka musamman ma dattijan zawarawa attajirai. Wani sa’in Anas ya kan kula su ba don komai ba kuwa sai don dan abin hasafin da sukan bashi.Daya daga cikin abin da Anas ya fi kauna a rayuwarsa shi ne hira da kyawawan mata, sau dayawa Anas ya kan tsinewa talauci sau daruruwa cikin zuciyarsa, domin a cewarsa shi ne ya shiga tsakaninsa da kyawawan mata masu aji. Duk da yake dai kyawunsa kan janyo ra’ayin kyawawan mata, to amma Anas bai taba gamsuwa ba domin shi ya riga ya sani, akwai irin kyawawan matan da kyawunsa bai isa ya janyo su ba. Wannan ita ta sa Anas ya yi kurda-kurda ya sami aiki a Lagwada Hotel. Duk da yake dai shi ba kowan kowa bane a otal din domin aikinsa ya fi karfi a rabon abinci, wani sa’in kuma ya kan nunawa baki dakunansu su ta hanyar daukar dakon yan jakunkunansu, to amma wannan bata dami Anas ba domin shi burinsa ya cika. Dan wannan ita ce hanya daya jal da zai yi ta ganin kyawawan mata iri-iri, yanda yake so duk kuwa da cewa bashi da ko kwabo. Babban abin farin cikin Anas shi ne ya ga ana liyafa a otal din, musamman ma ta bakin aure, domin tana bashi damar gani kyawawan mata wani sa’in ma har yazanta da su. Anas yana daya daga cikin irin samarin nan marasa zuciyar nema, wadanda harkullum kwanan duniya burinsu su ci BULUS ba tare da sun sha wahala ba. Dan haka.Wadanda harkullum kwanan duniya burinsu su ci bulus ba tare da sun sha wahala ba. . Dan haka Naira dubu takwas din da ake biyan Anas a wata sun isa su sashi farin ciki, tun da dai ba zai iya kokarin samun abin da ya fi haka ba.Anan, sai Sidi mai jaka ya yi shiru ya dago kai ya dube ni.”Nas, ina fatan kana fahimtar hoton Anas da nake ta kokarin zana ma” Na gyada kai na ce.”Ina fahimta” Sidi mai jaka ya gyara zama sannansai ya ce.”Bari to in koma da kai can baya kadan inda nake cewa Anas yana zagaya wa a otal din cikin farin ciki, lokaci- lokaci ya kan shafi aljihunsa a fakaice domin baya son mutane su fahimci cewar dan albashin Naira dubu takwas din aljihunsa yake tabawa. Haka nan shi kuma bashi da imanin da zai iya jurewa daidai da minti gudabai taba aljihunsa ba domin ji yake yi kamar kudin za su zube.Anas ya ci gaba da zagaya wa a dakin karbar bakina otal din ya gaisa da wancan ya yiwa wannan wasa har dai ya kawo daidai kan kanta inda Balaraba mai bada dan mukullan dakuna ke zaune. Anas ya matsa kusa da kantar ya dora hannunsa sannan ya dubi Balaraba da kyakkyawar fuskarsa ya hasketa da murmushi fararen hakoransa suka fito fili.”Hajiya Balaraba ya ya garin ne?”Balaraba ta dubeshi da murmushi sannan ta turo biron dake hannunta cikin kunne ta fara juya shi, tana kanne ido.”Lafiya lau Anas. Har ka tashi ne?”Anas ya dubi agogo sannan ya dube ta.”Da saura dai Balaraba.” ya dan yi shiru sannan sai ya ce.”Balaraba ba ki ga motsin Halima ba ne?” Balaraba ta girgiza kai.”Ban ganta ba, rabona da ita tun jiya da yamma kamar ya yanzu da ta zo neman ka.” Balaraba ta ci gaba da susa da biron cikin kunnenta.”Anas, wai don Allah yaushe za ka daina yaudarar yayan mutane ne?” Anas ya dubeta da murmushi ya ce.”Sai kin shirya Balaraba.” Balaraba ta harareshi.”Me kake nufi da sai na shirya?”Anas ya shafi kyakkyawar fuskarsa.”In har kin yarda za ki aure ni, me zai sa na ci gaba da yaudara? Daman ke ce ai ki ka ki da tuntuni kin amince dani da tuni na yi aure na huta.” Balaraba ta kyalkyale da dariya.”Oh! Anas Allah ya rufa asiri wallahi wadda bata san ka ba ka cuce ta.” Ta dan yi shiru ta sunkuyarda kai.Balaraba bazawara ce, sau uku tana aure tana fitowa. Da yake tana da sakamakon diflomarta a hannu kuma basira ta bace mata maimakon ta yizamanta a dakin miji sai ta nemi aiki a otal, a lokacin watanta takwas kenan da fara aiki. Tun sa’ar da ta fara dora idanu akan Anas ta ji duk duniya babu wanda take kauna sai shi. Balaraba kyakkyawa ce daidai misali, to sai dai kuma bata cikin irin tsarin matan da Anas ke so, domin a cewar Anas duk macen da ta fiye gajarta bata cika kyakkyawa ba ko da kuwa tana da kyawun fuska. Balaraba ta so ta cusa kanta a wurin Anas,to amma irin jeri-jerin matan da kan zo neman Anas tun daga cikin gari har otal din, shi ya gargadi Balaraba ta hadiye maitarta ta yi shiru. To sai gashi kuma yanzu Anas da kansa yana zolayarta da zancen soyayya. Duk da yake Balaraba ta tabbata karya yake sai da kalaman nasa ya faranta mata rai.”Balaraba.” Anas ya kira sunanta. Balaraba ta juyo frgigit.”Tunani n me ki ke yi?” Balaraba ta dago kai ta dubeshi na dan tsawon lokaci sannan sai ta ce.”Kana da labarin kayatacciyar liyafar da za a yi yau a otal din nan?” Anas ya dubeta cikin mamaki.”Tun jiya na sami labari a wurin Sabi’u amma ni bai ce dani ta hadu ba.” Balaraba ta dube shi.”Ai kuwa tun…” Kalamanta suka makale a fatar bakinta ba ta karasa ba. Anas ya dubeta cikin mamaki sai ya ga bashi take kallo ba bayansa take kallo. Can wajen kofar shigowa. Anas ya yi mamaki domin duk kusan lokaci guda jama’ar dake cikin dakin tarbar bakin suna surutai suka yi shiru na dan lokaci. Anas ya juyo sosai domin ya ga abin da ke faruwa. A daidai lokacin ne to ya hangesu.Wasu kyawawan mata ne suka shigo kowaccen suta ci kwalliya ta gani ta fada. Anas ya ji yawun bakinsa ya kafe, sannan sai ya lura daya daga cikin yan matan tana tura kujerar guragu ta farinkarfe akan kujerar a zaune sanye da kayan alfarma masu tsadar gaske, wata budurwa ce gurguwa, za ta yi kimanin shekaru ashirin da bakwai.Koda Anas ya ci gaba da kallon gurguwar da yan matan ke turawa, sai ya yi ajiyar zuciya.”Kai amma fa an yi asarar kayan kwalliya.” Balaraba ta dubeshi da dan murmushi ta ce.”Me ya sa ka ce haka?” Anas ya dan yi shiru sannan ya dada waigawa a karo na biyu ya kalli gurguwar, sannan ya juya ga Balaraba.”Kin san ni ban cika shiri da munanan mata ba.Dube ta fa gurguwa mummuna amma kayan jikinta sun fi na kowa tsada, ai dole in ce an yi asarar kayan kwalliya.” Balaraba ta fashe da dariya.”Kai dai Anas wallahi ba ka da kaico, me ya sa kake son muzanta munana? Suma fa Allah ne ya haliccesu kamar yadda ya halicceka kyakkyawa kuma idan ya so yana iya sa wa ka aure ta…Me ya sa kake son muzanta munana? Suma fa Allah ne ya haliccesu kamar yadda ya halicceka kyakkyawa, kuma idan ya so yana iya sa wa KA AURE TA.” Anasya harare ta.”Allah sawwake, kin ga Balaraba ni fa bana son mugun fata, tun da abin na ki haka ne ma ni kin ga tafiya ta.” Anas ya juya cikin sauri ya nufi cikin otal din a daidai lokacin ne to ya hango Sabi’u cikin sauri ya matsa gareshi.”Sabi’u ka ga wata mummuna da alamun kudi.” Sabi’u ya dubi Anas ido da ido, akwai wani yanayi a irin kallon da yake yi da ya sa Anas ya jigwiwarsa ta yi sanyi.”Ya ya na ga kana yi min wani kallon uku ahu?” Sabi’u dan lukuti, gajere ma’aboin son sa kayan turawa duk kuwa da cewa ba wani kyau suke yi masa ba, ya gyara tsayuwa sannan ya dubi Anas “Ka san inda kake wage bakinka, in kuwa ba hakaba wata ran za ka kwana a ciki. Shin ka san waccan gurguwa ko wace ce kuwa?” Anas ya girgiza kai ya ce.”Fahimtar dani.” Sabi’u ya gyara wandonsa wanda ke kokarin sullubewa ya fado.”Ni na san ba ka santa ba shi yasa kake kokarin muzantata. To bari in fada ma, ka ga duk munin nan nata, wallahi ba muni bane a gurina, kuma ka ga dai gurguwa ce to ni a gurina kafafunta sunfi naka sau dubu amfani.” Sabi’u ya dan yi shiru sannan sai ya dago hannunsa ya dan daki kirjin Anas ya ce.”Wannan gurguwa da kake gani ita ce Mabaruka S. Faruk, daya daga cikin matan da suka fi kowacce arziki a matan Afirka.” Sabi’u ya ya balligoro ya jefa a bakinsa sannan ya dubi kyakkyawar fuskar Anas da murmushi.”Na san ka sha jin labarinta, me yiyuwa a zahiri ma baka taba ganinta ba, to yau gata a otal din ka, bikin cika shekarunta ashirin da takwas a duniya za a yi. Mu kanmu nan otal din ba karamar sa’a muka yi ba, domin da liyafar a Landan za a yi sai Mabaruka ta ce ba za ta iya doguwar tafiya a cikin jirgi ba domin wai juwa kedamunta wannan shi ya sa su zuwa nan, ina fatan ka fahimce ni? Dan haka Anas ina son ka yishiru da bakinka domin otal din nan ta yi muguwar cin riba da liyafar nan da za a yi, idan ka sake manaja ya ji kalamanka akan Mabaruka, na rantse ma har da gemun tsohona ba za ka sake awa guda a gidan nan ba za a sallame ka daga aiki.” Anas fuska na tsiyayar da gumi ya dubi Sabi’u a tsorace. Ya mari bakinsa da hannu”Shegen baki yau ya kusan ya janyo min tsiya.” Sabi’u ya fashe da dariya ya ce.”Zo mu je mu fara shirye- shiryen abubuwan da za su bukata, ka san fa muke da alhakin kula dasu.” Sabi’u ya juya cikin sauri Anas ya bi shi a baya da sassarfa kamar doki. A zuciyarsa yana tunani, Mabaruka! Cab! Ai kuwa ya sha jin labarinta ba tun yau ba. Wani abokinsa ya taba cewa dashi. “Anas duk matan kasar nan babu mai arzikin Mabaruka gurguwa, kai bar ma ta kasar nan duk Afirka sai an tona. To amma a tsammanin Anas da ya ji an ce tafi kowacce mace kudi a Afirka ya dauka zai ganta wata kyakkyawa ajin farko, irin matan nan masu shekia fuska kamar madubi irin wadanda duk tsananin duhun dare sai kaga surar fuskarsu saboda tsabar kyau. Abin da Anas ya gani ya sashi kaduwa musamman ma yanzu da aka ce dashi wannan yankwananniyar matar mai tababben hanci kamar begila ita ce Mabaruka gurguwa uwar kudi! Allah mai yadda ya so. Anas ya ce cikin zuciyarsa.Tun karfe biyar na yamma aka fara liyafar farfajiyar otal din babu masaka tsinke duk inda ka duba motoci ne manya-manya masu bawo. Da yawa daga cikin bakin basu sami damar shigowa da motocinsu ba saboda cunkuso.Anas da sauran ma’aikatan dake bangaren girke- girke suka yi ta rabon kayan lashe-lashe da makulashe. Dakin da ake liyafar tangamemen gaske ne, wanda aka gina shi da zummar ya dauki mutum dari uku ba tare da wani ya shaki numafshin dan uwansa ba, Anas ya fara waige-waige yana kokarin ya karewa Mabaruka kallo.Ya ce gaba da zagaya wa lokaci guda kuma cikin jama,a yana yin abin da ya kamata sai dai kuma akwai wani abu da ke damun Anas sa’ar da ya kawo kusa da inda su Mabaruka suke zaune da manyan kawayenta. Jikinsa na bashi cewa kamar kallonsa ake yi a baya. Wannan ita ta sa Anas juyawa a wayance ya dubi bayansa. Gabansa ya fadi ras! Sa’ar da suka hada idanu da Mabaruka, ko shakka ba ya yi shi take kallo, haka nan har da murmushi a fatar bakinta. Anas ya ji bugun zuciyarsa ya karu lokacin da yaga kamar mabaruka ta daga hannu ta yafato shi. Anas ya shiga cikin rudani domin yana fargabar kada ya je wurin kuma ya kasance ba shi take kira ba.Anas ya waiga bayansa domin ya ga koda wani take sannan ya sake juyowa, sai ya ga ta sake yafuto shi da hannunta. Cikin rawar jiki ya nufi inda take zaune tare da sauran kyawawan matannan. Anas ya ji duk gwiwarsa ta yi rauni kamar ba za ta iya daukarsa ba domin kyawun matan da suka kura masa idanu ya yi yawa, ko kusa ko alama basu yi kama da irin yan matan da yake mu’amala da su a baya ba.Anas ya ratsa a hankali ta tsakanin kyawawan tebura ya karasa gaban Mabaruka. Yana zuwa saiya rankwafa a gabanta ya ce.”Gani ranki ya dade ko bani ki ke kira ba?” Mabaruka ta dubeshi da mummunar fuskarta ta saki wani abu da take tsammanin wai tattausan murmushi ne.”Kai nake kira mana” Ta dan yi shiru, sannan ta ci gaba.”Daman so nake na fada ma don Allah ku yi sauri ku gama shirye-shiryen mana, ka ga kamata ya yi ace tun da wurwuri kun gama komai kafin mu zo” Anas bai iya dago kai ya kallisauran yan matan da ke bayanta ba, to amma yatabbata duk kallonsa suke.”To ranki ya dade” Anas ya amsa. Ya yi kamar yamike tsaye ya koma kan aikinsa to amma sai ya ga alamun bata gama bayaninta ba. Mabaruka tadubeshi ido da ido, kana sai ta yi kasa-kasa da muryarta ta ce dashi.”Ka bar aikin haka nan ka tafi ka gyara jikinka sosai, ka jirani a waje idan an tashi ina son ganinka. “Kasa-kasa da murya, Ehemm.. Anas ya dubeta cikin mamaki, lokaci guda kuma ya godewa hayaniyar al’ummar dake wurin liyafar domin ya tabbata hatta kyawawan matan dake jere a bayanta ma ba su ji abin da ta ce dashi ba ballantana sauran jama’a. Shi kansa yasan ba dan yana kallon motsin fatar bakinta ba da ba zai taba fahimtar abin da ta ce ba. To amma duk da haka yana shakkar abin da ta ce dashi. Dan haka sai ya ya dubeta a rude ya ce. “Ban fahimce ki ba ranki ya dade?” Mabaruka ta yi masa murmushi ta maimaita. “Ka je ka sake kayan dake jikinka ka kuma jirani a waje, idan an tashi zan turo a yi min kiranka ina son magana da kai.” Kusan awa daya da rabi ya shafe zaune karkashin wata dukurkusar bishiya mai kama da ta dabino dake farfajiyar otal din yana jiran tsammani zuciyarsa cike da tambayoyi sama da guda dari. Amma manya-manyan tambayoyin da suka fi damun zuciyarsa sune; shin mene ne dalilin ganawa dashi? Shin laifi ya yi mata? To ai kuwa har murmushi take yi masa sa’ar da take bayanin. To mene ne dalilin da zai sa ta ce ya sake kayan dake jikinsa? Babu mamaki ji ta yi kamar jikina yana wari. Anas ya ce da kansa. Duk da yake dai sa’ar da ya baro wurin liyafar sai da ya yi ta shinshina jikinsa domin ya ji ko wari yake yi, to amma har zuwa wannan lokacin da yake sake kayan dake jikin nasa Anas bai gamsu ba, lokaci- lokaci sai ya sunsuna hannun rigarsa kana ya duba agogon. Sa’a daya da rabi kenan yana zaune a gurin yana jira. Tab! Anas ya yamutse fuska cikin damuwa. A karo na farko a rayuwarsa ta harkar mata sai ya ji ya fadi babu nauyi domin a tarihinsa wata mace bata taba sashi ya yi jiranta daidai da na mintuna biyar ba, sai dai ita ta jirashi. Amma sai gashi yau tarihin ya sauya, wai Anas da kansa ne yake zaman jiran wata nannadaddiyar gurguwa mummuna mai dogon hanci da fadi kamar nakiya, lallai duniya juyi-juyi! Wannan tunani shi ya sa Anas ya saki wani tattausan murmushi a cikin duhun daren da ya fara shigowa sannan ya dada jingina bayansa a jikin bishiyar da yake zaune, ya share gumi daga goshinsa a zuciyarsa ya ce. “Kada ka damu Anas, a da can kyawawan mata sun yi jiranka, a yanzu kuwa kai ne kake jiran mummuna da kudi, ko ba komai dai ba talaka kake jira ba. Abin ya kan baiwa Anas mamaki, wata sa’ar ma har dariya idan ya tuna da cewa wai daya daga cikin matan da ta fi kowace kudi a Afirka yake jira! Anas na nan a zaune yana ta sake-sake bai ji zuwanta ba sai muryarta ya ji a bayansa ta ce. “Ka zo wai tana kira”. Anas ya juya firgigit domin ganin mai zazzakar muryar. Daya daga cikin kyawawan matan nan ce ke tsaye a kansa. Da yake ita kadai ce a wurin sai Anas ya sami damar kare mata Kallo sosai. Budurwar dake tsaye a kansa doguwa ce fara, kyakkyawar gaske mai hasken fata. Budurwar za ta yi kimanin shekaru goma sha takwas, ko sha tara me yiyuwa ma ashirin, abu ne mai wuya ka iya fadin shekarunta kai tsaye, domin kyawun fuskarta ma’abociyar annuri da kwarjini sun isa su sa duk wani mai iya hasashen shekaru cikin rudani. Budurwar tana da manyan idanu farare tas! Wadanda duhun dare bai hana Anas ganin fararen idanun ba, wani abu da ya so tsayarwa Anas numfashi shi ne kundukukinta mai annuri gami da shafaffiyar mararta wacce ta bayyana a fili sakamakon tsukakken dinkin bakar shaddar dake jikinta. Kafarta fara sol gwanin sha’awa cikin bakin takalmi. Anas a zuciyarsa ya ce da za a barshi ko da daidai da na dakika guda ne ya sumbaci kafarta da babu abin da zai hana shi ya bada albashinsa na wata guda. . “Tana ina?” Anas ya tambaya cikin karfin hali zuciyarsa na harbawa, lokaci guda kuma ya mike tsaye. “Zo mu je na kai ka inda take.” Budurwar ta ce dashi. Babu alamun bakin ko farin ciki a fuskarta. Budurwar ta juya tana rausaya. Anas ya bi ta a baya kamar tunkiya. Sannu a hankali suna tafe har ta kawo shi filin da ake fakin da motoci na ota din. Anas ya godewa Allah, domin har suka isa wurin bai hadu da ko ma’aikacin otal din kwaya daya ba, domin sun dade da yi masa muguwar lambar yawan mu’amala da mata. To amma duk da haka sai da Anas ya raya a zuciyarsa cewa inama su hadu da Sabi’u, domin abin alfahari ne ya ganshi da wannan zukekiyar. Sa’ar da suka kawo farfajiyar sai Anas ya lura duk kusan tarin motocin nan sun baje, sauran da suka rage basu fi guda ashirin ba kawai. Anas na bin dudurwar a baya har ta zo dashi jikin wata mota katuwar (Jeep) Shudiya. Tun kafin su karasa kofar motar ta bude sannan sai muryar Mabaruka ta ratsa kunnensa. “Sannu da zuwa lallai ka cika alkawarinan mabaruka ce zaune a bayan motar ita kadai, sannan a gidan gaba akwai direba wani dogo ne, fari bafulatani. Mabaruka ta dubi kyakkyawar budurwar ta ce. “Na gode Ummi, sai goben kenan idan kin zo. Budurwar ta yi murmushi a karo na farko ta dubi Mabaruka ta ce. “To Mabaruka, Allah maimaita mana, sai da safen, bari in yi sauri ga su fati can a mota suna jirana.” Sannan ga mamakin Anas sai ta juya gare shi ta haske shi da murmushi ta ce. “Malam sai da safe.” Ta juya cikin sauri ta bar wurin. Anas ya bi ta da kallo, a zuciyarsa yana cewa kai lallai kudi ma dai wallahi banzaye ne domin basu san inda ya kamata su je ba. Koda ya kwatanta kyawun Mabaruka Miloniya da budurwar, sai ya ga tamkar ka kwatanta alli da bakin gawayi ne. “Ga shi har dare ya fara yi.” Muryar Mabaruka ta katsewa Anas tunaninsa. Anas ya juya firgigit sannan ya saki wani fatalwar murmushi ya ce. “Ranki ya dade gani.” Mubaruka ta kura masa idanu na tsawon lokaci, akwai murmushi a fuskarta. “Da za ka kirani da sunana Mabaruka ina gani zai fi” Anas ya dan rankwafa cikin girmamawa to amma ba ita yake girmamawa ba, miliyoyin kudin da ya ji labarin ta mallaka yake girmamawa. “To ranki…Mabaruk a.” Mabaruka ta fashe da yar dariya. “Ka kuwa iya fadar sunan” Anas ya ji wani daddadan kamshi sai hurowa yake daga cikin motar. A iya tsawon lokacin da ya yi yana aiki a otal din ya sha jin kamshi iri-iri daga jikin yan birni da masu hannu da shuni da yan kwalisa masu kunan bakin wake da yan kuru, amma a duk cikin su bai taba jin kamshin da ya kai koda rabin wanda ke hurowa daga motar Mabaruka ba. “Idan ba za ka damu ba, ba zan kuma takura maka ba, zan so ka shigo motar nan mu tafi tare da kai.” Mabaruka ta ce da Anas tana duban fuskarsa. Anas ya dubeta cikin tsananin kaduwa ya ce baki na rawa. “Mu tafi…ina?” Mabaruka ta dubeshi da murmushi. “Gidana nake son mu tafi tare da kai domin akwai maganganun da nake son mu tattauna da kai masu muhimmanci” Anas ya dubi nannadadun kafafunta kana ya dago kai ya ce. “Har yanzu ban fahimce ki ba” Mabaruka ta yi ajiyar zuciya ta ce. “Duk abin da zan fada ma anan ba zai gamsar da kai ba, shi yasa nake so na tafi gidana da kai inda zamu samu damar tattaunawa sosai” Ta dan yi shiru tana nazarin fuskarsa ganin cewa har yanzu a rude yake sai ta ce. “In kuma har yanzu ba ka gamsu ba bari in fito fili in fada ma abin da zamu tattauna. So nake na saye ka!” Anas ya ji gabansa ya fadi ya dubi Mabaruka a rude. Mabaruka ta dubi Anas ta fashe da dariya ta ce “Me ye na ga ka hada fuska kana jin ba zan iya sayen naka bane?” Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya dubeni “Nas wannan shi ne karshen wannan dogon zaren labarin” Na dubeshi cikin kaguwa “Haba Baba ya ya sai da labarin ya dauko dadi za ka katse ni anan?” Sidi mai jaka ya tsikari katon tubani daya ya jefa a baki kana ya dube ni ya ce. “Nas kenan, har kullum ba ka fahimtata in ban da abin ka ai sauran zararrukan labarin da ke gaba sun fi wannan ma dadi nesa ba kusa ba. Ka yi min afuwa Nas zan koma da kai can baya shekaru ashirin da takwas da suka wuce kada ka damu sannu a hankali zan dawo da kai kan tsohon zaren labarin da na gama yanzun nan na hada maka bakinsu in kulle guri guda” Na gyara zama sannan na ce dashi. “To Baba Sidi, ina sauraronka” Abin da yake bani mamaki ga lamarin Sidi mai jaka shi ne irin yadda yake bada labarin ko sarkewa ba yayi. . SIDI MAI JAKA ya dubi kwanon tubanin dake gabansa ya dubeni cikin murmushi, sannan sai ya tura tsinke ya tsikari wani dankareren tubani ya tura a baki. “Nas duk duniya babu abin da na fi so kamar tubani” “Haka ne” Na ce dashi. Sidi mai jaka ya dubeni. “Me yiwuwa ka yi mamakin irin yadda nake ta zubo maka labari bana ko tsayawa” Na gyada kai. “Kwarai kuwa” Na ce dashi “Domin a wancan karon da na zo duk kusan mintuna goma sai ka tsaya” Sidi mai jaka ya fashe da dariya. Sannan ya sunkuyar da kai ya ce. TSOHON ALKAWARIN da ka cika min ne ya sa nake ta kwararo labarin nan ba wakafi balle aya” Na dubeshi cikin mamaki. “Wane tsohon alkawari kuma?” Sidi Mai jaka ya dubi kwanon dake gabansa ya ce. “Tubanin da ka yi min alkawari shekaru biyu da suka wuce shi nake nufi da tsohon alkawari. Domin ba duka mutum bane a wannan zamanin kan iya cika alkawari” Sidi mai jaka ya dan yi shiru sannan sai ya dubeni ya ce. “Nas, ina son ka dauki zuciyarka cancak ka mayar da ita shekaru ashirin da takwas da suka wuce a lokacin ma ba a haifi Mabaruka ba” Na dago da kai cikin kaduwa. “Shekaru ashirin da takwas?” Sidi mai jaka ya gyada kai. “Kwarai kuwa, domin shi ne zaren labarin mu na biyu.” Ya dan yi shiru kana ya tsikari tubani ya jefa baki sannan ya dubeni. “Nas, shekaru ashirin da takwas da suka wuce, wasu ma’aurata guda biyu wadanda ke cikin tsananin shauki na kaunar junansu sun kasance zaune a wani fankadeden falo na alfarma wanda a takure zai iya cin mutune sittin ba tare da wani ya shaki numfashin dan uwansa ba. A zaune a daya daga cikin kujerun wani mutum ne dogo, baki, sanye da farar riga suwaita da shudin wanda na shadda, kansa babu hula, hakan shi ya bayyana matashin sankonsa a fili, da yawa daga cikin wadanda suka sanshi a lokacin, sun riga sun yi imani da cewa mutumin ba zai dade da gashi a kansa ba, domin gashi dai a lokacin bai fi shekara talatin da biyar ba a duniya, amma dogon sankon ya gama cinye rabin gashin kansa. Wannan dogon sanko dake kan mutumin bai hana matarsa Aliya mutuwar kaunarsa ba, duk kuwa da cewa a lokacin ma tana da cikin dan wata takwas Wannan mutum mai dogon sankon sunansa A. Faruk. Ba karamin mutum bane, domin a fagen kudi biloniya ne, mamallakin kamfanoni ashirin da takwas a nan kasar. Jita-jita kuma na cewa wai yana da kamfanunnuka sama da goma a kasar Amurka, da kuma wani katon asibiti a kasar Birtaniya. Lokacin da ya auri matarsa Aliya tana yar shekaru ashirin daidai. In ban da yawan maganganu n yan uwa da babu abin da zai sa ya yi aure a lokacin. Domin tun yana dan saurayi kafin ya yi arziki ya taba neman wata yarinya Murja, wani direban mota ya kasa shi, tun daga wannan bai kara sha’awar ya nemi wata mace ba a duniya sai da ya hadu da Aliya. Da farko sa’ar da aka yi bikinsu da Aliya bai taba tsammanin auren zai sami wata kyakkyawar nasara ba. To amma kwanaki uku kacal da yin auren sai ya fuskanci ashe Aliya mace ce ta gari mai iya kissa da soyayyar janyo hankalin maza. Wannan ita ta sa a yanzu A. Faruk yake mutuwar kaunar matarsa Aliya. Duk inda zashi koda kasashen ketare ne tare suke tafiya, to amma yanzu da yake cikinta ya tsufa sun fi wata uku a gida Najeriya suna renon cikin. Aliya ta muskuta akan kujerar ta shafa cikinta ta ce. “Kwanta Mabaruka yar gata.” A. Faruk ya ajiye jaridar dake hannunsa kana ya shafi dogon sankonsa ya dubi matarsa Aliya cikin murmushi. “Aliya, ke fa wallahi ba kya rabuwa da rigima in ban da abin ki wa ya ce dake mace za ki haifa da har ki ke sanya mata suna Mabaruka?” Aliya ta harareshi, sannan ta mike da kyar, ta nufo inda yake, tana zuwa sai ta kwanta akan cinyarsa a rigingine kana ta shafo cikin nata ta dubeshi ta ce a tausashe. “Ni na san mace ma zan haifa in Allah ya yarda.” Faruk ya fashe da dariya ya dubeta. “To yanzu da har ki ka sa mata suna Mabaruka idan kika haifi namiji kuma me za ki sa masa? Kamata ya yi ki zabi sunaye biyu, na mace da na namiji, ina ganin zai fi kyau idan namiji ne mu sa masa suna Mabaruki.” Aliya ta fashe da dariya. “Kai (darling) don Allah ka daina sa ni dariya, kar ka sa cikina ya yi ciwo.” Faruk ya dubeta. “A’a, to ke kin ga laifina? Tun da dai kin ce idan mace ce za ki sa mata Mabaruka ni kuwa idan namiji ne sai in sa masa Mabaruki.” Aliya ta kamo wuyansa cikin dariya ta matso da fuskarsa kusa da tata, ta dora bakinta akan kunnensa ta ce. “Kai a tunaninka idan na haifi mace da wa za ta yi kama?” Faruk ya dan dago kansa sama ya dubi kyakkyawar fuskar Aliya, sannan Faruk ya dan dago kansa sama ya dubi kyakkyawar fuskar Aliya sannan ya tuna da dogon sankonsa, gami da tababben hancinsa wanda sau da yawa, shi yake hana shi ganin madubi, sai ya dubeta da murmushi ya ce. “Ina fatan ko mace, ko namiji za ki haifa Allah ya sa ya yi kama da ke Aliya. Aliya ta rungumo shi cikin farin ciki domin ita kanta ta san kyakkyawa ce. Anan, sai Sidi Mai Jaka ya yi shiru, sannan ya sa hannu ya goge gumin da ke sartu akan goshinsa. Me yiwuwa zafi ne, babu mamaki kuma zazzafan yajin tubanin ne ya sashi gumi. Sidi Mai Jaka ya dubeni ya ce. “Nas, wani sa’in matasan mata sukan bani mamaki, da zarar sun sami ciki sai kaga suna ta zaben, wai sun fi son su haifi mace, ko namiji ko kuma mai kama da su, ko kyakkyawa…hak a dai za ka ji suna ta kawo tsarabobi iri daban-daban kai ka ce su ke da ikon halitta. Ni a ganina Nas, gara a bar wa Allah zabi domin shi ne gwani akan komai ko kuwa me ka gani?” Na gyada kai cikin sauri. “Haka ne. Ci gaba baba.” Sidi mai jaka ya dubi kwanon tubanin dake gabansa kana ya girgizaq kai cikin takaici, domin duk yawan tubanin nan dake ciki ya nhadidiyesu kamar zakara wadanda suka rage basu fi kwaya goma ba. Sidi Mai jaka ya canki na goman karshen ya jefa baki kana ya ci ga. “Nas, wata guda da yan kwanaki, da faruwar wannan hira da na baka labari dazu tsakanin ma’auratan biyu, sai Aliya ta haihu. Ta wani bangaren haihuwar ta zo musu kamar yadda suka zata tun farko to sai dai kuma ta wani bangaren haihuwar ta zo musu a murde, musamman ma Aliya. Lokacin da Aliya ta haihu bata san inda hankalinta yake ba, sai bayan kusan sa’a guda da haihuwar ne sannan likita ta zo gabanta da murmushi ta ce. “Ina taya ki murna kin haifi mace.” Aliya ta yi matukar farin ciki da jin cewa mace ta haifa, amma sa’ar da likitan ta miko mata jaririyar da ta haifa sai duniyar jin dadin Aliya ta birkice lokaci guda. Aliya ta dubi jaririyar cikin kaduwa, ko kusa ko alama jaririyar bata yi kama da ita ba, gashi dai lafiyayyace sosai to amma irin tabebben hancin mahaifinta ya mamaye kusan rabin fuskarta, bugu da karin bakin ciki ga Aliya kuma jaririyar ba ta da kafafu domin duk a shanye suke sili-sili kamar maburgi. “Wannan…kafaf un nata ba za su gyaru ba?” Aliya ta tambayi likitan muryata na rawa. Likitan ta girgiza kai cikin jimami. “Babu wani likita a duniya da ya isa ya gyara kafafun nan nata. Ki godewa Allah da ya kawota duniya cikin koshin lafiya, ba kya ganin idan ki ka dauke shanyayyun kafafun lafiyarta kalau.” A daidai lokacin da likitar ta yi shiru sai jaririyar ta bude idanu. Aliya ta dubeta tayi kamar za ta fashe da kuka Ga mamakinta sai jaririyar ta dubeta ta washe baki cikin murmushi Aliya ta rungume yar jaririyarta cikin kuka ya ce. “Ina son ki Mabaruka, ina son ki haka nan domin haka Allah ya so ya gan ki.” Shekaru ashirin suka shude kamar wasa, a cikin shekaru ashirin din nan babu irin gatan duniyar da Mabaruka bata gani ba. Anan Najeriya ta yi makarantar firamare dinta, amma duk sauran karatunta a Burtaniya ta yi. Duk da kasancewar Mabaruka gurguwa kuma mummuna, iyayenta basu ki nuna mata tsananin soyayya ba. Wani Ikon Allah kuma tun daga kan Mabaruka, Aliya ba ta sake haihuwa ba, wannan shi ya kara tsananin kaunarsu a gare ta. Mabaruka ta tashi cikin jin dadi, da gata marar misaltuwa, ga ta dai gurguwa amma duk satin duniya sai ta hada hadaddiyar liyafa, wani sa’in kuwa sai ta tara guragu irinta, ta sa su bi layi a kofar gida, ita ko a yi ta turata akan keken guragu na musamman tana raba musu kudi, tufa, ko abinci. Kudi ba matsalar Mabaruka bane, domin mahaifinta Alhaji Faruk biloniya ne, ya gama tara mata su gashi kuma ita kadai ce bata da ko kani guda daya. Wata rana Mahaifinta ya taba cewa da ita. “Mabaruka, duk abin da ki ke so ki yi da kudi ki yi kawai kar ki ji tsoron komai ki yi ta kashewa tun da dai naki ne. Ki godewa Allah da ya yi ki gurguwa da uba biloniya.” Mahaifin Mabaruka ya mutu tana da shekaru ashirin da hudu a duniya, sakamakon wani mummunan hadarin jirgin kasa da ya ritsa da shi a kasar Indiya. Mahaifin nata Faruk ya bar duniya da bakin cikin har Allah ya karbi ransa bai ga mijin yar sa abar kaunarsa Mabaruka ba. Sau da yawa ya kan so ya tambaye ta shin ko ta sami saurayi To amma idan ya tuna da yadda take ita ba kyau ba a fuska hakan nan ga ta gurguwa sai ya yi shiru domin ko kadan bai san ya yi abin da zai sosa mata rai Duk da haka nan sau da yawa ya kan yi alfahari da ita domin ta yi matukar kama dashi musamman ma tababben hancinsa mai kamar begila. Sa’ar da mahaifinta ya rasu, sai duk kusan kamfanunnukansa da makudan kudinsa gami da sauran muhimman kadarorinsa suka koma karkashinta. Cikin kankanin lokaci ta zamo tabani ka ga sarki, ga ta dai gurguwa kuma mummuna, amma fuskarta ta fi komai kyau ga duk wanda ya santa a zahiri da badini ba don komai ba kuwa sai don dimbin arzikinta. Lokacin da mahaifin Mabaruka ya cika shekaru hudu da rasuwa, sai mahaifiyarta Aliya ta yi kiranta wata rana da yamma ta ce da ita. “Mabaruka kina tunanin aure kuwa?” Mabaruka ta sunkuyar da kai cikin taraddadi, domin ta san tun da take wani saurayi bai taba dubanta a matsayin ta burgeshi ba, sai dai ya dubeta a matsayinta na macen da ta fi kowa arziki a cikin matan Afirka. “Ina yi.” Ta ce da mahaifiyarta kanta a sunkuye. Aliya ta dubeta cikin tausayi, domin ta san ko ita da ta sha miya a duniya ta fi Mabaruka kyan gani a fuska. “In dai kin sami wanda ki ke so sai ki sanar dani, kin ga ke kadai nake da ita a duniya, shi yasa nake matukar son na ga jikokina a duniya tun ina da sauran numfashina.” Mabaruka ta yi shiru tana sauraren mahaifiyarta, yanayin fuskarta a birkice. Ita kanta ta san mummuna ce, sau da yawa in ta kalli madubi sau daya ba ta son ta kuma kallo a karo na biyu, amma ta kan gode Allah da ya yi mata dimbin dukiya. Aliya ta yi nazarin fuskar yar ta na tsawon lokacin sai ta ga duk hankalinta ya tashi. Ta san abin da ke damunta dan haka sai ta dubeta da murmushin karfafa gwiwa ta ce. “Kada ki damu da yadda Allah ya yi ki Mabaruka, abin da nake so ki kula shine kina da dukiya, kin san kuwa a wannan zamanin ba ta da na biyu.” Ta dan yi shiru tana nazarin fuskar Mabaruka. “Ina fatan kuna fahimta ta?” Aliya ta ce da ita tana dubanta ido da ido. Mabaruka ta girgiza kai a sanyaye. Akwai alamun kwalla a idanunta. To amma bata bari mahaifiyarta ta gane ba domin ta san hakan na iya tayar mata da hankali. “Abin da nake so da ke Mabaruka shi ne ki duba ki waiga, ki hanga da idanunki, duk fadin garin nan, idan kin hango namijin da ki ke so, ki ka ga ya kwanta miki a rai ko wane ne shi ki yi kokarin ki shawo kansa ya zo nan gida gurina!” Mabaruka ta dubi mahaifiyarta cikin kaduwa ta ce. “Mama…ya ya za a yi na iya kawo shi har gida? Sai dai in shi ne ya ganni ya zo ya ce yana sona.” Aliya ta dubeta gami da dariya. “Mabaruka kenan. Na fahimci har yanzu ba ki san irin yadda mutane suka dauke ki bane. To bari in fada miki duk kasar nan ke ake labari saboda tsabar kudin da ki ka gada. Duk da yadda ki ke ganin ki din nan ki ke raina kanki kin fi karfin raini, domin kudinki ya wanke duk wani nakasu naki. Saboda haka ina son ki sani cewa babu wani da namiji da za ki kirawo a girin nan ya ki zuwa gare ki ko shi wane ne, domin kina da babban makamin da ya fi nukiliya tasiri, dan in ba kudi babu zancen nukiliya balle aikinsa.” Aliya ta dan yi shiru tana duban fuskar Mabaruka sannan sai ta daga hannu ta nuna fuskarta ta ce. “Na baki daga nan zuwa sati guda duk namijin da ki ka gani ya yi miki ki yi kokarin ki kawo min shi nan.. Nan da rana ya ta yau kenan…. Ranar da ta yi daidai da cikarta shekaru ashirin da takwas a duniya! Mabaruka ta ji wani zazzafan gumi ya fara lullubeta. Tambayar da ta fi damun zuciyarta shi ne, shin a cikin mako guda ya ya za a yi ta sami saurayin da ta ke so, ta kuma iya jawoshi har gida! Sidi Mai jaka ya yi shiru anan, sannan ya dubeni da murmushi ya ce. “Nas, ka ga abin da nake fada ma ko? Ai daman sai da na ce da kai kayi hakuri da sannu zan hade ma bakin zaren labarin biyu na daure. Gashi kuwa na daure ma su kamar yadda na yi maka alkawari.” Na dago kaina gami da ajiyar zuciya “Haka ne.” Na ce dashi “To ya ya kuma bayanin can inda muka baro, inda Mabaruka ta ce da Anas ya shiga mota su tafi.” Sidi mai jaka ya dubeni ya yi murmushi ya ce. “Nas kenan, na dai fuskanci ka fi son can daya bangaren labarin ban yi mamaki ba a matsayin ka na saurayi dole ne labarin soyayya da kudi ya burge ka.” Sidi Mai jaka ya yi shiru kana ya tsikari tubani guda ya jefa a baki ya dubeni idanunsa na zubar da ruwa kamar kuturu saboda masifaffen yajin dake cikin tubanin “Nas, ina son ka kaddara a cikin zuciyarka cewa ga Mabaruka da Anas nan zaune a cikin tangamemen falon gidansu Mabaruka suna fuskantar mahaifiyarta Aliya “Na kaddara.” Na ce dashi cikin sauri domin na gama kaguwa na ji yadda za ta kasance. Sidi mai Jaka ya goge hawayen dake zuba daga idanunsa sannan ya ci gaba. Daga lokacin da katuwar (Jeep) din ta ajiye su Anas da Mabaruka a farfajiyar gidan zuwa lokacin da suka ratsa akalla Falo Bakwai ANAS YA GAMA FITA DAGA HAYYACINSA domin a iya tunaninsa bai taba imani da cewa akwai gidan da ya kai na su Mabaruka tsaruwa ba a duk fadin garin. Gashi dai Anas ma’aikacin otal ne, haka nan otal din ita ce uwa ga duk wata otal dake fadin garin wajen kayatuwa, amma sa’ar da ya ga irin tsari da ni’imar da aka shirya a gidansu Mabaruka sai ya ga duk darajar otal din ta zube a gurinsa, ta koma tamkar kango a zuciyarsa. A tunanin Anas ya dauka irin kayatattun gidajen nan da ya kan gani a finafinan Turawa, ba za a iya taba samunsu anan ba sai a kasashen turawan, domin abu ne mai wuya ace irin yadda almajirai ke cika tituna taf da barace-barace da kuma tarkacen marasa aikin yi da talakawan dake ta sintirin neman abinci sau daya a rana a titunan Najeriya, wai za a sami mai arzikin da har zai iya gina irin wannan! Hakika Anas ya yi masifar kaduwa sa’ar da ya shiga gidansu Mabaruka domin bashi da maraba da irin wadanda yake gani a finafinan turawa. Anas ya yi imani da cewa da ace za a dauke shi a cikin barci bai sani ba a jefashi a gidan, idan ya farka ya ganshi ciki babu abin da zai hana ya ce aljannu ne suka dauko shi suka kawo shi London. Lokacin da suka isa babban falon gidan karfe takwas da yan mintuna. Sa’ar da Aliya ta shigo dakin tuni har Anas ya zabi bangare guda na daga tarin kujerun dake dakin ya lume a ciki, to sai dai kuma duk wanda ya ganshi ya san a bala’in tsorace yake, domin a rabe yake a gefe guda ya yi fakare baya ko kwakkwaran numfashi kamar jikakken zakara. Aliya ta matso zuwa tsakiyar falon, ta dubi Anas da tattusan murmushi. “Ina son ka saki jikinka Anas ka dauka a zuciyarka cewa nan gidan ku ne.” Anas ya ji gabansa ya fadi ras! Rabon da da wani ya ce dashi nan gidansu ne, tun ziyarar sa gidan wata budurwarsa Safiya wadda iyayenta suka so su makala masa ita, da kyar Anas ya samu ya tsere, domin a duk fadin duniya abokan gabarsa guda biyu ne, talauci da aure! Aliya ta nemi kujera ta zauna. Daga inda take zaune tana fuskantar su Anas, hakan nan ta lura da cewa Anas duk a rude yake tuni har ya faera zubar da gumi duk kuwa da ni’imar rabar dake kwararowa dakin. A zuciyarta, Aliya na cewa lallai abin ma zai zo da sauki tunda ma ya gama tsorata dani, don haka sai ta kalli Anas kai tsaye ta ce. “Ina fatan ta fada ma dalilin da ya sa ta kawo ka gidan nan?” Anas ya dubi Mabaruka a rude, Mabaruka ta yi masa murmushin yake, sannan ta sunkuyar da kai a kunyace a zuciyarta tana cewa, oh! Yau na shiga uku za a tursasa mutum ya aure ni ba tare da yana kaunata ba. Ganin Anas ya yi shiru sai Aliya ta dube shi ta ce. “Bawan Allah mene ne sunanka?” “Sunana Anas….” Ya ce bakinsa na rawa. Aliya ta sake duban kyakkyawar fuskarsa ta ce, “Ina son ka dubi yarinyar nan da kyau ya ta ce.” Anas ya dago kai cikin kaduwa ya dubi mummunar fuskar Mabaruka na dakika uku sannan ya sunkuyar da kansa. “Na…kalleta.. .” Aliya ta yi murmushi “Anas, abin da ya sa na ce ka dube ta shi ne, domin ka ajiye hotonta a cikin zuciyar ka, domin ita ce matar da za ka aura.” Anas ya dago kai cikin tsananin kaduwa, “Hajiya…ban fahimce ki ba?” Aliya ta dubeshi da murmushi. “Sannu a hankali za ka fahimce ni ka kuma fahimci dalilin da ya sa na ce da kai ita za ka aura.” Ta dan yi shiru tana mayar da numfashi. “Da farko dai ina son ka sani cewa ni ce na sa Mabaruka na ce da ita duk namijin da ta gani ta ji ya kwanta mata a rai ta kawo min shi…..Abu na biyu kuma shi ne tun da aka haifi Mabaruka bata taba neman wani abu ta rasa ba, shi yasa to na ce da kai ita za ka aura, domin kaunarka ce ta sa ta kawo min kai.” Anas ya ji kamar an dora masa buhun alhaki a tsakiyar kansa, domin ko mosti baya iya yi zaune yake ya yi mutuwar tsohuwa sai idanunsa ne ke ta kifkiftawa kamar idanun barawon akuya, to amma zuciyarsa na kai kawo. Cab! Na auri gurguwa mummuna! Ai da na auri wannan ma gara na auri uwar domin ta fita komai da komai.Anas ya share gumi sa’ar da zuciyarsa ta tuno masa da cewa wannan mummunar gurguwar fa da ake kokarin cusa masa, sunanta KUDI! “Anas.” Aliya ta katse tunanin sa. Anas ya dago kai ya dubeta. “Ina son ka bani hankalin ka nan.” Anas ya dube ta ido da ido ya ce. “Ina jin ki.” “Idan ba ka san wannan yarinyar dake gabana ba bari in fada ma. Ka ga duk fadin kasar nan babu wata mace da ta mallaki kashi daya bisa hudun dukiyar da ta mallaka haka nan ita ce mace ta biyu a kudi a cikin duk matan Afirka Da mun biya ta mutane da tuni an aure ta ko dan a amfani kudin da take dashi, to amma kuma ni na fi son ta zabi wanda take so da kanta.” Aliya ta dan yi shiru tana mayar da numfashi. “A yanzu kai ta gani ta ke so shi ya sa ta kirawo ka gare ni. Anas ina so ka auri Mabaruka domin auren ta alheri ne a gare ka.” Ta sake yin shiru a karo na biyu sannan sai ta dubeshi ta ce. “Nawa ake biyanka a wannan busasshiyar otal din da kake aiki?” Anas ya hadiyi yawu da kyar kwakwalwarsa sai juyawa take yi cikin kokon kansa. “Du…dubu takwas!” Aliya ta dubeshi ta fashe da dariya ta ce. “Dubu takwas! Kyakkyawan saurayi kamarka a dubu takwas? Ko kuwa kullum ne ake biyanka dubu takwas din? Anas ya girgiza kai. “Wata-wata ake biyana.” Idanun Aliya suka zazzaro waje cikin tsananin kaduwa. “Wata guda a dubu takwas.” Cab! Allah rufa asiri.” Ta yi shiru na dan lokaci sannan ta sake duban Anas. “Idan yanzu na baka manajan daya daga cikin kamfanunnukanta albashin naira dubu dari biyu ya yi ma…a wata guda nake nufi.” Anas ya ji zuciyarsa ta harbo da karfi kamar kibiya tana kokarin fasa masa kirji, dubu dari biyu! Tun da yake bai taba tsammanin zai sami dubu hamsin ma ba a duniya lokaci guda. “Ya…yi min.” Ya ce da kyar domin makogwaronsa ya bushe. Aliya ta yi murmushi sannan ta ci gaba da cewa. “Ka je gida ka turo iyayenka domin nan da sati guda za a daura muku aure. Ina son kuma ka sani cewa daga yanzu duk inda kake so a duniya za ka iya sa kafar ka, haka nan ban da albashinka, duk karshen wata na yi maka alkawarin naira dubu dari daga cikin ribar da nake samu karshen wata a kamfanina na atamfa, sannan a matsayin kyauta ta musamman da zan yi ma a matsayin ka na angon yata zan saya ma wannan busasshiyar otal din da kake aiki a ciki, in sa a rugujeta a sake gina ma ita, in ya so sai ka zabi sunan da ka ga ya dace ka sa mata.” Aliya ta yi shiru tana numfasawa, sannan sai ta mike tsaye ta dubi Anas ta ce. “Ka yarda zaka aure ta?” Anas ya ji kamar katanga ta fado masa a tsakiyar baya. Abu daya da ya tabbatarwa kansa shi ne in duk za a bashi duniyar nan domin ya kaunaci wannan mummunar gurguwa ba zai taba iyawa ba, to amma da albashin naiura dubu dari biyu a wata, da naira dubu dari a sama da kuma kyautar otal din da za a bashi, ya tabbatar ko da Mabaruka kuturwa ce sai ya aureta. Cak! Yau na zama miloniya cikin sa’a guda… Ya ce cikin zuciyarsa, koda ya tuna da cewa lagwada otal za ta zama tasa sai ya ji wani zazzafar gumi na farin ciki ya zubo masa tuntuni ya dade yana addu’ar Allah ya bashi damar da zai rama wulakancin da manajan otal din ke yi musu, sai gashi a banza yanzu dama ta samu a bagas. Wani busasshen murmushin mugunta ya subucewa Anas nan da nan ya dauki alkawarin cewa duk ranar da ya mallaki ota din sai ya tikawa dan dukurkushin manajan dundu a tsakiyar baya. “Anas!” Aliya ta katse masa tunani “Tunanin me kake… Baka amince bane?” Anas ya girgiza kai cikin sauri sannan ya ce. “Kin ce cikin sati za a daura auren ni ko yanzu naira dubu takwas ce daidai a aljihuna ita ma ta albashin da aka biyani ce dazu da yamma.” Aliya ta yi murmushi sannan ta ce “Tun da ka amince ina kai ina fargabar kudi, nan gidansu ka zo.” Ta dan yi shiru sannan sai ta ce. “Kana jin naira miliyan goma zata isheka fara shirye-shirye kafin zuwa jibi”. Anas ya ji yawun bakinsa ya kafe ya dube ta a rude. “Miliyan goma kika ce ko kuwa dubu goma.” Aliya ta fashe da dariya sannan ta dubi yarta Mabaruka wacce ke gefe ta yi tagumi tana sauraronsu ta ce “Miliyan goma na ce ko sun yi ma kadan a kara ma?”**** Sidi mai jaka ya yi ajiyar zuciya sannan ya dubi kwanon tubanin dake gabansa cikin takaici duk yawan tubanin nan ya hadiyesu baki daya saura kwaya uku kacal cikin kwanon. “Nas ga labari ya dauko dadi gashi kuma tubanina ya zo Gangara. Irin wannan abin shi yakansa wani lokacin na ji duk na tsani bada labari domin tubanin nan tamkar mota ce da man fetur idan babu shi ka san ban cika abin kirki ba”. Sidi mai jaka ya yi shiru yana kallon cikin kwanon tubanin sannan ya dubeni fuskarsa a murtuke. “Kamata ya yi ka karasa min zuwa sallar Azuhur, idan na koma gida sai na sa kakata ta sake yi ma wani tubanin.” Nan da nan fuskar Sidi mai kaja ta washe. “shi yasa nake son ka NAS. Domin daga na yi motsi sai ka gane abin da nake nufi.” ya dan yi shiru, sannan sai ya ce, bari a gurguje na kulla maka wani sabon zaren labarin da wannan, domin naga kamar lokacin sallah ya kusa.” Sidi Mai Jaka ya tsikari tubani na ukun karshe ya jefa a baki sannan ya dubeni. Nas, ina son ka dauka cewa tuni har an daura auren Anas da Mabaruka gurguwa.” “Na dauka.” Na ce da shi. Sidi mai jaka ya dubeni, sannan ya ci gaba. Wato Nas, watanni biyun da suka biyo bayan bikin Anas sun yi matukar jefa Anas a cikin sabon yanayi. Lokacin da Anas ya bar gidan su Mabaruka bai tsaya ko ina ba sai wurin iyayensa, jikinsa na rawa ya ce da su aure zai yi. Lokacin da labarin auren nasa ya watsu a cikin dangi sai aka yi ta zuwa ana taya mahaifansa murna, domin duk garin babu wanda bai san ko wacece Mabaruka ba. Da yawa daga cikin mahassada suka yi ta zunde, tsegungumi da gulma, suna cewa wai in ba lalacewa ba ina kyakkyawa kamar Anas ina auren gurguwa mummuna. Wasu daga cikin masoyansa sun taya shi murna, domin sun san duk da dai bai yi dacen mata ba, to amma ya yi bankwana da talauci har abada, wannan a gurinsu ya isa abin farin ciki, domin a tunaninsu Anas ya gama samin kwanciyar hankali da nutsuwa. To kamar yadda suke tunani NAS hakanan ta kasance a cikin watanni biyun da suka biyo bayan bikinsu, domin Anas ya sami hutun da bai taba tsammani ba a iya tsawon rayuwarsa. Da farko dai da yake daman shi ba damuwa ya yi ba da wani addini ba kullum kwanan duniya Anas baya tashi daga barci sai karfe goma sha daya na safe, sannan ne zai tashi ya yi wanka, sannan ya nufi wurin aiki. Zamantakewarsa da Mabaruka ta bashi mamaki, domin ya sami Mabaruka macece mai iya dadin magana, da tarairaya, duk kuwa da cewa gurguwa ce, wani sa’in sai su tafi bakin (Swimming pool) su yi ta wasa da katuwar bal marar nauyi, Mabaruka na zaune akan kujerarta a bakin ramin ruwan, shi ko yana ciki, idan ya jefo mata, sai ta cafe ta jefa masa. Wani sa’in kuwa sai Anas ya dauketa a mota su yi ta yawo a cikin gari suna bin guraren shakatawa abinsu da yake Anas gwanin ban dariya ne, sai ya yi ta yi Mabaruka tana dariya. Wannan ita tasa sau biyu ko uku kawai Anas ke zuwa gurin aiki a sati. “Kada ka dami kanka Anas da yawan zuwa wurin aikin nan kudi ne, muna dashi albashinka kuma ko kaje ko baka je ba dole ne a baka.” Mabaruka ce ke cewa Anas haka a wata safiya suna karin kumallo. “Anas, zamanka kusa dani ya fi min zuwanka aiki, domin ni har kullum idan na dubeka sai na ji zuciyata ta yi fari tas, dan haka ne bana son rabuwa da kai koda dai dai da kankani…domin …” Ta dan yi shiru tana duban Anas. Anas ya dube ta sa’ar da ya ji tayi shiru. “Domin muma me…?” Mabaruka ta dube shi. “Domin bana son wata mace ta mallaki zuciyarka a duniya idan bani ba, shi yasa ka ga na ce ma sau biyu kawai za ka ke zuwa aiki a sati.” Anas ya ji zuciyarsa ta harba, ko a lokacin da yake yawon banzan sa, babu abin da ya tsana a rayuwarsa irin mace mai naci, wacce zata makale masa kamar cingam ta hanashi shan iska. Sidi mai jaka ya dago kai ya dubeni da murmushi sannan ya ce “Nas, wata uku su Mabaruka suka yi cikin farin ciki, daga wannan kuma basu kara samun koda dai dai da sa’a daya ba ta farin ciki, domin a safiyar wata rana ne Mabaruka ita da kanta ta yi sanadiyar kawo karshen duk wani farin ciki nasu! Wata rana da safe aka yi sa’a Anas ya farka tun da asussuba, koda yake ba farkawar Allah da Annabi bace. Anas na kwance kawai sai ya ji idanunsa sun bude. Abin ya ba shi mamaki dan haka sai ya dubi agogo. Karfe hudu na asuba agogon ya nuna. Anas ya tashi zaune cikin mamaki, ya dubi Mabaruka gurguwa kwance a kusa da shi a takure kamar kunkuru tana ta barci abinta, mummunar fuskarta a yatsune. Anas ya dauke kai zuciyarsa na wasi-wasin dalilin da ya sashi farkawa a wannan lokaci. Tsawon lokaci yan zaune akan gadon, sannan ne to maganar Mabaruka ta fado masa. “…bana son wata mace ta mallakeka a duniya idan bani ba…” Wani zazzafan gumi ya barkowa Anas, sa’ar da ya tuno da wannan kalami nan da nan ya sake duban mummunar fuskar Mabaruka. A zuciyarsa ya ce cab! Ba zata yiwu ba duk kyawawan matan dake duniyar nan na rasa wacce zan kare rayuwata da ita sai wannan! Anas ya share gumi sannan ya dada kallon Mabaruka tsigar jikinsa ta dauki rawa.Sannan ya dada kallon Mabaruka, tsigar jikinsa ta dauki rawa. Dole ne na sami hanyar da zan rika zagayawa gari ni kadai, ya ce cikin zuciyarsa, wani abu da ya fi baiwa Anas tsoro da al’amarin Mabaruka shi ne ya fahimci tana da bala’in Kishi. Sau da yawa idan suna tafiya a mota da taga ya dauke idanunsa gefe guda ya kalli inda mata suke sai ta kalleshi ta ce. “Me kake kallo?” Anas ya kan ji zuciyarsa kamar za ta fashe saboda haushi. Me take nufi ne da zata hana shi kallon kyawawa bayan duk da tarin miliyoyin kudin nan nata yar karamar yarinyar dake talla a gefen tituna ta fita fasali Bayan da wannan kuma akwai wata rana da yamma wata kawar Mabaruka wai ita Amal ta ziyarci Mabaruka Lokacin da ta samesu zaune suke cikin tangamemen lambun shakatawar gidan Anas yana karantawa Mabaruka wani littafi na hausa wai shi SIRRINSU. Tun kafin Mabaruka ta gama gaisawa da Amal ta kura masa idanu. Anas ya lura da irin kallon da take yi masa, dan haka sai ya yi sauri ya sunkuyar da kansa kamar yana kallon littafin da yake karantawa duk kuwa da cewa a fakaice kallon kyawawan kafafunta yake yi ta kasan littafin. “Tashi ka koma daga ciki kadan bamu guri zamu gana, idan mun gama zan sa a kirawoka.” Mabaruka ta ce dashi, Anas ya mike tsaye simi-simi kamar tunkiya ya wuce cikin gidan zuciyarsa na kuna. Kalmar ta yi matukar kona masa rai, to amma tunda dai an saye shi ya yarda ya amince babu abinda zai iya domin kowa ya sayi rariya ai ya san ta zub da ruwa. Idan har akwai abu daya da Anas ya tabbatarwa da zuciyarsa shi ne ba zai taba yarda ya batawa Mabaruka rai ba, domin ya san hakan na nufin rabuwa da ita, shi ko ya san a yanzu ya gama sabo da jin dadi kum… “Anas.” Ya juyo firgigit sa’ar da muryar Mabaruka dake kwance kusa da shi ta katse tunaninsa. Mabaruka ta dubi agogo, sannan ta yi mika ta dubi Anas cikin mamaki ta ce. “Lafiya na ganka a zaune haka tunda asussuba.” Ta dan yi shiru sannan sai ta miko siraran hannunta ta shafi bayan Anas. “Ko ba ka da lafiya ne?” Ta rikoshi ta mike zaune, nannadaddun kafafun da Anas ya tsana fiye da komai a jikinta suka fito fili. Anas ya girgiza kai. “Kaina ne ya ke dan sara min…amma na san nan da dan lokaci zai bari daman lokaci- lokaci yakan yi min haka.” Mabaruka ta dubeshi cikin shakka da mamaki ta ce. “Ina jin rashin yawan motsa jiki ne…” Ta dan yi shiru, sannan sai ta ce ya kamata na hada mana wata hadaddiyar liyafa ta shakatawa a gidan nan, ina ganin haka zai sa ka dan warware, kuma kamata ya yi bayan liyafar mu tafi kasashen turai hutu, domin tuntuni ya kamata ace mun tafi mun yi (honey moon) dinmu a can, dadin da bana ji sosai ne ya hana.” Ta dan yi shiru tana duban fuskar Anas “Ko kuwa ya ka gani.” Anas ya ji wani dadi ya lullubeshi domin tabbas ya san irin liyafar miloniya me take nufi ko shakka ba ya yi za a tara zuka- zukan mata kyawawa, abin da idanunsa suka fi kaunar gani fiye da komai a duniya. Don haka sai Anas ya dubeta cikin sauri ya ce. “Kwarai kuwa haka za a yi liyafa ba lallai kin zo da dabara.” Suka fashe da dariya, sannan Mabaruka ta dora kanta bisa cinyarsa ta rungumoshi fuskarsa kusa da tata, abin da Anas ya yi matukar tsana, ta ce. “Anas wai don Allah me ka fi kauna fiye da komai a duniya?” Anas ya dubeta cikin mamaki domin tambayar ta zo masa a bazata, kadan ya rage ya ce da ita kyawawan mata, to amma da yake tsohon kwararre ne a sanin tarkon mata ya fahimceta don haka sai ya dubeta da tattausan murmushin yaudara ya dada rungumota a kirjinsa ya ce. “Abin da na fi kauna a duniya ki ke son ki sani?” Mabaruka ta gyada kai cikin murmushi. Anas ya dubeta a tausashe duk kuwa da cewa zuciyarsa kamar ta tsage saboda haushi ya ce. “Ke na fi kauna fiye da komai a duniya.” Mabaruka ta lumshe idanu cikin tsananin farin ciki Tun da take a duniya bata taba jin kalamin da ya faranta mata rai kamar wannan ba. Wani zazzafan hawaye na farin ciki ya yi sartu akan fuskarta. *** Sidi mai jaka ya dauki dunkulallen tubanin karshe ya jefa a bakinsa, ya dubi kwanon cikin takaici, sannan ya dubeni ya ce. “Nas, ranar liyafa ta zo. Kamar yadda Anas ya yi tsammanin tun farko haka ta kasance domin duk kusan kala-kala ta kyawu na mata babu wadda ba a hada a wurin ba. Liyafar ta sami halarta mata kyawawa ashirin da uku, maza goma kacal wadanda mafi yawa ma daga cikinsu duk Anas ya girmesu. Aka yi ciye-ciye da shaye-shaye a tangamemen lambun shakatawar, aka saki kidan dujal yan mata da samari masu karancin kunya suka fara tikar rawa. A can gefe guda gindin wata katuwar lema fara, Mabaruka gurguwa ce da angonta Anas, ta caba kwalliya ta gani ta fada, to amma a wurin Anas kukun dake rabon abinci ma a wurin tafi Mabaruka kyawun fasali. . A daidai lokacin da liyafa ta yi liyafa ne to zazzakar murya mai kama da sarewa ta daki dodon kunnen Anas Nan da nan ya ji numfashin sa ya dauke ko shakka ba ya yi ya san mai muryar. “Yaya Mabaruka ki yi hakuri don Allah wallahi unguwa muka je sai yanzu na sami damar karasowa.” Mai zazzakar muryar ce ke magana sa’ar da ta matso kusa da su cikin sauri. Anas ya kura mata idanu cikin tsananin shauki, zuciyarsa na harbawa, rabonsa da ganinta tun ranar da ya fara haduwa da ita. In ba dan muryar ba da zai yi wuya ma ya ganeta domin ta dada tsayi kadan ta dan kara kauri haka nan kyawunta ya dada bayyana a fili har daukar idanu fuskarta ta ke yi. Anas ya yi mamakin ganinta matuka. Budurwar mai zazzakar murya ba wata bace da ta wuce Ummi, budurwar da ta kirawo wa Mabaruka Anas a ranar da suka fara haduwa a wurin liyafar bikin haihuwar Mabaruka. Sidi Mai jaka ya dan yi shiru sannan ya dubeni ya ce. “Nas, ina fata ka tuna ta?” Na gyada kai cikin kaguwa domin na fahimci kamar ma yanzu ne labarin tsohon zai fara dadi. Sidi mai jaka ya ce “Yawwa Nas, sannan ya ci gaba. Mabaruka ta dubi budurwar cikin farin ciki sannan ta ce. “Ba ki da kirki Ummi kada ma ki yi kokarin wani kare kanki, idan yanzu kin zo a makare, to me ya hana ki zuwa liyafar aurena?” Ummi ta rufe fuska cikin dariya, sannan a karo na farko sai ta dubi Anas da tausasshen murmushi ta matsa kusa da shi ta durkusa ta ce. “Yaya Anas ina wuni…” Anas ya ji wani dadi marar misaltuwa ya kwarara cikin zuciyarsa. Cikin sauri ya tausasa murya ya ce. “Lafiya lau…Ummi!” Idan ya yi kuskurensa na farko kenan kiran sunan nata da ya yi. Ummi ta dubeshi cikin mamaki ta ce. “Ashe ba ka manta suna na ba.” Murmushin Anas ya fadada. “Ai…tun…tun …” Ya yi shiru sanda ya lura Mabaruka ta sunkuyar da kai ta mance dasu. Anas ya mike tsaye jikinsa na rawa ya dubi Mabaruka ya ce. “Darling bari in dan zagaya na barku ku gana.” Nan da nan fuskar Mabaruka ta washe domin zamansa da Ummi shi take tsoro. “Kwarai kuwa gara ka bamu wurin domin muna son mu yi sirrinmu na mata.” Anas ya mike ya nufi cikin farfajiyar lambu inda samari da yan mata ke ta sheke ayarsu, babu wanda ya kula dashi, domin ba a sanshi ba matar aka sani, sai yan tsirarun da suka sami damar halartar liyafar aurensa ne ke gane shi, suma shekeke suke gayar dashi, domin sun san shi ba kowan kowa bane ya dillalin kashi. Anas bai iya tsayawa cikin jama’a ba, sai ya zagaya can bayan lambun ya nemi karkashin wata inuwa mai yawan bishiya ya zauna. Bayansa jingine da bishiyar, daga inda yake zaune yana iya jiyo kida na tashi gami da hayaniyar samari da yan mata. Anas ya lumshe idanunsa, sannan wutar kauna da bege ta fara kona cikin zuciyarsa. Ko shakka ba ya yi kaunar Ummi ta fada zuciyarsa, tun sa’ar da ya fara ganinta irin begenta ya shuka kansa cikin zuciyarsa, a yanzu irin ya girma ya fito fili. Abin da ya fi damun Anas shi ne bai san yadda za a yi ya girbi bishiyar kaunar dake cikin zuciyarsa ba. Mabaruka! Ya kira sunanta a sanyaye, ita ce kadai babbar katangar dake tsakaninsa da Ummi haka nan… “Anas.” Zazzakar muryar ta katse tunaninsa. Ya juyo firgigit, ya ce bakinsa na rawa. “Ummi.” Ummi ta dubeshi da murmushi ta ce. “Ashe nan ka dawo Mabaruka na can tana jiranka.” Anas ya dubeta ya sunkuyar da kai ya ce a sanyaye. “Har kun gama tattaunawar?” Ummi ta gyada kai da murmushi sannan sai ta sunkuyar da kai tana wasa da siraran yan yatsunta Tsawon lokaci matasan biyu suna nan tsaye suna duban juna Wutar bege ta dada ruruwa cikin zuciyar Anas musamman sa’ar da iska ta buga kamshin turaren dake jikinta zuwa hancinsa. “Ummi.” Anas ya kirawo sunanta a sanyaye. Ummi ta matsa kusa dashi sannan ta dago kai ta dubeshi ido da ido ta ce “Anas.” Anas ya yi sororo jiki na rawa ya kasa cewa da ita komai akwai wani irin kwarjini a jikinta da ya karya zuciyar Anas duk kuwa da kwarewarsa a harkar mata. To amma duk da haka sai ya sake ta yan maza ya ce. “Ummi..wani abu ne ke damuna wallahi na rasa yadda..” Ummi ta katseshi ta hanyar dora hannu a bakinta ta ce “Ba sai ka fada ba, na san abin dake damunka sai dai nan ba wurin da ya dace a yi irin wannan magana ba ce.” Ta yi shiru sannan sai ta mika masa wata yar takarda ta ce. Gashi nan sai mun hadu, ka yi sauri ka koma tana can tana jiranka ka santa da zargi.” Tana gama fadin haka sai ta juya da sauri ta bar shi anan tsaye. Wani zazzafan gumi ya kwararo tun daga keyarsa har zuwa gadon bayansa. Ya ji kamar ya bi bayanta a guje domin ya tabbata a yanzu bashi da wani sauran.Sannan ya dada kallon Mabaruka, tsigar jikinsa ta dauki rawa. Dole ne na sami hanyar da zan rika zagayawa gari ni kadai, ya ce cikin zuciyarsa, wani abu da ya fi baiwa Anas tsoro da al’amarin Mabaruka shi ne ya fahimci tana da bala’in Kishi. Sau da yawa idan suna tafiya a mota da taga ya dauke idanunsa gefe guda ya kalli inda mata suke sai ta kalleshi ta ce. “Me kake kallo?” Anas ya kan ji zuciyarsa kamar za ta fashe saboda haushi. Me take nufi ne da zata hana shi kallon kyawawa bayan duk da tarin miliyoyin kudin nan nata yar karamar yarinyar dake talla a gefen tituna ta fita fasali Bayan da wannan kuma akwai wata rana da yamma wata kawar Mabaruka wai ita Amal ta ziyarci Mabaruka Lokacin da ta samesu zaune suke cikin tangamemen lambun shakatawar gidan Anas yana karantawa Mabaruka wani littafi na hausa wai shi SIRRINSU. Tun kafin Mabaruka ta gama gaisawa da Amal ta kura masa idanu. Anas ya lura da irin kallon da take yi masa, dan haka sai ya yi sauri ya sunkuyar da kansa kamar yana kallon littafin da yake karantawa duk kuwa da cewa a fakaice kallon kyawawan kafafunta yake yi ta kasan littafin. “Tashi ka koma daga ciki kadan bamu guri zamu gana, idan mun gama zan sa a kirawoka.” Mabaruka ta ce dashi, Anas ya mike tsaye simi-simi kamar tunkiya ya wuce cikin gidan zuciyarsa na kuna. Kalmar ta yi matukar kona masa rai, to amma tunda dai an saye shi ya yarda ya amince babu abinda zai iya domin kowa ya sayi rariya ai ya san ta zub da ruwa. Idan har akwai abu daya da Anas ya tabbatarwa da zuciyarsa shi ne ba zai taba yarda ya batawa Mabaruka rai ba, domin ya san hakan na nufin rabuwa da ita, shi ko ya san a yanzu ya gama sabo da jin dadi kum… “Anas.” Ya juyo firgigit sa’ar da muryar Mabaruka dake kwance kusa da shi ta katse tunaninsa. Mabaruka ta dubi agogo, sannan ta yi mika ta dubi Anas cikin mamaki ta ce. “Lafiya na ganka a zaune haka tunda asussuba.” Ta dan yi shiru sannan sai ta miko siraran hannunta ta shafi bayan Anas. “Ko ba ka da lafiya ne?” Ta rikoshi ta mike zaune, nannadaddun kafafun da Anas ya tsana fiye da komai a jikinta suka fito fili. Anas ya girgiza kai. “Kaina ne ya ke dan sara min…amma na san nan da dan lokaci zai bari daman lokaci- lokaci yakan yi min haka.” Mabaruka ta dubeshi cikin shakka da mamaki ta ce. “Ina jin rashin yawan motsa jiki ne…” Ta dan yi shiru, sannan sai ta ce ya kamata na hada mana wata hadaddiyar liyafa ta shakatawa a gidan nan, ina ganin haka zai sa ka dan warware, kuma kamata ya yi bayan liyafar mu tafi kasashen turai hutu, domin tuntuni ya kamata ace mun tafi mun yi (honey moon) dinmu a can, dadin da bana ji sosai ne ya hana.” Ta dan yi shiru tana duban fuskar Anas “Ko kuwa ya ka gani.” Anas ya ji wani dadi ya lullubeshi domin tabbas ya san irin liyafar miloniya me take nufi ko shakka ba ya yi za a tara zuka- zukan mata kyawawa, abin da idanunsa suka fi kaunar gani fiye da komai a duniya. Don haka sai Anas ya dubeta cikin sauri ya ce. “Kwarai kuwa haka za a yi liyafa ba lallai kin zo da dabara.” Suka fashe da dariya, sannan Mabaruka ta dora kanta bisa cinyarsa ta rungumoshi fuskarsa kusa da tata, abin da Anas ya yi matukar tsana, ta ce. “Anas wai don Allah me ka fi kauna fiye da komai a duniya?” Anas ya dubeta cikin mamaki domin tambayar ta zo masa a bazata, kadan ya rage ya ce da ita kyawawan mata, to amma da yake tsohon kwararre ne a sanin tarkon mata ya fahimceta don haka sai ya dubeta da tattausan murmushin yaudara ya dada rungumota a kirjinsa ya ce. “Abin da na fi kauna a duniya ki ke son ki sani?” Mabaruka ta gyada kai cikin murmushi. Anas ya dubeta a tausashe duk kuwa da cewa zuciyarsa kamar ta tsage saboda haushi ya ce. “Ke na fi kauna fiye da komai a duniya.” Mabaruka ta lumshe idanu cikin tsananin farin ciki Tun da take a duniya bata taba jin kalamin da ya faranta mata rai kamar wannan ba. Wani zazzafan hawaye na farin ciki ya yi sartu akan fuskarta. *** Sidi mai jaka ya dauki dunkulallen tubanin karshe ya jefa a bakinsa, ya dubi kwanon cikin takaici, sannan ya dubeni ya ce. “Nas, ranar liyafa ta zo. Kamar yadda Anas ya yi tsammanin tun farko haka ta kasance domin duk kusan kala-kala ta kyawu na mata babu wadda ba a hada a wurin ba. Liyafar ta sami halarta mata kyawawa ashirin da uku, maza goma kacal wadanda mafi yawa ma daga cikinsu duk Anas ya girmesu. Aka yi ciye-ciye da shaye-shaye a tangamemen lambun shakatawar, aka saki kidan dujal yan mata da samari masu karancin kunya suka fara tikar rawa. A can gefe guda gindin wata katuwar lema fara, Mabaruka gurguwa ce da angonta Anas, ta caba kwalliya ta gani ta fada, to amma a wurin Anas kukun dake rabon abinci ma a wurin tafi Mabaruka kyawun fasali. . A daidai lokacin da liyafa ta yi liyafa ne to zazzakar murya mai kama da sarewa ta daki dodon kunnen Anas Nan da nan ya ji numfashin sa ya dauke ko shakka ba ya yi ya san mai muryar. “Yaya Mabaruka ki yi hakuri don Allah wallahi unguwa muka je sai yanzu na sami damar karasowa.” Mai zazzakar muryar ce ke magana sa’ar da ta matso kusa da su cikin sauri. Anas ya kura mata idanu cikin tsananin shauki, zuciyarsa na harbawa, rabonsa da ganinta tun ranar da ya fara haduwa da ita. In ba dan muryar ba da zai yi wuya ma ya ganeta domin ta dada tsayi kadan ta dan kara kauri haka nan kyawunta ya dada bayyana a fili har daukar idanu fuskarta ta ke yi. Anas ya yi mamakin ganinta matuka. Budurwar mai zazzakar murya ba wata bace da ta wuce Ummi, budurwar da ta kirawo wa Mabaruka Anas a ranar da suka fara haduwa a wurin liyafar bikin haihuwar Mabaruka. Sidi Mai jaka ya dan yi shiru sannan ya dubeni ya ce. “Nas, ina fata ka tuna ta?” Na gyada kai cikin kaguwa domin na fahimci kamar ma yanzu ne labarin tsohon zai fara dadi. Sidi mai jaka ya ce “Yawwa Nas, sannan ya ci gaba. Mabaruka ta dubi budurwar cikin farin ciki sannan ta ce. “Ba ki da kirki Ummi kada ma ki yi kokarin wani kare kanki, idan yanzu kin zo a makare, to me ya hana ki zuwa liyafar aurena?” Ummi ta rufe fuska cikin dariya, sannan a karo na farko sai ta dubi Anas da tausasshen murmushi ta matsa kusa da shi ta durkusa ta ce. “Yaya Anas ina wuni…” Anas ya ji wani dadi marar misaltuwa ya kwarara cikin zuciyarsa. Cikin sauri ya tausasa murya ya ce. “Lafiya lau…Ummi!” Idan ya yi kuskurensa na farko kenan kiran sunan nata da ya yi. Ummi ta dubeshi cikin mamaki ta ce. “Ashe ba ka manta suna na ba.” Murmushin Anas ya fadada. “Ai…tun…tun …” Ya yi shiru sanda ya lura Mabaruka ta sunkuyar da kai ta mance dasu. Anas ya mike tsaye jikinsa na rawa ya dubi Mabaruka ya ce. “Darling bari in dan zagaya na barku ku gana.” Nan da nan fuskar Mabaruka ta washe domin zamansa da Ummi shi take tsoro. “Kwarai kuwa gara ka bamu wurin domin muna son mu yi sirrinmu na mata.” Anas ya mike ya nufi cikin farfajiyar lambu inda samari da yan mata ke ta sheke ayarsu, babu wanda ya kula dashi, domin ba a sanshi ba matar aka sani, sai yan tsirarun da suka sami damar halartar liyafar aurensa ne ke gane shi, suma shekeke suke gayar dashi, domin sun san shi ba kowan kowa bane ya dillalin kashi. Anas bai iya tsayawa cikin jama’a ba, sai ya zagaya can bayan lambun ya nemi karkashin wata inuwa mai yawan bishiya ya zauna. Bayansa jingine da bishiyar, daga inda yake zaune yana iya jiyo kida na tashi gami da hayaniyar samari da yan mata. Anas ya lumshe idanunsa, sannan wutar kauna da bege ta fara kona cikin zuciyarsa. Ko shakka ba ya yi kaunar Ummi ta fada zuciyarsa, tun sa’ar da ya fara ganinta irin begenta ya shuka kansa cikin zuciyarsa, a yanzu irin ya girma ya fito fili. Abin da ya fi damun Anas shi ne bai san yadda za a yi ya girbi bishiyar kaunar dake cikin zuciyarsa ba. Mabaruka! Ya kira sunanta a sanyaye, ita ce kadai babbar katangar dake tsakaninsa da Ummi haka nan… “Anas.” Zazzakar muryar ta katse tunaninsa. Ya juyo firgigit, ya ce bakinsa na rawa. “Ummi.” Ummi ta dubeshi da murmushi ta ce. “Ashe nan ka dawo Mabaruka na can tana jiranka.” Anas ya dubeta ya sunkuyar da kai ya ce a sanyaye. “Har kun gama tattaunawar?” Ummi ta gyada kai da murmushi sannan sai ta sunkuyar da kai tana wasa da siraran yan yatsunta Tsawon lokaci matasan biyu suna nan tsaye suna duban juna Wutar bege ta dada ruruwa cikin zuciyar Anas musamman sa’ar da iska ta buga kamshin turaren dake jikinta zuwa hancinsa. “Ummi.” Anas ya kirawo sunanta a sanyaye. Ummi ta matsa kusa dashi sannan ta dago kai ta dubeshi ido da ido ta ce “Anas.” Anas ya yi sororo jiki na rawa ya kasa cewa da ita komai akwai wani irin kwarjini a jikinta da ya karya zuciyar Anas duk kuwa da kwarewarsa a harkar mata. To amma duk da haka sai ya sake ta yan maza ya ce. “Ummi..wani abu ne ke damuna wallahi na rasa yadda..” Ummi ta katseshi ta hanyar dora hannu a bakinta ta ce “Ba sai ka fada ba, na san abin dake damunka sai dai nan ba wurin da ya dace a yi irin wannan magana ba ce.” Ta yi shiru sannan sai ta mika masa wata yar takarda ta ce. Gashi nan sai mun hadu, ka yi sauri ka koma tana can tana jiranka ka santa da zargi.” Tana gama fadin haka sai ta juya da sauri ta bar shi anan tsaye. Wani zazzafan gumi ya kwararo tun daga keyarsa har zuwa gadon bayansa. Ya ji kamar ya bi bayanta a guje domin ya tabbata a yanzu bashi da wani sauran.Wani zazzafan gumi ya kwararo tun daga keyarsa har zuwa gadon bayansa. Ya ji kamar ya bi bayanta a guje domin ya tabbata a yanzu bashi da wani sauran farin ciki a duniya da ya wuce Ummi, to sai dai kuma wani bangare na hadamammiyar zuciyarsa na cewa “Uhum-uhm Anas ka bi a hankali yanzu fa zabinka biyu ne ya rage a rayuwarka ta duniya, ko dai ka zabi kudi da tashin hankali ka bar Ummi, ko kuma ka zabi Ummi ka bar kudi. *** Karfe goma sha daya saura minti uku na dare, Mabaruka da Anas suka shiga dakin kwanansu. Tun daga sa’ar da ya koma wurin. Mabaruka a farfajiyar lambun ya lura da cewa lallai yau akwai masifa domin ta cika ta yi fal har wani kumbura take yi. “Ina ka tafi ka zauna ina ta nemanka?” Mabaruka ta tambayeshi a fusace sa’ar da Anas ya dawo ya zauna a kusanta. Bi a hankali dan samari wata zuciya ta ce dashi. “Ina can baya a zaune muna gaisawa da bakin ki.” Mabaruka ta dubeshi a yatsine cikin tsananin zargi sannan ta dauke kai gefe guna. Har bayan da suka gama sallamar baki suka shiga dakin kwanan nasu Mabaruka bata kara cewa dashi uffan ba. Anas ya lura saboda tsabar fushi bakinta har wata kumfa-kumfa yake fitarwa, haka nan duk illahirin jikinta rawa yake yi kamar kamun zazzabi. Anas ya tura Mabaruka akan kujerarta daf da jikin gadon kamar yadda suka saba, sannan ya yi yunkurin daukanta ya daura akan gado. Ga mamakinsa sai ya ji ta buge hannunsa a fusace. “Ka da ka taba ni!…Na ce da kai kada kabani munafuki…!” Anas ya ja baya cikin kaduwa a tsorace. “Me na yi miki?” Mabaruka ta kifa fuskarta akan cinyarta, sannan sai ta fashe da kuka mai karfi jikinta sai rawa yake yi kamar zata fado daga kan kujerar. Tsohon lokaci sai ta dago kai ta ce. “Me ye…hadinka da Ummi?!” Anas ya yi kokari ya sa alamun rudewa akan fuskarsa ya ce. “Ummi kuma…ba kawarki ba ce ni ban ma taba ganinta ba sai sau biyu kuma duk a dalilin ki.” Mabaruka ta ci gaba da shisshikar kuka sannan ta nuna shi da dan yatsa ta ce. “Anas, ina son ka sani cewa na aureka ne don ni kadai ba don ka samar min kishiya ba. Na yi maka abin da duk duniya babu wanda ya isa ya yi ma haka ba don komai ba sai don cikar farin cikina.” Ta dan yi shiru tana mayar da numfashi. “Tun farko sai da na ce sayenka zan yi Anas ban fada maka ba? Idan kuwa haka ne to kai nawa ne ba na kowa ba, don haka daga yau sai yau zan gargade ka, babu kai babu Ummi, koda ta zo gidan nan bana son ka kara ko da kallonta ko gaisawa ban yarda ku yi ba, kai ba ma Ummi ba duk wata mace a duniya in ta wuce kanwarka ta jini ko mahaifiyarka ban yarda ku gaisa da ita ba, kuma daga yau ka daina zuwa wurin aiki, zan ci gaba da biyanka albashinka na fi son daga yanzu kullum kana tare dani kana faranta min, duk inda zaka daga yanzu tare zamu ke tafiya, dare da rana safe da yamma, ruwa da iska kai ko bala’ine bai isa ya rabamu ba, domin muna tare zan manne ma kamar cingam domin sayenka na yi.” Mabaruka ta yi ajiyar zuciya sannan ta daga dan yatsa ta nuna shi ta ce. “Idan kuma kana ganin da takura, to ina shawartarka da ka rubuta min takardar sakina yanzun nan, sai ka hada naka ya naka ka bar min gidana, amma ka tuna daga lokacin ka daina karbar albashin naira dubu dari biyu ka daina karbar kudin da mahaifiyata ta ke baka duk wata ka kuma daina hawa motocina kai hatta kayan da ka saya da kudin mahaifiyata sai ka ajiye min kayana kuma sai ka yi sallama da fita wata kasa a duniya domin na san a rashin zuciya da lalaci irin naka da wahala in zaka yi arziki a duniya mutumin da ko sallah baya iya yi!” Anas ya yi tsaye sororo cikin tsananin kaduwar da bai taba irinsa a duniya ba. Wani abu mai kamar gare-gare ya fara yawo a cikin kwakwalwarsa, nan da nan ya ji cikinsa ya murda kamar zai yi amai Cikin sauri ya dubi Mabaruka baki na rawa ya ce “Ki yi hakuri Mabaruka abin duk bai kai da zafin haka ba.” Anas ya dada dafe ciki sannan ya dubi Mabaruka. Mabaruka ta sake fashewa da kuka. Anas ya ji ba zai iya daurewa kukanta ba dan haka sai ya ruga bandaki a guje yana zuwa sai ya fara keta amai. Bayan tsawon lokaci ya gama zubar da abincin da ya ci a wurin liyafar. Daga bandakin yana iya jiyo shisshikar kukan Mabaruka hakan shi ya tuna masa da guntuwar takardar da Ummi ta bashi cikin sauri ya laluba aljihunsa ya dauko takardar sannan sai ya warwareta ya fara karantawa…… . Anas Tun da nake a duniya ban taba sanin mene ne so ba domin ni ko zance ma bana fita wurin samari To amma tun ranar da na dora idanuna a kanka sai na ji duk duniya bani da abin so kamar ka. Na yi matukar farin ciki sa’ar da na dubi cikin kwayar idanunka, sai na tabbata kai ma kana kaunata. Haka nan na yi bakin ciki da ya kasance wannan gurguwa ta yi min shigar sauri ta aureka. Wannan shi ya sa na yi amfani da damar wannan liyafa domin na isar da sakon zuciyata zuwa gareka Na gode, zan tsaya anan, idan har abin da nake zargi gaskiya ne, na san zaka so mu hadu. Ga adireshina nan a kasa, zan jiraka gobe gida tun daga karfe bakwai na dare har zuwa goma na dare…sai na ganka mai… Ummai. Anas ya kankame takardar a kirjinsa cikin farin ciki sannan kuma cikin tsananin rudewa. “Daga yanzu duk inda za ka muna tare zan manne maka kamar cingam!” Ya tuna da kalaman Mabaruka. “Ina jiranka gobe a gida…” ya kuma tuna da kalaman Ummi na karshe. Anas ya lumshe idanunsa, sannan ya kara takardar wasikar akan hancinsa, ya shaki kamshin turaren jikin Ummi dake jikin wasikar, cikin jin dadi. Daga can falo ya jiyo gurnanin kukan Mabaruka. Anas ya yi sauri ya toshe kunnensa domin baya son kukan ya bata masa farin cikin da yake, kai da zai yiwu ya gwammace ya kwana cikin bandakin rungume da wasikar Ummi! Sidi mai jaka ya yi shiru lokaci guda. Na dubeshi cikin kaduwa na ce bakina na rawa. “To mana Baba Sidi…ci gaba mana ya ka tsaya bayan labarin ya gama daukar dadi.” Sidi mai Jaka ya dubi kwanon tubanin dake gabansa cikin takaici, sannan ya dubeni da kyau ya ce. “Kada ka bari dadin labari ya dauke ka, saurara da kyau ka ji kiran sallah ake yi. Tashi ka je ka yi sallah idan an idar da sallar sai mu sako wani sabon zaren labarin.” Yana gama fadin haka sai ya mike tsaye ya dauki tsohuwar butarsa ta karfe mai kwarin tsiya ina tsammanin butar tafi shekaru arba’in. Na mike tsaye cikin sauri na ce. “Baba Sidi dan Allah…da na gama sallah fa zan dawo.” Baba Sidi ya dubeni da murmushi ya ce. “Idan za ka dawo ka tabbata ka dawo min da karin tubani, domin idan babu shi, to babu labari Nas, na riga na fada ma ni da tubani tamkar tsohuwar mota ce da man fetur. Ya juya cikin sauri da butarsa a hannu ya nufi waje zai yi alwala. *** Ban sami damar dawowa wajen Sidi mai jaka ba sai bayan sallar La’asar sakamakon tsayawa da na yi a sake dafa min sabon tubani. “Kai dan nema, bana son shakiyancin banza, me kuma zaka sake yi da tubani. Na dauka dazu-dazun nan na yi ma cikin kwano guda?” Kakata ce ke fadin haka. Na dubeta da dariya. “Kin ga in za ki dafa min ki dafa, in kuma ba haka ba yanzun nan in baki takardar saki akan tubani.” Ta fashe da dariya. “Amma kuwa da ka yi abin kunya wallahi ka saki matarka saboda tubani?” Daga karshe bayan mun sha cacar baki kusan mintuna bakwai, na shawo kanta da kyar, ta sake cika min kwano da tubani, a wannan karon har sun fi wadancan girma domin ba a son ranta ta yi su ba. Na riski Baba Sidi mai jaka zaune akan tsohuwar kujerar katakonsa yana jan carbi, tun kafin na gama yi masa sallama ya dago kai ya dubi kwanon dake hannuna cikin fara’a, kamar karamin yaron da ya yi ido biyu da alewa mai tsinke. “Tsohon alkawari a karo na biyu, lallai Nas ka kyauta min.” Ya ce sa’annan ya mika hannu ya karbe kwanon daga hannuna tun ma kafin na ajiye shi da kaina. Sidi mai jaka bai jira komai ba, sai kawai ya bude kwanon tubanin ya fara juya tubanin da yan yatsunsa bayan wani dan lokaci ya tabbata da cewa sun juyu yadda ya ke so don haka sai ya can ku wani kato ya jefa cikin bakinsa sannan ya dubeni. “Nas, ina fatan dazu kana biye dani a labarin da na fara baka.” Cikin sauri na gyada kaina. “Kwarai kuwa ka tsaya inda Anas ya shiga bandaki ya fara karanta wasikar Ummi harma take cewa dashi tana son ganinsa a daren washe garin ranar Sidi mai jaka ya gyada kai da murmushi. “Wani lokaci ina son mutum mai saurin rike al’amura a cikin kwakwalwa nan da nan ba tare da mantuwa ba.” Na dubeshi da murmushi a karo na farko na ce. “Ai kuwa in ka dauke labarai babu abin da kwakwalwata ke iya rikewa domin koda sunan mutane in ba dadewa muka yi da kai ba sai ka yi ta zuwa ina kiranka da kai!” Sidi mai jaka ya fashe da dariya sannan ya canko wani katon tubani ya sha ya ji jajur dashi ga girma kamar dankali ya miko min. “Ungo wannan Nas jefa a bakin ka.” Na yi saurin girgiza kai cikin kaduwa. “Allah kuwa karbi baka jiba yadda tubanin nan ya yi dadi..Wani zazzafan gumi ya kwararo tun daga keyarsa har zuwa gadon bayansa. Ya ji kamar ya bi bayanta a guje domin ya tabbata a yanzu bashi da wani sauran farin ciki a duniya da ya wuce Ummi, to sai dai kuma wani bangare na hadamammiyar zuciyarsa na cewa “Uhum-uhm Anas ka bi a hankali yanzu fa zabinka biyu ne ya rage a rayuwarka ta duniya, ko dai ka zabi kudi da tashin hankali ka bar Ummi, ko kuma ka zabi Ummi ka bar kudi. *** Karfe goma sha daya saura minti uku na dare, Mabaruka da Anas suka shiga dakin kwanansu. Tun daga sa’ar da ya koma wurin. Mabaruka a farfajiyar lambun ya lura da cewa lallai yau akwai masifa domin ta cika ta yi fal har wani kumbura take yi. “Ina ka tafi ka zauna ina ta nemanka?” Mabaruka ta tambayeshi a fusace sa’ar da Anas ya dawo ya zauna a kusanta. Bi a hankali dan samari wata zuciya ta ce dashi. “Ina can baya a zaune muna gaisawa da bakin ki.” Mabaruka ta dubeshi a yatsine cikin tsananin zargi sannan ta dauke kai gefe guna. Har bayan da suka gama sallamar baki suka shiga dakin kwanan nasu Mabaruka bata kara cewa dashi uffan ba. Anas ya lura saboda tsabar fushi bakinta har wata kumfa-kumfa yake fitarwa, haka nan duk illahirin jikinta rawa yake yi kamar kamun zazzabi. Anas ya tura Mabaruka akan kujerarta daf da jikin gadon kamar yadda suka saba, sannan ya yi yunkurin daukanta ya daura akan gado. Ga mamakinsa sai ya ji ta buge hannunsa a fusace. “Ka da ka taba ni!…Na ce da kai kada kabani munafuki…!” Anas ya ja baya cikin kaduwa a tsorace. “Me na yi miki?” Mabaruka ta kifa fuskarta akan cinyarta, sannan sai ta fashe da kuka mai karfi jikinta sai rawa yake yi kamar zata fado daga kan kujerar. Tsohon lokaci sai ta dago kai ta ce. “Me ye…hadinka da Ummi?!” Anas ya yi kokari ya sa alamun rudewa akan fuskarsa ya ce. “Ummi kuma…ba kawarki ba ce ni ban ma taba ganinta ba sai sau biyu kuma duk a dalilin ki.” Mabaruka ta ci gaba da shisshikar kuka sannan ta nuna shi da dan yatsa ta ce. “Anas, ina son ka sani cewa na aureka ne don ni kadai ba don ka samar min kishiya ba. Na yi maka abin da duk duniya babu wanda ya isa ya yi ma haka ba don komai ba sai don cikar farin cikina.” Ta dan yi shiru tana mayar da numfashi. “Tun farko sai da na ce sayenka zan yi Anas ban fada maka ba? Idan kuwa haka ne to kai nawa ne ba na kowa ba, don haka daga yau sai yau zan gargade ka, babu kai babu Ummi, koda ta zo gidan nan bana son ka kara ko da kallonta ko gaisawa ban yarda ku yi ba, kai ba ma Ummi ba duk wata mace a duniya in ta wuce kanwarka ta jini ko mahaifiyarka ban yarda ku gaisa da ita ba, kuma daga yau ka daina zuwa wurin aiki, zan ci gaba da biyanka albashinka na fi son daga yanzu kullum kana tare dani kana faranta min, duk inda zaka daga yanzu tare zamu ke tafiya, dare da rana safe da yamma, ruwa da iska kai ko bala’ine bai isa ya rabamu ba, domin muna tare zan manne ma kamar cingam domin sayenka na yi.” Mabaruka ta yi ajiyar zuciya sannan ta daga dan yatsa ta nuna shi ta ce. “Idan kuma kana ganin da takura, to ina shawartarka da ka rubuta min takardar sakina yanzun nan, sai ka hada naka ya naka ka bar min gidana, amma ka tuna daga lokacin ka daina karbar albashin naira dubu dari biyu ka daina karbar kudin da mahaifiyata ta ke baka duk wata ka kuma daina hawa motocina kai hatta kayan da ka saya da kudin mahaifiyata sai ka ajiye min kayana kuma sai ka yi sallama da fita wata kasa a duniya domin na san a rashin zuciya da lalaci irin naka da wahala in zaka yi arziki a duniya mutumin da ko sallah baya iya yi!” Anas ya yi tsaye sororo cikin tsananin kaduwar da bai taba irinsa a duniya ba. Wani abu mai kamar gare-gare ya fara yawo a cikin kwakwalwarsa, nan da nan ya ji cikinsa ya murda kamar zai yi amai Cikin sauri ya dubi Mabaruka baki na rawa ya ce “Ki yi hakuri Mabaruka abin duk bai kai da zafin haka ba.” Anas ya dada dafe ciki sannan ya dubi Mabaruka. Mabaruka ta sake fashewa da kuka. Anas ya ji ba zai iya daurewa kukanta ba dan haka sai ya ruga bandaki a guje yana zuwa sai ya fara keta amai. Bayan tsawon lokaci ya gama zubar da abincin da ya ci a wurin liyafar. Daga bandakin yana iya jiyo shisshikar kukan Mabaruka hakan shi ya tuna masa da guntuwar takardar da Ummi ta bashi cikin sauri ya laluba aljihunsa ya dauko takardar sannan sai ya warwareta ya fara karantawa…… . Anas Tun da nake a duniya ban taba sanin mene ne so ba domin ni ko zance ma bana fita wurin samari To amma tun ranar da na dora idanuna a kanka sai na ji duk duniya bani da abin so kamar ka. Na yi matukar farin ciki sa’ar da na dubi cikin kwayar idanunka, sai na tabbata kai ma kana kaunata. Haka nan na yi bakin ciki da ya kasance wannan gurguwa ta yi min shigar sauri ta aureka. Wannan shi ya sa na yi amfani da damar wannan liyafa domin na isar da sakon zuciyata zuwa gareka Na gode, zan tsaya anan, idan har abin da nake zargi gaskiya ne, na san zaka so mu hadu. Ga adireshina nan a kasa, zan jiraka gobe gida tun daga karfe bakwai na dare har zuwa goma na dare…sai na ganka mai… Ummai. Anas ya kankame takardar a kirjinsa cikin farin ciki sannan kuma cikin tsananin rudewa. “Daga yanzu duk inda za ka muna tare zan manne maka kamar cingam!” Ya tuna da kalaman Mabaruka. “Ina jiranka gobe a gida…” ya kuma tuna da kalaman Ummi na karshe. Anas ya lumshe idanunsa, sannan ya kara takardar wasikar akan hancinsa, ya shaki kamshin turaren jikin Ummi dake jikin wasikar, cikin jin dadi. Daga can falo ya jiyo gurnanin kukan Mabaruka. Anas ya yi sauri ya toshe kunnensa domin baya son kukan ya bata masa farin cikin da yake, kai da zai yiwu ya gwammace ya kwana cikin bandakin rungume da wasikar Ummi! Sidi mai jaka ya yi shiru lokaci guda. Na dubeshi cikin kaduwa na ce bakina na rawa. “To mana Baba Sidi…ci gaba mana ya ka tsaya bayan labarin ya gama daukar dadi.” Sidi mai Jaka ya dubi kwanon tubanin dake gabansa cikin takaici, sannan ya dubeni da kyau ya ce. “Kada ka bari dadin labari ya dauke ka, saurara da kyau ka ji kiran sallah ake yi. Tashi ka je ka yi sallah idan an idar da sallar sai mu sako wani sabon zaren labarin.” Yana gama fadin haka sai ya mike tsaye ya dauki tsohuwar butarsa ta karfe mai kwarin tsiya ina tsammanin butar tafi shekaru arba’in. Na mike tsaye cikin sauri na ce. “Baba Sidi dan Allah…da na gama sallah fa zan dawo.” Baba Sidi ya dubeni da murmushi ya ce. “Idan za ka dawo ka tabbata ka dawo min da karin tubani, domin idan babu shi, to babu labari Nas, na riga na fada ma ni da tubani tamkar tsohuwar mota ce da man fetur. Ya juya cikin sauri da butarsa a hannu ya nufi waje zai yi alwala. *** Ban sami damar dawowa wajen Sidi mai jaka ba sai bayan sallar La’asar sakamakon tsayawa da na yi a sake dafa min sabon tubani. “Kai dan nema, bana son shakiyancin banza, me kuma zaka sake yi da tubani. Na dauka dazu-dazun nan na yi ma cikin kwano guda?” Kakata ce ke fadin haka. Na dubeta da dariya. “Kin ga in za ki dafa min ki dafa, in kuma ba haka ba yanzun nan in baki takardar saki akan tubani.” Ta fashe da dariya. “Amma kuwa da ka yi abin kunya wallahi ka saki matarka saboda tubani?” Daga karshe bayan mun sha cacar baki kusan mintuna bakwai, na shawo kanta da kyar, ta sake cika min kwano da tubani, a wannan karon har sun fi wadancan girma domin ba a son ranta ta yi su ba. Na riski Baba Sidi mai jaka zaune akan tsohuwar kujerar katakonsa yana jan carbi, tun kafin na gama yi masa sallama ya dago kai ya dubi kwanon dake hannuna cikin fara’a, kamar karamin yaron da ya yi ido biyu da alewa mai tsinke. “Tsohon alkawari a karo na biyu, lallai Nas ka kyauta min.” Ya ce sa’annan ya mika hannu ya karbe kwanon daga hannuna tun ma kafin na ajiye shi da kaina. Sidi mai jaka bai jira komai ba, sai kawai ya bude kwanon tubanin ya fara juya tubanin da yan yatsunsa bayan wani dan lokaci ya tabbata da cewa sun juyu yadda ya ke so don haka sai ya can ku wani kato ya jefa cikin bakinsa sannan ya dubeni. “Nas, ina fatan dazu kana biye dani a labarin da na fara baka.” Cikin sauri na gyada kaina. “Kwarai kuwa ka tsaya inda Anas ya shiga bandaki ya fara karanta wasikar Ummi harma take cewa dashi tana son ganinsa a daren washe garin ranar Sidi mai jaka ya gyada kai da murmushi. “Wani lokaci ina son mutum mai saurin rike al’amura a cikin kwakwalwa nan da nan ba tare da mantuwa ba.” Na dubeshi da murmushi a karo na farko na ce. “Ai kuwa in ka dauke labarai babu abin da kwakwalwata ke iya rikewa domin koda sunan mutane in ba dadewa muka yi da kai ba sai ka yi ta zuwa ina kiranka da kai!” Sidi mai jaka ya fashe da dariya sannan ya canko wani katon tubani ya sha ya ji jajur dashi ga girma kamar dankali ya miko min. “Ungo wannan Nas jefa a bakin ka.” Na yi saurin girgiza kai cikin kaduwa. “Allah kuwa karbi baka jiba yadda tubanin nan ya yi dadi..”Ungo wannan Nas jefa a bakin ka.” Na yi saurin girgiza kai cikin kaduwa. “Allah kuwa karbi baka jiba yadda tubanin nan ya yi dadi har ya fi na dazu.” Na dada girgiza kai. Sidi mai jaka ya zunkuda kafada, “Ka cuci kanka Nas, ni duk abincin duniya ban ga abin da zai zo a na biyun tubani ba a gare ni. Ya sake tsikaro guda ya jefa a bakin salatinsa sannan ya juya ya dubeni idanunsa na zubar hawaye kamar kuturu. “Nas, zaren labarin dana fara baka labari dazu ya kare iyakarsa kenan.” Na dubi Sidi mai jaka cikin kaduwa. “Haba Baba Sidi, kai fa ka ce dani Ummi ta ce tana son ganinsa washe garin ranar, kuma yanzu ka ce dani wai zaren labarin ya kare.” Sidi Mai Jaka ya yi murmushi “Haba Nas kai fa yanzu mun zama jiki sai dai ka fadawa wani ni, sanin kanka ne idan na ce da kai zaren labari ya kare to ya kare din tabbas, dole ne sai na sako sabo sannan na jona ma shi da bakin wannan tsohon labarin da na saka. Ya dan yi shiru, sannan ya sunkuyar da kai. Nas ina son ka dauki zuciyarka cancak ka maishe da ita can wani lokaci, kuma wani zamani mai dan tsayi na a kalla shekaru ashirin da biyar da suka gabata. Na dubi Sidi mai Jaka cikin mamaki bani da abin cewa dan haka sai na gyada kai na ce dashi “Na mayar.” Sidi Mai jaka ya ce “Yauwa Nas haka nake so da kai.” * * Shekaru ashirin da biyar da suka wuce wani dogon mutum fari siriri buzu-buzu balarabe-balarabe, ya sauka a garin nan dauke da yar tabarmarsa ta kaba akai yana neman inda zai sauka. Ba don komai ba kuwa sai don lokacin da ya sauka a garin nan cikin dare ne tare suke da matarsa ita ma kusan irin kirar su daya to sai dai kuma kyakkyawa ce ta gani a fadawa sarki. Wannan mutum dogo fari siriri babu komai a cikinsa sai hanji domin rabonsa da abinci kwana biyu kenan haka ma matarsa. Haka nan kuma yadda cikinsa yake hakanan aljihunsa yake, karaf babu ko karfanfana. Mutanen guda biyu mace da mijinta suka shigo birni, mijin na gaba dauke da tabarmar kaba, ita ko matar na biye dashi a baya dauke da wasu tsummokarai da ita kanta bata san amfaninsu ba. Me yiwuwa dai tana dauke da tsummokaran ne don cika umarnin mijinta, babu mamaki kuma sabo da yi ne wai gawa da gatsine. To koma dai mene ne wannan mutane dauke suke da muguwar yunwa ga kishi ga gajiya, ga babu tabbacin gurin kwana, sannu a hankali suna yawo cikin birni tsakanin manya- manyan gine-gine na alfarma can sai matar ta jefar da kayan tsummokaran dake kanta ta durkusa, ta rike ciki. “Wallahi…mai gida ni na gaji.” Ta ce cikin wata irin bakuwar Hausa. Mutumin ya ajiye tabarmar keson dake kansa sannan ya dubi dankareren gidan dake gabansu wanda ke ci reras da fitulu kamar rana. Ya dubi matarsa cikin tsananin tausayi. “Ban ga laifinki ba HINDATU, ai kin yi ma kokari.” Ya dan yi shiru idanunsa akan katon gidan dake gabansu. “Gashi wannan gidan ma kamar babu kowa a cikinsa, da sai in karasa na barato mana dan abin da zamu sa a bakinmu.” Matarsa Hindatu ba ta ce komai ba, maimakon hakan ma sai ta kwanta a kasa ta dora kanta akan kullin tsummokaran ta kurawa sararin subhanahu idanu. Hankalin mijinta ya dada tashi, ya san cewa dadin ta yunwa ce kawai, duk wannan mai sauki ne, domin sun riga sun saba da jin yunwa, tun sa’ar da yaki ya barke tsakanin buzaye yan tawaye da gwamnatin kasarsu basu kara samun damar wani jin dadin rayuwa ba. Koda yake can ma ba wani cikin kwakkwaran jin dadi suke yi ba, to amma akalla dai kafin barkewar yaki suna da kwanciyar hankali wannan da sauran matsalalo halayyar yaki marasa adadi su suka sa wadannan mutane sabo da duk wata irin wahala, a cikinsu har da ma jimirin yunwa. Dan haka abin da ya sa hankalin mijin matar nan Hindatu ya tashi shi ne, ya san tana da juna biyu, akalla zai kai wata uku. Tun sa’ar da ya ki ya barke suka fita gudun hijira mutumin ya fitar da ran cewa matarsa zata sami damar haife cikin, kullum kwanan duniya cikin zullumi yake, yana sauraron zubewar cikin, amma cikin ikon rabbana har zuwa wannan lokaci matar bata ko taba ciwon kai ba ballantana a yi zancen zubewar cikin sai yanzu da ta fadi a gabansa ta ce dashi ta gaji ga kuma muguwar yunwa. Dogon mutumin ya mike tsaye sannan ya sake duban matarsa cikin damuwa kana ya dubi sararin samaniya sai ya ga tuni ya hade da gajimare an kuma fara rugugin aradu haka nan Walkiya sai haskawa take yi wal- wal kamar tana daukar hotonsu. “Sannu Hindatu dan jirani kadan na karasa kofar gidan can me yiwuwa idan nayi sa’a ko masamu wani ya taimakomu da abin da za mu sa a bakinmu.” Hindatu ta runtse idanu sannan ta budesu cikin karfin hali ta dubi mai gidanta ta ce. “Kada ka damu je ka gani, Allah baka sa’a.” Cikin sauri na ban mamaki idan aka yi la’akari da rama da kuma bakar wahalar dake jikinsa mutumin ya nufi kofar gidan kai tsaye kirjinsa na harbawa. Har sa’ar da ya kai ga tangamemiyar kofar me kamar kofar gari bai ga motsin ko da halitta daya ba a duk tsawon kwararo sai wasu karnuka guda uku dake can karshen kwararon suna ta faman haushin babu gaira babu dalilin kamar sun yi ido biyu da aljan. Mutumin ya matsa kusa da kofar ya tsaya cikin shakka, domin bai san abin da ya kamata ya yi ba Shin buga kofar zai yi ko kuwa sallama zai yi. To idan ma ya yi sallama wa zai ji shi? Ya tambayi kansa. Yana nan tsaye cikinsa na kugi kamar tukunyar talge, sai ya ji kamar dagacan sashen hagu na katuwar kofar ana tabata. Mutumin ya yi sauri ya dan ja da baya lokaci guda kuma ya dubi bangaren hagu na jikin kofar. A lokacin ne to ya fahimci ashe a jikin katuwar kofar akwai wata yar karamar kofa daga hannun hagu wacce akalla mutum guda zai iya wucewa ta ciki, wannan yar karamar kofa ita ce ake motsawa ba a ko dade ba sai ta bude. Wani dan matashin yaro fari kyakkyawa ma’abocin kyawun sutura da cikar hallita ya fito daga cikin gidan sannan ya kurawa dogon mutumin idanu baya ko kiftawa. Dogon mutumin ya dubi yaron, sai ya rasa ma me zai ce masa. Domin da ido mutum na iya tsammanin dan saurayin yaron ya kai shekara goma sha uku ko sha hudu, to amma a gaskiyar al’amari yaron shekarunsa goma cif-cif da kwana biyu, domin shekaran jiya-jiya din nan aka yi bikin cikar shekarunsa goma da haihuwa. “Sannu Malam.” Yaron ya ce da mutumin cikin ladabi. “Yauwa dana, sannunka dai.” Ya dan yi shiru sannan sai ya dubi yaron ya ce. “Da Allah dan samari idan da hali taimakon abinci nake nema duk kankantarsa, wallahi mu baki ne bamu san kowa ba, ga matata can kwance akan titi, yunwa ce ta hanata tafiya” Yaron ya dubi mutumin na dan tsawon lokaci, a zuciyarsa yana tunanin ja da baya a guje ya rufe gida domin me yiwuwa mutumin nan dake tsaye a gabansa mahaukacine, dubi fa kayan dake jikinsa, koda yake dai irin kayan da yake gani ne jikin buzayen dake gadin gidansu, to amma shi wannan nasa sun ji jiki da yawa. “Ka ce abinci kake so?” Yaron ya tambaya. Mutumin ya gyada masa kai sannan ya dada da cewa. “Ko da kadan ne wanda zan bawa matata da Allah a taimaka min, so nake na bata ta dan ci mu yi gaba” Yaron ya daga kai ya dubi hadarin da ya mamaye sararin samaniya, sannan sai ya dubi mutumin cikin tausayi ya ce. “Ina zuwa” Cikin sauri ya shiga cikin gida. Ba a dade ba sai ga yaron tare da masu gadin gidansu mutum uku biyu buzaye daya tsohon soja, hakanan kuma da wani mutum dogo kakkaura wankan tarwada sanye da babbar riga amma kansa babu hula, ko shakka babu shi ne ya yi kama da mamalakin dankareren gida. Dogon mutumin dake tsaye, ya dubi mutumin a tsorace, domin ya tabbata kashinsa ya bushe a tsammaninsa kamashi zasu yi a matsayin barawo ko mahaukaci. Tun kafin su karaso gurin mutumin sai ya ji maigidan nan na cewa sauran masu gadin. “Wai wani mutum ne da matarsa anan kofar gidan suke neman taimakon abinci a gurin Abdulmalik shi ne na fito da kaina gara mu je mu gani ko wane irin mutum ne, duniyar nan yanzu ba abin yarda ba ce.” Dogon mutumin ya zube gaban mai gidan ya gaida shi. Maigidan ya dubi dogon mutumin ya ce. “Malam kaine me neman taimakon abinci?” Mutumin ya gyada kai ya ce. “Ni ne ranka ya dade, wallahi zuwan mu kenan garin nan ni da matata, ga ta can a bayan yunwa ce ta kayar da ita ta kasa tafiya kuma tana da ciki wata uku, wannan shi ya takurani nake neman wannan abinci kafin Allah ya bani masauki, domin mu ba mutanen wannan kasa ba ne yaki ne ya koromu gudun hijira.” Kalamin dogon mutumin ya karya zuciyar maigidan, nan da nan sai ya ji tausayinsa ya kamashi, musamman ma daya ji tare suke da matarsa kuma tana da ciki wata uku. Wannan shi ya fi tayar masa da hankali. Domin yau shekarunsa ashirin da yin aure, tun daya auro matarsa Hajiya Sa’adatu basu sami damar haihuwa ba sai bayan shekaru goma suka haifi Abdulmalik, tun daga kansa kuwa basu kara samun koda batan wata ba har zuwa wannan lokaci. “Yanzu ina matar taka take?” Dogon mutumin ya nuna can bayansa ya ce. “Ga ta can yallabai” Mai gidan ya dubi masu gadinsa guda uku ya ce. “Ku je dashi ku taho da matar, ku sameni a tsakar gida.” Sannan sai ya kama hannun Abdulmalik suka shige farfajiyar gidan ma’abociyar shuke-shuken da kamshin furanni. Ba’a dade ba, masu gadin suka shigo farfajiyar gida tare da.Ba’a dade ba, masu gadin suka shigo farfajiyar gida tare da dogon mutumin da kuma matarsa Hindatu. Suna isowa sai mutumin da matar tasa suka zube gaban alhaji suka sake gaidashi. Mai gidan ya dubi tsohon sojan nan mai gadinsa ya ce. “A kaisu dakin nan na kusa da injin bada wuta su kwana a ciki yanzu zan sa a kawo musu abinci ina son kuma a lura dasu kaji ko?” Tsohon sojan ya rusuna ya ce “An gama alhaji” Sannan sai ya dubi dogon mutumin da matarsa ya ce. “Ku biyoni mu tafi.” Ramammun mutanen guda biyu kyawawa suka bishi a baya, gami da godiya. Mai gidan ya bisu da kallo cikin tausayi yana tunanin abin da ya kamata ya yi domin taimakonsu. “Wallahi baba mutanen abin tausayi ne dubi matarsa da kyar take tafiya” Mutumin ya dubi dansa Abdulmalik ya gyada kai, bai ce komai ba. Sidi mai Jaka ya yi shiru sannan ya dubeni ya ce. “Nas, ina fatan kana biye dani akan wannan dogon zaren labari” Na gyada kai cikin kaguwa na ce. “Ina biye da kai baba Sidi, sai dai kuma ni wannan labarin duk jinsa na ke yi kamar sabo daman har yanzu ban ji alakarsa da wannan ba” Sidi Mai Jaka ya dubeni da murmushi sannan ya dubi kwanon tubanin dake gabansa ya cafka daya ya jefa abakinsa ya dube ni. “Nas kenan, amma dai yanzu ai ka isa ka baiwa wani labari, sanin kanka ne in har na sako sabon zaren labari to ko shakka babu in Allah ya yarda sai na hade shi da wancan na baya, shi yasa ba ka gane alakarsu ba, to amma ka jira sannu a hankali lokacin da zaren labarin zai rikida ya koma kan wancan su hade da juna ba zama ka sani ba” “Haka ne, ina to sauraronka” Sidi Mai Jaka ya dada jefa tubani daya a baki ya ce “Dadina da kai kenan Nas, iya sauraron labari, ba ka gajiya da saurare” Na fashe da yar dariya. To ai labarin naka ne wani sa’in dole ma a saurareka domin sai kayi kamar kayi gabas da mutum sai an jima can sai a sameka a yamma” Baba Sidi ya fashe da dariya sannan ya dube ni ya ci gaba da cewa. “Nas, tun daga wannan rana da mai gidan ya sauki dogon mutumin nan da matarsa basu kara barin gidan ba, har sai da ta Allah ta kasance a kansu.” Na dago kaina na dubi Sidi mai jaka cikin sauri na ce dashi. “Kada kace na tari numfashinka baba Sidi, ina da tambaya.” Sidi mai jaka ya dubeni cikin mamaki. “Me kake son tambaya.” Na dubeshi na ce. “Ni tun da ka fara bada sabon zaren labarin, kake ta ambaton wani dogon mutum, da kuma mai gidan daya sauke su, gashi dai ka siffanta su, kace sunan matarsa Hindatu, sunan dan mai gidan daya sauke su Abdulmalik, to shi dogom mutumin da mai gidan ya ya sunansu?” Baba Sidi ya dan yi shiru na dan lokaci sannan sai ya dubeni da murmushi ya ce. “Wani lokacin mutane kan bani mamaki, wai idan kana basu labari dole ne sai ka fadi sunan mutunen,” Sidi mai jaka ya danyi shiru sannan sai ya ce. “Sunan dogon mutumin Saifullahi, mai gidan kuma Alhaji Kabiru. Nas ina fatan ka gamsu.” Na gyada kai na ce “Eh, ci gaba” Sidi mai jaka ya dora daga inda ya tsaya. Washegarin ranar da Alhaji Kabir ya sauki bakin, tayi mutukar faran tawa bakin rai, domin yasa masu gadin gidansa sun bincikesu daga karshe suka gane cewa lallai da gaske yan gudun hijira ne kuma ya ki ne ya koro su. Dan haka sai Alhaji Kabiru ya ce a ci gaba da basu abinci, daga nan har zuwa ranar da matar Saifullahi zata haihu. To amma duk da haka sai da alhaji Kabir ya gana da masu gadinsa a sirrance ya ce suna fa kula da bakin nan, domin mutum na yau ba abin yarda bane domin sai ka dauko mutum daga rana ka sashi a inuwa, shi ko ya tura ka cikin wuta Sidi mai jaka ya dubeni cikin mamaki A haka Saifullahi da matarsa Hindatu suka zauna cikin farin ciki, a karshen watan da suka sauka a gidan ne to wasu sangartattun yan fashi suka ziyarci gidan alhaji Kabir A ranar da yan fashin suka zo tun karfe hudu na yamma ake tafka ruwan sama haka nan yan fashin basu tashi zuwa ba sai ana daf da fara sallar asuba lokacin suka karaso ko shakka babu sun rigaya sun gama sanin abin da za su yi dan haka cikin ruwan sanyi barayin su goma sha tara kamar tururuwa suka cafke masu gadin buzaye cikin ruwan sanyi yayin da tsohon sojan nan ya yi kokarin kawo musu turjiya hakan shi yasa cikin ruwan sanyi suka danne shi suka yi masa yankan rago kai tsaye kuma suka wuce inda Alhaji Kabir yake shi da iyalinsa. “A can bangaren hadiman gidan Saifullahi ya ji idanunsa sun bude ya farka daga nannauyan barci sannan sai ya ji jikinsa ya fara rawa babu gaira babu dalili cikin sauri ya taba matarsa Hindatu. . Matar ta mike zaune cikin firigice, ta dube shi a tsorace da yake har yanzu razanar ya ki bata gama saketa ba. “Me…nene?” Saifullahi ya dubi matarsa ya ce. “Ji na yi haka kawai idanuna sun bude, duk yadda aka yi wani mugun abu ne ke shirin faruwa a gidan nan.” Ya dan yi shiru yana saurare kamar zakara. “Dauko min damarar layuna da guraye na.” Cikin sauri na mamaki ga macen dake da ciki wata uku da kuma magagin barci jikinta, ta mike ta nufi inda tsummokaransu suke ta mika masa jakar gurayen. Cikin yan mintuna Saifullahi ya daura gurayen, sannan ya mike tsaye. “Bari in je in gani.” Hindatu ta dubeshi da murmushin karfafa gwiwa ta ce. “To, Allah kiyaye bacin rana Allah bada sa’a.” Saifullahi ya juya cikin sauri ya fice daga dan dakin. Hindatu ta bishi da kallo, ko kusa ko alama bata fargabar komai, domin ta yi imani da cewa in dai ba karfin kaddarar karar kwana ba, babu abin da zai sami maigidanta, ta riga ta san sirrin dake tattare da gurayen, ta ga yadda suka ratsa ta tsakanin sojojin yan adawa akan iyakar kasarsu, suka tsallako ba a gansu ba, ba a kuma samesu koda da alburushin bindiga guda daya ba duk kuwa da irin barin wutar da ake yi. Saifullahi ya matsa wata katuwar laya mai kamar makami da ke kwibinsa na hannun dama. Sannan ya nufi cikin gidan, ya tabbata a lokacin in ba Allah ba, ko ifiritu bai isa ya ganshi ba. Saifullahi ya hangi barayin daya bayan daya har su goma sha tara sun mammakale a loko-loko guda biyar daga cikinsu tsaye a kofar babban dakin shakatawar gidam. Saifullahi ya zaro wani bakin guru daga kugunsa wani dogo mai kamar maciji ya zagaya barayin dashi har sau biyu, nan da nan barayin suka sankare a gurin basa ko motsi kamar itatuwa. Saifullahi ya barsu a gurin, sannan ya ringa bin barayin daya bayan daya yana zagaya su da gurun ba tare da sun ganshi ba har sai da ya kamar dasu baki daya, sannan sai ya nufi kofar falon, ya zagaye barayin ya kwankwasa kofar dakin shakatawar a hankali. Shiru-shiru bai ji motsin komai ba, Saifullahi ya dada kwankwasa kofar da karfi, har sau goma. Tswon lokaci, sai ya ji kamar motsi an nufo kofar a hankali kamar a tsorace. “Alhaji ni ne…Sanifullah i.” Saifullahi ya ce cikin tattausar muruya. “Saifullahi…l afiya ina masu gadin?” Saifullahi ya tausasa murya ya ce. “Yan fashi ne suka kama su, sun kuma kashe tsohon soja.” Alhaji Kabir ya rike numfashi a tsorace. “Yanzu ina barayin?” Ya tambaya a tsorace. “Gasu anan waje duk na kama maka su.” “Kai kadai Saifullah?” “Kwarai kuwa ai ikon Allah ya fi da haka.” Tsawon lokaci, bai fito ba, can sai ya leko a hankali a tsorace sannan sai ya ja da baya saboda mutanen da ya gani guda biyar duk a sankare kamar itatuwa. “Kada ka ji tsoro Alhaji, kana iya fitowa, babu abin da zasu iya har sai idan na ga dama da ikon Allah, sannan zasu yi motsi.” Alhaji Kabir ya dubi Saifullahi cikin kaduwa. “Jirani to ina zuwa, bari na bugawa yan sanda waya.” Mintuna goma bayan haka gidan ya cika da jami’an tsoro. An kame barayin gaba dayansu, tun daga wannan rana sai Saifullahi ya sami cikakken yanci, Alhaji Kabir ya gama yarda dashi, ya kuma bashi shugabancin masu gadin gidansa. Sannu a hankali watanni suka shude, har cikin Hindatu matar Saifullahi ya isa haihuwa, ran nan da safe sai ta fara nakuda, Alhaji Kabir da kansa ya bada mota a kaita asibiti. Kusan sa’o’i biyu suna jiran labarin haihuwa, a cikin masu jiran akwai Alhaji Kabir, matarsa Hajiya Sa’adatu, Abdulmalik da kuma Saifullahi. A cikin wannan sa’ar ne abubuwa biyu suka faru, farin ciki da bakin ciki, domin Hindatu ta haifi wata kyakkyawar budurwa, mai kyawu na ban mamaki, ita kuwa Hindatu Allah ya yi mata cikawa. Tun daga wannan rana Saifullahi bai sake samun lafiya ba. A ranar da za a radawa jaririyar suna, jikin mahaifinta Saifullahi ya matsa, tun da sassafe ya sa masu gadi suka roki Alhaji da ya zo yana son ganawa da shi domin ba zai iya zuwa da kansa ba. Alhaji kabir ya zo dakin mai gadin cikin gaggawa, Saifullahi ya dago kansa da kyar ya dubeshi ya ce bakinsa na rawa “Alhaji, jikina ya tsananta min, haka nan kuma bana jin zan warke daga wannan rashin lafiya tawa.” Alhaji Kabir ya matsa kusa da mutumin cikin tausayawa ya ce. “Ka da ka ce haka Saifullahi, ai ita cuta ba mutuwa ba ce” Saifullahi ya girgiza kai ya ce. “Ba zan rayu ba Alhaji, domin na ji a jikina, Shi yasa na kiraka domin na baka abu daya da na mallaka a duniya wanda da shi ne kadai zan iya saka maka abin da ka yi min a duniya” Ya dan yi shiru yana mayar da numfashi. “Alhaji a duniya bani da wanda ya fi ka, na dauke ka a matsayin dan uwa, amini, ka mutunta ni, ka taimakeni a lokacin da nake matukar bukatar taimako” Saifullahi ya tura hannunsa cikin wasu tsummokara dake gefensa ya dauko wata tsohuwar jaka ta bakin yadi ya mikawa Alhaji Kabir. “Wannan shi ne kyautar da zan yi maka ta musamman, guru ne, da layu guda uku. Sirri ne na tsarin kai da mahassada, da su ne Allah ya taimakeni na kama barayin nan” Ya dan yi shiru sannan ya ci gaba. “Ga Yata nan jaririya, na baka ita, ka taimake ni dan Allah ka rike min ita, idan an jima in za a sa mata suna, ka sa mata suna Nana firdausi, domin sunan mahaifiya ta ne” Ya fara tari, sannan sai ya yi karfin hali ya dago ya dubi Alhaji Kabir idanunsa na zubar da kwalla. “Alhaji wannan ita ce alfarmar da nake nema, za ka yi min..?” Cikin sauri Alhaji Kabir ya amsa masa. “Na amince Saifullahi, in Allah ya yarda zan rike ta kamar yar da na haifa a cikina kuma ina fatan ma Allah ya baka lafiya” Washe gari da aka yi sunan Firdausi mahaifinta Saifullahi ya bar duniya, a lokacin kwananta takwas kawai a duniya. Bayan an binne Saifullahi, sai Hajiya Sa’adaru ta fito dauke da kyakkyawar jaririyar ta sami maigidanta zaune a falo shi da dansa Abdulmalik, ta zauna kusa da maigidanta, sannan ta kurawa jaririyar idanu ta ce. “Oh, Allah mai yadda ya so, Allah gwanin iya halitta, ka dubi wannan kyakkyawar halitta, kai wallahi Alhaji ina bala’in son jaririyar nan, ba don komai ba. Sai don irin maraicinta, da kuma kasancewar sunan mahaifiyata ne nima aka sa mata” Alhaji Kabir ya dubi matarsa ya ce. “Ki riketa da kyau cikin aminci da kulawa kamar yadda za ki rike danki Abdulmalik.” Hajiya Sa’adatu ta rungume jaririyar ta dubi maigidanta, sannan sai ta dubi kyakkyawar fuskar jaririyar ta ce. “Daga yau kin zama yata, Allah ya raya ki UMMI na” Tun daga wannan rana ne sunan Ummi ya bi wannan jaririya. Sidi mai jaka ya juyo da murmushi ya dubeni. Ni kuma na dubeshi cikin bazata. “Baba Sidi, kana nufin ka ce min wannan jaririyar ita ce Ummi din da Anas ya kamu da ciwon Kauna?” Sidi Mai Jaka ya fashe da dariya ya ce. “Nas kenan, ai daman sai da na fada ma sai na baka mamaki, sannu a hankali zan dawo da kai na jone ma bakin zaren labarin, gashi kuwa tun ma kafin na jone shi din har ka fara ganin alakarsu da wancen tsohon zaren labarin da muka saka” Na dubi Sidi mai jaka cikin kaduwa. “Wai Baba Sidi kana nufin ka ce ita wannan kyakkyawar Ummi din iyayenta ba ma wata tsiya ba ce a garin nan” Sidi mai jaka ya gyada kai ya ce. “Kwarai kuwa Nas, dan ma ka tari numfashina, domin har yanzu zaren labarin bai kare ba, bari in gama saka ma shi, idan na gama zaka fahimci rudanin dake cikin wannan labari” Na gyara zama na dubi Sidi mai jaka cikin doki na ce “Ci gaba, ina saurare” Sidi mai jaka ya jefa tubani daya a baki ya ci gaba.**** Sannu a hankali Nas Ummi ta fara girma kullum ta Allah kyawunta karuwa yake yi. Ba mutumin dake ganinta a waje ba lokaci-lokaci hatta Alhaji Kabir da matarsa Sa’adatu dake ganinta kullum suna mamakin kyawu irin na Ummi Wani abin ban mamaki shi ne tun ranar da aka haifi Ummi kullum a hannun Abdulmalik take wuni yana yi mata wasa. Gashi dai shi ba mace ba amma kullum yana makale da jaririyar dan haka har sa’ar da Ummi ta kai shekaru goma a duniya, duk inda zasu tare suke da Abdulmalik a lokacin nan shi yana da shekaru ashirin a duniya Amma duk da haka kusan tsayin sa daya da Ummi Wani sa’in sai Abdulmalik ya dauki Ummi a mota su yi ta yawo kantuna-kantuna inda ake sayar da kayan lashe-lashe da makulashe idan sun je sai Abdulmalik ya juyo ya kalli Ummi cikin fara’a a tausashe ya ce “Ummi, dauki duk abin da ki ke so” Cikin farin ciki da kauna irin ta dan uwa sai ta dubeshi ta ce “Abdulmalik kana shagwaba ni!” A duk lokacin da ta ce haka sai Abdulmalik ya ji zuciyarsa ta dada narkewa da begenta domin tun ranar da aka haifi Ummi Abdulmalik ya fara sonta tun ma bai san mene ne kauna ba. Don haka sannu a hankali shekaru na shudewa har wannan son ya juye zuwa kauna. To sai dai kuma abin da Abdulmalik ya kasa fahimta shi ne a duk tsawon zamanin nan Ummi a matsayin dan uwanta na jini ta daukeshi domin bata taba sanin cewa ba uwarsu daya ba ubansu daya ba. Abdulmalik ya riga ya fi kowa sanin cewa Ummi ba yar uwarsa ba ce ta jini Domin shi ne ma ya yi sanadiyyar haihuwarta a gidan, to amma daidai da rana daya bai taba nuna mata alamu ba A bangaren iyayen Abdulmalik kuwa sun dade suna kallon irin alakar mai karfi dake kulluwa tsakanin yaran guda biyu, koda yake ga zuciyar Alhaji Kabir bai taba daukar alakar yaran a bakin komai ba face kawai sabo da kuma yan uwantaka. . To amma ranar wata laraba da yamma sai matarsa Sa’adatu ta dubeshi ta ce. “Alhaji, wai kuwa kana lura da al’amarin yaran nan?” Maigidanta Kabir ya dubeta cikin mamaki. “Kamar ya ya ina lura dasu? Wannan ai dole ne domin kuwa yayana ne.” Sa’adatu ta dubeshi cikin yar damuwa ta ce. “Ba abin da nake nufi kenan ba.” “To me ki ke nufi?” Sa’adatu ta gyara zama ta ce. “Wato ni gani na ke yi kamar Abdulmalik kaunarta ya ke yi.” Alhaji Kabir ya dubeta baki bude cikin mamaki ya ce. “Yau ga ikon Allah, to daman mutum ba dole ne ya kaunaci dan uwansa ba.” Sa’adatu ta girgiza kai. “Abin ya wuce da haka ina tsammanin begenta ya ke yi.” Alhaji Kabir ya kura wa matarsa idanu na tsawon lokaci, sannan sai ya yi kasa-kasa da murya ya ce. “Kada fa ki manta cewa, har yanzun nan Ummi ba ta san cewa ba mune iyayenta ba.” Sa’adatu ta yi murmushi. “Idan ita ba ta sani ba, ai shi Abdulmalik ya san ba yar uwarsa ba ce ta jini. Kuma abin da ya sa ka ji na fada ma haka shi ne, yanzu da ka leka cikin dakinsa za ka ga duk ya zagaye shi da hotunan Ummi, kowannensu ya rubuta (My love) Alhaji Kabir ya dada duban matarsa na tsawon lokaci, akwai alamun tunani a fuskarsa, can sai ya yi ajiyar zuciya ya ce. “To, sai mu bar wa Allah komai, ya yi ikonsa, Allah zaba musu abin da ya fi alkairi.” . A bangaren Abdulmalik, sannu a hankali har Ummi ta kai shekaru goma sha bakwai. Kullum wutar begenta sai dada ruruwa cikin zuciyarsa take yi, ita ko in ka dauke soyayya irin ta yan uwantaka bata dauke shi a bakin komai ba. Amma duk da haka nan dai kullum suna tare basa rabuwa. Wata rana da yamma Ummi ta shiga dakin Abdulmalik ta ci kwalliya, fes,fes, hakan shi ya sa zuciyar Abdulmalik harbawa. A ranar ne to Abdulmalik ya ji kamar ya amayar mata da boyayyen sirrin zuciyarsa, to amma sai ya tuna kashedin da mahaifinsa ya yiwa duk wani mutum dake gidan inda yake cewa. “Kada wani daga cikinku ya sake ko da da wasa ya fadawa Ummi cewa mu ba iyayenta ba ne.” Wannan shi ya sa Abdulmalik hadiye maitarsa. Zuciyarsa na harbawa ya dago kai ya dubeta cikin yabawa da abin da ya gani ya ce. “Kai, amma fa kin kara kyau Ummi.” Ummi ta dube shi cikin dariya ta ce “Na gode yaya Abdul.” Ta dan yi shiru tana kallon jeren hotunanta ko ina a cikin dakin sannan ta dubi Abdulmalik ta ce. “Duk duniya babu yan uwan dake kaunar juna kamar mu, dubi fa Yaya Abdulmalik duk ka bi ka wani shagwaba hotunana kamar wata budurwarka. Wannan ko budurwa ce ai ba karamin kaunarta kake yi ba.” Abdulmalik ya sunkuyar da kai da dan murmushi, wata zuciya na cewa da shi, fada mata kawai cewa ita fa ba yar uwarka ba ce ta jini. To amma sai gargadin mahaifinsa ya sake dawowa zuciyarsa dan haka sai ya dago kai ya dubi Ummi da Murmushi ya ce. “Ummi kenan. Ina za ki ne na ga kin caba kwalliya haka?” Ummi ta dube shi da murmushi sannan ta ce. “Ina zani, ko dai ina zamu, bikin taya murnar ranar haihuwar wata kawata zaka rakani.” Abdulmalik ya dubeta cikin mamaki ya ce. “Kin manta ne cewa ina da jarrabawa ta karshe a makaranta, kin san ina bukatar karatu.” Ummi ta yi sauri ta rufe fuska cikin dariya. “Oh! Dan Allah Yaya Abdulmalik ka yi hakuri, wallahi mantawa na yi ashe kana da jarrabawa gobe.” Abdulmalik ya mike tsaye. “Mu je na raka ki sai na dawo.” Ummi ta mike tsaye ta dube shi ta ce. “Wallahi nima dan muna bala’in mutunci ne da MABRUKA da ba zan je ba tun da kaima ba za ka ba.” Abdulmalik ya yi murmushi. “Ai ba komai. Yaushe zaki dawo?” Ummi ta lumshe idanu ta dan daga kai sama. Abdulmalik ya kurawa wasu siraran zane guda uku da suka yiwa kyakkyawan wuyanta kawanya. “Nan da karfe tara na dare zamu dawo.”*** . Sidi Mai Jaka ya dubeni ya ce ina fatan kana fuskantar inda labarin ya dosa da kyau? Na gyada kai cikin sauri. “Ina fuskanta.” Sidi Mai Jaka ya ci gaba. A daren ranar da Ummi ta dawo daga walimar bikin zagayowar haihuwar Mabaruka ne to Abdulmalik ya fara ganin canjin yanayin karara a fuskar Ummi Karfe tara na dare da yan mintuna ta dawo, Abdulmalik ya ji shigowarta babban falo dan haka sai ya ji wani farin ciki ya lullubeshi domin tuntuni ya matsu da ya ga ta dawo domin baya iya yin sama da sa’a biyar bai ganta ba Wani sa’in ko a makaranta yake sai ya yi ta bugo mata waya duk bayan sa’a guda dan kawai ya ji muryarta Don haka sa’ar da ya ji motsin dawowar Ummi sai ya ajiye takardun bokon da yake karantawa ya lumshe idanu yana jiran shigowarta domin ya san alkawari ne sai ta shigo dakin. Tsawon lokaci shiru babu motsin UmmiDomin ya san alkawari ne sai ta shigo dakin. Tsawon lokaci shiru, babu motsin Ummi sannu a hankali har mintuna talatin suka shude bata shigo dakin ba. Abdulmalik ya mike tsaye cikin tsananin damuwa da mamaki domin a iya saninsa da Ummi ko kayan jikinta ba zata sauya ba sai ta zo gare shi su yiwa juna Sallama Cikin sauri Abdulmalik ya fita daga dakinsa ya ratsa ta falo ya nufi dakin Ummi. Abdulmalik ya dan kwankwasa kofar dakin a tausashe sannan sai ya yi sallama ya shiga. Ummi na kwance akan gado, sanye da kayan da ta fita da su walimar, ko cire su bata yi ba, ta kurawa saman dakin idanu bata ko kiftawa kamar mai kallon allon sinima. Abdulmalik ya tsaya cak a tsakiyar dakin kamar an dasa shi, ya kurawa Ummi idanu cikin tsananin mamaki da kaduwa domin ya fahimci ashe Ummi bata san ma ya shigo dakin ba. “Ummi…” Ya sake maimaitawa a karo na biyu kamar mai biya karatu. Ummi ta juyo firgigit ta tashi zaune akan gadon. Ta dubi Abdulmalik. “Tunanin me ki ke yi haka?” Ummi ta dubeshi da murmushi. “Ka yi hakuri don Allah Abdulmalik wallahi ban san ka shigo ba.” Abdulmalik ya matsa kusa da ita ya zauna daga can nesa da ita a bakin gadon ya kura mata idanu. “Na ji shigowarki, ina ta jira ko za ki zo, ba ki zo ba shi ne na ce bari ni nazo da kaina na gani ko lafiya.” Ummi ta sunkuyar da kai sannan ta yi ajiyar zuciya kana ta dago kai da murmushi ta dubi Abdulmalik ta ce. “Lafiya lau Yaya Abdulmalik bala’in gajiya na yi.” Tun kafin ta gama fada Abdulmalik ya san karya take yi, domin alamun damuwar dake fusakarta tamkar bakin rubutu ne akan farar takarda. Abdulmalik ya ji zuciyarsa ta sosu, bai ji dadin abin da ta fada ba, domi a duk iya tsayin zamani, tun ranar da aka haifeta ya fara daukarta, har zuwa yau bata taba fada masa karya ba sai yanzu. Abdulmalik ya dubi Ummi cikin shakka, ya girgiza kai ya ce. “Kada ki ce haka Ummi, ba gajiya ba ce kawai ke damunki akwai matsala ta daban.” Ummi ta dubeshi da wani fatalwan murmushi akwai alamun kunya a fuskarta ta ce. “Gaskiya ne Abdulmalik wallahi akwai abin dake damuna, ka kuma yafe min dan Allah ka san ban taba yi ma karya ba sai yau…” Ta dan yi shiru tana murmushi sannan sai ta dada da cewa. “Yau din ma kunya ce wallahi ta sa ni yin karya.” Abdulmalik ya yi ajiyar zuciya kana ya dubeta cikin shauki ya ce. “Na yafe miki Ummi…ai kin san duk laifukanki a gurina yafaffune har ma da wanda ba ki yi ba.” Ummi ta yi dariya ta sake sunkuyar da kai Abdulmalik ya sake nazarin fuskar Ummi cikin damuwa ya ce. “Fada min sirrin dake zuciyar ki Ummi me ke damun ki ne?” Ummi ta dauke kai gefe guda na tsawon lokaci, haka nan a duk iya tsayin wannan lokaci akwai alamun murmushi-murmus hi da kuma damuwa-damuwa a fuskarta. Shi dai Abdulmalik ya kura mata idanu cikin mamaki bai tari numfashinta ba. Tsawon lokaci, sannan Ummi ta juya ta dubeshui, ta ce bakinta na rawa. “Yaya…..Abdul malik…wallahi irin abin da nake yawan karantawa ne a cikin littattafan labarai na Hausa ya faru a kaina.” Abdulmalik ya ji gabansa ya fadi ras! Ya dubi Ummi. “Me ki ke nufi.” Ummi ta dauke kai gefe guda a kunyace ba tare da ta hada idanu da shi ba ta ce. “Wallahi…wani na gani a gurin liyafar nan naga ya burge ni.” Abdulmalik ya ji zuciyarsa ta harba. “Har yanzu ban fahimce ki ba Ummi, waye wani, kuma ya burge ki kamar ya ya.” Ummi ta sake dariya ta ce. “Yaya Abdulmalik ji na yi wallahi ina masifar kaunarsa a zuciyata, a yanzu din nan haka ji nake yi kamar mun dade da sanin juna.” Ta dan yi shiru ganin Abdulmalik bai ce wani abu ba sai ta dada da cewa “Za ka yi mamaki idan na ce da kai Mabaruka ce kawai ta turani na yi kiransa.” Abdulmalik ya dago kai ya dubeta da murmushin karfin hali, amma a badini tuni har zazzabi ya rufe shi “Ummi kenan. To yanzu ya ya za ki yi kenan? Kin ga mutum kin ce kina sonshi amma ba ki san ko wane ne shi ba ba ki san inda yake ba baki san ko da sunan shi ba.” Ummi ta matso kusa da Abdulmalik ta ce “Ma’aikacin otal din da aka yi liyafar ne, na ji Mabaruka ta kira shi da suna ANAS!” Abdulmalik ya sunkuyar da kai Ummi ta dubeshi cikin damuwa. A tunaninta halin da ta tsinci kanta ciki ne ke damun Abdulmalik domin ta san irin yadda yayan nata Abdulmalik ke matukar sonta don haka sai ta ce dashi a tausashe “Ka da ka dami kanka Yaya Abdulmalik na san duk abin da ya shafe ni kai ya shafa. Ni dai abin da nake so shi ne ka tayani don Allah mu same shi ka ga kaunarsa” Ta dan yi shiru sannan sai ta dubi Abdulmalik ta ce “Kana jin kuwa zai iya kaunata?”*** Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya dubeni da murmushi sannan ya dubi tubanin Tubanin dake gabansa cikin damuwa domin tuni ya hadiye sama da kashi uku bisa hudun tubanin A zuciya ta na ce kai wannan tsoho da cin tsiya yake domin na tabbata yawan tubanin da ya hadiya tun daga rana zuwa yanzu ya ishi katti goma su ci su koshi amma sai gashi shi kadai duk ya hadidiye su kamar rumbu “To Nas ka ga abin da nake fada maka tun farko ko? Sai da na ce da kai ni ne mai saka labari kamar injin saka, na hade ma shi guri guda, gashi kuwa sannu a hankali na nuna maka alakar zarurrukan labarin guda biyu.” “Haka ne Baba Sidi.” Na ce dashi Sidi mai jaka ya canko wani katon tubani mai kama da dankali ya gutsiri rabi, sauran ya fado a cikin kwanon Sidi mai jaka ya dubeni ya ce. “Nas, wannan shi ne karshen wannan dogon zaren labarin, yanzu abin da ya rage shi ne na gaggauta na daura ma bakin zarurrukan labaran guda biyu kafin nan da sallar magariba, domin bana son labarin ya kai mu har bayan sallar magariba.” Na yi sauri na gyada kai na ce. “Ni ma ai na fi son haka.” Sidi mai jaka ya gyada kai ya ce. “To Nas, bari yanzu ne zan koma kan wancan tsohon zaren labarin da muka bari lokacin da zamu tafi sallar azuhur, inda mauka baro Anas yana karatun wasikar da Ummi ta bashi.” Ya dubeni ido da ido. “Ka tuna da gurin?” Na gyada kai na ce. “Kwarai kuwa, ba inda ka ce har ma yana jiyo kukan matarsa Mabaruka ba daga cikin bandakin?” Sidi Mai jaka ya fashe da dariya yace. “Nas kenan, da ace yadda kake rike labari a kwakwalwarka haka nan kake rike karatu da ba karamin malami za a yi ba wata rana, to sai dai kuma na fahimci kamar kwakwalwarka ta fi iya rike labari fiye da komai.” Nima sai na fashe da dariya, na ce. “Baba Sidi kena.” Sidi mai jaka ya yi gyaran murya sannan ya ce. “Nas, dauki zuciyarka cancakat ka mayar da ita cikin bandakin nan, inda muka baro Anas dazu yana karatun wasikar da Ummi ta bashi.” “Na mayar.” Na ce dashi. Yauwa Nas. Anas ya ci gaba da juya takardar a hannunsa, zuciyarsa dauke da abubuwa guda uku masu kama da kishiyar juna. Ka ga na farko dai akwai farin ciki, domin Anas bai san abin da zai iya kwatanta farin cikinsa da kalmar Ummi ba, inda tana kaunarsa da kanta. Na biyu akwai tsana mai tsanani cikin zuciyarsa, domin a yanzu duk duniya babu abin da ya tsana kamar matarsa Mabaruka. Domin tuni Anas ya riga ya san wannan mummunar gurguwa ita kadai ce katangar karfen dake tsakaninsa da babbar masoyiyarsa Ummi. Abu na uku kuwa dake dafe a zuciyar Anas shi ne tsananin fargaba, don Anas ya tabbata sai dai ya zabi tsakanin mummunan aski da sa kai a wuta, domin muddin ya ci gaba da mu’amula da Ummi, rabuwarsa da Mabaruka ta zo kenan, shi ko ya san a yanzu koma me yiwuwa har abada Mabaruka ita ce babbar rumfar da ta rufe kansa da inuwa ta yi masa katanga da zafin ranar talauci. Wadannan abubuwa guda uku su suka hadu suka cunkushe zuciyar Anas, don haka yana nan bandakin yana maimaita karatun wasikar Ummi har sai da ya karanta ta sau kusan talatin. Bai tashi komawa dakin kwanan su ba sai da ya tabbata a lokacin Mabaruka ta gama fushinta ta yi barci. Anas ya nufi dakin kwanansu cikin sanda, a lokacin kusan biyu da rabi ne na dare. Ko kusa ko alama baya son ya sami Mabaruka ido biyu bata yi barci ba, domin Anas ya gama gajiya da ita, kai hatta muryarta baya son ji. Murya daya ce kawai ke yawo cikin kwakwalwarsa muryar Ummi. Anas ya yi boyayyiyar ajiyar zuciya sa’ar da ya tura dakin kwanan nasu ya shiga. Domin ya ga a cikin duhu yake. Tabbas ta yi barci, Anas ya ce cikin zuciyarsa Sannu a hankali ya sauya kayan dake jikinsa sannan ya lallaba ya haye bisa gadon ba tare da ya yi wani kwakkwaran motsi ba ya kwanta haka nan bai ma yarda koda jikinsa ya taba jikinta ba Anas ya yi lamo kamar ya mutu gashi dai baya ko motsi amma idanunsa a bude yake garau Zuciyarsa dauke da hoton kyakkyawar surar Ummi Yana nan kwance zuciyarsa fari fat lokaci guda kuma yana tunanin hanyar da zai bi a gobe ya gujewa Mabaruka domin ya sami damar ganawa da Ummi Anas na nan cikin wannan haki can sai ya ji agogo ya buga karfe daya sannan ne fa ya ji abin da yasa gashin jikinsa mimmikewa tsaye “Anas.” Muryar Mabaruka ta ratsa duhun dake dakin ta daki dodon kunnensa. Anas ya zabura cikin kaduwa Bai taba tsammanin Mabaruka ba barci take yi ba. “Mab…Mabaruka …dama ba barci ki ke yi ba.” Mabaruka ta yi ajiyar zuciya ta ce a sanyaye cikin karayar zuciya. “Ya zan iya barci Anas bayan kana fushi dani.” Hakan kawai da ta ce sai Anas ya ji dan tausayinta ya kamashi.Ya zan iya barci Anas, bayan kana fushi dani.” Hakan kawai da ta ce sai Anas ya ji dan tausayinta ya kamashi. Don haka sai ya yi karfin hali ya ce. “Ki yi hakuri Mabaruka…wann an duk wani al’amari ne na rudin shaidan.” Ga mamakin Anas sai ya ji Mabaruka ta yi wani irin nannauyan ajiyar zuciya, sannan sai ta juyo shi ta rungume shi ta kankameshi ta ce. “Ka yafe min Anas, ka kuma manta da duk abubuwan da na fada ma na bakaken maganganu, wallahi masifar kaunarka da kishinka ne suka sani…” Ta yi shiru tana numfashi sama-sama daga nan bata kara cewa komai ba, a haka barci ya dauke ta hannayenta kankame da jikin Anas babban masoyinta a duniya. Shi ko Anas, yadda ya ga rana haka ya ga dare bai runtsa ba. Ga dai Mabaruka rungume da shi cikin shaukin bege, amma shi ji yake yi kamar a rungume yake da kaya. Washe gari da safe suna karin kumallo sai Anas ya fuskanci duk da yake dai ba cikin fushi Mabaruka ta tashi ba amma babu alamar walwala sosai a fuskarta haka nan da kyar ta kai abinci sau biyu bakinta. Ka bi ta a hankali dan samari wannan gurguwa ita ce babbar inuwar rayuwar ka Wata zuciya ce ke baiwa Anas Shawara Wata zuciya ce ke baiwa Anas shawara. Anas, ya mike tsam daga inda ya ke ya koma kusa da Mabaruka ya zauna, sannan ya dauki yan siraran hannayenta ya rikesu a tausashe ya sa alamun damuwa na karya a fuskarsa, sannan sai ya matsa da bakinsa kusa da kunnen ta ya ce. “Mabaruka…me ke damunki ne, na ga duk kamar ba kya cikin walwala, ko har yanzu fushin ki ke yi dani? Ba na nemi afuwar ki yafe min ba?” Mabaruka ta langabe kai duk da yake dai bata yi masa murmushi ba, to amma fuskarta ta nuna alamun jin dadin tarairayar da ya yi mata. “Anas, wallahi zuciyata ce ke cikin fargaba.” Anas ya dubeta cikin mamaki, sannan ya matse hannayenta a cikin nasa ya ce. “Fargabar me kuma, Mabaruka? Kina da kudi da duk wani jin dadin duniya da ki kebukata, tun da dai Allah ya hore miki dukiya, haka nan kuma kina da ni, ga ni kusa da ke, to mene ne kuma na fargaba?” Mabaruka ta dago kanta ta dubi Anas cikin mamaki ta ce a sanyaye. “Ina da kai fa ka ce?” Anas ya gyada kai ya ce. “Kwarai kuwa kina da ni, ni ba mijinki ba ne?” Mabaruka ta dan lumshe idanu sannan sai ta bude su ta dubi Anas. “Ka ga ni kuwa fargabar da nake yi gani nake yi kamar kwace min kai za a yi, rabuwarmu ta zo.” A wannan dan takin lokacin da take kalamin sai Anas ya ji tausayinta ya sake kama shi a karo na biyu. Tabbas ya san batunta gaskiya ne, domin tuni ma in dai batun soyayya ne an riga an raba su, abinda ya rage tsakaninsa da ita a yanzu shi ne auren kaddara. “Ka da ki ce haka Mabaruka, bai kamata ba irin wadannan kalamai marasa dadi suna fitowa daga bakin ki.” Anas ya dauke kai gefe guda fuskarsa cikin damuwa. Da ace za ka ga fusakarsa a lokacin, mutum sai ya rantse da Allah cewa abin da yake fada har zuciyarsa haka nan yake. Mabaruka ta yi wata kwakkwarar ajiyar zuciya ta dubi Anas. “Ba ni lemo na sha.” Anas ya mike cikin sauri ya tsiyayo mata tacaccan lemo cikin kofin alfarma sannan ya zauna kusa da ita kana ya dan janyota jikinsa ya kara mata kofin a bakinta Cikin farin ciki mara misaltuwa Mabaruka ta fara shan lemon kadan-kadan har sai da ta shanye gaba daya. Abin ya baiwa Anas mamaki domin bai taba ganin ta yi haka ba. Amma ga Mabaruka hakan da ta yi akwai dalili mai karfi dalilin kuwa shi ne rabon da Anas ya yi mata irin wannan tarairaya tun daren amarcinsu na farko “Lemon ya ishe ki ko na karo miki?” Anas ya tambayi Mabaruka a tausashe Mabaruka ta dubeshi da murmushi a karo na farko ta girgiza kai “Ya ishe ni.” Ta dan yi shiru sannan sai ta ce “Ina ma ace kullum haka muke da na fi kowa farin ciki a duniya” Anas ya sunkuyar da kai gami da murmushin yake shi kansa kunyar hada ido yake yi da ita domin a zuciyarsa cewa yake yi ina ma wannan tarairayar da yake yiwa Mabaruka ace Ummi ce Abin da Mabaruka ba ta sani ba shi ne duk wannan tarairaya da Anas ke yi mata kokari yake yi ya sami hanyar da zai bi ya sulle ya ziyarci Ummi “Daga yanzu zan manne ma kamar cingam duk inda za ni muna tare.” Kalaman Mabaruka suka fado zuciyarsa Anas ya ji gumi ya fara tsiyaya ta bayansa duk kuwa da cwa wayewar gari kenan kuma koda ma babu sanyin iskar safiya akwai na na’urar sanyaya daki. “Tunanin me ka ke yi Anas?” Mabaruka ta tambayeshi babu zato babu tsammani ashe duk abin da yake yi tana lura da fuskarsa Adaida lokacin ne to wata dankareriyar karya ta darsu a zuciyar Anas ya riga ya san ita ce damar sa ta karshe ta samun damar zuwa gurin Ummi dan haka sai ya dubi Mabaruka ya ce a tausashe. “Kin san ina da abokai a cikin gari da yawa wadanda rabon da mu gana dasu tun kafin na aureki shi yasa ki ka ga na shiga cikin damuwa saboda ina fargabar kada su ga kamar dan na sami canjin rayuwa ne shi yasa na watsar da su.” Mabaruka ta dan yi shiru na lokaci tana kallon kofin da ke gabanta. Zuciyar Anas ta fara harbawa da karfi, yana jiran ya ji abin da za ta ce, ya san idan ta ki amincewa bashi da damar ganin Ummi, haka nan kuma idan tare zasu fita nan ma bashi da damar zuwa gurin Ummi kenan. Tsawon lokaci, sannan Mabaruka ta dubeshi a tausashe ta ce cikin murmushi. “Kuma ka ki ka sanar dani tun dadewa ko tsorona ka ke ji?” Ta dan fashe da dariya. Jin haka shi ya sa Anas ya washe baki har kunne, zuciyarsa kamar ta fasa kirjinsa saboda doki. Anas ya dada rungumo Mabaruka. “Ya ya zan ji tsoron matata?” Wannan abu da ya fada shi ya kara narkar wa da Mabaruka zuciya, cikin sauri ta dubi Anas. “Yaushe za ka je ku gaggaisa da abokan naka?” Anas ya yi sauri har zai ce yau, sai wata zuciya ta ce dashi bi a hankali Anas, wannan nannadaddiyar matar ta fi ka wayewa. “Duk lokacin da ki ka ce Mabaruka haka za a yi, in ma kina ganin za ki iya jure shiga gargada da kwari da tudu irin na unguwanninmu na yan Allah baku mu samu sai mu tafi tare ki rakani, domin ba na son rabuwa da ke.” Mabaruka ta dage kai cikin murmushi, sannan ta girgiza kai ta ce. “A’a ni ba zan iya shiga gargada ba, kana ganin ma so nake yi mu tafi london hutu, amma rashin doguwar tafiya a jirgi ya hanani” Ta dan yi shiru. Zuciyar Anas sai harbawa take yi yana jiran ya ji abin da za ta ce. “Anas.” Ta kira sunansa a sanyaye. “Na’am, Mabaruka.” Anas ya amsa cikin kwararren murmushinsa na mayaudara. Mabaruka ta ce. “Idan ka tafi kamar karfe hudu na yamma sai yaushe za ka dawo?” Anas ya dan yi jim sannan sai ya dube ta, ya ce. “In ba dan abokan nawa suna da yawa ba da sai in ce dake karfe takwas ma ina gida, to amma me yiwuwa na kai har wajen tara.” Ya dubeta ido da ido. “Babu damuwa?” Mabaruka ta kama hannunsa cikin farin ciki ta gyada kai ta ce. “Na kara ma awa daya, amma kada ka wuce karfe goma, domin ko ruwa ba zan sha ba sai ka zo ka ba ni.” Ta dan yi shiru tana duban Anas, suka yiwa juna murmushi. “Idan za ka fita sai ka dauki motata shudiyar lexus din nan, kada abokan ka su raina min kai!” *** Sidi mai jaka ya dubeni babu ko saurarawa ya ce. A can gidan su Ummi, Abdulmalik ya tsinci kansa cikin damuwar da bai taba shiga irinta ba, domin kwanansa guda cur) babu dare ba rana, yana ta faman rubutu ne. Na dubi Sidi mai jaka cikin mamaki. “Rubutun me kuma?” Sidi mai jaka ya ce. “Saurareni da kyau ka ji dalili.” Ka ga Nas, tun ranar da Ummi ta halarci liyafar gidan Mabaruka, inda ta baiwa Anas yar rubutacciyar wasika, tana komawa gida sai ta wuce kai tsaye zuwa dakin dan uwanta Abdulmalik. “Yaya Abdulmalik.” Ta kira sunansa tun daga kofar dakin cikin doki da farin ciki. Abdulmalik ya dago kai cikin damuwa ya dubi kyakkyawar fusakarta domin ya san labarin da ta zo dashi ba zai taba faranta masa ba. Daman tun da yamma kafin ta tafi sai da ta sameshi ta ce. “Yaya Abdulamalik…M abaruka ta gayyace ni liyafa a gidanta.” Abdulmalik ya boye kunar zuciyarsa ya dubeta da murmushin da bai kai zuci ba. “Ki ce yau kin sami damar ganin mutumin na ki.” Ummi ta sunkuyar da kai. “Uhm, shi da ma yake da mata, ni na san ma ai zai yi wuya in zai kulani.” Abdulmalik ya ji zuciyarsa kamar za ta fashe. “Namiji ai na mace hudu ne.” Ummi ta gyada kai ta ce. “Yanzu yaya Abdulmalik idan mun hadu da shi ya ya zan yi?” Abdulmalik ya dube ta ya ce. “Duk da yake dai nima ba sanin irin al’amuran soyayyar nan na yi sosai ba, to amma ina ganin tunda dai ke mace ce, ba za ki rasa dabarar da za ki bi ba wajen nuna masa cewa kina kaunarsa. Sai dai kuma ki bi a hankali kada babbar kawarki ta kamaki kina kokarin sace mata miji.” Suka fashe da dariya, A haka suka rabu. Wannan shi ya sa lokacin da ta dawo sai ta shiga dakin cikin farin ciki ta zayyanawa Abdulmalik duk abin da ya gudana tsakaninta da Anas “Yaya Abdul kana jin zai zo gobe din kuwa?” Abdulmalik ya ji murmushinsa ya fara daukewa “Me zai hana, tun da dai idan aka yi la’akari da abin da ki ka ce shima ashe ya dade yana kaunar ki” Ummi ta yi tsalle a tsakar dakin ta dire cikin farin ciki ta ce. “Wallahi Yaya Abdul ba ka ga yadda na ruda shi ba jikinsa har rawa yake yi” Abdulmalik ya cije baki sannan ya dage kai. Ummi ta daina tsallen da take yi ta dube shi cikin damuwa. “Yaya Abdul…ba ka da lafiya ne na ga kana cije baki?” Abdulmalik ya dubeta. “Kaina ne ke sara min da ciwo tun da safe” Ummi ta dube shi cikin.TSOHON ALKAWARI-14 . “Kaina ne ke sara min da ciwo tun da safe” Ummi ta dube shi cikin damuwa. “Bari in dauko ma magani” Abdulmalik ya yi sauri ya girgiza kai. Sannan ya yi mika. “Ina tsammanin gajiya ce ta yi min yawa, na san idan na sami isasshen barci zan warware zuwa safe” Ummi ta kura masa idanu cikin damuwa na tsawon lokaci. “Bari to na tafi na barka ka huta, domin zuwa na yi mu yi bankwana, na kuma fada ma cewa gobe ne da daddare muka yi dashi zai zo…in dai zai zo din” Ta mike tsaye. Abdulmalik ya dubi kyakkyawar fuskarta. “Ina taya ki fatan alheri Allah ya sa ya zo din” Ummi ta yi murmushi ta ce. “Ameen Yaya Abdul, Allah ya karbi addu’arka, wallahi yau da kyar zan yi barci” “Ai ba ke kadai ba” Abdulmalik ya ce cikin zuciyarsa. “Sai da safe Yaya Abdulmalik.” Ummi ta ce da faffadan murmushi. Sannan sai ta fice daga dakin. Tana fita sai Abdulmalik ya kifa kai akan cinyarsa, ga mamakinsa sai ya ji wani zazzafan hawaye ya fara kwaranya akan fuskarsa. Yana nan zaune har karfe biyun dare ta gota barci bai samu ba, domin Abdulmalik ya riga ya san cewa idan ya yi lako-lako yana ji yana gani kwado zai leko daga tafki ya yi masa kafa ya koma. Tabbas idan ya yi wasa yana ji yana gani Ummi, abin da ya fi kauna fiye da komai a duniya za ta sulale ta tsakanin yan yatsun ikonsa. A lokacin ne to dabarar ta fado zuciyar Abdulmalik. A kullum zuciyarsa kan fada masa cewa hanya daya ce kawai zai bi ya magance wannan bala’i dake kokarin afka masa. Ita ce ya kira Ummi ya yi mata bayanin cewa ita fa ba yar uwarsa ba ce ta jini, ya kuma yi mata bayanin irin yadda ta shige zuciyarsa. To amma kashedin mahaifinsa shi ke taka masa birki. Wata zuciyar ta kan ce dashi me zai hana ka sanar da mahaifiyarka halin da ake ciki. Kunya ba za ta bari ba. Ita ce amsar da Abdulmalik ke fadawa zuciyar tasa. Yana cikin hakan ne to ya kasa barci, kawai sai dabara ta fado masa Abdulmalik ya dauko littafin rubutu, mai shafi dari da sittin, ya dauki biro ya fara rubuta labarin tun farkon haduwarsa da marigayi Saifullahi mahaifin Ummi. Sidi mai jaka ya dubeni da murmushi “Nas, wannan labari da Abdulmalik ya rubuta shi ne sanadiyyar duk wani labari da nake baka a halin yanzu.” “Kamar ya ya kenan, ban fahimce ka ba Baba Sidi?” Na ce dashi. Sidi mai jaka ya ce. “Za ka fahimce ni ne, amma sai nan gaba, kai dai rabu dani na karasa labarin nan, na ga magriba ta karaso, bana son labarin nan ya kaimu har bayan isha.” ya dauki tubani ya jefa a baki sannan ya ci gaba. Washe gari tun kafin magariba Ummi ta shiga wanka, ba ita ta fito ba sai karfe shida da rabi. Bayan ta yi sallah sai ta shiga kwalliya, sai da ta shafe sa’a guda tana kwalliya. Bayan ta gama shafe-shafe da feshe- feshen turare, sai ta wuce kai tsaye zuwa dakin Abdulmalik domin tun da safe suka yi dashi cewa shi ne zai rakata hirar, domin Ummi ta ce dashi ba ta son a san alakar a cikin gida har sai Anas ya zo a kalla sau uku. “Har kin shirya kenan?” Abdulmalik ya dubeta cikin karaya. Ummi ta yi murmushi ta dubeshi ta ce. “Dubanni da kyau Yaya Abdul…dan Allah na yi kyau? Idan ban yi ba fada min na yi sauri na sake shiga kada ya zo ban gama shiryawa ba.” Abdulmalik ya kurawa kyakkyawar halittar idanu. Ba wai yana kallon Ummi bane don ya ba ta amsar tambayar da ta yi masa ba, yana kallonta ne da idanun bege da tsananin shaukin ina ma ace shi ya mallake zuciyar ta baki daya. Kai wannan Anas da sa’a yake a duniya. Abin da ya fi damun Abdulmalik da kuma bashi mamaki shi ne, wai shin shi wannan Anas din kamar ya ya yake, wane irin kyawun siffa ce dashi, ko kuma Ilimi, ko kuma dadin baki, da har wannan kyakkyawar ta mace da tsananin kaunarsa. “Ya ya ka ganni Abdulmalik, na yi kyau?” Zazzakar muryar Ummi ta sake ratsa kunnen Abdulmalik. Ya yi ajiyar zuciya ya ce. “Kin yi kyau wallahi sosai ma kuwa.” Ummi ta yi tsalle cikin murna ta ce. “Har na ji dadi wallahi, tashi to mu tafi.” Abdulmalik ya mike tsaye da kyar kamar ya hadiyi tabarya sannan ya ce. “Idan momi ta tambaye kin inda za mu ki ce da ita kanti zamu je siyayya.” *** Karfe takwas saura kwata na yamma Anas ya shigo titin a cikin katuwar motar shudiya kirar Lexus yana tafe yana bin wakar kidan turawa abinsa cikin farin ciki da wannan rana. Tun da ya auri Mabaruka bai taba samun yanci irin na wannan rana ba. Ga shi dai daman tun ranar da ya aureta ya yi tsalle ya fice daga kurkukun talauci ga motocin hawa sai wacce ya zaba ga sutura Kusan kullum sai ya sa sabon kaya na yamma daban na safe daban. Ga aljihunsa a cike taf da mikakkun takardun kudi na kashewa, amma duk a banza bai jin dadinsu ba don kome ba kuwa sai dan wannan nacacciyar gurguwa kamar yadda ya kirata, wacce ke manne da shi kullum kamar cingam. Dan haka a yanzu da ya shigo cikin titin sai ya dubi kujerar motar dake hannun damansa cikin farin ciki domin yau Allah ya raba shi da cingam, lokaci guda kuma sai ya dubi takardar da ke hannunsa na dama, yayin da hannunsa na hagun kuma yake sarrafa matukin motar. Tabbas titin ne. Anas ya ce cikin zuciyarsa, sannan sai ya dada kallon takardar kwatancen da Ummi ta bashi, kana ya sake dago kai yana nazarin jerin gidajen dake gurin yana kokarin hangen mai lamba ashirin daga cikin su. A daidai lokacin ne to hasken fitilar motarsa ta hasko masa abin da ya sa yar autar hantar cikinsa kadawa. Sannan sai ya fara musu da zuciyarsa, kai wannan ba ita ba ce, ya ce da kansa, sa’ar da ya hangi kyakkyawar hallitar tsaye a jikin katangar wani sabon gida da ba a gama ginin sa ba. Ita da wani saurayi ne kyakkyawa dogo fari mai dogon saje da dogon hanci mai doro daga tsakiya sai ka ce hancin Larabawa. Anas ya ji wani bakin kishi ya turnuke zuciyarsa sa’ar da ya tabbata lallai Ummi ce ba wata ba. Abin da ya fi bata masa rai shi ne saurayin da ke tsaye da ita shima kyakkyawa ne, duk da yake dai Anas bai ga alamun saurayin ya zo da mota ba, to amma a yanayinsa babu alamar talauci ko kankani a jikinsa. Sannu a hankali ya ja birki ya tsaya a daf da su kana sai ya rage hasken fitilar motar kadan ya dada nazarin fuskar Ummi. Abin ya bashi mamaki, domin ya lura da cewa sun juyo inda yake, sun zubawa motar idanu. Sidi mai jaka ya yi shiru, kana ya sheka wata uwar hamma ya dubeni a yatsine ya ce. “wato Nas, tubani na da dadi, amma tsiyata da shi saurin sa mutum barci, ga shi da sa cikin mutum ya yi nauyi wata sa’ar sai in ji kamar na hadiyi duwatsu.” “Dan ma ka saba cin sa.” Na ce dashi a kagauce domin na matsu na ji yadda za a yi. Sidi mai jaka ya dafa cikinsa da busassun yan yatsunsa gami da dan runtse, idanu sannan sai ya dubeni ya ce. “Sannu a hankali Nas, Anas ya tuko motar zuwa inda suke ya tsaya, lokaci guda kuma ya sauke gilasan motar. Cikin sauri Ummi ta nufo gindin tagar motar, Abdulmalik na biye da ita a baya, a lokaci guda kuma ya ji wani matsanancin bakin ciki ya lullube shi Na shiga uku ya ce a cikin zuciyar sa, Ashe Anas din shima kyakkyawa ne.” “Anas…” Mabaruka ta kira sunansa a kunya ce. “Ummi…” Shima ya kira sunanta, sai dai har yanzu zuciyarsa na bugawa domin bai fahimci matsayin saurayin dake biye da ita a baya ba. Ummi ta lura tun da ta zo gurin idanun Anas akan Abdulmalik suke don haka sai ta yi sauri ta dube shi ta ce. “Anas…ga Yayana Abdulmalik ba ku gaisa ba.” Sannan sai ta juya ta dubi Abdulmalik da faffadan murmushi ta ce. “Yaya Abdul…ga Anas dina da nake baka labari yau dai Allah ya hada ku.” Cikin sauri gami da ajiyar zuciyar jin dadi abin da ta ce, Anas ya bude kofar motar ya fito, sannan ya mikawa Abdulmalik hann. “Yaya barka da yamma.” Samarin biyu suka cafke hannun juna, kana suka dubi juna ido da ido, Abdulmalik ya riga ya san matsayin Anas a gurin Ummi, to sai dai shi Anas bai san matsayin Abdulmalik ba a gurin Ummi, duk da yake dai ta ce dashi wai Yayanta ne, akwai wani abu a yanayin fuskar Abdulmalik da ya jefa shakka cikin zuciyar Anas, tabbas abin ya jefa shi cikin kaduwa, domin irin yanayin da yake gani a fuskar Abdulmalik, ya sha ganinsa a fuskokin gomomin samarin da ya sha kwace musu yan mata a baya, to amma da yake a yanzu bashi da wata kwakkwarar hujja abar dogaro, sai ya dubi Abdulmalik ya kuma cewa. “Ya ya ayyuka…ko kuma ya ya karatu zan ce…” “To, karatun dai…ai har yanzu yayan naka dalibi ne.” Abdulmalik ya ce a karo na farko. Aka sake yin shiru na yan mintuna, Ummi na kallon Anas, shi kuma na kallon Abdulmalik, Ummi ce ta fara bata shirun. “Yaya…Abdulma lik yau dai Allah ya hadaku da Anas din da nake baka labari.” Ba na fatan na kara haduwa da shi. Abdulmalik ya ce cikin zuciyarsa, sannan sai ya ce a fili. “Malam…Anas, ta sha bani labarin ka…ga shi sai yau Allah ya hadamu.” Ya dan yi shiru yana duban Ummi kana sai ya ce. “Daman zuwa na yi mu gaisa da wanda kanwata ke so…ni zan koma, gara na barku ku dan zanta.” Yana gama fadin haka sai ya fara juyawa da baya. Ummi ta dubeshi cikin mamaki- mamaki kaduwa-kaduwa, domin ta fahimci lallai yana cikin damuwa. Na shiga uku. Ummi ta ce a ranta.Ummi ta dubeshi cikin mamaki- mamaki kaduwa-kaduwa, domin ta fahimci lallai yana cikin damuwa. Na shiga uku. Ummi ta ce a ranta. Yaya Abdulmalik jininsa bai hadu da na Anas ba. Ta kuma fadi cikin zuciyarta, sannan sai ta ce a fili. “Yaya Abdulmalik…ta fiya za ka yi tun yanzu?” “Eh mana, ai gara na ba ku waje ku yi hirar ku…na sa kannena a gaba?” Ya fadi gami da jeho wani takurarren murmushi. To sai dai kuma ba Anas ba wanda tuni daman ya gama fahimtar Abdulmalik, hatta Ummi ta gane cewa murmushin yake ne tabbas ta san yayanta yana cikin damuwa. “Sai an jimanku…” Abdulmalik ya kuma fada sannan cikin sauri ya juya ya nufi gidan su. Suka zuba masa idanu har sai da ya shige cikin gidan ba a samu wanda ya ce kala ba. Ummi ta yi ajiyar zuciya sannan ta sunkuyar da fuskarta akan kirjinta cikin yar damuwa. “Ya ku ke da shi?” Anas ya tambayi Ummi yana dubanta cikin zargi, wani bakin kishi na kokarin tsaga masa zuciya. “Yayana ne.” Ummi ta bashi amsa kai tsaye lokaci guda kuma ta kalleshi ido da ido. Anas ya dubi fuskarta na tsawon lokaci yana nazari a cikin duhun daren, abin ya bashi mamaki domin a yadda ya ga tana kallonsa da karya take yi ba za ta taba iya hada idanu da shi ba. To amma me ya sa kyakkyawan saurayin mai hancin larabawa yake irin wannan dabi’a haka kamar wanda yake tsakiyar kogin begen Ummi? Tambayar kenan da Anas ya kasa amsawa kansa. “Kina nufin yayanki na uwa daya uba daya ko kuwa dai kawai yaya ne na yan uwa.” A wannan karon Ummi ce ta dube shi da wani tattausan murmushi ta ce. “Oh…Anas kenan, lallai na fahimci kai ma kana da kishi kamata.” Ta dan yi shiru lokaci guda kuma ta dafa kofar motar dake bude da hannunta na hagun ta dubi Anas ta ce. “Ka da ka bari kishi ya hana mana jin dadin hirarmu ta farko da kai.” Cikin sauri Anas ya sassauta fuskarsa duk kuwa da cewa har yanzu zuciyarsa tafasa take yi. “Ki gafarce ni Ummi, masifar sonki ce ta yi min yawa a cikin zuciya, irin yadda nake kaunar ki ko kuda ya sauka a kanki sai na yi kishi da shi…to ballantana kuma wannan kyakkyawa da ki ka ce wai yayanki ne.” Ummi ta fashe da wata zazzakar dariya, wacce sautinta ya sa wasu yan gajerun samar dake can gefe guda suna jiran fitowar tasu budurwar suka juyo cikin sauri suka kalli bangaren da su Ummi da Anas suke. “Kai Rabe…ka ji wata cika tana dariya kamar ana busa sarewa.” “Ummi kenan.” Daya saurayin ya ce da abokin sa “Duk unguwar nan babu cikar da ta kai haduwar ta, ba ka ganin gashinta daga nan har sheki yakeyi kamar madubi, to don ma da daddare ne da rana ce in ka kalli gashin kanta sai ya dauke maka idanu.” “Allah mutumi na…to ko barin wannan kucakar zamu yi mu koma can mu gwada sa’ar mu.” Daya saurayin ne yake fadawa Rabe haka. “Rufawa kanka asiri.” Rabe ya ce da saurayin. “Ummi me shegen girman kai kamar ibilishiya tun da nake ban taba ganinta da wani saurayi ba sai yau…kuma in ban da rigimarka ma ina kai ina Ummi? Zoben dake danyatsanta guda daya fa sai ya yi ma dinkin sallah karama da sallah babba har sau uku, kuma ya bar ka da ya canjin kashewa…samar i yan hutu ma masu kafafu hudu da iya kwalisa ba ta sauraresu ba sai kai mai katon kai da fadi kamar faranti.” “Ka ga bana son iskancin banza…kai din kyau ne da kai ko dan ba ka kallon madubi.” Saurayin ya ce da Rabe a kufule. A daidai lokacin da Rabe ya fara kokarin mayar da martani ne to, kofar wani gida ta bude sannan wata yar gajeriyar budurwa fara ta fito cikin sauri ta nufi inda su Rabe suke, ko da ta zo giftawa ta kusan inda su Ummi suke, sai ta tsaya turus ta Kalli Anas sama da kasa sannan ta dauke kai ta dubi Ummi ta ce. “Yaya Ummi ina wuni.” “Lafiya kalau Hasiya…ya ya ki ke?” “Lafiya nake.” Shiru Hasiya ta dan yi sannan sai ta sake duban Fuskar Anas ta ce. “Lalatacce mayaudari nan kuma ka dawo?” Anas ya ji gabansa ya fadi sannan zuciyarsa ta harzuka ya dubi budurwar a kidime yana kokarin tuna inda ya san ta. “Ai ba za ka iya tunani ba mayaudari tun da muna da yawa a gaban ka.” Tana gama fadin haka sai ta juyo ta dubi Ummi ta ce. “Ki bi a hankali Yaya Ummi kada ki sake dashi domin ba zan so ace kin fada tarkon sa ba.” Tana gama fadin haka sai ta juya gami da cewa. “Bari in je in fatattaki wadancan yan iskan…duk sahunsu guda da wannan da yake gabanki, kar ki yarda da shi mai kyan dan maciji ne.”***** . Ummi ta yi sororo a rude tana kallon Anas yayin da shi kuma Anas ya dubeta a tsorace baki na rawa ya ce. “Ummi…wannan kuma wacce mahaukaciya ce?” Ummi ta yi ajiyar zuciya a kidime kana ta ce. “A iya sani na dai tana da hankali.” Ta dan yi shiru, sannan sai ta dauke hannunta daga kan kofar motar. “Daman kun dade da sanin juna ne kai da ita?” Cikin sauri Anas ya girgiza kai “Ko kusa ko alama ni ban ma taba ganinta ba wallahi sai yau.” Ga mamakinsa sai ya ga Ummi ta zunkuda kafada sannan ta haskake shi da murmushi ta ce. “Me yiwuwa wani ne mai kama da kai ya taba yaudarar ta na san halin Hasiya wani sa’in rudaddiya ce.” “Yauwa ko da na ji fa” Anas ya ce gami da ajiyar zuciya, sannan ya share gumi lokaci guda kuma ya yi sauri ya sauya zancen da cewa. “Ummi wai don Allah uwa daya uba daya ki ke da Abdulmalik.” “Ummi ta fashe da wata sassanyar dariyar jin dadin ganin Anas yana kishi a kanta. “Har yanzu dai ba ka yarda ba kenan.” “A’a ba wai ban yarda ba ne…amma ni abin ne yake bani mamaki, ni sai na ga kamar shima sonki yake.” Ummi ta girgiza kai ta ce. “Anas, wallahi yayana ne, uwa daya uba daya, ni dai abin da nake tunani me yiyuwa wani abu ne daban yake damunsa ko kuma ganin zai tafi ya bar ni ni kadai ka san tun muna kanana bama rabuwa tare muke duk inda zamu tafi yawan lokuta ma barci ne ke rabamu to ka san ban taba yin saurayi ba sai a kanka ina jin abin da yake damunsa kenan.” Anas ya karkada yan makullayen dake hannunsa ya ce, “Na yarda da ke Ummi.” Sannan sai ya hango inda su Hasiya da samarinta suke tsaye gabansa na faduwa, haka nan wani zazzafan gumi ya fara sartu akan doron wuyansa tabbas sai yanzu ya tuno ta. A daidai lokacin ne to ya dubi agogo sai ya ga ashe har goma na dare ta wuce. Sannan ne to ya ji gaba daya duniyar nan ta yi masa bakinkkirin. Mabaruka ce ta fado a ransa kwata-kwata ganin kyakkyawar fuskar Ummi ya gama mantar da shi komai a wannan lokacin baya iya ganin komai sai Ummi. “Ummi ni zan tafi…sai yaushe kenan?” Ummi ta dubi fuskar Anas sai ta ga duk ta jike da gumi nan da nan ta fahimci halin da ya ke ciki. “Oh…na san fa ashe tana can tana jiranka ko?” Anas ya sunkuyar da kai “Ummi tun da na yi aure ban taba samun farin ciki kamar na yau ba…dan haka ina rokonki da ki yi shiru da bakin ki kada ki bata min farin cikina na wannan rana ta farin ciki.” Yana gama fadin haka sai ya shiga motar ya rufe kofa sannan ya sako kansa ta tagar motar ya ce. “Ummi tun da nake ban taba kaunar wata mace a duniya da gaske har zuciyata ba sai a kanki.” Ummi ta dan rankwafa kadan ta ce “Na yarda da kai Anas…sai yashe za ta sake bamu ranar haduwa?” “Wa ki ke nufi? ban fahimce ki ba.” “Matarka mana Mabaruka na yi mamakin ma yadda aka yi ta barka kazo.” Anas yaji kamar ta watsa masa wuta a fuska. “Ba ta isa ta juya ni ba Ummi duk lokacin da naga dama zan iya zuwa gurin ki.” ya dan yi shiru sannan sai ya ce “Ki jira ni zan zo jibi” A haka ya tuka motar ya fice daga layin Ummi ta bi motar da kallo ga mamakinta sai ta ji gaba daya ma ta shiga cikin rudani domin a da kafin ya zo ta dauka idan ya zo ba za ta iya rabuwa dashi ba sai da kuka saboda tsabar kaunar da take yi masa amma a yanzu ta shiga wasi-wasin zuciya, bata san mene ne dalili ba. A can cikin motar Anas ya ji hawayen bakin ciki ya fara sartu akan kuncinsa Shin ya ya abubuwa zasu zama haka ne ya ya aka yi duk sa’a ta ta kwace min, don me yar iskar nan Hasiya za ta yi min haka. A da kafin Anas ya zo ya dauka zai bar gurin Ummi dauke da farin cikin da bai taba jin irinsa a duniya ba To amma a yanzu wani karamin digo na kalanzir ya riga ya fada a cikin kokon ruwan shan kaunarsa ya kuma ji a jikinsa cewa in ba wani abu daga Allah ba dan digon kalanzir din nan sai ya gurbata dukkan illahirin dandano na ruwan shan kaunarsa A karo na farko tun bayan da ya girma sai Anas ya fara kokarin yin addu’a to sai dai kuma har sa’ar da ya fara hangen fitulun lantarkin da ke makale a jikin katangar gidan Mabaruka gurguwa bai iya tuno koda addu’a daya ba *** Sidi mai jaka ya yi shiru kana ya harari kwanon tubanin da ke gaban sa ya mika busassun yan yatsunsa guda uku ya cafko wani katon tubani mai siffar kwado ya dago shi sama yana nazarinsa sai da ya dade a haka sannan ga mamakina sai na ga ya mayar da tubanin cikin kwanon ya dubeni cikin nadama ya ce “Nas cikina ya gama cika amma har yanzu bakina na muradin ci gaba da taunar tubanin nan.” “Haka ne” na ce da shi “Ci gaba Baba Sidi na matsu in ji karshen labarin nan…sai na ji duk ma ka dada ruda labarin.” Sidi mai jaka ya saki wata kekasasshiyar dariya”Ci gaba Baba Sidi, na matsu in ji karshen labarin nan…sai na ji duk ma ka dada ruda labarin.” Sidi mai jaka ya saki wata kekasasshiyar dariya ya dubeni ya ce. “Ai Nas zararrukan labarin ma sun zo karshe…bari na yi sauri na saka maka na karshe sai mu hadasu da sauran zararrukan labarin mu daure.” “Haka ne.” Na ce da shi. Sidi mai jaka ya dubi kwanon tubanin cikin takaici ya yi kamar zai dauki daya sai dai ya sauya shawara ya dubeni ya ce. Nas, tun karfe takwas na daren ranar da Anas ya tafi gurin Ummi, Mabaruka ta caba kwalliya, sannan ta sa hadiman gida suka shirya musu kayan shaye-shaye da tande-tande na musamman. Shiru-shiru karfe tara ta wuce babu Anas babu labarinsa, wannan shi ya sa Mabaruka gurguwa rarrafawa gaban dan gajeren madubin da aka yi mata na musamman ta dubi mummunar fuskarta a jiki sai ta ji kamar ta fashe da kuka, domin ta lura duk kwalliyar da ta yi ta damalmale. Cikin sauri ta rarrafa zuwa bandakinta na musamman ta kuma kwashe mintuna talatin tana wanka gami da shafe-shafe da goge-goge, fitowarta ke da wuya daga bandakin sai tangamemen agogon azurfa wanda mahaifiyarta ta bata ya dauki rurin karfe goma na dare. “Na shiga uku.” Mabaruka ta fada a fili kai ka dauka tare suke da wani a dakin “Me ya tsayar da Anas ne har yanzu?” Mabaruka ta tambayi kanta, Nan da nan sai ta ji jikinta ya dauki rawa, zuciyarta ta fara harbawa sannan sai ta fara zargin kanta da wauta. Dan me zan bar shi ya tafi shi kadai? Ta kuma tambayar kanta to sai dai wannan karon Mabaruka na da amsar tambayar cikin zuciyar ta. Anan sai Sidi mai jaka ya dan yi shiru yana kallona, sannan sai ya ce. “Nas akwai wani sirri da Mabaruka take son sanar da Anas tun kusan kwanaki uku da suka shude amma yar rashin jituwar da suka samu a daren da aka yi liyafar nan shi ya sa ta boye masa. “Wanne sirri ne wannan?” Na tambayi Sidi mai jaka. “Bi ni a hankali Nas, ni ma zakin mazallako ne kawai da daga ciki yana rokon uba kwabo shi ya sani azarbabin fada ma, amma da sannu zan kawo ka kan zancen, kai dai bani aron hankalin ka mu koma kan zaren labarin da muke. “Na baka.” Na ce da shi. Sidi mai jaka ya dan faki idanuna sannan sai ya mika hannu ya zaro tubani guda ya jefa a bakinsa kana ya ci gaba da cewa. “Abin da ya sa Mabaruka ta bar Anas ya tafi shi kadai shi ne ta san cewa Anas fa ba kaunarta yake yi ba ko kankani, ita ce dai ke kaunar sa, haka nan ta tabbata muddin ta uzura da manne masa, to za ta sa ya kuma tsanarta a cikin zuciyarsa wanda hakan na iya kawo sanadiyyar rabuwarsu. Duk da irin kuri da cika baki da mabaruka ke masa cewa idan ba zai iya ba ya ajiye mata duk dukiyarta ya bar mata gidanta, babu abin da Mabarukan take tsoro da fargaba irin rabuwa da Anas, domin ta san idan ta rabu da shi tana iya haduwa da cutar da za ta kawo ajalinta a kusa, wannan dalili shi ya sa duk da tana zargin karya Anas yake yi ba gurin abokansa za shi kawai ba Mabaruka ta kyale shi ya tafi shi kadai, tare da fatan me yiwuwa idan ta bashi yana yan walawa shi kadai yana iya dan kaunar ta ko daidai da kwayar zarra ne, haka nan tare da karfin gwiwar cewa idan ya dawo zata fada masa abin me yiyuwa zai iya sa shi farin cikin da dole ne ma ya tarairayata ko da bai so ba. Wannan shi ya sa Mabaruka ci gaba da kwalliya tun magriba har zuwa karfe goman dare bata gama ba. “Bari in sa wannan shudiyar rigar me yiwuwa ta burgeshi, na ga ran nan da na sa irin ta kamar yana satar kallona.” Mabarua ce ta ci gaba da zance da kanta sa’ar da take kokarin sa rigar. Bayan ta gama sai ta sake rarrafawa zuwa gaban madubi ta kuma duban kanta a karo na goma sha uku. Abin da ta gani ya dan faranta mata rai babu dai yabo babu fallasa, domin ba katon goshinta ba kawai, hatta dan tababben hancinta mai kamar kataura ya dan mike sakamakon matsar da ya sha a hannunta, haka nan fuskarta na dan sheki, to sai dai kuma ta fuskanci kamar hoda ta so ta yi mata yawa a fuskar Wannan ya sosa mata rai, dan haka a fusace sai ta mika hannunta zuwa kan gado ta janyo wani abu da take tsammanin me yiwu rigarta ce, da zummar ta yi sauri ta goge hodar dake fusakarta domin duk sosunan kwalliyar sun hade da kalolin hodoji iri-iri sun baci. Janyo abin ke da wuya sai ta ga ashe wandon Anas ne. Cikin farin ciki sai ta kara wandon mijin nata akan fuska, sannan ne fa kudundunnaniyar takardar fara ta fado daga cikin aljihun wandon. Mabaruka ta ji gabanta ya fadi ras, tun kafin ma ta dauki takardar. Hannunta na rawa ta dubi takardar cikin tsananin zargi sannan sai ta jefar da wandon gefe guda ta dauki takardar ta fara karantawa…. . “…..Ni ce Ummi.” Mabaruka ba ta iya maimaita karatun takardar a karo na biyu ba, sai ta kifa kai a jikin gadon ta fashe da kuka mai karfin gaske wanda har rawar da gangar jikinta ke yi ta sa gadon shima ya dauki rawa Kofar dakin ta bude a hankali sannan Anas ya shigo fuska a turbune shigowarsa ke da wuya sai ya tsaya turus kamar wanda ya ji shi cikin fasassun duwatsu a cikin duhun dare. “Ku…kukan me ki ke yi Mabaruka ba gani na dawo ba.” Mabaruka ta dago kai jiki na rawa cikin kuka ta ce. “Mene ne amfanin dawowar ka tsohon mayaudari! Ai sai ka koma can gidan su Ummin ka kwana a can…!” Ta kara fashewa da kuka. “Ban fahimci abin da ki ke nufi ba.” Anas ya ce cikin shakka, domin bai san munafukin da ya fada mata daga gidan su Ummi yake ba. “Ya za a yi ka fahimce ni, tun da ka tsaneni! Ba ka kaunata!! So kake na mutu da bakin cikin kaunarka ko Anas?” Hakan da ta fada sai Anas ya ji tausayinta ya kamashi. Ga mamakinsa sai ya ga Mabaruka ta rarrafa inda ya ke tsaye ta rike kafafunsa cikin kuka ta ce. “Anas….don Allah ka yi min rai ka kaunace ni ko da daidai da na kwana daya ne… Haba Anas don ka ga ni mummuna ce…dan ka ga ni gurguwa ce….shi ne kake son kashe ni.” Ta sake fashewa da kuka. Anas ya ji kwalla ta zo idanunsa, cikin sauri ya durkusa a gabanta ya dafe kanta. “Daina kuka Mabaruka bari in yi miki bayanin abin da ke zuciyata.” “Ba sai ka yi ba Anas, na ri ga na sani…ni dai ina rokon don Allah ka kauna ce ni kada ka sa bakin ciki ya kashe ni, ni da danka da ke cikina!” Anas ya ji kamar an zunguri zuciyar sa da allura. “Wanne dana ki ke nufi a cikinki?” Ya tambayeta a rude. Mabaruka ta dada kankameshi sannan ta fashe da kuka ta ce. “Anas tun shekaran jiya na ke son fada ma likita na ya sanar da ni ina da ciki wata uku!”*** Na dubi Sidi mai jaka a rude nace “Haba Baba Sidi ya ya tun dazu ka ke labarin nan amma ba ka ce tana da ciki ba sai yanzu?” Sidi mai jaka ya dubeni da busasshen murmushinsa ya ce. “Nas ke nan, abin da ba ka sani ba shi ne idan na fada maka tun dazu cewa tana da ciki ai na ragewa labarin dadi, haba Nas kai sai ka ce ba marubuci ba. Bari in sako maka zaren labari na karshe sai in hadasu da wannan na kulla ko ma kai ga karshen labarin nan.” “Haka ne.” Na ce dashi ba musu. Yauwa Nas, ta yanzu ina son ka sa a zuciyar ka cewa ga Ummi nan ta fito daga dakinta a rude, wannan kuwa fitowa da ta yi a washe garin ranar da Anas ya zo mata zance ne. Ummi ta dubi dan karamin agogon da ke sanye a santalelen hannunta, karfe hudu da mintuna biyar agogon ya nuna. Cikin sauri sai ta nufi kofar dakin Abdulmalik ta kuma kwankwasawa, a karo na goma sha takwas a ranar. Shiru ba a amsa ba, Ummi ta dada rudewa. Shin ina Yaya Abdulmalik ya tafi ne tun da sassafe har yanzu bai dawo ba. Abin da ya dada tayar mata da hankali shi ne a daren jiya sa’ar da ta shigo gida bayan sun rabu da Anas, ba ta tsaya a ko ina ba sai dakin Abdulmalik, domin tana da tambayoyi masu yawan gaske da take bukatar amsarsu. Lokacin da ta isa kofar dakin sai ta hango wutar dakin a kunne take, to sai dai kuma kamardakin a rufe. Me yiyuwa har ya yi barci. Ummi ta ce a ranta, to amma sa’ar da ta matsa kusa da kofar dakin sosai, sai ta ji motsi a cikin dakin kamar ana taba takardu. “Salamu alaikum.” Umma ta yi sallama lokaci guda kuma ta tura kofar dakin. Ga mamakinta sai ta ji kankam kofar dakin a rufe take. “Yaya Abdulmalik bude min na dawo” Ummi ta ce Shiru ba a amsa ba “Yaya Abdulmalik.” Ta sake kiran sunan a karo na biyu “Ina jin ki Ummi..ki bari sai gobe ma hadu” Ummi ta ji gabanta ya fadi nan da nan ta ji jikinta ya dauki rawa kamar zazzabi zai rufe ta Wannan shi ne karo na farko da yayan nata ya fara fushi da ita amon muryarsa ya fadi sakon da ke zuciyarsa “Yaya Abdulmalik..me na yi maka? Ka bude min mana” “Babu abin da ki ka yi min Ummi ta fi dakinki kawai ma hadu gome…yanzu wasu yan rubuce- rubuce nake yi bana son a dame ni” ummi ta ji kamar ya watsa mata wuta Cikin kunan rai ta jingina bayanta a jikin kofar dakin idanunta suka fara ambaliyar kwalla na mintuna biyu sannan a hankali sai ta nufi dakinta domin ta tabbata ba zai bude mata kofar ba Tana zuwa dakinta sai ta fada akan gadonta ta fashe da kuka tabbas jinin Abdulmalik bai hadu da na Anas ba Ummi ta fada a ranta*** Na dubi Sidi mai jaka a rude na ce A wan nan lokacin ne to kalaman Hasiya suka fado mata “Ki bi a hankali Yaya Ummi kardai… wan nan lokacin ne to kalaman Hasiya suka fado mata “Ki bi a hankali Yaya Ummi kada ki sake dashi domin ba zan so ace kin fada a tarkon sa ba” Shin ko abin da ta fada gaskiyar ne, shin ko Yaya Abdul Shima ya san halin Anas ne shi yasa yake fushi da ni. Ummi ta kuma tambayar kanta, sannan sai ta dada fashewa da kuka, a haka barci ya dauketa. To amma kafin barcin ya saceta sai da ta yiwa kanta alkawarin cewa in dai har alakarta da Anas ne ya batawa Abdulmalik rai, to babu mamaki za ta rabu da Anas duk kuwa da irin kaunarsa da take yi, domin da ta bakantawa yayanta Abdulmalik gara ta rabu da abin da take kauna. Washe gari da sassafe, tana idar da sallah sakamakon makara da ta yi da bata tashi da asuba ba, sai ta nufi dakin Abdulmalik cikin sauri ta tura kofar dakin babu ko sallama sai ta ji kofar a rufe. Cikin sauri ta juya da baya a kidime ta nufi dakin mahaifiyarsu. “Mama ina Yaya Ya tafi?” “Ya fita tun da duku-duku nima ban san ina za shi ba, ya dai ce dani ba zai dawo ba sai can yamma. Tun daga wannan lokaci Ummi ke ta faman safa da marwa daga dakinta zuwa dakin Abdulmalik har zuwa yanzu babu shi babu alamarsa. Hawayen bakin ciki ya yi sartu akan kumatunta. Ummi ta yi sauri ta goge sannan ta nufi dakinta ta zauna a bakin gado ta kurawa kofar dakin nata idanu cikin takaici. Wannan shi ne lokaci mafi tsayi a rayuwarta da ta taba zama ita kadai ba tare da dan uwanta Abdulmalik ba a kusa da ita. Tana nan zaune ta zubawa kofar dakin nata idanu tana jiran ta ga ta inda Abdulmalik zai bullo, sai aka yi sallama. Da farko muryar mahaifiyarta ta fara ji daga waje tana cewa. “Ki shiga tana ciki.” Cikin sauri Ummi ta goge hawayen da ke kumatunta ta mike tsaye, a daidai lokacin da ta ji an sake cewa. “Salamu alaikum.” Sannan sai ta ji an nufo kofar dakin. Ummi ta dubi Hasiya sa’ar da ta shigo dakin. “Sannu da zuwa Hasiya dama wallahi ina son ganin ki.” “Ni ma son ganin naki ne ya kawo ni Yaya Ummi.” Hasiya ta ce lokaci guda kuma ta zauna a bakin gadon ta dubi Ummi. “Ga ni me ki ke son yi min?” “Ke ma ai kin sani.” Ummi ta ce tana dubanta “Wai dan Allah abin da ki ke fada min jiya a gaban wannan saurayin nawa gaskiya ne?” Hasiya ta fashe da dariya ta ce “Oh! Yaya Ummi kenan, ta wallahi kima daina kiransa da suna saurayin ki…don kin ga nima din nan babu irin abin da bai fada min ba amma daga karshe ya koma kan wata kawata Samira..wallahi sai da na yi rashin lafiya da kyar Allah ya yaye min masifar kaunar sa daga zuciyata na huta.” “Wai ki na nufin ki ce saurayin ki ne da?” Ummi ta tambaya. Kina shakka kenan to bari ki ga zahiri.” Hasiya ta bude cikin jakar da ke kan cinyarta sannan ta zaro wani hoto ta mikawa Ummi, “Kalli wannan.” Ummi ta zurawa hoton idanu cikin kaduwa. Tabbas Anas din ta ne, shi da Hasiya a bakin otel din da suka yi liyafar bikin zagayowar ranar haihuwar Mabaruka gurguwa, abin da ya fi kona mata rai a hoton shi ne, hannun Anas na hagu dare-dare yake akan kafadar Hasiya. Hannun Ummi na rawa ta mikawa Hasiya hoton. “Ungo abin ki.” Hasiya ta girgiza kai ta ce “Ki rike shi a gurinki, idan ya dawo ki nuna masa hoton ki tambaye shi me ya sa bai aure ni ba.” Hasiya ta mike tsaye ta ce “Bari in karasa gida Yaya Ummi…daman daga unguwa nake shi ne na ce bari in biyo ta nan domin ba zan bari wannan kyakkyawan macijin ya sake saran yar uwata mace ba. Sai an jima.” Da haka ta fice daga dakin ta bar Ummi cikin kaduwa dauke da hoton a hannunta, ba tare da ta iya yi mata ko da rakiya ba. Bayan ta kalli hoton na mintuna biyar sai ta mike tsaye, sannan ta daga karkashin matashin kanta ta jefa hoton, kana sai ta mike cikin sauri ta nufi dakin Abdulmalik domin ta sake dubawa ko ya dawo. Tana zuwa kofar dakin sai ta sake turawa babu sallama domin a tunanin ta idan ta yi sallama Abdulmalik ya ji muryarta me yiyuwa ba zai bude ba, zuciyarta na harbawa das! Das!! Das!!! Ta shiga dakin, tana shiga sai ta yi turus, Abdulmalik baya cikin dakin. Sannu a hankali ta shiga dakinta jikinta na rawa sannan ne to ta hangi tarin takardu farare an cikesu da rubutu akan wani dan teburin gilashi dake kusa da gadon Abdulmalik, sannan sai idanunta ya kai ga wata takarda fara kwaya daya jal akan gadon a jikinta an rubuta kamar haka;- Masoyiyata Ummi ki karanta takardun dake kan teburin nan domin amsoshinki duk suna cikin takardun…” Hannunta na rawa ta dauki takardar ta juyata a hannunta sannan sai ta dauki sauran takardun dake kan teburin jiki na rawa ta zauna akan gadonsa ta fara karanta wani abu mai kama da almara..labarin wadansu mutane da yaki ya korosu suke gudun hijira. Sidi mai jaka ya dubeni da murmushi ya ce “Ina fatan dai kana biye dani Nas?” “Kwarai kuwa Baba”. “Yawwa Nas, to bari mu koma kan wancan tsohon zaren labarinmu inda muka bar Anas a durkushe a gaban matarsa Mabaruka gurguwa. Sidi mai jaka ya yi shiru sannan sai ya sake zarar wani katon tubani ya jefa a bakinsa ya dubeni ya ce. “Ba zan iya hakura da cin tubani ba Nas, sai dai tumbina ya fashe Tsawon dakika talatin Nas, Anas yana durkushe a gaban Mabaruka cikin tsananin kaduwa yaya ma za ta bari ta yi ciki? Anas ya tambayi kansa, wani bakin ciki ya lullube zuciyarsa. A haukan Anas ya gama imani da cewa babu makawa Mabaruka mummunan jariri ko jaririya za ta haifa masa a matsayin dansa. Wannan tunani shi ya sa wani zazzafan gumi barkowa akan goshin Anas. Cikin karfin hali Anas ya ciccibi Mabaruka ya kwantar da ita akan gado sannan ya kwanta a kusa da ita ya yi shiru, domin kwakwalwarsa lokacin ba za ta iya tunanin komai ba sai na Ummi. A zuciyarsa yana cewa, ina ma ace cikin nan Ummi ce ta yi shi a matsayin matarsa. Tsawon lokaci suna nan haka a kwance ba sa ko motsi cikin bacin rai, can sai Mabaruka ta yi ajiyar zuciya ta ce a tausashe. “Anas…” “Na’am.” Anas ya amasa bayan jinkirin kusan minti guda. “Ban ji ka ce komai ba ko ba ka farin ciki da dan da zan haifa ma” Anas ya ji kamar Mabaruka ta soka masa kibiya a tsakiyar zuciya. Shiru na yan dakiku, Anas bai amsa ba. “Anas…ba ka ce komai ba!” Mabaruka ta ce cikin wata irin shakakkiyar murya tana shirin fashewa da kuka. “Me ki ke so in ce dake?” Anas ya ce da ita a fusace. Hakika tuni ya gama yankewa zuciyarsa shawara shi fa ya gaji da wannan daurin talala da mulkin mallaka. Cikin kaduwa da jin abinda ya ce Mabaruka ta turar da hannunsa ta dan dago kai ta dubi fuskarsa a cikin dan hasken fitilar dakin dake ajiye akan wani teburi na alfarma. “Anas…ba ka kaunata ko?…” Anas ya yi shiru na yan dakiku bai amsa ba sannan sai ya tashi zaune ya ce. “Mabaruka ya kamata mu fuskanci gaskiya, sanin kanki ne tsakani da Allah cusa min ke aka yi…ba wai bana kaunarki bane amma…” “Ya isa haka!” Mabaruka ta daka masa tsawa cikin wata karyayyiyar murya. “Ba sai ka karasa ba Anas, na yarda tabbas ba ka kaunata.” “Ka da ki zarge ni, ki zargi mahaifiyarki Mabaruka da kuma ke kanki.” Aka sake yin shiru na yan mintuna. “Ummi ce ko?” Mabaruka ta bata shirun da wannan tambaya. “Ba zan boye miki ba Mabaruka…wall ahi duk duniya babu wacce nake kauna kamar ta. Mabaruka ta ji kamar ya watsa mata wuta a doron zuciya. Wani abu mai kamar amai ya zo ya toshe mata makogwaro. “Anas…mu sawwake wa juna ina ganin shi zai fi ko?” “Kwarai kuwa…nima da niyyar da na zo kenan.” Cikin sauri kamar da wasa sai Anas ya lalubi aljihunsa ya zaro takardar da tun a cikin mota ya rubuta a lokacin da zai yi fakin da ita a gareji. Hannunsa na rawa ya mika mata ya ce baki na rawa. “Na sake ki saki biyu.” Mabaruka ta karbi takardar ta karata a kirjinta, kana ta lumshe idanu, ga mamakin Anas, sai ya ga ta dubeshi ta ce. “Don Allah taimaka ka kaini falo.” Anas ya ciccibeta, cikin damuwa domin tausayinta ya gama lullube zuciyarsa, to amma babu abin da zai iya akan hakan. Lokacin da ya ajiyeta, sai ta dube shi ta kuma cewa. “Dan Allah koma daki ka jirani.” Ta dan yi shiru sannan sai ta kuma cewa “Za ka bari gari ya waye ko yanzu za ka fita?” Anas ya dubeta a rude sannan ne to fa dimbin asarar da zai dibga ya darsu a zuciyarsa, tabbas ya san ya rabu da masifa ya fada masifa. Domin a gurinsa Mabaruka masifa ce, haka kuma rabuwa da ita ma na nufin sake shiga cikin masifar talauci Koda yake dai ai ina da yan kudi a banki da gida da mota da kuma otal din da mahaifiyarta ta bani Anas ya fadawa kansa “Duk abin da ki ka ce haka za a yi in ba kya son ganina yanzu ma sai in tafi” Mabaruka ta danne kukan dake kokarin kufcewa daga makogwaronta. “Dan jirani a dakin to ina zuwa” Anas ya koma cikin dakin ya zauna gami da ajiyar zuciya Ga mamakinsa sai ya ji tamkar an dauke masa wani katon kaya mai nauyin tsiya daga doron bayansa Sannan ne to ya jiyo sautin muryar Mabruka daga cikin falon tana yiwa Mahaifiyarta waya Tsawon mintuna talatin Anas na nan zaune yana jran dawowar Mabruka gurguwa lokacin ne ya juyo sautin injin mota an shigo farfajiyar gidan Cikin sauri Anas ya mike a rude ya nufi taga ya leka. Tun kafin ya gama bude labulen tagar ya hangi dogon direban gidansu Mabaruka ya budewa Hajiya Aliya kofar katuwar (Jeep) din nan baka ta fito jikinsa na rawa Anas ya nufi falon inda Mabaruka take Anas ya sameta zaune akan kilishin dake mamaye da tsakar dakin kan talfon din rike a hannunta ta kwantar da kanta akan kujerar dake daf da ita gaban rigarta sharkaf da hawaye “Me ya kawo mahaifiyarki kuma cikin wannan maganar? Don me ba ki fada min ita za ki kirawo ba?” Mabaruka ba ta dago kai ba balle ma ta kalleshi sai ta ce a sanyaye “A GABANTA MUKA FARA AGABANTA NAKE SON MU ƘARE.” A GABANTA MUKA FARA AGABANTA NAKE SON MU KARE.” Kofar babban falon ta bude Hajiya Aliya ta shigo a fusace bata ko damu da ta zauna ba sai ta dubi Anas ta ce “Tun da ka sake ta me kuma ka ke jira sai ka fice ka bar mata gidanta.” Babu kunya, babu tsoro sai Anas ya dubeta ya ce “Gidanta ko gidana? Na dauka ke ki ka fada da bakinki kin bani gidan nan?” Hajiya Aliya ta dubeshi shekeke ta ce Duba bayan ka wannan shine Yarima Gangariya na mallaka masa wan nan gida kuma daga zarar ta haihu za’a daura musu aure Hajiya Aliya ta dubeshi shekeke ta ce “Kai dai jahili ne wallahi Anas kai ka taba gani inda aka baiwa mutum kyautar gida babu shaidu kuma babu takardu? Ko ka taba ganin inda aka baiwa mutum kyautar otal babu shaidu kuma babu takardu?” Anas ya ji wani zazzafan gumi ya karyo masa Hajiya Aliya ta dubeshi ido da ido ta ce “Ka yiwa kanka matsiyaci sai ka koma cikin talaucin ka motar da na baka na kwace kayata domin daman duk takardunta yana hannuna haka ma gidan da kuma otal din da na baka duk na kwace su. Daga yanzu ba kai babu karbar ko kwabo daga kamfanunnukanmu matsiyaci.” “Bai kamata ki yi min haka ba?” Anas ya ce cikin kaduwa domin a shashancinsa bai taba tunanin haka ba. “Ba ka da hankali Anas tashi ka fice min daga gida. Rufeshi zamu yi a cikin daren nan in koma da yata gida ka yi ma sa’a wallahi da yan kudin da suke bankinka ma sai na yi hanyar da za su salwanta…amma ka yi sa’ar ta.” Ta dan yi shiru tana duban Mabruka. “Ita ce ta ce na kyale ma kudin da ke cikin ma’adanin ka. Sai ka fice Allah ya bamu alheri.” Anas ya dubi Mabruka a rude sannan sai ya juya zuwa cikin dakin. Ba a dade ba ya hado kayan sawarsa a cikin jakunkuna guda uku ya ratayo su da kyar sannan ya dubi Mabruka ya ce. “Na gode Mabruka.” Sannan sai ya fice daga dakin. Wani abin mamaki shi ne tun da Mabruka take da Anas, bai taba fada mata kalmar da ta amince da ita har zuciyarta ba sai wannan godiyar da ya yi mata. Koda Anas ya nufi farfajiyar gidan sai dogon direban nan ya tare shi, ya karbi biyu daga cikin jakunkunan uku ya ce. “Mabruka ce ta ce duk inda ka ke son zuwa na kai ka.” Anas bai san menene mutunci ko so ba sai yanzu. Abin mamaki sai ya ji hawaye ya yi sartu akan kuncinsa. Koda direban motar ya fara tafiya da su sai Anas ya yi ajiyar zuciya. A kalla dai ko da na rasa arziki ina da wacce na fi kauna da so a duniya Ummi! Anas ya ce da kansa. “Yallabai ina zan kai ka?” Anas ya dubi direban a rude sannan yace. “Bari in tuna”**** Ummi ta ji hawaye ya yi sartu akan kundukukinta sa’ar da ta gama karanta takardun. Hawayen da ke zuba a yanzu hawayen bakin ciki ne da farin ciki. Bakin cikin shi ne ya ya ma za a ce wai wadannan mutane da tun da ta fara budar ido su take gani a ce wai ba mahaifanta bane yayin da kuma farin cikin shi ne yanzu ta fahimci tana da damar mallakar abin da ta dade tana kauna tun da ta zo duniya. Haba gaskiya fa ta ji ba ta san rabuwa da shi tana bege da shaukin son zama da shi ashe ba dan uwanta ba ne na jini. Ba ta ji shigowarsa ba sai inuwarsa ta gani a kanta. Ta juya a razane, sai suka yi ido biyu da Abdulmalik. Nan da nan sai ya yi murmushi sannan ya mika mata wani farin kyalle ya ce a tausashe. “Goge hawayen ki.” Ummi ta ji kunyarsa ta rufe ta, ta kasa hada ido da shi, kanta a sunkuye ta karbi kyallen gami da ajiyar zuciya. “Abdulmalik, me ya sa baka fada min ba tuntuni…kuma dan Allah wannan abin da ka rubuta min gaskiya ne?” Abdulmalik ya dubeta da murmushi ya ce. “Na taba fada miki karya?” Ummi ta yi sauri ta girgiza kai. “Kuma na ji kin kira sunana kai tsaye na dauka ni yayanki ne ko kin fasa yayan da ni?” Ummi ta rufe idanu a kunya ce ta ce “Ni na isa, ai har abada kai Yayana ne kuma…” Ta yi shiru ba ta karasa ba. Abdulmalik ya zo kusa da ita ya zauna da murmushi ya ce. “Karasa mana kuma me?” Ummi ta fara wata sassanyar dariya. “Ni ba zan karasa ba.” “Allah sai kin karasa.” Abdulmalik ya ce cikin dariya. Uimmi ta dago kanta ba tare da ta kalli fuskarsa ba, ta dubi hotonta dake manne a jikin bangon dakin sannan ta ce. “Rufe idanunka, ka miko hannunka na rubuta maka abin da na ki karasawa.” Cikin farin ciki sai Abdulmalik ya rufe idanunsa, sannan ya mika mata tafin hannunsa. Cikin sauri Ummi ta yi rubutu akan tafin hannunsa, sannan sai ta dauki takardun da ya bar mata ta karanta ta rike a hannunta sannan sai ta ruga a guje ta fice daga dakin. . Abdulmalik ya zo kusa da ita ya zauna da murmushi ya ce “Karasa mana kuma me?” Ummi ta fara wata sassanyar dariya. “Ni ba zan karasa ba.” “Allah sai kin karasa.” Abdulmalik ya ce cikin dariya Uimmi ta dago kanta ba tare da ta kalli fuskarsa ba ta dubi hotonta dake manne a jikin bangon dakin sannan ta ce “Rufe idanunka, ka miko hannunka na rubuta maka abin da na ki karasawa.” Cikin farin ciki sai Abdulmalik ya rufe idanunsa sannan ya mika mata tafin hannunsa. Cikin sauri Ummi ta yi rubutu akan tafin hannunsa sannan sai ta dauki takardun da ya bar mata ta karanta, ta rike a hannunta sannan sai ta ruga a guje ta fice daga dakin ta nufi dakin mahaifiyar Abdulmalik domin ta fasa kwai. Abdulmalik ya bude idanu a daidai lokacin da Ummi ta fice daga dakin kana ya dubi tafin hannunsa sai ya ga Ummi ta rubuta YAYANA MIJINA ! . Sidi mai jaka ya ja doguwar hamma ya kuma karawa sannan ya dubi kwanon tubanin dake gabansa ya ce “Nas na fa gaji.” Na dube shi cikin kasuwa na ce “Ka da dai ka ce min karshen labarin kenan?” Sidi mai jaka ya girgiza kai ya ce “Ba karshensa ba kenan amma saura dan kadan saurara na karasa maka sai mu watse” Na ce to, Sidi mai jaka ya dube ni kana ya ci gaba. Washe garin ranar karfe takwas daidai dan kabu-kabu ya sauke Anas a kofar gidan su Ummi idanunsa sai zubar da ruwa suke kamar tsohon kuturu domin rabonsa da ya hau kabu-kabu tun kafin satin da zai hadu da Mabruka Anas ya aika yaro zuciyarsa cike da farin ciki duk kuwa da sauyin rayuwa da ya same shi na gaggawa cikin sa’a ashirin da hudu kacal A daren jiya bai yi barci ba duk kuwa da cewa a dakin otal ya kwana amma dakin bai kai ko da rabin dakin kwanansu da Mabruka ba * A can cikin gida Ummi ta dubi Abdulmalik ta ce. “Mutumin ka ne, don Allah zo mu je ka labe daga bakin kofa ka ji yadda za mu kare da shi.” Cikin murmushi Abdulmalik ya dube ta ya ce. “A’a, kada mu koma kamar yara kanana mana, ke dai je ki ku gama da shi ina nan.” Ummi ta dube shi da dariyar zolaya ta ce. “Kai dai tsoro ka ke kada su Mama su ganmu tare, to mene ne kuma bayan sun san komai.” “Sun san me?” Abdulmalik ya tambaya a tsora ce. “Takardun da ka rubuta suna gurin mama…” Ta fashe da dariya, da haka ta fice ta bar shi anan baki bude. Anas ya ji wani farin ciki marar misaltuwa ya lullube shi, sa’ar da ya hango kyakkyawar fuskar Ummi ta leka kofar gidan cikin sauri ya tareta da faffadan murmushi. “Hajiya Ummita.” Ummi ta dube shi shekeke ta ce. “Ranka ya dade…yau a kasa ka zo ina motar?” Anan ne to Anas ya gama karkade dan sauran abin da ya rage na kaunarsa dake zuciyarta. “Wannan marar mutuncin gurguwarce ta kwace motar…kin san fa mun rabu da ita jiya da daddare saboda ke.” Ummi ta dube shi cikin takaici ta ce “Kana nufin ka saki Mabaruka?” Anas ya gyada kai “Mene ne to amfanin zama da nacacciya. Matar da za ta hanaka walawa.” Ummi ta kura masa idanu, yanzu kam ta tabbata duk abin da Hasiya ta fada akan wannan saurayi mai kyawun dan maciji gaskiya ne. Ummi ta dubeshi ido da ido ta ce. “Amma bai kamata ba ace ka saki Mabruka, dubi fa son da na ga tana yi maka Anas yanzu kai ko tausayinta ba ka ji?” Anas ya fashe da tattausar dariyar da ya sha satar zuciyar yan mata da ita ya ce. “Don me zan tausaya mata bayan tana son ta raba ni da ke.” Ummi ta sake dubansa ta ce “Anas, wai me ya sa ka ke kaunata?” “Saboda kina da masifar kyau Ummi, ko ke ba kya ganin kanki ne.” “Shi kenan abin da ya sa ka ke kaunata?” Anas ya gyada kai sannan ya dube ta ya ce “Ke fa me ya sa ki ke kaunata?” Ummi ta dube shi na tsawon lokaci kana sai ta dauke kai gefe guda ta ce “A da dai saboda kana burge ni ne kawai idan na dubeka shi yasa nake sonka.” Anas ya dubeta cikin mamaki ya ce “A yanzu fa?” Ummi ta girgiza kai ta ce “Ka daina burge ni Anas, kai bari in fada maka ma infact na tsaneka domin ka fiye son kanka.” Anas ya ji wani abu kamar tafasasshen ruwa ya fara wanke masa fuska. “Ummi in wasa ne wannan ki ke yi dan Allah ki bari Ummi domin yana iya sa ni hauhawar jini.” Ummi ta girgiza kai ta ce “Ban taba yin wasa da kai ba, wadanda suka sha wasan da kai dai sun yi, irin su wadannan.” Ta zaro hoton da Hasiya ta ba ta, ta mika masa. Anas ya karba hannu na rawa, nan da nan sai ya ji kwalla na kokarin kwace masa. “Haba Ummi, yanzu wannan yar iska ce za ta rabani da ke'” Ummi ta kuma girgiza kai ta ce “Ka da ka sake daukar alhakin baiwar Allah wanda ka dauka a da ma ya ishe ka wallahi babu ruwanta a cikin wannan zance.” Anas ya yaga hoton dake hannunsa gida biyu a fusace yace. “To idan ba ita ba ce me ya sa za ki ce kin tsaneni Ummi? Me ya sa! Na dauka ke ki ka rubuto min a takarda kina kaunata ??”TSOHON ALKAWARI-19 KARSHE . Na dauka ke ki ka rubuto min a takarda kina kaunata?” “Wannan da ke nan Anas jiya na sake shawara ka san duniya juyi- juyi kullum da irin abin da take zuwa” Anas ya matso kusa da Ummi cikin kaduwa ya ce cikin karyayyiyar murya “Na ji na yarda Ummi kin tsane ni amma ina son don Allah ki taimaka ki fada min mene ne dalilin da ya sauya miki ra’ayi a kaina?” “Yanzu ka yi tambaya?” Ummi ta ce tana ja da baya cikin shirin shigewa gida “Abin da ya bani tsoro da kai Anas guda daya ne jal shi yasa na tsaneka akan dole” “Mene ne.” Anas ya tambaya kusan cikin kuka. “Ka da ka bada yan maza Anas yanzun nan zan fada maka” Ta dan yi shiru tana gyara lullubin koren gyalen mai shara-shara da yake kanta sannan ta dube shi ta ce “Ga ni na yi Anas aurenka yana da hadari” “Saboda me Ummi? Saboda me ki tuna fa ni mai kaunar ki ne” “Na yarda Anas kana kaunata” Ummi ta ce cikin murmushi “Amma abin da na yi tunani shi ne, duk mutumin da bai tausaya wa zuciyar gurguwa abin Allah sarki ba to kuwa ba zai taba tausayawa mai kafafu kamata ba” Ta juya cikin sauri ta shige gida ta bar Anas sororo a tsaye yana lissafin irin asarar da ya yi . Sidi mai jaka ya mike tsaye ya yi doguwar mika ya ce “Nas labarin nan fa ya kare in kuma ba so ka ke in shiga yi maka karya ba ka san kuwa karya LINZAMIN SHAIDAN CE” . “Haba Baba Sidi ai ba ka fada min yadda Mabruka ta kare da cikin ba” Sidi mai jaka ya dubeni da murmushi ya ce “Nas kenan daman da gangan na kyaleka na dauka za ka mance da sauran bakin zaren labarin da muka bari bamu dinke ba amma tunda ka tuna bari in dinke ma shi a gurguje Sidi mai jaka ya gyara tsayuwa ya ce “Nas watanni shida sun shude kamar wasa an daura auren Abdulmalik da Ummi har ma tana da ciki wata dayashi kuwa Anas ya koma matsiyacinsa yan kudin ma da suka rage a asusunsa duk ya kashesu a banza domin dan zaman da ya yi da mabruka ya yi sabo da jin dadi Haka nan ma Mabruka ta haifarwa Anas wata kyakkyawar ya mace amma kwanakinta bakwai a duniya ta rasu. Anas ya yi ta rusa kuka shi kadai a daki domin ya so a ce ta rayu don ko banza dai in Mabruka ta mutu yar ce za ta gaji duk dukiyar shi ko yana iya zuwa ya karbe yarsa da dukiyarta ka ga ya zama miloniya kenan . Sidi mai jaka ya dubeni cikin murmushi ya ce Nas wato mutum dai sai dai ka bar shi da halinsa amma hali zanen dutse ne” “To yanzu ina Anas din yake?” Na tambaye shi “Nas kenan kai dai ka cika son jin kwakkwafin labari na dai fahimci so ka ke ka sa dattijo ya shiga karya” Anan sai na fashe da dariya Sidi mai jaka ya dubeni da murmushi ya ce “Na ji an ce wai Anas din ma ya samu tabin hankali tun da yar jaririya da aka haifa masa ta mutu amma fa labarin wai ne har yanzu bani da tabbacinsa” Sidi mai jaka ya dubeni kana sai ya juya ya ce “To Nas Allah ya dada sada mu da alheri sai wata rana” . Dattijon ya shige cikin gida abinsa ya bar ni nan tsaye ina kokarin hada zarurrukan labarin . KARSHE

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: