MAJNOON complet

 MAJNOON complet
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 16 Apr, 2019
Upload Time 1:41 am
Last Modified Date October 25th, 2021
Last Modified Time 11:46 am
Hits 3849 Hits
Author

Writer Group Unknown / NIL
Novel Genre No genre attached
Comment No Comments

Description

MAJNOONComplete
NameMAJNOON
Size444kb
AuthorMr Smiles
File Typetxt
uploaderMr Dlhausanovels
ebook compilerShuraih 99%
date modified13 September, 2020
descriptionhausa FICTION

DANDANO

Shine sunan da dandazon yara kekiransa yana tafiya suna binsa a baya Wasu daga cikin yaran dake biyarsa har rigarsa sukeja Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa,

 

amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake** Tafiya yakeyi yaran kuwa sai binsa sukeyi suna masa ihu, wani lokaci idan yagaji da ihun yakan dan juyo yabi yaran da gudu sai su zura da gudu.. Hakadai yaci gaba da tafiya, idan yaga bola a gefen titi yakan tsaya yayi tsince2 sa kafin yaci gaba da tafiya, Wata waka naji yaran sun fara masa suna cewa

 

“ga maj nun uban tanbele, ga maj nun uban tanbele ” shikuwa sai dukawa kasa yakeyi yana tsintar ledojin pure water, yana kwasar rawa ga alama wakar tanai masa dadi.. *** *** *** A hankali take taku kamar batason taka kasa, matashiyar budurwace yar shekaru 20 cikin shigar kamala tufafin hausawa atamfa da zani sai kuma katon hijab data saka har kasa. Hannnun rike da ‘Yar karamar kula ta abinci…

 

Dai dai kwanar wani layi ta kunnu kai Tun daga nesa ta hangi yara sunai masa waka, “Ga maj nun uban tanbele” Wani zarr taji jikinta yadauka, dasauri takarasa gurin duk ta watse yaran sannan ta dubesa ta saukar da murya tace “haba ! Haba meye haka katsaya yara suna mai maka waka kana rawa” sai tayi shiru tana kallonsa kafin yadago kai ya kallesa,

 

sannan tace “ko so kake na fasa aurenka kane ?” Maj nun yayi saurin girgiza mata kai “a a nadaina ” yana gama fada yayi sauri yazauna ya langwabe kansa Murmushi tayi tadawo kusa dashi tazauna ta mika masa kular datazo dashi “ga abincika maza ka cinye kabani kular na wuce gida, tun kafin Abbana yadawo ” Da karfi ya firgi kular yana kokarin budewa, da kyar yasamu ya iya budewa shinkaface da namomi akai, karkade hannunsa kawai yayi ya fara aikawa cikinsa sako.

 

Kura masa ido tayi tana kallosa cike da tausayi, bata ankaraba tafara hawaye, wani iri takeji a zuciyarta akansa, tarasa sanin ko meye wata zuciyar tace mata sona wata zuciyar kuwa tace mata tausayine… ita kanta takasa baya kanta amsa, *so ne ko tausayi*

 

Tana zaune tana tunani harya kammala canye abinci ya miko mata kula “ungo” maganarsa tafitar da ita daga duniya tunanin datake ciki, tadan zabura kadan, sannan ta kirkiri murmushi tace “harka cinye ” yace “eh ” yana wasa da tsunmar rigarsa, Mikewa tsaye tayi shima ya tashi ta dubesa tayi murmushi tace “nizan wuce gida sai nazo da dadare” Maj nun ya hada kansa da kafada yace “nibanason kitafi kitsaya, muyi fira ” yakarasa maganar yana gunguni Dariya tayi kafin tace ” to shikenan idan nazo dadare zamuyi firar yanzudai zan wuce gida” “Tohm..

 

toh yaushe zamuyi aure” maj nun yafada yana cizon rigarsa Murmushi tayi tana kalloso tace “gobe ” Tsalle yayi yana ihu cike dajindadi yace “idan mukayi aure a jirgi zan daukeki nakaiki india” Dariya tayi sosai, saida taga yafara kuluwa sannan ta tsayar da dariyarta tace “tohm shikenan nidai na tafi sai anjima” tana gama fada ta fice tabar gurin, saida tayi nisa kan dashu saikuma tatuna da maganar daya fada takara saka dariya.. sai kace itama haukar takee Saita fara tafiya ta juyo ta kalle sa tagansa sai tsalle yake wani irin mugun tausayinsa takeji, Hakadai taci gaba da tafiya cike da tausayin maj nun daidai kwatar layinsu ta hangi wata bakar mota da karfi taja da baya gabanta ya fadi sosai “innalillahi wa inna ilaihin raju un ” itace kalmar data subuce daga bakinta..

 

Tayi rau rau da ido kamar zatayi kuka, nan ta fara salati harta samu na tsuwa tadan wani lokaci sai kuma taci gaba da tafiya Takai dap da Motar taji ankira sunan ” *Rumaisa* !!!” Gabanta yafadi ko juyowa batayiba taci gaba da tafiyar ta ..

 

Da sauri yafito daga cikin motarsa ya tari gabanta sukayi ido hudu, ya marairaice fuska kmar zainyi kuka yace “haba rumaisa meyasa bakijin tausayin zuciyatane, plx kitsaya ki saurareni dan Allah koda na minti biyune ” Hawaye sunka cinciko a idon rumaisa,

 

 a duk lokacin data gansa wani irin bakin ciki takeji ya ziyarci zuciyarta, Muryarta tafarasa rawa kalilan abu zai iya sakata kuka, bude bakinta kuwa sai kuka “wai menai maka kake bibiyana kahanani jindadin rayuwata dan Allah ka fita harkata” *Fahad* yayi shiru yana sauraron kukanta, zuciyarsa na masa kuna, kwata2 bayason ganin kukan rumaisa, idan tana kuka shima jiyakeyi kamar zai tayata, muryarsa na rawa yace ” sonki nake rumaisa zuciya ta tsunduma a cikin kogin sonki, iduwana basa muradin ganin kowa saike, a koda yaushe kece a mafarkina,

 

plx rumaisa dan Allah kisoni” Hawayenta ta share ta sakar masa wani irin tsaki tace ” ko kai kadaine namiji a duniya bazan sokaba, daidai da dakika daya bantabajin ina sonkaba” kafita daga harkata, kabano hanya na wuce ” tanakarasa maganar tana kokarin turesa, shikuwa sai binta yake a duk gefen dataje yana fadan plx rumaisa, Da taga bayada niyar bata hanya taturesa ta wuce, A karo na biyu yakara shiga gabanta yana fadan plx rumaisa, wlh ke kadaice a raina, nayi miki alkawarin zan chanza halina idan har kika amince da soyayya ta, kiduba fa kigani wannan ma kadai ai kinyi jahadii… Bata jira yakarasa kalmarsa ta jahadi ba ta wanka masa wawan mari tas kakeji kafin tace “bana son, kuma natsani ganinka

 

” takarasa maganar tahuci ta zagaya ta gefensa ta fice.. Tsayi yayi a guri daya sai kace bushanshiyar bishiya Dafe gefen kumatunsa yayi yana mai jin zogin marin da rumaisa tai masa, Hartayi masa nisa kadan yak’wala mata kira tajuyo ya saukar da hannunsa akan kuncesa ya share hawayensa yace ” bazan iya hakura dakeba, domin kece muradina, tunda nabiki ta laluma amma kinki aminta dani dan haka yau zan saceki” Yana gama fadan hakan yajuya ya shiga motarsa yabar unguwar “Mahaukaci” rumaisa tafada fuskarta a ya tsune sannan taja Tsaki taci gaba da tafiyarta harta isa bakin gidan su gabanta faduwa yake akan maganar daya fada mata nacewa nasaiya saceta…

 

Tana isa kofar gidansu tatura kofar tashiga a harabar gidan taga motar abbanta a gefe yayi parking, cak ta tsaya guri daya, gabanta yayi mummunan faduwa, bugun zuciyarta yakara karfi, duk tsoro yakamata, domin tasan dacewa da suci karo da Abba akan maganar majnoon to gwanda ta fada rijiya zaifi mata sauki, da kyar ta iya taka kafafunta takarasa bakin kofar falo, A hankali take tura kofar falo tashiga tare dayin sallama, jin sallamarta yasa ya mike tsaye yana jiran shigowarta..

 

 A tsaye ta samesa fuskarsa a murtuke😡 Sau daya tadaga kai suka hada ido da sauri ta sauke kanta kasa, sum sum take tafiya kamar ba lanka ajikinta, gabanta sai faduwa yake tanufi dakinta… RUMAISA!! Cikin hargowa yakira sunanta saida ta kusan faduwa akan tsoro Hawaye suka soma zubo mata a hankali takarsa gurinsa, tas tas yadauketa da mari biyu kyawawa saida tasaki kara tayi baya tadafa kan kujera,

 

Da gudu umma tafito daga dakinta cikin baccinta tajiyo karar mari, Alhaji lafiya” itace kalmar da umma take fada tana kokarin karasowa gurinsu, rumaisa najin muryarta ta tamike da gudu ta rungumeta tana kuka, cike da masifa yafara mata magana “bana hanaki zuwa gurin majnoon dinnan ba, wato kin maida maganata maganar banza, nizaki mayar karamin mutum, wannan shine karo na biyar kenan danayi miki a kansa amma kinki jih, to wlh kisani yau kinyi kuma kinkai karshe, gobe gaben nan zan daura miki aure da *faisal*, tunda nalura dacewa bakida hankali, meye abinso acikin mahaukaci, shashashar yarinya” Rumaisa takara fashewa da kuka jin yakira sunan faisal, kuma da furucinsa na cewa gobe zai daura mata, batajin zata iya rayuwa da wani da namiji a duniyar nan idan ba majnoon bane,

 

tana manne a jikin umma tafito ta gurkusa a gaban abba tana kuka ta rike masa kafa ” dan Allah abba kayi hkr wlh banason faisal” A fusace abba ya dukar da kansa kasa yana kallonta yace “idan bakya sonsa idan na aura masa ke ki kashesa” yana gama fada ya firgi kafarsa yabar falon yanufi dakinsa.. Durkusawa tayi kasan cafet tana kuka sosai, a lokacin umma takaraso gurinta fuskarta ba annuri tadafata tabaya ” rumaisa” Dasauri tatashi ta rungume umma tana kuka tace “umma nashiga ukku, abba zaimun aure da faisal, kuma wlh umma bana sonsa” …..

 

MAJNOON complete hausa novel written by Mrs J moon TXT,PDF,DOC,DOCX EBOOK – Novel Infomation

  • Name: Majnoon
  • Author: Mrs J Moon
  • File Type: txt/text,
  • Uploader: Mr Hausa Ebooks
  • Compliler: Mr Hausa Ebooks
  • Price: Free
  • Source: Hausa Ebooks
  • Group: NIL
  • Published date: 16 April, 2019
  • ISBN: NIL

Description:-

No description

you are proceeding to download MAJNON hausa novel complete document was a book written by Mrs J Moon

Also download Birnin Sarauniya hausa novel complete document

Copyright Claim

If you are the right owner of this novel and you want us to removed it on our site, please mail us at hausaebooks@gmail.com for removal.

Download

DOWNLOAD NOW

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: