ABOKAI littafi na biyu 2 part 6

 ABOKAI littafi na biyu 2 part 6
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 11 Feb, 2019
Upload Time 4:32 pm
Hits 183 Hits
Comment No Comments

Description

ABOKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- by Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2019
Part 6
.
***
Tangamemen dakine mai matsakaicin tsayi, hasken kwan lantarki ya haska dakin tarwai ta yadda ko Allurace ta fadi za a ganta daliban makarantar government college ne rututu zaune a cikin dakin, kowanne mutum ya duba daga cikinsu zaiga tashin hankali muraran akan fuskarsa, tun lokacin da dan ta’addan yashigo ya kashe Emmanu’el, sannan yayi gargadi ga hukuma kan su sakar musu shugaba, tun lokacin daliban suka tsinci kansu cikin wawakeken fili mai cike da tsoro da firgici,
.
Dayawa daga cikin daliban hawayene ke zubowa daga idanuwansu, Zullumi da Tunanin mutuwa ya hanasu rintsawa don gani suke a kowanne lokaci yan ta’addan zasu iya bindigesu,
Kalilan ne daga cikinsu ke Addu’a kan Allah ya fidda su daga wannan kangi, ya tseratar da rayuwansu
.
Haidar,jibrin,mansir da hasan na can gefe daya kusurwan yammacin dakin, idanuwansu yayi luhu luhu alamun sun ci kuka, hankalinsu ya tafi ga Aliyu dake kwance a tsakiyarsu, Abotace mai karfi ta shiga tsakaninsu, wacce ta kauda masu da tunanin Rabuwa,
,,,
Lokaci na farko Aliyu ya bude idanuwansa tun bayan sumarsa, a hankali numfashinsa ya fara dawowa , mansir da idanunsa ke kan Aliyu yana ganin haka ya fashe da dariyan farin ciki, yana cewa “Aliyu! Aliyu, ya farka ashe ba mutuwa kayi ba Sarkin Dariya”
Cikin kankanin lokaci bakin cikin daya mamaye zukatan Abokan ya rikide izuwa farin ciki,
Haidar da jibrin suka tallafawa Aliyu ya mike zaune ya jingina da bangon dakin,
A hankali ya fara kallon dakin da suke ciki, cikin tu’ajjibi yace “A ina ne muke, ya akayi muka zo nan, shin ba a makaranta muke ba”
.
“Kada ka damu aboki zamu sanar dakai” jibrin ya fada yana dubansa, Aliyu yacigaba da kallon tarin daliban dake cikin dakin, dukkansu ya sansu domin dayawa daga cikinsu ma ajinsu daya,
.
Wani irin mugun zogine ke ziyartar kansa hakan tasa yakai hannu ya taba inda ke yi masa zogin se dai cikin mamaki sai yaji danshi danshi a hannunsa, koda ya dubi hannun sai yaga hannun ta rine da jini, mamaki gamida tsoro suka bayyana a fuskarsa,
Nan take kwalkwalwarsa ta fara tunano masa abubuwan da suka faru a baya,
Shi dai yasan yana kwance a makaranta wasu mutane dauke da bindigogi sun shigo dakinsu inda suka nemi su cutar da Abokansa shi kuwa ya hana hakan tasa daya daga cikinsu ya buga mai kotar bindiga,,,, iya abinda masarrafin kwalkwalwarsa ta iya tunanowa kenan,,,,
A firgice ya dubi abokannasa yace da su “sune, nasan cewa sune suka kawo mu nan,to waima me mukai masu ne “
.
Kofar dakinne ya bude wani jibgegen kato mai kama da mutanen farko ya shigo dakin hannunsa rike da bindiga, kai tsaye ya nufi wajen da Abokan suke,
“Wato ku yan iska ko, na sami labarin gardamar da kukai yayin kawo ku nan”
Jibgegen dan ta’addan yafadi yayinda ya isa wurin Abokan,
.
Gaba dayan daliban dakin suka juyo suna kallon jibgegen dan ta’addan a matukar razane,
Abokan suka dubi jibgegen dan ta’addan cikin bacin rai Aliyu ya fara kokarin mikewa tsaye haidar ya rikesa ya ce “koma ka zauna ka huta,”
Haidar ne ya mike tsaye ya na mai karewa dan ta’addan kallo kafin yace “shin menene gamin mu da ku, nasan dai kun yi garkuwa da mu ne domin cikar burinku, dan Allah na rokeku da ku rabu damu, bawai ina nufin ku sakemu ba ina nufin ku dena shiga harkanmu” haidar ya karisa maganar yana hada hannuwa da saukar da kai kasa
.
Aliyu da zuciyarsa ke tafarfasa sabida kaskantar da kan da haidar yayi cikin sauri ya mike tsaye duk da su jibrin sunyi kokarin rikeshi amma ya fincike jikinsa daga nasu,
“Haba haidar ya zaka zo kana kaskantar da kanka a gaban wani banzan bazara, maciyi amanan kasarsa….” Bai rufe bakinsa ba jibgegen dan ta’addan ya manna bakin bindigarsa akan kwakwalwar Aliyu,
.
Idanuwan Jibrin,haidar,mansir da hasan suka zazzaro a firgice suka duka akan guiwowinsu hasan yace da jibgegen dan ta’addan,”na rokeka da kada ka kasheshi, kuruciyace ke dibarsa dun Allah kai hakuri”
Jibgegen dan ta’addan ya dubi ilahirin dakin inda ya ga dukkan daliban hankalinsu ya karkata ne gareshi, wasu dalibai dake gaba kadan da jibgegen dan ta’addan sai bari suke tamkar sun zauna a kan injin markade, tsaban kaduwa ma daya daga cikinsu har fitsari ya saki a wando baima san yayi ba
.
Haidar,mansir,jibrin da hassan suka dukufa suna baiwa jibgegen dan ta’addan hakuri akan kada ya hallakamasu ABOKI, inda hawaye ya runga kwarara daga idanunsu yana bin kuncinsu,
Azucciye Aliyu ya dubesu kana ya dubi jibgegen dan ta’addan dake gabansa ya ciji lebba lokaci guda ya kade bindigar dake hannun jibgegen danta’addan , bindigar ya fadi a gefe, kafin danta’addan ya ankara Aliyu ya sanya dukkan karfinsa ya gabza mai naushi a fuska, jibgegen danta’addan ya shafa bakinsa inda Aliyu ya naushesa yana girgiza kai, haidar,hasan,jibrin da mansir sunyi matukar razana da abunda Aliyu ya aikata cikin sauri suka rikosa lokacin daya ke kokarin hambarar danta’addan
.
“Aliyu kana cikin hayyacinka kuwa,shin kasan me kake kokarin yi” haidar ya fada yana jijjiga Aliyu
“Cikin hayyacina nake, Aboki domin babu yadda zan bari a wulakanta abokaina akan idanuwana”
Aliyu ya fadi cikin bacin rai, mansir ya dubi aliyu yace “dun Allah kabari Aliyu mutanennan basu da imani zasu iya hallakamu”
“Duk abin dakaga sun mini to haka Allah ya kaddara, ko basu kashe ni ba wataran sai na mutu to me zaisa naji tsoron mutuwa, dun Allah ku sakeni tun kafin dan iskan ya tsere” aliyu yafadi yana kokarin kwace kansa daga hannun abokannasa
.
Daliban dake dakin sunyi matukar firgita da abunda Aliyu yayi har wasunsu suka fara kuka suna ganin tamkar Aliyu ya yanki musu tikitin mutuwa ne,
Jibgegen dan ta’addan ya mike tsaye ya nufi wurin da bindigarsa ke yashe a kas, ganin haka yasa Aliyu yayi yunkuri ya kwaci kansa daga hannun abokansa, cikin sa’a ya zame da ga rikon da sukai masa, kai tsaye ya ruga a guje ya nufi wurin da jibgegen katon ke tsaye,yana isa yasa guiwan hannunsa yaiwa danta’addan dundu a baya
.
Danta’addan ya duka da nufin ya dau bindigarsa kwatsam sai yaji saukan wani abu a gadon bayansa ya cije baki sakamakon radadin daya yaiwa bayan nasa dirar mikiya
Aliyu dake tsaye a bayan danta’addan ya suri bindigar danta’addan dake yashe a kasa ya nuno danta’addan da bindigar ,
Haidar,mansir,jibrin da hasan tun lokacin da Aliyu ya kwace daga hannunsu sukai kokarin rukosa amma suka kasa hakan yasa suka biyoshi a guje koda sukaga abunda ke rike a hannunsa sai dukkaninsu suka tsaya a kame,
Daliban dake cikin dakin suna kallon duk abunda ke faruwa suka kwakkwanta a kas zuciyoyinsu cike da fargaba da tsoro,
.
A kame danta’addan ya tsaya lokacin da ya ji bakin bindiga ta tokari keyarsa, a hankali ya juyo ya fuskanci aliyu yana mai daga hannuwansa sama alaman ya mika wuya,
“Aliyu me kake shirin yi ne,maza ka gaggauta yarda la’anannen abun dake hannunka” haidar yafadi yana duban Aliyu
Aliyu ya juyo ya dubesu yai murmushi yace “bazan taba yada bindigar nan ba ABOKAI, a kullum kuna yimin kallon dan wasan barkwanci sedai baku san cewa zuciyata a kekashe take akan kasata da Al’umman da suke ciki, na gwammaci rayuwata ta salwanta domin kare dubban rayuka” yana gama fadin haka ya daka wa firgitattun daliban dake yashe akas tsawa yace “dukkanku ku mike tsaye,”
A gigice daliban suka mike Aliyu ya kalli inda abokan nasa ke tsaye cikin tu’ajjibi yace da su “ABOKAI da iznin Allah,da taimakon Allah zamu tsira daga hannun mugayen mutanen nan”
Mansir wanda yafi dukkan abokan tu’ajjibi ya matso kusa da aliyu yace “Aboki abun dana ke son ka fahimta shine sufa yan ta’addan nan sunyi garkuwa da mune don gwamnati ta sake musu mutuminsu, nasan cewa nan da dan kankanin lokaci gwamnati zata sake shi, kuma suma dolensu su rabu damu, kaga kenan gwamma ka rabu dasu har burinsu ya cika”
,
“Shin kasan irin ta’addancin da suke shirin aikatawa, ko kasan dalilin dayasa suke bukatan mutumin nasu ne, a nawa fahimtar gwamma mu dukkanmu rasa rayukanmu da ace gwamnati ta saki masu shugaba, don Allah kadai yasan me suke shirin aikatawa” aliyu ya fadi haryanzu bindigar na rike a hannunsa tana kallon jibgegen dan ta’addan daya daga hannuwansa sama
.
Jibrin ya kariso ya dafa kafadar Aliyu yace mai “Aliyu abun da mu keson ka fahimta shine ‘yan ta’addan basa da imani dazu dazu suka bindige Emmanuel na benue house har lahira a dedai inda kake tsayen nan, dun Allah ka ajje bindigannan ka bashi hakuri, domin kuwa ba zamu iya hakurin jure rashinka ba”
Aliyu yayi murmushi ya dubi jibrin yace” RAYUWA KO MUTUWA dole a cikinsu yau kaddarata ta zabi daya, sedai kuma tuni kaddarata ta zabar min MUTUWA don ceton rayuwar wasu, fatana shine koda na rasa raina kuyi kokari ku tseratar da mutanenmu” Aliyu na idar da fadin hakan ya juya ya dubi jibgegen katon dan ta’addan ya daka matsa tsawa “A ina hanyar fita yake” dan ta’addan ya nuna mai kofan daya shigo da yatsa, Aliyu ya dubi daliban yace ku biyoni, ya manna bindigar a kugun jibgegen dan ta’addan yace “muje”
.
Suna isowa bakin kofan dan ta’addan ya kama marikin kofar ya murda sannan ya bude kofar wanwar, hasken rana ya dallare ma daliban idanuwa har wasu suka sanya hannuwansu suka kare,
Danta’addan ya juyo ya dubi Aliyu yana nuna bakin get din daya kusan katange gidan da hannu yace “ga kofar fita can” Aliyu ya dan jinjina kai kafin yace “to yi maza kaje ka bude mana”
“Ai. Abude kofan take” dan ta’addan ya fadi cikin garjejiyar muryarsa,
“Toh muje” Aliyu ya tasa keyansa, daruruwan daliban government college dake a matukar tsorace tamkar ace kyat su ruga na biye da su, cikin daliban nan kuwa har da Abokan Aliyu wayanda suke a gaba-gaba suna kalle-kalle
Suna karisawa bakin Get din Aliyu yakai hannu da nufin ya bude, kwatsam sai yaji muryan haidar yana cewa “A’a Aliyu kada ka bude”
Aliyu ya juyo yai arba da haidar,mansir,jibrin da hassan dukkansu hannuwansu a hade,
“Me yasa kace kada na bude” aliyu ya tambayi haidar
Mansir yayi murmushi ya dafa kafadar aliyu yace “haba Aboki shin a tunaninka kai kadaine ke dauke da zuciya mai kishin kasansa,muma da muke a tsaye a gabanka duk irin zuciyar ce garemu, ko kai tsammani kake zamu zuba ido muga kana gwagwarmaya batare da mun agaza maka ba, wannan abota dake tsakaninmu ta wuce duk yadda muke tsammani, saboda haka muna tare dakai duk rintsi da tsanani duk wuya duk kunci ba zamu rabuba” mansir na gama fadin hakan ya ajje tafin hannunsa akan iska,
Cikin kwarin guiwa jibrin ya dora nasa hannun akan na mansir a haka Abokan suka hada hannayensu wuri guda alaman Hadaka,
.
Haidar ya numfasa yace “dukkanmu mu matsa gefe dan iskannan ne ze bude kofar” yafadi yana iza keyar danta’addan,
Maimakon dan ta’addan ya bude kofar sai yai zuru da idanuwa yana nazari a zuciyansa,
Tsawan da hasan ya daka mai ne ya dawo dashi cikin hayyacinsa, dukka daliban suka matsa gefen gate suka labe, danta’addan ya kama marikin Gate din gidan ya fara janyowa, yana bude kofarne Al’amarin ya faru, al’amarin daya tsorata Daliban har suka juya da nufin su koma dakin da suka fito haidar ya daka masu tsawa suka dawo,
,
Lokacin da danta’addan ya bude kofar sai gani sukai ya tsandare a tsaye bayannan sakaanni sai ya fadi a kasa rikica kai kace giwace ta fadi,
Da sauri Aliyu yayi na gungure ya rufe kofar, ya juyo ya dubi jibgegen danta’addan dake kwance a kasa matacce, harsashi ya huda kirjin dan ta’addan sai zubar da jini take, ABOKAN suka jinjina kai hasan ne yafara cewa “me kuka fahimta cikin lamarinnan”
“Shakka babu yan ta’addan sun san da fitowanmu, toh amma taya akai suka sani” mansir ya fadi yana share zafafan gumin dake ambaliya akan fuskarsa
Jibrin yaja doguwar numfashi ya sauke yace”Yanzu de duk ba wannan ba, wata dabarace zata fidda mu”
“Me zai hana mu zagaya ta bayan gidan sai mu haure katangar” haidar yafadi yana duban fuskokin abokannasa domin ganin ko shawararsa ta sabu karbuwa,
__
ABOKAN suka amince da shawaran haidar suka dunguma gaba dayansu harda sauran daliban suka nufi wata doguwar hanya da zata sada su da wani bangare na gidan, suna cikin tafiyar ne haidar ya ce “Allah ya fiddamu daga wannan kangi lafiya”
“BA AMEEN BA” wata kakkausar murya ta basu amsa, dukkansu suka juya don ganin mamallakin kakkausar muryar, abunda idanunsu ya gani yayi matukar kidima wasu daga cikin daliban,

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: