ABOKAI littafi na biyu 2 part 5

ABOKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- by Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2019
Part 5
.
Kwamishina ya katsesa ta hanyar daga mai hannu yace “ka same ni a ofishina yanzu” yana gama fadin haka ya fice daga magarkaman,
Cikin fushi Acp kamalu ya dubi dan ta’adda sidi dake zaune yana murmushin mugunta yace “naso ace na sameka da wannan alburushi, ka godema Allah daya turo kwamishina ya sa hannuna ya kuskureka,”
.
“Shin a tunaninka me yasa kwamishina ya hanaka hallakani, nasan zakai zaton ko shima dan hannuna ne, A’a kawai de yarana ne sukai aikinsu na tabbata nan da awanni ashirin da hudu zan fice daga kazamin ofishin nan naku cikin girmamawa”
Dan ta’adda sidi ya fadi hallau murmushin mugunta na shimfide akan fuskarsa
.
Zuciyar acp kamalu ta fara tafarfasa, ma’aunin fusatarsa takai 100% cikin fushi ya fice daga magarmakan don ko muddin ya tsaya ya cigaba da sauraren maganganun da dan’ ta’addan ke fada masa wayanda sukafi madaci daci a zuciyarsa zai iya bindige dan ta’addan har lahira,
.
____
“Menene amfaninsa garemu da kuma Al’umma yallabai, mutumin daya kasance bara gurbi bashi da buri da ya wuci daukan rayukan al’umma, dan ta’adda fa kenan yallabai yayi kisa cikin mutane, shin me ne alfanun kareshi”
Acp kamalu yafadi cikin salama yana fuskantar kwamishina Abdullahi makeri
.
“Bawai na hanaka kasheshi bane So nake kafin ka kasheshi ka kalli wannan majigin” kwamishina ya fada lokacin daya mikawa acp kamalu wayan dake hannunsa
Acp kamalu ya karbi wayar, yana kai dubansa kan fuskar wayarne yayi arba da babban tashin hankalin da baiyi tsammani faruwansa ba,,
Daliban makarantar government College ne rututu a cikin makeken daki, dayawa daga cikin daliban babu abunda suke sai kuka,
A zagaye da daliban wasu mutane ne cikin bakaken kaya sun rufe fuskokinsu da bakin kyalle idanuwansu kadai ake iya gani, mutanen suna rike da dogayen bindigogi kirar AK47 a hannuwansu, daya daga cikin mutanen ya fito tsakiyan dakin ya tsaya ya fara kalle-kalle yace
“Daliban makarantar government College keffi ne muka kwamuso. A bisa kama mana shugaba da hukuma tayi, ku hukuma kui sani cewa kun taro babban tashin hankalin da bata da ranan karewa, ” dan ta’addan na zuwa nan a maganarsa sai ya kamo dalibi daya daga cikin daliban dake zazzaune suna kuka ya dora bakin bindigarsa a kan saurayin yace “mun baku nan da sa’o’I ashirin da hudu ku sako mana shugabanmu SIDI in ko ba haka ba, zamu kashe daliban nan duka,” yana gama fadin haka ya danna kunamar bindigarsa, nan take karar fitar Alburushi ta karade dakin, saurayin dalibin dake gabansa ya fadi kasa matacce gefen kansa a fashe, jini na bulbulowa ta cikin kan
.
Koda daliban dake cikin dakin sukaga haka sai dukkansu suka gigice, zuciyoyinsu ya fara dukan tara-tara, tsananin tsoro,firgici ya lullubesu, cikin kankanin lokaci Dakin ya hautsine da ihu gamida kukan dalibai,
.
Dan ta’addan daya kashe dalibin ya dakawa daliban tsawa yace “shut up”
A matukar firgice daliban suka hadiye kukansu hawaye na kwaranya daga idanuwansu,
“Wannan fansa ce, fansar kashe dan uwana da kukai, izan har baku sako mana shugabanmu nan da awanni ashirin da hudu ba kamar yadda na fadi sai na kashe dukkan daliban nan na aiko maku da gawarwakinsu” dan ta’addan ya fada sannan ya fice daga dakin.
_____
“Inna lillahi wa’inna ilaihii ra ji’uun,” acp kamalu ya fadi, lokaci guda gumi ya fara karyo masa, ya ciro hankicin ya share gumin daya karyo mashi,
Kwamshina yace “A jiya da daddare ne aka saka video din a youtube, nima constable Ubaidu ne ya nuna min, dazu da safe, nasan yanzu kusan dukkan mutanen kasannan sun kalli video din nan”
.
“Yanzu yallabai menene mafuta,” acp kamalu ya tambayi kwamishina
“Ba maganan gaggawa bane,dole sai mun zauna da manyan kasannan anyi shawara, kasancewar makarantar ba gama gari bace, Daliban ma da akai garkuwa dasu yawancinsu ba yan jihar nasarawa bane , “
Kwamishina ya bashi amsa yana mai mikewa tsaye ya fice daga ofishin,,,
___
Iyayen Daliban da yan ta’addan sukai garkuwa da su, sun shiga wani irin hali yayin da mummunan labarin ya riskesu sun koka sosai gameda tsaron makarantar, da yawa daga cikin iyayen daliban sun fito kafar yada labarai suna masu rokon gwamnati data taimaka ta saki dan ta’addan
.
Har yanzu mutane sun kasa gane fuskan dalibin da dan ta’addan nan ya kashe, sakamakon dan duhu duhu da hoton video din yayi,
.
Wannan mummunan lamari mara dadin saurare ita ta sanya cikin gaggawa shugaban kasan Nijeriya Umar Bahaje ya dawo gida Nijeriya,
Saukarsa a filin jirgi keda wuya yan jarida sukai masa maraba da tarin tambayoyinsu wayanda yawanci duk akan batan daliban makarantar government college ne, “yallabai wani mataki za’a dauka gameda batan yaran makaranta”
“Yallabai za’a fanshe su da dan’ataddan kenan”
“Yallabai shin an gano ko waye dalibin da yan ta’addan suka kashe?”
Irin wayannan tambayoyi da makamantansu sune yan jaridan sukaita korawa shugaban kasa su
Shugaban kasa umar bahaje ya gyara zaman farin tabaransa ya dubi yan jaridan yace dasu “dafarko dai Ina mika sakon ta’aziyata ga iyayen dalibin da ya rasa ransa, duk da haryanzu ba’asan ko waye ba, da yardan Allah nan da sa’o’I kalilan zamu dawo ma iyayen yara, da ‘yayansu cikin koshin lafiya,”
Yana gama fadin hakan yai wuce warsa inda jami’an tsaro suka take masa baya
***=======***
Yan ta’addan ne su Uku a zazzaune saman manyan lallausan kujerun da suka bada gudumma wajen kawata tangamemen falon,
Hankulansu ya tafi ga tangamemen talabijin bango dake manne a jikin bangon falon, inda aka hasko shugaban kasar nijeriya yana korawa yan jaridu bayanai,,
“Lallai shugaban kasa ya yanke kyakkyawan shawara, da ya yarda zai sako Oga, “
Audu ya fada yana duban jagwa,
Jagwa yayi tsaki gami da yamutse fuska yace “ai dolensu su sako oga, ku suna so ko basa so”
“Kwantan bauna zamuyi masu, da zarar sun sako oga mu dana wa la’anannen dan sandan nan tarko, dun kuwa sai mun fanshe rayuwar dan ‘uwanmu”
Aba yawo ya fada cikin bacin rai
Audu ya jijjiga kai yai kwafa ,

Subscribe to our newsletter
Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Leave A Reply

Your email address will not be published.