ABOKAI littafi na biyu 2 part 4

ABOKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- by Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2019
Part 4
.
***=====****
Makarantar government college na dauke da sashi-sashi gamida bangare-bangare, kasantuwar makarantar ta kwanace yasa aka gina gidaje da dama aka kebancewa malaman makarantar,
Hatta gidan shugaban makarantar ma a cikin makarantar take kuma bata da banbanci da sauran gidajen
.

Shugaban makarantar government college mai suna malam yahuza ne kwance a saman tangamemiyar gado mai sanda, dattijon ya kasance baki ne ya saki baki yana surnano munshari, bakajin sautin komai a cikin madaidaicin dakin face sautin munsharinsa mara dadin sauraro
,
Bayan shudewan kankanin lokaci, wayar salulan dake ajjiye a saman hannun gadon da dattijon ke kwance akai ta fara burari sautin wakar mamman shata na futa daga cikinta,
.
Cikin kasala dattijon mai suna Yahuza ya mike zaune yana mai mika,
mika hannu yayi ya dau wayar tasa, ya danna sannan ya kara a kunnensa, “hello me yafaru ne muhammed da sanyin safiyarnan, ka danno min kira, “
Dattijo yahuza ya fada yana mutsistsika idanuwansa,
Lokaci guda dattijon ya zazzare idanuwa alamar kaduwa cikin daga murya yace “Inna lillahi wa’inna ilaihirraj’un , yaushe abun ya faru” ya fada sannan ya sauko daga kan katifar , alamun baccin dake tunkushe a idanuwansa da zu sukai fitar burgu,
.
“Okey muhammed ga ninan zuwa yanzu” dattijo yahuza ya fadi yana mai ajjiye wayar akas,
Cikin sauri ya shirya cikin manyan kaya zariya, ya fice daga dakin,
Yana fitowa daga cikin dakin ya nufi wani sashe na makarantar cikin sauri
Irin yanayin yadda yake tafiyar ma ya isa ya fahimtar da mutun cewa a matukar razane dattijon yake,
______
“Yallabai ina kwance a gidana shugaban dalibai (headboy) ya kirani a waya yake sanar dani wai daliban Gongola house da benue house an tashi da safiyarnan ba’a gansu ba daga siniyoyin har juniyoyin,
Ban yi kasa a guiwa ba na kiraka na sanar dakai”
Bakin mutumin da ke zaune akan kujera ya fada yana fuskantar malam yahuza,
.
“Inna lillahi wa’inna ilaihirra ji’uun, wannan masifa dame tai kama, Allah kadai yasan ko me ya faru da daliban nan, amma yanzu bamuga ta zama ba, dole mu sanarwa da jami’ai yanzu don asan halin da alke ciki”
Dattijo ya fadi yana duban mr mohammed dake zaune a gabansa, lokaci guda ya ciro wayar salulan dake aljihunsa ya yayi dan latse-latse a wayar kana ya kara a kunnensa
____
Cikin kankanin lokaci Labarin batan yaran makarantar government college keffi ya karade ilahirin Nijeriya tamkar ruwan dare, ya kasance ko wata gidan talabijin, gamida gidan rediyo labarin suke, hatta a kafar sadarwa ta zamani (social media) sai da mutane sukai ta yayata labarin
Inda wasu mutanen ‘yan kara wa labari gishiri ke cewa Aljanu ne suka kwashe yaran, dama tun can ana rade-radin akwai aljanu da gwaigwai a makarantar,
Irin wayannan labarai na shaci fadi suke ta zagaye kafar sadarwa,gidajen talabijin hade da gidjen rediyo
.
Acp kamalu dan jihar Zamfara ne acan yayi karatun islama da na boko har ya kaiga shiga jami’a duk da mahaifinsa malam Koje ba wani karfi ne da shi ba amma hakan bai hana ya dage sosai ganin ya samawa kamalu karatun boko ba, har dannasa kamalu wanda ya kasance mai matukar hazaka, ya kai ga zama dan sanda mai babban mukami,
.
Tun daga lokacin da kamalu ya fara aiki sai ya kasance yana tafiyar da aikinsa cikin gaskiya, baya taba sassauta wa masu laifi, ko karban Rashawa,
Irin yanayin jajircewarsa cikin aikin yasanya manyansa suka runga sauya masa wuraren aiki ,
.
Sanin irin kwazonsa da jajircewarsa akan aikin nasa ya sanya aka damka masa kes din sidi kashe babba kashe yaro, da yaransa inda aka daura mai alhakin kamosu,,,
___
Acp kamalu na zaune cikin ofishinsa yana nazarin wasu takardu,yana sanye ne da shudin rigan kanti mai dogon hannu hade da farar wandon jeans, ya maida hankali sosai wurin nazarin takardan dake ajjiye kan teburin daya tokare gabashi da yamman ofishin,
.
Kofan ofishin ne ya bude wani tsamurarren dan sanda ya shigo yana zuwa ya sarawa Acp kamalu, yace “sir dan ta’addan nan ba karamin dan ta’adda bane babu irin azabar damu gana masa ba amma yaki fada mana wanda ke basu aiki, yanzu haka ya na can a kwance a magarkama sai dariya yake tamkar zautacce,”
,
Acpn kamalu ya mike tsaye batare daya dubi tsamurarren kurtun dan sandan ba yace mai “ok ku koma bakin aikinku kawai bazan je na duba shi”
“Ok sir” dan sandan ya fadi sannan ya juya ya fice daga dakin,
,
Fitansa ke da wuya acp kamalu ya fito daga ofishin nasa ya nufi bangaren magarkama kai tsaye ya wuce magarkamar da aka kulle dan ta’adda sidi a ciki,
Yana shiga yayi arba da dan ta’addan shimfide a kasa yana murmushi, Sidi ya dago kai ya dubi acp kamalu yace “jiya kace muddin ban sauya ra’ayi ba zaka kawar dani a yau, shin kazo ka kawar danin ne”
,
Acp kamalu ya jawo wata kujeran karfe da ke girke a cikin magarkaman, ya zauna ya dubi sidi “har yanzu ina kan bakata, dun haka in kana da wasiyya maza ka fadota tun kafin harsashin bindigata ta ratsa cikin kwakkwalwarka” yafada alokacin daya zaro karamar bindiga daga mararsa,
.
Dan ta’adda sidi ya bushe da dariya, yana yi yana kyakyatawa wannan dariyar itace ta fusata acp kamalu, cikin fushi ya dirkawa dan ta’adda sidi Alburushi a kafan hagunsa,

Tsananin zafin da ta ziyarci kafan dan ta’addan ne ta sanya babu shiri ya kwarma ihu, wacce tai ansakuwwa a ofishin yan sandan baki daya,,
Har yanzu bakin bindigar Acp kamalu yana fuskantar Sidi, “ai ba lokaci daya zan kasheka ba, sai na jiyar dakai dacin mutuwa kafin na hallaka ka”
Acp kamalu ya fadi dan ya tsantsa na kokarin danna kunamar bindigar
.
“Kasani cewa muddin ka kashe ni to ka tsokano tsuliyan dodo ne, domin kuwa yarana baza su taba bari ku zauna lafiya ba, iyanzu da kuka kamani ma nasan ba shiru zasuyi “
Dan ta’adda sidi ya fadi cikin yanayin mugun hali,
.
“Kamar yadda muka kamaka muka kasheka, suma haka zamu kamosu mu kashe shu,” acp kamalu ya fadi haryanzu bakin bindigarsa na fuskantar dan ta’addan dake kwance magashiyan akas, kafarsa ta hagu tana bulbulo da jini,
.
Dan ta’dda sidi ya cije baki sakamakon radadin da kafar tasa ke masa wanda yake haurawa har tsakiyan kansa, yaja doguwar nishi yace “shawara nake baka kada ka kasheni, kada ka kasheni”
,
Acp kamalu yayi tsaki “shawarar taka ta banza,amshi wannan”
Yafadi yana mai kokarin sakin Alburushi daga bindigarsa,
Kwamishina Abdullahi makeri ne ya shigo magarkaman a guje Dede lokacin da acp kamalu ke kokarin kashe dan ta’addan,
Cikin kankanin lokaci ya fahimci abun da mataimakin nasa ke kokarin yi hakan yasa ya kariso a guje don ya tsaida matemakin nasa,,
Yana karasowa wurin ne Karar fitar alburushi gamida ihun dan ta’adda sidi suka karade magarkaman..
__
Kusan abubuwa uku ne suka faru lokaci daya,
Ihun da dan ta’adda sidi ya kwarma, danna kunamar bindiga da Acp kamalu yayi gamida sauri da kwamishina yayi ya ya canja akalar hannun acp kamalu ta fuskanci wani sashi daban na magarkamar ta hanyar dukan hannun da yayi da kafarsa
.
Dan ta’adda sidi ya sadakar cewa ya mutu, a firgice ya dafe gefen cikinsa, amma cikin mamaki sai yaji babu wani radadin daya ziyarci jikinsa, yayi karfin hali ya mike zaune yana dudduba jikinsa ko zaiga inda acp kamalu ya harbesa, amma babu..
.
A fusace acp kamalu ya juyo don ganin wanda yai doki hannunsa
Lokaci guda ya kame sannan ya sarawa kwamishina, yace “yallabai naga babu amfanin ajjiyesa tunda yaki fadan waye ubangidan sa shine nai..”
Kwamishina ya katsesa ta hanyar daga mai hannu yace “ka same ni a ofishina yanzu”

Subscribe to our newsletter

Leave A Reply

Your email address will not be published.