ABOKAI littafi na biyu 2 part 3

ABOKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- by Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2019
Part 3
.
Agurguje daliban suka karisa fita daga dakin,
*****=====******
Lokaci guda haidar,jibrin,Hassan da mansir suka mike daga wurin Aliyu suka fara dumfarar yan ta’addan, izan ka kalli fuskokinsu zaka tsinkayi babban tashin hankali shimfide akan ta hakanan kuwwan fansa na tashi daga cikin idanuwansu,
.
Yan ta’addan biyu suka seta bakin bindigoginsu yana fuskantar ABOKAN,
“Ku tsaya a inda kuke ko yanzun nan mu aika daku,inda na aika dan uwanku” Audu ya fadi yana kokarin sakin harsashi
Cikin zafin nama silli ya wafce bindigarsa lokacin daya fahimci kudurinsa yace “haba Audu so kake ka batamana shiri, bafa kisa ya kawo mu nan ba, “
.
Ran Audu a bace ya dubi silli yace “dan ubanka bakaga su neman kashe mu suke ba, zuwa garemu sukefa” Silli ya juya ya dubi Abokan har yanzu suna kokarin kusanto inda suke,
Ba shiri Audu da silli suka fara ja da baya don sunyi matukar razana da yanayin da suka tsinkaya a fuskar ABOKAN
.
Haidar,jibrin,hassan da Mansir tafiya suke idanuwansu a rufe basa ganin komai face yan ta’addan nan, babu abunda ke tashi a zuciyoyinsu face wutar fansa, ….
Haka suka cigaba da nufar yan ta’addan da bakar fuska, duk da kashedi gami da barazanar da yan ta’addan ke yi masu hakan bai sa sun tsaya ba,,,
.
“HhhhHhhhhhjjjjj” sautin nishi ya fara tashi daga bayan Abokan, cikin sauri Abokan suka juya lokacin da suka jiyo sautin ko tantama basa yi sautin na fitowa ne daga jikin Abokinsu Aliyu dake kwance a kasan dakin,,,,
Da gudu suka isa wurinsa, suka iske idanuwansa a bude hancinsa na surnano nishi sama-sama
.
Mansir ya mike ya debo ruwa a karamin kofi ya zuba wa Aliyu aka, sannan ya bashi ya sha,
Duk wannan Abu dake faruwa yan ta’addan biyu suna daga nesa a tsaye, hakanan daliban dakin ma suna takure a gefe daya, zuciyoyinsu cike fal da tsoron shedanun yan ta’addan nan,,
.
Audu ya fisge bindigarsa daga hannun Silli sannan ya nufi wurin Abokan wayanda suke durkushe,
Hasan ya tallabo bayan Aliyu suka zaunar da shi, har yanzu bai gama dawowa cikin hayyancinsa ba,
“Aliyu kana jina? Nine Aboki” haidar ya fadi yana jujjuya tafin hannunsa a gaban fuskar Aliyu
Kwatsam ba zato ba tsammani sai gani Abokan sukai an janye Aliyu daga zaunen da yake, an daga shi sama,
.
“Kai wai su waye ku ne? Me mu kai maku ne ” hasan ya fadi cikin muryan bacin rai
Audu ya zaro doguwar wuka daga mararsa ya aza a wuyan Aliyu sannan yace “Mune Guguwan Annoba, anai mana inkiya da Gobara daga Kogi, mune muka gagari nahiyar Africa, ba ku mana komai ba, hakanan ba cutar da ku muka zo yi ba amma muddin ku kayi taurin kai kuka bin umarninmu to dukkanku sai mun hallakaku sannan mu aiwatar da kudurinmu, kuma takan Dan uwan kunnan zamu fara”
.
“Me kuke son mui maku, dun Allah kada ku kashe shi koma menene zamuyi maku” jibrin ya fadi hawaye na bin kumatunsa
Silli ya kariso wurin
Audu ya dubeshi yace ” a fara aiki silli”
Rufe bakin Audu ke da wuya Silli ya dubi daliban yace da su ” ku wuce mu tafi”
Ba musu daliban dake a matukar tsorace wayanda adadinsu yakai ashirin suka nufi kofan dakin, ,,,
Suna zuwa bakin kofan ne suka ci karo da abinda ya sanya da yawa daga cikinsu sakin fitsari a wando,
.
Doguwar bakin bindigace ta faro danno kai cikin dakin sannan Aba yawo ya shigo dakin fuskarsa tamau ya dubi daliban dake bakin kofan,ya daka masu tsawa “dan ubanku baza kuyi sauri ba”
A firgice cikin tsananin tsorata daliban suka fita daga dakin
Suna futowa suka yi arangama da wasu daliban,,
.
Audu ya saki Aliyu cikin matukar galabaituwa Aliyu ya sulale zai fadi kasa, kafin ya kai kasan haidar da mansir suka dago shi, haidar ne yayi goho mansir ya dora masa Aliyu a bayansa sannan suka fice daga dakin…
….
Cikin kankanin lokaci yan ta’addan suka yashe gaba dayan dakunan kwanan dalibai na GONGOLA HOUSE da BENUE HOUSE, cikin sa’a basu samu wani mishkila
.
Gungun dalibai ne da adadinsu yakai dari biyu 200 hade da shaidanun yan ta’adda hudu ke ratsa cikin dokar dajin, dajin yayi tsit sakamakon dare daya tsala in kadauke kukan kananun kwari dana tsuntsaye gamida karar taka busassun ganyayyaki da daliban ke mutanen ke takawa babu wani sauti dake tashi,,,,
.
Doguwar tafiyace ta kai su ga inda yan ta’addan suka faka doguwan motarsu har a lokacin Abokan biyar na tare da juna zuciyoyinsu a cike da bakin ciki, bawai kwashe su da yan ta’addan sukai bane ke damunsu , Halin da dan uwansu,Amininsu kuma Abokinsu Aliyu ya fada shine babban abun dayai matukar tayar musu da hankali
.
Kafin wannan daren da Abokan suka kirashi da MUMMUNAN DARE Abokan sun kasance suna rayuwa cikin farin ciki, Annushwa, gamida fara’a
Amma bayan wanzuwar daren sai farincikin dake rayuwansu ta juye izuwa bakin ciki, Annashwar da suke wa junansu ta rikide izuwa ruwan hawaye,,, akoda yaushe fuskokinsu cikin fara’a take, da yawa daga cikin dalibai sukan ce da su “ABOTAR ku tana birgemu,”
“Ina ma ina daga cikinku”
“Ban taba ganin ABOKAI irin ku ba Arayuwata”
Irin wayannan maganganu dama wasu sune dalibai,malamai da ma’aikatan makarantar ke cewa da su
.
Jagwa dake gaban daliban ya nufi bayan doguwar motar ya bude murufinta, yai wa daliban inkiya da hannu kan cewa su shige cikin motar,

****=====****
Sidi kashe babba kashe yaro asalinsa dan Adamawa ne, tun yana shekarun yarinta ya shiga Duniya neman kudi, A lokacin bai fi shekaru goma sha biyar ba, ya kware sosai wajen sane da yanke aljihun mutane, ya yawata gari gari a sassan Nijeriya, kafin daga baya ya koma fashi da makami inda ya hada gungun yaransa su biyar wayanda suma duk a yawon duniyar suka hadu,
.
SIDI kashe babba kashe yaro yayi ta’adddanci babu adadi a kasan Nijeriya , a ka’idansa muddin aka futa aiki to babu babba babu yaro duk wanda ya kawo wargi kashe sa ake, hasalima ta nanne ya samo sunan KASHE BABBA KASHE YARO
.
____
Karamin dakine mai wadataccen fadi, hasken kwayayen lantarki ya karade dakin,
Acp kamalune zaune kan kujera, a gabansa kuwa dan ta’adda Sidi kashe babba kashe yarone,
Acp kamalu yaja doguwar numfashi ya idanuwansa na kan dan ta’addan da kamanninsa suka canja yace “kana baiwa kanka wahala kana kana bama shari’a wahala, izan da ace ka sanar damu abubuwan da muke bukatan ji daga gareka da tuni yanzu haka kana magarkama, amma taurin kanka ya hanaka, kasani nan da gobe muddin baka fada mana wa ke saka ku aikata ta’addanci ba, to ni da kaina zan harbeka”
.
Koda dan ta’adda sidi yaji haka sai ya bushe da dariya sai da ya dau lokaci mai tsayi yana dariyar, sannan yai shiru, cikin dakewa yace “me nene mutuwa, kai kake tsoronta bani ba, don ni kullum acikinta nake, yan sanda ku ke tsoron mutuwa amma mu yan ta’adda bama tsoronta hasalima bamu santa ba”
.
“Ai ko gobe zan dandana maka dacin mutuwa” Acp na kamalu ya fadi sannan ya mike tsaye ya nufi kofan ficewa daga dakin, sai da yakai bakin kofar dakin ya juyo ya dubi dan ta’adda sidi yace “na baka daga yau zuwa gobe, ka canja shawara domin kuwa babu makawa gobe sai na alburusheka”
Yana gama fadin hakan ya fice daga dakin,
Dan ta’adda sidi ya sake fashewa da dariya a karo na biyu ya dau tsawon lokaci yana kyakyatawa, lokaci guda ya tsaida dariyan da yake ya dauki wani sanda dake ajjiye a gefensa da taimakon sandan ya mike tsayi, cikin dingisawa ya nufi gabashin kusurwan dakin, ya daga kai sama yana kallon CCTV camera dake like a saman bangon dakin, yayi murmushi mai ciwo sannan yace “ku yan tsinannu da sannu zakuyi nadamar abun da kuka aikata mana,”
……
Jami’an yan sanda biyu dake zaune a cikin ofishin acp kamalu suna kallon abun dake faruwa tsakanin Acp kamalu da dan ta’adda sidi a cikin na’ura mai kwakwalwa, suka jinjina kai
“Kana ganin yallabai zai iya kashe shin ” jami’in dake gefen dama ya fadi yana duban dayan dan sandan
“Ai muddin yallabai ya fadi magana to se ya cikata, hala baka da labarin irin jajircewansa, sabida gaskiyansa hade da kwazonsa a aiki yasa ake tayi masa canje canjen wurin aiki, kuma duk garin da yaje sai ya share yan iskan cikinta ya zuba su cikin kwandon shara, bindige dan ta’adda a wurinsa ba wani abune mai wahala ba,”
Dan sandan dake gefen hagu ya fadi yana kokarin mikewa tsaye
“Tab lallai lamarinsa ya girmama”

Subscribe to our newsletter

Leave A Reply

Your email address will not be published.