TASKU littafina daya 1 part 8

 TASKU littafina daya 1 part 8
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 04 Dec, 2018
Upload Time 12:40 pm
Hits 192 Hits
Comment No Comments

Description

TASKU
kirkirarren labari
daga Shuraih 99%
Littafi na daya 1
Part 8
.
. Daga nan bansan kome ya faru dani ba , Idanuwa na ne suka fara budewa, na dan fara gani dishi dishi, . Toh a sannan ne idanuna suka washe na fara gani da kyau, . Kwance nake bisa wani katifa mai dan karen laushi, a gefena ga mahaifiyata! Da mahaifina, Gefen haguna kuwa, Mjd nagani shida Anas , . Na dan mike da kyar na jingina da bangon wAjen wanda nake tunanin asibiti ne, . “Sannu, koma ka kwanta,” mahaifiyata ta fada, a lokacin data ke dubana . Sai a sannan ne na lura da kafata na hagu , wani dogon karfe ne a gefen gadon a sakale ajikin karfen wani farin bandeji ne wanda ya taimaka wajen tallafo kafata, izuwa sama, Wajenda wannan karen ya dan kara min cizo, an dabaibayeshi da bandejii . Sai a wannan lokacinne a bubuwan da suka faru dani suka fara zarya a cikin kwalkwalwata . Na tuna lokacin dana bingire kasa, abin da kunnuwana suka jiye min na karshe shine*n sautin kukan rufaidah, . Na dubi mahaifiyata nace mata “umma ya akayi na zo wajennan,” . “Abokinka ne ya dauko ka, kaida wata yarinya, a can wani angwa,” ta ce dani tana duban mjd . Mjd najin haka ya matso kusa dani sannan ya dafa kafaduna,” Nazo gidankune nemanka shine aka sanar dani baka nan, dana tambayi umma shine tace min tun da mukayinnan ne haryanzu ba ka da wo ba” Yadan sauke ajiyar zuciya sannan yaci gaba”toh a lokacinne nakira wayarka, bayan an dauka ne naji sautin mace kuma da alamu kuka take, anan ta sanar dani halin da kake ciki, tai mani kwatancen, wajen da kuke , Ina zuwa kuwa na iske baka cikin hayyacinka, nan na daukoku izuwa wannan a sibitin yanzu haka ita tana wancen bangaren, amma abin dana keso dakai, ka kwantar da hankalinka babu abinda ya sameta, kawai, dai dan kurkurjewan da tayine ake yi mata treatment nashi” . Na mayar da dubana wajen mahaifina , wanda ya hada rai tamkar an turo masa da sakon mutuwa, “baba…..” Yada katar dani ta hanyar daqa mani hannu alamar baya bukatar wani zance. . ********* *********** ****** Zaune nake a tsakar gidanmu, a gefe ga ummata, tana gyaran shinkafa, , Yau kwana daya kenan da sallamata daga asibiti, Tun alokacin na fahimci mahaifina yana daddaure mani, Koda na gaishesa sai dai ya amsa a cikin daure fuska, sabanin daa . . Gidan mu gidan mutuncine sannan mahaifina malamine, Sunansa, Mu’azu toh sabida malumtarsa sai ake kiransa da Malam Mu’azu, Ummana itace kadai matarsa, sunanta, Maryam, ana mata lakabi da mairo, ni kuma umma nake kiranta, kuma nine kadai dan da suka haifa a duniya, . Bakaramin ji dani mahaifina yake ba, dun ya nunamani gata, tun ina karamin yaro, har nafara girma, toh a sannan ne yasaka ni awata makaranta ,SOKOGA,private ce nayi nursery da primary acan daga baya kuma na koma KDF acan ne nayi secondry school dina , Dana idar sai na sami admission a NSUK, ina karanta fannin Engineir, , Shekaruna biyu kenan da fara aiki da wata kamfani na kera kayan motoci da na mashina, a Abuja, . A ka’ida ta duk ranar jumu’a, ina zuwa gida nayi hutun mako tare da mahaifana, . Wannan makonma hutun nazo dana san abin da zai faru dani kenan tabbas da na hakura da wannan hutun, , Muna namu Allah na nashi, Wannan shine takaitaccen tarihina . Kubiyoni a part 9 . Its Shuraih 99%

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: