TASKU littafina daya 1 part 7

TASKU
kirkirarren labari
daga Shuraih 99%
Littafi na Daya 1
Part 7
.
. Wasu murdamurdan karnukane su biyu, jikinsu sur gashi, girman kowani dayansu yakai girman kosashshen rago, baki bude suka nufo mu suna haushi, , Sam sam karka dauka wai ina jin tsoron karnuka , Toh ni da anguwarmu ma cike yake da karnuka . Toh amma da nai arba da wayannan kosasssun karnukan sai da hantata ta kada , domin ban saba ganinsu ba . A dai fina-finan indiya da america ina ganinsu, toh amma a zahiri dai yaune mukayi kicibis dasu . Koda wayannan karnuka suka fara kusanto mu Sai rufaida ta rude ta tsuguna a kasa ta rufe fuskarta, . Haryanzu wukar dana cire a kugun katonnan yana hannuna , Nan na kara damkeshi da kyau tamau, . Karnukan suka daka tsalle a lokaci daya suka fado jikina , a sannan ne suka mangareni na fadi akasa, . Rufaida na ganin hakan sai ta taso daga tsugunen data ke ta dauki wani shirgimemen dutse, Tayi nasarar jefar kare guda da wannan dutsen sai dai , dutsen bai jimata rauni ba, . Karnukan dukkansu suka juya izuwa kanta, na tabbata izan har suka, isa gareta , lamari ya baci . Cikin sauri na yi gudu na wawuri kare daya na yafa da kasa sannan na caka mai wuka a kafarsa daya, nan ya kwanta sai shureshure yake, dayan karen na ganin haka, sai ya dubeni sannan ya nufo ni cikin gudu . Koda ya rage baifi zira’I kadan muhadu ba sai ya daka tsalle ya fado jikina yasanya gaba daya farcensa a gefen wuyana bakinsa kuwa wadda take wangame tana saitin maqokwarona, nufinsa ya fasa makoshina da fikarsa . Koda na fahimci manufarsa, sai na yunkura don na yi cilli dashi amma naji na kasa sakamakon dannenin da wannan karen yayi, . Karfin tsiyane da shi, da kyar na tureshi daga jikina, . Sannan na bishi na kama bakinsa na caka mai wukar a tsakiyar ka har sai da ta fito ta cikin bakinsa nan take yafadi kasa matacce, , Na nufi wajen rufaida wacce tagama tsorata da wayannan karnukan . Nakama hannunta muka tashi tsaye, Toh a daidae wannan lokacin ne al’amarin ya faru, Wani radadine ya ziyarce kafata, na’zata ko zarto ne aka sa za’a yanke kafar, sai a sannanne idona yai arba da dayan karennan ya damfara wa kafata cizo, . Na janye kafata daga bakinsa, na dan rarrafa, ina cikin rarrafen ne naji hannuna ya taba wani abu , . Bakomai bane illa guntun bulo, ji nayi saukar karennan a ruwan cikina, . Ai ban tsaya wata bata lokaci ba na rarumi wannan bulo din na maka masa aka, Nan yayi gefe, ya bingire a kasa koda naga haka sai na tashi, na hau ruwam cikinsa, nai ta maka masa wannan bulo din aka har sai da bulo din ya juya izuwa gari, , Sai a sannan ne hankalina ya dawo jikina na yunkura na mike tsaye , , ******** *********** ******** , Munyi tafiya mai nisa a cikin wannan daren, Har muka iso daidai wajen wani gada wanda a akasar wannan gada ba komai bane illa wani katon kogi, shi wannan kogin ana mai lakani da mahannu, . Muna zuwa daidai gadan na turje sakamakon kafata data ke yimin wani mugun ra dadi, . Na dubi rufaida na ce da ita, “duk da mun kasance muna cikin halin tashin hankali, toh wannan bazai sa na gagari furta miki sakon zuciyata ba” . Ta dubeni cikin alamun rashin fahimtar inda zance na ya nufa “Tun lokacin dana fara ganinki, lokacin da idanuwa sukai arba da wannan kyakyawar fuskar taki, tun a sannan wani mashi mai dauke da dafin sonki ya ca keni a kahon zuciyata, Kece kawai maganin wannan dafin sam sam wannan lalurar dake jikina bai dameni ba, Don muddin akan kine zan iya, sadaukar da rayuwata, Kisani Rufaida I NA SONKI, Bawai so na fatan baki ba sannan bawai so irin na mayaudara ba , ke wata ginshikice na a cikin rayuwata” Ina gama fadin wannan kalmar na bingire kasa sumamme. Daga nan bansan kome ya faru dani ba , . Ku biyo ni a part 8

Subscribe to our newsletter
Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Leave A Reply

Your email address will not be published.