TASKU littafi na daya 1 part 3

 TASKU littafi na daya 1 part 3
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 04 Dec, 2018
Upload Time 12:12 pm
Hits 202 Hits
Comment No Comments

Description

TASKU
kirkirarren labari
daga Shuraih 99%
Littafi na Daya 1
Part 3
.
.
“Amma Fa daga ninta kaga yar babban gida, ” cewar mjd
.
“Ba yar babbar gida ba koma meye sai , amininmu ya shawo kanta” anas yafada yana kallona , yana dariya
.
Na dubesu a tsanake nace “koma dai menene gobe zamu ga gidansu ai” .
**************
Ina Kwance nake bisa kan katifata , idanuwana radau suna kallon katakon silif(batre)
A sannan ne A gogon bangon dake rataye a jikin bangon dakina ya nuna karfe 1:00AM, na dare,
.
Wannan ne ya tunasar dani daga nannauyan tunanin dana fada,
.
Yanzu haka wajen awanni biyu kenan da tafiyan su mjd da Anas
Tun daga lokacin nake ta Allah Allah barci ya daukeni Amma ina dana runtse idanuwana sai fuskarta ta bayyana yayin da siraran lebbanta ke furta kalamai tamkar bazasu furta ba
.
Naso ace na baiyana mata sakon zuciyata ,
Naso ace Na san sunanta
Naso ace nasan gidansu
.
Duk wayannan ban damu dasu sosai ba saboda nasan gobe duka zan sansu amma ,abin dana damu da shi sosai shine, shin zata karbi kokon barana,
Shin zata amince dani a matsayin masoyinta
Shin zata yadda nazama abokin rayuwarta
.
Da irin wayannan tunanin ne har karfe biyu yayi a sannan ne wani nannauyan barci ya ziyarci idanuwana .
***************
Bani da farkawa ba sai wajejen 7 bakwai na safe,
A sannan ne na tashi na nayi wanka sannan nayi kalaci(break) da shike yau Take RANAR SALLAH
.
Wata shadda tace fara mai daukar idanu Na sanya sannan na sanya hula zanna bukar fara sol amma tuntunta bakine sidik.
.
Sai kiran nomban mjd nake amma taki shiga ,
.
Dadai na gaji da kirar sai na fito daga gida , nan na tare dan acaba, nai mai kwatancen wajenda zai kaini,
.
Saukana keda wuya na nufi wajen bakaniken ,
Ina zuwa na tarar dashi yana gyara wata mota, nai mai sallama, sannan nace mai “Dafatan ka idar da gyaran”
.
“Sai oga an idar ko tuntuni”
“Da kyau ai hakan yayi”
Daga nan na shiga cikin motar na tashe ta sannan na hau kwalta,
.
Daidai lokacin dana faka a kofar gidansu mjd , daidai lokacin shi kuma ya fito Yana sanye da shadda shima farace amma bai sanya hula ba,
Sai wata kalar aski daya yi mai taken dakalin shedan(punk)
.
Yana ganina yazo muka tafa sannan yace dani” baba ai nasan sai ka rigeni isa wajen bakaninkennan “

“A’a nai ta kiran wayarka amma ban sameka ba shiyasa kawai naje na dauko”
.
“Oh shit wayan tana hannun kanwata wallahi, amma no problem, muje kawai”
Ya bude gidan gaba na mai zaman banza ya shige,
“Ina muka nufa” nafada yayin da nima nake kokarin shigowa cikin motar,
“Masallaci mana”
“Ok” kawai na fada sannan na tashi motar muka nausa
*************
Hon na rangada a bakin get din gidan sannan wani tsakurarren mai gadi ya fito hannunsa rike da kulki , sai da yazo daf da motar ya kare mata kallo sannan ya je ya bude get din
.
Awan mu biyu kenan da tashi daga masallacin idi,
A sannan ne muka rankayo izuwa adress din data bamu,
.
Tabbas gidan ya hadu ba laifi muka nufi wajen parking
.
Bayan mun parking motar mun fito mun tsaya,
.
“Toh sai mu shiga koh yallabai” mjd ya fada yayin daya fara tafiya yana dumfarar kofar da zata sada shi cikin gidan,
Nan nima na mara mishi baya
.
Maigadin ne yai mana iso cikin rantsastsen falon maigidan,
Muna zama shima ya fito ya dubemu sannan muka gaisa,
Bayan mun gaisa ne yake tambayarmu ” ko kune rufaida tace mani zaku kawo mani mota”
.
“Kwarai kuwa mune nan baba” Mjd yabashi amsa “Kuyi hakuri da abin daya faru jiya”
.
“Babu komai baba ai komai mukaddarine daga Allah,”
.
“Ni kaina saida nayi mata fada akan irin abun datai maku da tace sai kun gyara motar”
.
“Samsam,karka damu da wannan ai komai ya riga ya wuce” Sai hira suke shida anas Ni ko sainaji wata sanyi acikin raina sakamakon jin sunanta danayi RUFAIDA na sake maimaita sunan a cikin zuciyata,
Nan na shiga rarraba idanuwa ko zanga ci sa’a na ganta, domin so nake na sake ganin kyakyawar fuskarnan tata,
.
Har muka idar da magana da mahaifinta wanda bai sanar damu sunansa ba
Muka fito daga cikin falon sannan muka durfafi kofan da zata sadamu da farfajiyar gidan
.
.
“Sannunku da zuwa” naji i muryar da bazan taba manceta ba acikin rayuwata, tana fadi ta bayana
Juyowar da mukayi ne mukai arba da,ita kamar kullum yauma tana cikin wani dogon rigane harkasa sannan ta yafa wani gyale wanda yai matukar dacewa da kalan rigan jikintan,
.
Ai bansan lokacin dana saki baki Galala ina kallonta ba . Tobe conti

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: