ABOKAI littafi na biyu 2 part 2

ABOKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- by Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2019
Part 2
.
“Kikkirrkirrrrkirr……”
Sautin karar bude kofan dakin ya katse masa tunani, lokaci daya ya mike ya dubi kofan dakin yana mai tu’ajjibi
.
“Waye wannan” Aliyu ya fadi cikin siririyar muryarsa
“Ubankane” Audu ya bashi Amsa yayin da suka shigo cikin dakin
A rude Aliyu ya dubesu duk da baya iya ganin fuskokinsu da abubuwan dake hannunsu amma yaaji ajikinsa ba mutanen kwarai bane
Tunani ya fara akan yadda akai har suka shigo dakin shi da kansa ya kulle kofan dakin ta waje sa’annan ya shigo ta taga, itama tagar ya garkameta
.
“Ya akayi kuka shigo mana daki” Aliyu ya tambaya cikin kakkausar murya
Silli yayi yar karamar dariya yace “fasa kwadon mukai”
“To in fasa kwadon kukai me yasa banji kara ba yayin dakuke kokarin fasawa” Aliyu ya sake tambaya
“Mun sanyawa bindigunmu salansa ce ta yadda ko kai muka harbe ba za’aji karan sauti ba, da hakane muka bazge kwadon” Audu ya fadi yana hasko bindigar dake hannunsa da tocila
.
Lokaci daya Aliyu ya razana sakamakon ganin abunda bai saba gani ba,
“Me mukai maku dun Allah kada ku cutar da mu”
“Ba ku mana komai ba,hakanan muddin kuka bi umarnin mu to zamu rabu lafiya, in kuma aka samu akasin haka, Alburusan bindigata a shirye suke da kasa tsere”Audu ya fadi yana jujjuya bindigarsa
Ya dago kai ya dubi siririn razanannen saurayin dake gabansa a hankali ya tako izuwa gaban saurayin, ya yunkura da nufin ya wuce gaba don ya iski gadon da su haidar ke kwance, kwatsam Aliyu ya sha gabansa yace “dun Allah kada ku cutar da su,domin kuwa sune rayuwata”
.
Audu ya dago kai ya dubi Aliyu ransa a bace yace “dan samari ka gaggauta cire hannunka daga jikina sannan ka matsa min a hanya kafin hushina ya tabbata akanka,”
Silli ya matso kusa da Audu yace “Audu inajin mu kyalesa kawai muyi aikin dake gabanmu domin kuwa lokaci yana dada karatowa”
.
Audu ya dubi silli kana ya dubi Aliyu yace “ok” yana gama fadi ya yunkura da nufin ya wuce amma sai Aliyu yaki matsa masa daga hanya, hakanne ya harzuka dan ta’adda Audu cikin fushi ya daki Aliyu da kotar bindigarsa a tsakiyan ka
.
Kakkarfan Ihu mai kara Aliyu ya saki gami da dafe kansa sannan ya fadi a kasa ko kwakkwaran motsi bai yi
.
Ansakuwwar karar ihun Aliyune ya farkar da dukkan daliban dakin daga barci,
A firgice Jibrin,haidar,hasan da mansir suka farka daga daddadan barcin da su ke, cikin razana suka dubi gabansu,
Anan sukai arba da abun da ya yi matukar tayar masu da hankali, Aliyu suka hango a kwance magashiyan kansa na bulbulo da jini,
“Inna lillahi wa’inna ilaihirra ji’uun” haidar ya fadi lokacin da ya sauko daga kan gadon da suke kwance
“Aliyu me ya sameka” jibrin ya fadi cikin muryan kuka lokaci guda abokan suka ruga don su isa inda Abokin nasu ke kwance, tsananin tashin hankalin da suka tsinci kansu a ciki shine ya makantar da su ga ganin shedanun yan ta’addan dake tsaye a gefen Aliyu,
.
Suna isa inda Aliyu yake kwance suka zube a kas jibrin yayi sauri ya tallafo kan Aliyu dake bulbulo da jini, yana kuka yace “haba Aboki ka tashi mana kada ka tafi ka barmu”
.
Cikin zafin nama haidar ya yanki wani gefe na rigar dake jikinsa ya nade kan Aliyu da shi,
Kalubale na farko kenan da Abokan suka taba tsintar kansu ciki, zuciyoyinsu na dukan tara-tara, hankulansu inyai dubu ya tashi,idanuwansu babu abunda suke sai bulbulo da kwalla,
Babu abunda ya kara tayar masu da hankali sai daukewar numfashin Aliyu, mansir ya kasa kunnensa a hancin Aliyu don jin ko yana numfashi, koda ya tabbatar baya numfashi sai ya dago kansa idanuwansa na zubda hawaye yana cewa “kada kai mana haka Aboki, dun girman Allah ka tashi,ya kake son muyi aboki” yana gama fadin hakan ya kifa kansa a tumbin Aliyu
.
Haidar,hassan da jibrin suka runga sumbatu suna kiran sunan Abokin nasu koda zai tashi,,,,
“Ai bazai taba tashi ba, domin kuwa yayi doguwan bacci wanda bazai taba farkawa, dama kun dena bawa kanku wahala kun mike mun wuce”
Kwatsam Abokan suka tsinkayi wata murya mara dadin saurare tana fadin haka,
Lokaci guda Abokan suka kai dubansu ga wurin da muryan ta fito inda sukai arba da yan ta’addan biyu, suna rike da dogayen bindigu
******========******
“Boys! Boys!! Boys!!! wake up, chidinma! Samson!! Abubakar!!! Habib!!! Steven!ismail,fahad, abeg wake up”
Tsorataccen matashin saurayin ya fadi yana duban daliban dake kwance cikin dakin,
A wurin daliban kuwa ko su san yanayi, sai ma gyara kwanciya da wasu daga cikinsu sukayi
Jagwa ya dubi aba yawo yace “Aba yawo kaga yan iskan yara harda gyara kwanciya, inaga sai mun aiwatar wa dayansu tukun”
“A’a jagwa kada ka fara in baso kake asirinmu ya tonu ba, ” aba yawo ya fada yana kusantar wurin da daliban ke kwance yana zuwa wurin ya sa tafkeken hannunsa ya shararawa daya daga cikin daliban tafi a baya,
.
A razane dalibin ya farka yana mai kurma ihu sakamakon zafin daya ziyarci bayansa,
A haka aba yawo ya runga bin daliban yana tashinsu ta hanyar sharara masu tafi,,,,
,,,,,,,
Dalibai ne da yawansu bazai wuce goma ba a tsastsaye sun takure kansu a wuri guda, yawancinsu suna sanye ne da guntayen wanduna da fararen singileti, kallo daya zakaiwa daliban ka tsinci tsoro karara shimfide akan fuskokinsu,
.
Yan ta’addan biyu Jagwa da Aba yawo suna tsaye a gaban daliban, bakin bindigoginsu na fuskantar daliban,
“Ku wuce mu tafi” jagwa ya fada yana yatsina fuska
Cikin tsoro daliban suka fara matsawa suna nufar kofan dakin aba yawo ya daka masu tsawa yace “kai kui sauri mana, kada ku bata mana lokac…..”
Karar ihun da ya ziyarci kunnuwan dan ta’addan ne ya katse Maganar tasa,
.
“Ihun me waye haka” Aba yawo ya fadi yana kallon jagwa
Jagwa ya yatsina fuska yace “inajin ko wani ne yayi taurin kai su kuma su Audu suka harbesa, kai ka san halin Audu baya da hakuri”
“To ai kuwa ya bata mana aiki dun karar ihunnan babu inda bai ansa ba a makarantar nan “
“Kai dan ubanku baza kui sauri ku fice daga dakin nan ba” jagwa ya fada yana dumfarar kofan dakin
.
Agurguje daliban suka karisa fita daga dakin,
Zancigaba

Subscribe to our newsletter
Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Leave A Reply

Your email address will not be published.