ABOKAI littafi na biyu 2 part 1

ABOKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- by Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2019
Part 1
.
Dare ne mai dauke da sassanyar iska, dake busowa ta jikin bishiyoyin da suka mamaye Dajin, Dajin yayi tsit baka jin motsin kowa sai hargowan iska da kukan tsuntsaye , gamida kukan kananun kwari
.
Doguwar mota trela mai tayoyi goma [ten tyre], ta faka a cikin kungurmin dajin mai yanayin ban tsoro,
.
Direban motar ya fito daga cikin motar yana sanye da bakar rigar sanyi, ya kifa hula hana salla a kansa,
Bayan yan dube-duben da direban yayi sai ya koma cikin motar,
.
Bayan shudewan lokuta kalilan sai mutane hudu suka diddirgo daga cikin motan, direban shine a karshe
daya daga cikin mutanen yace “kai silli futo mana da kayan aiki,”
Wanda aka kira da silli ya koma cikin motar,
Izan ka dubi mutanennan zaka ga ba wasu bane illa, JAGWA,AUDU da ABA YAWO sai kuma direban motar,
Silli ya sauko daga kan motar hannunsa rike da jibgegiyar akwatin karfe, ya damfare akwatin da kasa, yace “ga kayan na kawo audu”
Audu yayi murmushi wacce tafi kama da kuka, ya sunkuyo ya kama murufin akwatin ya budeta
.
Dogayen bindigogine kirar AK 47 maqire a cikin akwatin, Audu yakai hannu yana shafa bindigogin, ya karkata bakinsa sannan ya bushe da dariyar mugunta sautin dariyar ta amsa a cikin dajin tamkar a ansakuwwa
.
Jagwa ya sunkuyo ya debi bindigu uku, ya mika wa Aba yawo daya, dayan kuma ya mikawa Silli, ya dubi audu yace “muje”
Audu ya dau bindiga daya ya tokare bakinta a sama, yace “dafatan kun dau hanyar da kyau yadda yanzu ba za mu manta taba”
“Haba Audu Sati daya fa muka dauka muna yin shirinnan ai babu inda muka manta don gaba daya Taswirar hanyar da ta makarantar gamida ta eriyar a kaina suke” Silli ya fadi yana kokarin rataya bindigar a kafadarsa
.
Gajeruwan tafiya ce ta kaisu ga riskan katangar makarantar Government College keffi, suka kariso jikin katangar da bata wuce kamu goma ba, sukai cirko cirko silli ya fiddo wata takarda daga cikin Aljihunsa, ya ajjiye a kasa sannan ya haska takardan da yar karaman tocila mai karamin haske, yace “wannan shine taswirar makarantar gaba daya, zamu shiga makarantar ta katangannan” ya nuna wani gefe a jikin taswirar sannan ya cigaba “hostel din makarantar guda Shida ne, dukkan su suna wurare daban daban, a tsarin da mukai hostel biyune zamu kama, dun haka muna shiga makarantar ta nan zamu fara cin karo da hostel din Gongola house, ta kanta zamu fara , bayan mun kame dukka daliban hostel din jagwa da aba yawo zasu iza keyarsu wurin da motarmu take, ni da kai ” ya nuna audu “sai mu wuce Benue house mu kama daliban hostel din duka, sai mu hadu a wurin da muka faka motarmu,,,”
Silli ya karashe bayanin yana duban fuskan Audu sannan ya dau taswirar ya jefeta cikin aljihu,
.
“Kace babu masu gadi a makarantar” jagwa ya tambayi Silli
Silli yayi wata fatalwar murmushi wacce ta kara fidda munin fuskarsa yace “babu masu gadi a makarantar, imma da su ai saimu kawar da yayan banza, jikokin fir’auna”
.
Yan ta’addan su hudu suka haura katangar makarantar inda suka fada cikin surkukin daji mai duhu a cikin dajin sukai ta tafiya har suka iso gaban Hostel din Gongola house
.
Fasalin Ginin da a kaiwa hostel din fasalin ginin zamanin da ne, an shafe bangon hostel din shudin fenti, hasken farin wata ya haskaka hostel din ,
.
Damar da yan ta’addan suka samu kenan wurin karewa hostel din kallo,lokaci daya yan ta’addan hudu suka tallafo bindigoginsu suka daidaita su a hannuwansu cikin sanda suka nufi dakunan kwanan daliban,
Jagwa da Aba yawo suka durfafi shashin dama yayin da Silli da Audu suka nufi shashin Hagu
“Yana ga dakunan a garkame da manyan kwaduna” Audu ya fadi yana duban dakunan hostel din dake garkame da manyan kwaduna Silli ya fiddo da salansan bindiga daga aljihunsa yace “ai daliban ne suke kulle kansu”
.
“Dole sai de mu balla kwadunan ” Audu ya fadi yana kokarin daura salansan bindiga a bakin bindigarsa,
Silli ya saita bakin bindigarsa a kan jibgegen kwadon dake sakale a jikin kofan dake gabansu,
Sannan ya saki ma kwadon wuta,
.
Ba shiri jibgegen kwadon ya balle, silli ya sanya bushasshen hannunsa dake boye cikin safa ya cire kwadon daga jikin kofar yai wurgi da shi gefe daya,
Ya kama marikin kofan ya bude dakin, sannan ya kutsa kai ciki,
…..
Jagwa da Aba yawo suka iso bakin wani daki, se dai wannan dakin babu kwado a jikinsa, jagwa ya kama marikin kofan dakin yaja da zummar ya bude amma sai kofan taki buduwa hakan ya tabbatar masu ta ciki aka kulle dakin
.
Cikin takaici aba yawo ya dubi jagwa yace “yanzu ya kenan zamuyi tunda yan iskan daliban nan sun kulle kofan ta ciki”
Jagwa ya danyi guntun nazari kafin yace “matsa min na jarraba wata dabara”
.
Aba yawo ya matsa daga bakin kofan dakin jagwa ya matso kusa, ya fara dukan kofan da hannu, kofan ta fara bada wani sauti sakamakon dukan da jagwa keyi mata,
.
“Who is that” wata murya ta fadi daga cikin dakin
Maimakon jagwa yayi magana sai ya cigaba da bubbuga kofan, “a’a who is that na, person dey sleep you come de distrurb him” aka sake fadi karo na biyu daga cikin dakin
Jagwa ya wage wawakeken bakinsa yace “kai open this door, you come dey sleep you no know weting dey happen “
.
“Cai what, ok but who are you” na cikin dakin ya tambaya
“Eh see this guy u dey ask me who I be, if you no open dis door toh you na go die there” jagwa ya bashi amsa
..
“Ok lemme open” aka fadi daga cikin dakin, kofan dakin ya fara motsi alamar ana kokarin budewa
.
Kofan dakinne ya bude wanwar, jagwa da aba yawo sukai arba da matashin saurayin daya bude kofan yana tsaye a bakin kofan babu komai a jikinsa face gajeruwan wandon kwallo, saurayin da bai kula da abubuwan dake hannun yan ta’addan ba yayi hamma gami da mika yace “ya bros wetin dey happen” ya fada cikin magagin bacci
.
Lokaci daya fuskan saurayin ya canja daga yanayin magagin bacci zuwa tsananin firgici, idanuwansa A bubbude ya daga hannunsa sama, bakin sa na kakkarwa jikinsa na bari tamkar mazari, “abeg bros don’t kill me” matashin saurayin ya fadi lokacin da tsinin bakin bindigar jagwa ya kusanci Tumbinsa,
.
Aba yawo yayi masa alamar yai shiru, a razane saurayin ya dora hannunsa daya akan bakinsa ya tsuguna a kas
Jagwa yayi masa inkiya da bakin bindigar akan su koma cikin dakin,
Matashin saurayin da yan ta’addan suka shige cikin dakin
…….
Yana kwance kan katifarsu ga sauran abokannasa a gefe suna sharar barci, fuskarsa na kallon silin dakin din yana murmushi a zahiri in ka gansa zakai tsammanin Silin dakin yake kallo amma abun bahaka yake ba a wurin Aliyu SARKIN DARIYA,
Tunanin Abar kaunarsa yake, yana mai zumudin gobe tayi, a yadda ya kudirta a ransa ba zai taba runtsawa ba har safiyar gobe, tun da Aliyu yake A rayuwarsa bai taba tsintar kansa a lambun farin ciki, mai cike da kayan Annashwa…..
“Kikkirrkirrrrkirr……”
Sautin karar bude kofan dakin ya katse masa tunani, lokaci daya ya mike ya dubi kofan dakin….
…..
Zan cigaba

Subscribe to our newsletter
Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Leave A Reply

Your email address will not be published.