TARKON MUTUWA littafi na Biyar 5 complet

TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Post:- Shuraih Usman
Littafi na hudu
Part 5 A
.
.
Kash ! rashin sani yafi dare duhu hakika masu iya
magana sunyi gaskiya da sukace ga magani a
gonar yaro amma bai saniba
Ashe mabudin dakin kasa inda aka boye su
hatyan da yaruwarsa abakin kofar shigowa falon
take,sai andaga daddumar da ma ake takawa
sannan a zare wani tubalin zinare da aka
shimfida akasa akayi ado dashi,kuma na farko
Sannan zata bude a taka matattalalar
benen izuwa kasan
da daddumar sai da boka daizur ya dafa ya
tattaba tubalin zinaren duka, gamma tunaninsa
da basirarsa batakai kan ya care tubalinba
.
bayan sun gaji da bincike basuga komai ba sai
sarki shamsal ya dubi sarauniya anisa yace
ki gafarcemu yake wannan Sarauniya kiyi sani
cewa aiki ne yajanyo muka saki wanna wahala
ayanzu dai bamuga Komai ba amma hakan ba
yana nufin mun cire zargi daga ranmu baneba
kamar yadda nake fada miki abaya zamu fara
yin bincike na biyu yayin da hadimaina
kwararrun iya bincike suka iso ayau dinnan
yanzu nida bokana Zamu koma masaukinmu mu
kwanta domin Rama barcin da muka rasa a yanzu
ba zamuci gaba da bincikeba sai da farkon
yammaci gama fadin Hagan keda wuya sai Sarki
shamsal da boka daizur sika juya suka fice daga
cikin turakar suka isa masaukinsu,
suka koma suka fara sabon barci ba tareda sunyi
kalaciba,
wanna shine abin da yafaru abirnin askandariya a
Daren dasu Sarki scandal suka hallara zuwa
kashe gari
acan birnin bindal kuwa tin lokacin da
Sarki scandal
yabar gari domin tafiya
farautar babban abokin gabarsa wato hartayn sai
aka shiga wata babbar masifa wacce ta
dugunzuma hankalin gaba daya masu mulki da
manyan Gari baki daya ba komai bace wanna masifa ba
face mulkin yarima zainur ya shirya rundina a cikin
Daren kawai sai wayar gari akayi akaga an
kama gaba daya manyan garin wadanda suka
kasance amintattun sarki shamsal wadanda zasu
iya sadaukar da rayuwar su dominsa an kashesu
sauran yan majalisar kuwa da manyan gari sai
gasu sun taru afada gaban yarima don yin
mubaya a yana zaune akan karagar mulki wani
bakon boka ma abocin kwarjii yana tsaye
abayansa
Yarima yanata kyakyata dariyar mugunta yagaji
a wannan lokaci fadar tayi tsit babu abinda akeji
kai bawai acikin fadarba har acikin gari ma duk
inda ka gifta sai dai kaji tsit saboda tsananin
firgitar da jama’a sukayi saboda sun sami labrin
cewa yarima zainur ya yi juyin mulki
nan take yan mata da zawarawa suka farayin
hijirar sirri don kada zaluncin sabon sarki ya fada
kansu
bayan yarima zainur yayi dariyar farinciki ya gaji
sai ya dubi gaba daya yan majalisar dake cikin
fadar da dukkan fadawa da dakaru wadanda har
izuwa wannan lokaci a firgice suke kamar kace
kyat su saki fitsari awando
yarima zainur yayi ajiyar numfashi cikin
murmushi yace
yaku jama’ata kuyi sani cewa komai nisan jifa
kasa zai fado ina mai tabbatar muku da cewa
lokacin zaman mahaifina akan wannan kujerar
mulkin ya kare har abada bazai sake zama akan
wannan kujeraba.don haka yanzu sabon sarki
sabon birni sabuwar rayuwa
kamar yadda nayi muku alkawari tun adaren jiya
kowannenku zan linka.masa albashinsa kuma zan
rinka kyautata muku
sabanin mahaifina da wani hakkin nakuma
cin yewa yake
abinda nake bukata daku kawai shine kada
dayanku yasa mini ido akan harkokina ko yace
zai ja dani indai kukayi hakan zaku sami arziki
mai yawa daga gareni wanda baku taba samuba
nasani cewa hankalinku a tashe yake akan
tunanin cewa idan sarki ya dawo bazai kyalekuba
kasheku zaiyi
to ku kwantar da hankalinku ku sani cewa babu
abinda sarki zai samo awannan tafiya face
ajalinsa
tabbacin haka shine gaba daya bokayen dake
wannan nahiyar tamu sunyi bincike sun tabbatar
da hakan
wannan boka da kuke gani kusa dani shine boka
arzus bin sharkub shima ya tabbatar da hakan
bisa wannan dalili nema yazo ya zauna tare dani.
domin biyan wata bukatarsa wacce ta kawoshi
wannan nahiya tamu tsawon shekara talatin baya
bai sami damar cikata ba
koda yarima zainur yazo nan azancensa sai gaba
daya mutanen da suke cikin fadar suka kamu da
tsananin mamaki kuma dukkaninsu suka kurawa
boka arzus bin sharkuf idanu cikin firgici
shekarar da boka arzus ya sauka anahiyar yayi
abubuwan al’ajabi da yawa wadanda suka
daurewa mutane kai yazamana cewa ana
girmamashi kamar za’a bauta masa komai
tsananiin cuta indai bata ajali bace,to indai boka
arzus yazo ya tsaya akan mutum to sai ya warke
ya mike sumul tammkar bai taba cutaba
komai talauci idan mutun mulki yake nema sai ya
samu ba neman suna ko daukaka,
bisa wannan daliline sarakan nahiyar sukayi ca
akan boka arzun kowannensu na zuwa da
bukatarsa yana biya masa
amma sarkin birnin bindal wato mahaifin sarki
shamsal ne bai taba zuwa gareshiba saboda shi
yana ganin shi bashida wani abu da zai nema
awajensa saboda Allah ya horemasa lafiya
daukaka gami da arzikin da babu me kamarsa
awannan nahiyar, bisa wannan daliline yazamana
cewa ansami rashin jituwa tsakanin koka arzur da
sarki
watarana boka arzur na tare da manyan
sarakuna guda uku na nahiyar a gidansa dake
can tsakiyar wani daji wanda ake kira jahal sai
kawai aka hango wani abu a can sama tamkar
tauraruwa ya taho yana feshin wuta kuma ya
nufo inda boka arzur ke zaune.
Nan take wadannan sarakuna uku tare da gaba
dayan hadiman boka arzur suka firgice suka ruga
da gudu suka kama buya a cikin gidan,ya zamana
cewa boka arzur kadai aka bari a zaune,ko
alamar tsoro babu a tare da shi,saboda ya yarda
da kansa ma sai ya dora kafarsa daya bisa dayar
ya kurawa wannan tauraruwa idanu yana jiran
isowarta.
sai da ya rage saura baifi taku biyarba
tsakaninsu sai tauraruwar ta fado kusa da shi agabansa
ta rikide ta zama sarkin bindal a cikin gagarumar
shigar yaki.
nan fa wayanda suka boye,suka fara firfitowa
suna kallon ikon Allah,kawai sai akayi kallon yan
dakiku sannan boka arzur yayi murmushi ya mike
tsaye daga kan kujerar da yake zaune ya dube
shi yace”lale marhaban da kai,”wanan Sarki mai
daraja tabbas nayi farinciki da wannan ziyarar
taka wacce ban taba zatoba don haka nayi maka
alkawarin zanbiya maka duk irin bukatar dakazo
mini da ita
kodajin haka sai sarkin bindal ya turbune fuska
yace banzo gareka don neman wata bukataba
saboda baka da abinda bani dashi na zone na
baka umarni katashi daga cikin yankin kasata
inason ka hada naka da anaka ka bar mana
nahiyarmu acikin kwanaki uku kacal inba hakaba
kuwa zaka rasa rayuwarka
nine kadai sarkin da kowa yake shakka a wannan
nahiya anayi mini ladabi kamar abin bauta amma
yanzu komai na neman dawowa gareka
to ka sani ba’ayin sarki biyu agari daya na fuskanci
cewa idan na kyaleka kaci gaba da harkokinka da
sannu zaka raba mu da mulkinmu
koda sarki yazonan azancensa sai boka arzur ya
takarkare ya bushe da dariya lokaci guda kuma
ya turbune fuskarsa yace
yakai wannan sarki ka sani cewa tinda nazo
wannan nahiya da niyyar na mulketa, da acikin
daredaya zan gama da ita .to amma nazone sabo
wani buri guda daya wanda ya rage mini arayuwata
Koda kuwa ban cika wannan burin a zamaninku
ba sai na cikashi ana yayanku ko jikokinku,burin
kuwa shine ina so na hattama wani sihirin tsafi
wanda na farashi tun ina da shekaru tara aduniya
wannan tsafi bazai kammalu ba har sai sarakai dari
da daya sun durkusa a gabana bisa gwiwoyinsu na
dafa kawunansu yayin da sukazo neman bukata
,wato nasa musu albarka ahalin yanzu sarakuna
arba’in da dayane jal suka durkusa agareni ina
neman hamsin da takwas kuma dole sai awannan
nahiya takune zan sami wadannan sarakunan da
nake nema saboda haka babu wanda ya isa yasa
nabar wannan nahiya face ba na num fashi adoron
kasa ko mujima ko mu dade kai ma sai kazo ka
durkusa agabana idan baka durkusa mini ba sai
danka ko jikanka yazo ya durkusa mini
gama fadin hakan keda wuya sai boka arzur ya
bushe da dariyar mugunta yayita kyakyatawa
kamar ba zai dai naba
al’amarin daya matukar fusata sarkin bindal ke
nan kawai sai ya zare takobinsa ya dako tsalle
daga inda yake tsaye tamkar an harboshi daga
cikin baka cikin bakin zafin nama boka arzur ya
kaucewa mummunan saran da sarki ya kawo
masa wanda saura kiris ya sare masa kai
kawai sai akaga shima boka arzur ya daga
hannunsa sama takobinsa ta baiyana yatari
sarki suka ruguntsume da azababben yaki ya
zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka
cikin zafin nama juriya da bajinta ta ban al’ajabi
sai da suka shafe sa’a guda suna bakin artabu da
kyar kowanensu ya sami nasarar yankar abokin
gwaminsa shi dai sarkin bindal agefen hannun
hagu ya yanki boka arzur
shikuma boka arzur akan cinyar dama ya yanki
sarkin bindal raunin baiyi wani zurfi sosaiba
koda sukaga cewa jarumtakarsu tazo daya sai
suka koma yakar juna da karfin sihirin tsafi
wohoho masifa ba’asamata rana wadannan
sarakuna uku dake wannan wurin tareda hadiman
boka arzur sunga turnuku irin wanda basu taba
ganiba kuma sunga tashin hankali wanda ya
firgitasu sukaji kamar su haka rami su shige ciki
hatta bishiyoyi da duwatsu dake cikin dajin sai da
suka rinka farfashewa suna karyewa .saboda
bala’in da jaruman biyu suke haddasawa
wani lokacin sai su rikide su zama manyan
dabbobin daji suyita gumurzu shikansa dajin
girgiza yakeyi kamar kasa zata rufta duk abinda
yake cikinta ya rufta ciki
ahaka sai da suka shafe sa’a uku suna masifaffen
yaki har sai da kusan ko ina ya kama da wuta
adajin asannan ne boka arzur da sarkin bindal
suka jugata ainun suka zube kasa sunata faman
yin haki da numfashi kamar ransu zai fita.
sai da suka dan jima kwance akasa suna hararar
juna sannan sarki bindal ya mike tsaye ya dubi
boka arzur cikin tsananin fushi da kiyayya yace
narantse da girman iyayena daga yau babu wani
sarki dazai kara zuwa gareka ya durkusa
agabanka muddin ina numfashi adoron kasa
kodajin wannan batu sai boka arzur ya mike
tsaye zumbir yace nima na rantse . da gemun
ubana har abada zuriyarka bazasu zauna lafiya ba
har tsakanin iyaye da ‘ya’ya sai an sami sabani
kuma sai wannan masarautar tabar hannunku ta
koma hannun wayanda ma basu gadaba
dajin wannan batu sai sarkin bindal yayi girgiza
ya zama tururuwa ya cilla izuwa cikin kololuwar
sama ya bace acikin gajimare tamkar bai taba
wanzuwaba
WANNAN SHINE ASALIN TARIHIN
DANGANTAKAR BOKA ARZUR DA GIDAN
SARAUTAR BIRNIN BINDAL
Lokacin da fadawa da jama’ar gari suka firgice
suka dimauce sakamakon ganin arzur acikin
fada alhalin sun san cewa tsakaninsa da marigayi
sarki ba’a ga maciji .
sai akayi tsit ana muzurai aka rasa wanda zaice
kala saboda tsoron fushin yarima
kwatsam sai akaga an turo kofar fadar da karfi
an shigo.
ba wani bane ya shigo ba face mahaifiyar yarima
kuyangi na take mata baya ta tunkari karagar
mulki idanunta sun kada sunyi jawur kai da gani
kasan cewa tasha kuka mai yawa sai da ya rage
saura baifi taku uku ba kacal tsakanita da yarima
sannan ta tsaya ta dubeshi afusace tana mai
nunashi da yatsa tace
yakai wannan wawan yaro mara tunani kayi sani
cewa wannan shine kuskure na karshe dazaka
tafka a rayuwarka
inbanda toshewar basira irin taka akan wane
dalili zaka hada kai da babban makiyin ubanka
domin kawai ka haye kan karagar mulkinsa
to kasani cewa indai nice uwarka kuma ina raye
acikin wannan gida wannan tsohon bansan bazai
cika burinsaba kuma saika sauka daga kan
wannan karagar muki kafin nahaifinka ya dawo
kafin ta gama rufe bakinta tuni yarima ya bushe
da dariyar mugunta kawai sai yamike tsaye daga
kan karagar mulkin ya tako daf da ita yadda suna
iya jin numfashin juna ya dubeta cikin tsananin
fushi yace
yake ummina idan kina son zaman lafiya dani
kawai ki tsaya a iya matsayinki na uwata amma
kada ki shiga cikin harkokin mulki
yana da kyau ki girmamani amatsayin sabon
sarki ina maitabbatar miki da cewa lokacin
abbana ya kare .
yadda ma baya dawowa, toshima ya tafi kenan
acikin wannan tafiya tasa zai riski ajalinsa birnin
bindal ya zama nawa nida masoyana
kafin yarim Ya gama rufe bakinsa sai mahaifiyar
tasa ta tari numfashinsa tana mai cewa
yadda duk kake zaton mahaifinka ya wuce nan
tabbas saiya sami nasara akan makiyansa domin
bai taba sa wani abu aransa ya kasa samuba
yanada tsananin sa’a da rabo kuma idan ya dawo
yaga wannan cin amana da kayi masa bazai dubi
cewa kai dansa bane kasheka zaiyi kuma gaba
dayanku wadannan yan majalisar da kuka bashi
hadin kai duk kasheku zaiyi
charaf sai boka arzur ya tari numfashinta yace
indai ina numfashi sarki shamsal bai isa yayiwa
dansa komai ba
kodajin haka sai mahaiffiyar yarima ta fusata
ainun har jikinta ya kama kyarma ta dubi yarima
cikin fushi har fuskarta nayin gyatssine tace
inason kazabi daya cikin biyu idan har wannan
shedanin boka zai zauna tare dakai
toni bazan zaunaba agarinnan gwara na bar
masarautar nan gaba daya
kodajin wannan batu sai yarima ya kyalkyale da
dariya al’amarin daya baiwa kowa mamaki kenan
acikin fadar
lokaci guda kuma ya murtuke fuskarsa yace
mahaifiya ta kiyi sani cewa yadda nake son
wannan mulki da rayuwata yafi yadda nake
kaunarki don haka kinada zabin ki tattara naki i
naki ki kara gaba
duk abinda kike bukata zan baki amma ki sani
idan kika tafi mun rabu kenan har abada bana
bukatar na sake ganinki arayuwata
koda yarima yazonan azancensa sai itama
mahaifiyar tasa ta kyalkyale da dariya
al’amarin daya matukar bashi mamaki kenan
daga can saita hade fuskarta ta dubeshi
cikin takaci sa’adda kwalla ta cika mata idanu
tace bana bukatar dukiyar datakai darajar kwayar
zarra aci acikin gidannan
yanzunnan zan tafi kuma zanyi nesa da wannan
marautar kuma bazan dawoba sai ranar da mijina
ya dawo, ka sani cewa har abada makiyi baya
zama masoyi
.
Daga www.facebook.com/hausaebooks
TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Post:- Shuraih Usman
Littafi na hudu
Part 5 B
.
.
boka arzur makiyin ubankane babu hujjar da
zatasa ya soka kawai zaiyi amfani dakaine don
biyan bukatarsa dazarar anci moriyar ganga za’a
yar da koranta ne
zaka yi nadamar wannan butulci dakyiwa
mahaifinka kuma saika zubarda hawaye da
idanunka
kafin ta gama rufe bakinta tuni yarima yadaka
mata tsawa yana mai cewa
don me bazanci amanar mahaifina ba alhalin ya
juya mini baya tun daga ranar da hatyan ya sare
mini hannu daga wannan ranar ya
tsaneni,yadaina nuna min so da kauna jama,a
sun
fuskanci cewar bazai taba bani karagar ba,
saboda na zāmana sarki yanzu tafi duk inda
kikeso kije
domin tafiyar taki zata fiye mana alheri gaba
daya,
dajin haka sai mahaifiyar yarima ta juya ta fuce
da sauri afusace tafice daga cikin fadar tana
zubar da kwalla saboda bakin ciki da takaici ma
ko waigowa bata sakeyi ba
shikuwa yarima koda yaga mahaifiyar tasa ta tafi
saiya bushe da dariyar farinciki sannan ya dubi
sarkin dogarai yace
inaso yau da yamma ku zagaya gida gida ku
kamo min gaba daya ‘yan matan garin nan da
zawarawa matasa banda tsofaffi kuzo min dasu
nan
kodajin wannan batu sai boka arzur ya yi wuf ya
dakatarda sarkin dogarai ya kama hannun yarima
yajashi izuwa gefe daya inda babu wamda zaiji
abinda zasu tattauna ya dubeshi yace
idan kaci gaba da wannan huldar ta mata duk
abinda mukasa agaban mu rushewa zaiyi
kodajin wannan batu sai hankalin yarima ya
dugunzuma takaici ya turnukeshi ya rasa abinda
ke masa dadi aduniya saboda a iya rayuwarsa
babu abinda ransa yakeso sama da yiwa mata
fyade
cikin alamun tsananin damuwa yarima ya dubi
boka arzur ya ce
shin zan iya tura dakaru zuwa wasu kauyuka
adebo min wadan nan mata?
boka arzur ya kada kai yace
ya shugabana dolene fa ka kawar da wannan
halayya taka idan har kanaso kayi nisan kwana
akan karagar mulki,, domin zina gami da zubar da
jini suna lalata sihirin tsafin danakeyi yanzu
kodajin haka saiya juya da sauri ya fice daga
cikin fadar cikin matsanancin fushi ya nufi
bangaren da turakar sarki take
da shigarsa cikin babban falo na sarki shamsal
sai yayi arba da wani babban hoto na sarki
shamsal wanda wani kwararren mai zane ya zana
an sakale wannan taswira acan saman bango
koda yarima ya kalli wannan hoto sai yaji ya
tsani mahaifin nasa fiyeda ko yaushe don haka
sai ya zare takobinsa ya daka tsalle sama ya
datsa hoton gida biyu ya fado kasa
karar sare hoton ne yasa hadimai suka rugo da
gudu izuwa cikin falon, sai sukaga hoton sarki
shamsal agabansa kuma arabe gida biyu sai
gaba dayansu suka sunkuyar da kansu kasa
kawai sai yarima ya daka musu tsawa yace su
fice daga cikin fadar gaba daya
kafin kace me?
sun fice gaba dayansu babu ko mutum daya
nan take yarima yaje inda aka ajiye tambulan
kayan shaye shaye
kawai saiya suri tambulan din giya guda daya ya
kafa abakinsa
yakama kwankwada harsaida giyar ta kare kaf
ko digo daya babu saura sannan yai jifa da
tambulan din kasa ya fashe
yana tangadi ya nufi cikin turakar barci,, har
wadansu kuyangi guda hudu sun biyoshi abaya
saiya daka musu harara suka koma da sauri
kawai saiya banko kofar dakìn ya fada kan gado
ya baje
nantake kuwa ya kama barci harda munshari
acikin garin bindal kuwa tuni labari ya riski
jama’a cewa
boka arzur ya hana wannan sabon azzalumin
sarki yin mugayen halayensa bisa hakane yan
mata da zawarawa suka kamu da farinciki
hakama iyayensu
nanfa iyaye da sauran mutanen gari suka ci gaba
da tsegumi iri iri wasu suce ai har mulkin
zaluncin da sarki shamsal yakeyi ada yanzu zai
ragu tunda an sami sauyin sarki wasu kuma suka
dinga cewa ai babu tabbacin hakan sai dai
abinda
aka gani tunda boka arzur ne ke mulkin birnin
afakaice tunda sai abin daya fada akeyi
wannan shine abinda yafaru abirnin bindal bayan
tafiyar sarki shamsal
Acan birnin askandariya kuwa jarumi hatyan da
‘yar uwarsa sadirat tunda suka bingire akan gado
suka kama barci tamkar gawa
dayansu bai farkaba har sai da dare ya raba
tsakiya
dai dai wannan lokaci ne jarumi hatyan ya farka
yana mai bude idanunsa a hankali.ba tare da jin
wata gajiya ko tsamin jiki ba
sai ya mike zaune ya dubi yar uwarsa sadirat
yaga ko motsin kirki batayi sai yayi murmushi
sannan ya mike tsaye ya kama kai kawo acikin
turakar yana mai mamakin yadda akayi yaji
kwarin jikinsa tamkar wani abu bai taba
lafiyarsaba
nantake tunani iri iri ya fara fado masa arai,da
farko yace yanzu idan sarki shamsal ya iso
garinnan ya riskemu nida yar uwata ai mun jefa
anisa da badi’atul nauwara acikin masifa
lallai yana da kyau agoben nan mu bar garinnan
mu kara gaba
wai shin da gaskene anisa tana sona kamar
yadda naga alamun cewa badi’atul nauwara tun
haduwarmu ta farko?
tayaya zan hada soyayyar aminai guda biyu kuma
gashi kowacce acikinsu tayi mini halaccin da bai
kamata na juya mata baya ba koda gama fadin
hakan sai hatyan ya lura ai
wannan daki da suke ciki bashine dakin da aka
saukesuba da farko
to yaushe aka dawo dasu nan basu saniba
amsar da hatyan ya kasa baiwa kansa kenan
alokcin da hankalinsa ya dugunzuma sakamakon
rashin ganin kofar fita daga wannan daki da suke
ciki
cikin kaduwa da mamaki hatyan ya shafa
dukkanin bangwayen dakin amma yaji shiru
kamar maye yaci shirwa
hakadai yaci gaba da dube dube da tabe tabe
gami da leke leke har karkashin gado amma duk
baiga wani wuri mai alamar kofar fita ba domin
ko ina a shafe yake
adaidai wannan lokacine sadirat ta farka daga
barcin koda taga hatyan yanata lalube kuma ta
lura cewa an sauya musu daki
sai itama hankalnta ya tashi,ta tashi tsaye da
sauri tasha gabansa tana mai cewa wai me ke
faruwa naga an chanja mana masaukin mu?
kodajin wannan tambaya sai hatyan ya dawo
cikin hayyacinsa yayi ajiyar numfashi sannan
yace
ina ganin dai saboda tsarone yasa aka kawomu
nan
babu mamaki su sarki shamsal sun iso sun fara
bincike
kodajin wanna batu sai saidira taji zuciyarta ta
buga da karfin gaske fiye da ko yaushe nan take
jikinta ya kama kyarma
koda ganinhaka sai hatyan yayi murmushi ya
dafa kafadarta yace
ki kwantar da hankalinki yake yar uwata kiyi sani
.cewa babu abinda zai samemu kuma ina
tabbatar miki da cewa idan har sarki shamsal na
nan to yau zai mutu
kodajin wanan batu sai sadirat ta sake firgita ta
dubi hatyan cikin firgici tace
yakai dan uwana kada ka kuskusra kace zakayi
wani abu domin baka da nasara akan sarki
shamsal yanzu sai dai nan da wadansu shekaru
kamar yadda bokaye suka fada
hatyan yace nidai banyi imani da duk
maganganun bokayeba abinda na yarda dashi
kawai shine sa’a da rabo
kin sani cewa ke baki isa ki hanani aiwatar da
duk abindana so yiba don haka kawai ki zuba ido
koda gama fadin hakan sai hatyan yaci gaba da
neman kofar fita daga cikin dakin ita kuwa
sadirat sai hankalinta ya dugunzuma ainun fiye
da ko yaushe
kwatsam sai su kaga wata kofa akasa ta bude
da kanta saiga matattakalar bene wacce tayi
sama
Ni dinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks

TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Post:- Shuraih Usman
Littafi na hudu
Part 5 C
.
.
Al’amarin da ya daure musu kai kenan suka
fahimci cewar inda suke dakin kasa ne, har
hatyan ya yunkura zai hau kan matattakalar
benen ya fice sai ga sarauniya anisa ta shigo ta
cikin matattakalar benen tare da wasu hadimanta
guda uku anisa tayiwa hatyan wani irin kallo na
zargi gamida dan guntun murmurshi tace
kadaina tunanin zaka kaiwa sarki shamsal harin
bazato don kawar dashi
domin bazaka taba samun nasara ba kamar
yadda yar uwarka ta fada maka haka al’amarin
yake, karonka da sarki shamsal na farko kayi
matukar sa’a da kawata badi’atul nauwara ta
kawo maka dauki
idan ka kuskura ka sake tarar sarki shamsal a
karo na biyu mutuwa zakayi indai ni ko ita bamu
kawo maka daukiba
koda sarauniya anisa tazo nan azancenta sai
mamaki ya turnuke hatyan
nan take ya gane cewa tabbas itama sarauniya
anisa tana da abinda take takama dashi walau
tsafi ko jarumtaka tunda tana fadin cewa zata
iya bashi kariya
yana cikin wannan tunanin anisa ta katseshi tace
yanzu gari ya waye kuma tun adaren jiya sarki
shamsal da bokansa suka bincike ko ina acikin
wannan gidan sarautar nawa suna nemanka basu
gankaba
a yanzu haka suna chan akwance suna barci nan
da cikar kamar sa’o’i uku wasu kwararrun
hadimansa masana iya bincike zasu iso garinnan
idan suka iso kuwa sai sun gano inda kuke
saboda haka dolene sai kun fice daga garinnan
yanzu a sirrance
ku sani cewa tafiyar sa’a biyu da rabi kacal
zakuyi abangaren kudu ku fice daga cikin
wannan nahiya gaba
wadannan hadiman nawa suna tare dani zamuyi
muku rakiya izuwa iyakar kasata da nahiyar dake
gaba kuma zamu kawar da duk wata shaida da
zata nuna sawunku ko wata alama ta cewar an
fita daga garinnan
yanzu sai kuyi sauri ku dauki kayanku mu tafi
domin bamuda isasshen lokaci koda sarauniya
anisa tazo nan azancenta sai jarumi hatyan yaji
wani irin bakin ciki ya turnukeshi badon komaiba
sai saboda ya ayyana aransa cewa takowanne
hali sai ya kaiwa sarki shamsal harin bazato har
masaukinsa
ba tareda wata gardamaba sai hatyan da sadirat
suka dauko jakunkunansu
anisa da hadimanta guda uku suka yi musu
jagora suka fice daga cikin gidan sarautar ta
wata barauniyar hanya wacce komai kwakkwafin
mutum bai isa ya iya gano akwaitaba
can bayan gidan sarautar bangaren kudu suka
fito ta karkashin kasa kuma ta cikin wani rairayi
wandaya lullube wata kofar katako
dafitowarsu sai suka mayarda kofar suka rufe
rairayi ya lullube tamkar bata taba wanzuwaba
agurin
tuni sun iske wadansu kosassun dawakai guda
shida daure awajen suna harbin iska
akan dawakai biyu akwai guzuri na matafiya
kawai sai sarauniya anisa ta dubi hatyan tace
ku kama wadancan dawakan biyu masu dauke da
guzuri ku hau sune naku
kafin dayansu yayi wani yunkuri tuni anisa ta
kama daya daga cikin ragowar dawakan ta hau
koda hatyan yaga irin hawan dokin da tayi sai ya
kamu da mamaki domin da gani kasan cewa ta
kware kuma sai manyan jarumaine suke yin irin
wannan hawan
alokacin da tayi tsallene rigar jikinta ta bayyana
tana sanye da matsatstsun tufafi na fatar damisa
wadanda suka bayyana gaba dayan siffofinta
kuma a sannan ne gashin kanta dake daure ya
zubo kasa harkan duga duganta
koda jarumi hatyan yayi arba da wannan
kyakkyawar sura tata saiya dimauce
domin a sannan ne ya gane cewa tafi sarauniya
badi’atul nauwara komai na kyan sura, kyan fatar
jiki da kuma kyawun fuska
batare da bata lokaci ba suka sukwani dawakan su
da gudu izuwa cikin daji sarauniya anisa ce akan
gaba
ai kuwa nan da nan ta baiwa su hatyan tazara
mai yawa sadirat ce acan karshen baya
sannan hadimanta guda uku, tsakanin dokinta
dana hatyan akwai tazarar kimanin taku ashirin
koda ganin haka sai shima ya karawa nasa dokin
kaimi ya zabureshi da gudun gaske
koda anisa ta fiskanci cewa hatyan ya karawa
dokinsa kaimi don ya kamota sai itama ta karawa
nata dokin kaimi
nan danan tazarar dake tsakaninsu ta sake
ninkawa takai kusan taku arba’in
koda sadirat da sauran hadiman sukaga an musu
nisa sai suka kara zage dantse
lokacinda hatyan yayi iya yinsa yaga ya kasa
kamo sarauniya anisa saiya fusata ya daka tsalle
sama daga kan dokinsa ya dirgo kasa yaci
gaba da falfalawa da gudu da kafafunsa shi kuwa
shikuwa dokin nasa saiya bishi a baya
wohoho! wanda Allah ya baiwa kyautar baiwa babu
yadda za’ayi dashi sai kallo
kafin cikar dakiku arb’in tuni hatyan yazò ya gifta
sarauniya anisa akan dokinta harya bata tazarar
data bashi
yana riskarta yayi mata murmushin sai kinzo
hatyan yaci gaba da gudu har izuwa wasu
dakiku masu yawa
kwatsam ba zato ba tsammani saiyaji taku
bayansa
al’amarin dayai matukar bashi mamaki kenan
domin shi azatonsa babu wani doki ko bil’adama
da zai iya cimmasa agudu face sarki shamsal
nan take yaji zuciyarsa tadan buga da karfi kawai
saiya tsaya ya juya domin yaga kowanene ke
shirin cimmasa
ba zato ba tsammani sai yaga ashe anisace
itama ta duro daga kan dokinta itama taci gaba
da gudu
cikin matùkar mamaki yayi sauri yaci gaba da
gudun don karta wuce she
nan dai suka jera sai gashi ya kasa tsere mata
al’amarin dayai matukar bashi mamaki kenan
waishin dama akwai wanda yake da. irin baiwar
da muke da ita nida sarki shamsal?
saida suka shafe kusan rabin sa’a suna gudu
sannan ne sarauniya anisa ta fara rage karfin
gudunta
koda ganin haka sai hatyan yayi murmushi yasan
cewa adade anayi sai gaskiya
kuma sai miya ta kare sannan ake sanin maci
tuwo
ko tafiyar dakika goma basù karasaba sai kawai
yaga anisa ta zube kasa sharaf tana haki
sai hatyan a kyalkyale da dariya yace
iyakar juriyar taki kenan a gudu
kodajin haka sai anisa ta maida masa da
martanin dariya ta dubeshi alokacin daya zauna
dishan daf da ita yana haki tace
ai nan ne daf da iyakar nahiyarmu da nahiyar
dake gabanmu
daganan tafiyar sa’a shida kachal zakayi ka shiga
nahiyar kasashen bakaken fata
kodajin wannan batu sai hatyan ya jiwata irin
matsanaciyar damuwa tazo masa tamkar yace
ya fasa ci gaba da tafiyar
waishin rabuwa. da anisa ce bayaso kokuwa ya
gaji da wannan gudun ceton ran da sukeyine?
amsar daya kasa baiwa kansa kenan
duk su biyun sai sukayi shiru har izuwa tsawon
yan dakiku adaidai wannan lokacine suka fara
hango hadiman anisa da sadirat bisa dawakai
daga chan nesa da kuma nasu dawakan guda
biyu
hatyan yayi ajiyar numfashi yana mai dan
sunkwui dakai kasa yace
yake wannan sarauniya yanzu gashi zamu rabu
kuma banida tabbacin zamu sake saduwa a
wannan rayuwa keda kawarki badi’atul nauwara
kunyi mana taimakon da bamu da abinda zamu
saka muku dashi nida yar uwata
kodajin wannan batu sai tayi murmushi tace ai
rabuwarmu anan ba itace rabuwarmuba duk inda
kuke muna tare daku kada ka damu abu daya
nake so dakai
ka zamo mai halacci kuma kayi hukunci bisa
adalci ga duk mutuminda mu’amala ta hadaka
dashi
kaso mutum gwargwadon yadda yasoka abu na
karshe ka kula da kanka karka bayarda zuciyarka
ga kowa sai wanda ka tabbatar da cewar shine
yafi dacewa dakai
sa’adda anisa tazonan azancenta sai jarumi
hatyan ya dubeta cikin matukar mamaki gami da
rashin fahimta yace
ya shugabata gaskiya kin batar dani ko ince
wadannan maganganun naki sunfi karfin
fahimtata
shin zaki fahimtar dani?
dajin haka sai anisa tayi murmushi tace
kada ka damu da sannu zaka fahimci komai anan
gaba
abu na karshe dazan sanar dakai shine idan ka
isa gari na gaba kada ka yarda da kowa face
wanda ka karanci halayyarsa,, ka fahimceshi
amatsayinka na bako duk inda ka shiga ka boye
baiwarka kuma ka kankantar da kanka ga jama’ar
gari ta hakane kadai zaka san sirrin gari da
jama’ar sa
ka jajurce wajen neman halak babu ruwanka da
haram
ko zalunci kayi taimako ga mai bukatarsa ka
zamo mai tausayi da jin kai
hakan zaisa kasake nasara bisa duk abinda kasa
agabanka
daga yau ka jajurce wajen bawa kanka horon
yaki da fada idan har kanason kadauki fansar ran
iyayenka akan sarki shamsal
domin karo dashi sai an shirya koda kuwa
shekarunka sunkai lokacinda da bokaye ke fadi
da wannan furuci nake yi maka bankwana sai
mun sake saduwa nan da wani lokaci kadan domin
lokacin komawata birnina yayi domin hadiman
sarki shamsl masana bincike sun kusa karasowa
gama fadin hakan keda wuya sai gasu sadirat sun
iso nantake hadiman nan uku suka fara goge
sawayen dawakan nasu
ita kuwa anisa saita rungume sadirat tana mai yi
mata ban kwana
taja dokinta ta kama ta hau ta zabureshi da gudu
alokacin da hatyan ya bita da kallo zuciyarsa
cike da wasu tambayoyi gamida rashin
fahimta
su kuwa hadiman nan uku sai suka ci gaba da
aikinsu na share sawayen dawakan kuma
kowannensu na ruke da dokinsa ar sukayi nisa
da ganin haka sai hatyan da sadirat suka kada
dawakansu suka tsallaka nahiyar suka nausa
cikin daji
KU SHA RUWA mukoma bakin fahama zamushiga
LITTAFI NA 6
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks

Subscribe to our newsletter
Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Leave A Reply

Your email address will not be published.

1 Comment
  1. […] Also download TARKON MUTUWA littafi na Biyar 5 complet […]