Download Hausa Novels,Musics,Videos and Movies for free

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 9

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 9
.
.
Bani da amsar data wuce eh na amince musaMman a wannan hali da sai inda tayi da ni
Ta matso da bakinta ta jonashi da nawa Abun da yafaru ya mantar dani lissafin dangina,
Shakka babu yau ne ranar shayar da juna zuma da madara
.
Zaune muke a falo muna makale da juna lokacin da kaunarta a raina ya karu da fiye da kaso tamanin cikin dari, ban iya sanin dalili ba amma meyiwuwa saboda bushashhar daren jiya ne daren da nake ta fatan Allah ya cigaba da maimaitashi
.
Ta kewayo hannayentaa biyu cikin wuyana “baka tambayeni a bunda mummy tace dani ba sanda za’a kawoni”
Na kura mata idanu “yaya zan tambayi sirrin da da uwa farida?”
Tayi murmushi “amma ka bayar dani ai sirrikana banga wanda zan boye maka ba”
Na karkace kai dana ji abun data fada”to me tace maki”
“Cewa tayi ta bani sati guda idan taga baka canza ba ni da ita”
“Na canza kamar yaya?”
Takara murmushi “kamar yadda mutun kan canja idan ya samu kwanciyar hankali,kuma na kudiri aniyar canja ka din ,zan mayar maka da jikina muhalli na hutawa, zanyi iya yina domin ganin cewa wata damuwa bata samu matsuguni a ranka ba, ta hanyar dandana maka kauna salo salo, salon rana zai kayatar da kai a yayinda na dare zai dameshi ya shanye
.
Nayi kasake dani”ni dama har akwai wani salon kauna da rana”
Tayi dariya “hala baka sanshi ba,to zaka sanshi daga yanzu “
Ta mike tsam , daki ta shiga ta bar ni nana cikin tunanin shin me zata yi, bayan yan dakiku da basu fi kaza ba sai ta fito
Numfashina ya tsaya cak bayan da naga shirin data yi, hakika in banyi a hankali ba farida so take ta zautani
.
Ta sunkuyo gare ni gami da kama hannuna tashi mu koma daki ko?”
Na zuba mata idanu
“Kunyarka din me zanji,idan naji kunyarka cutarka zanyi, ba zaka sami kaunar da kake bukata ba, to amma izan so kake naji kunyar ka fada min”
Shiru nayi ni cece bayan ta riga ta fara sangartani tuni na mike na bita dakin domin ganin abunda zatayi da ni ko tantama banayi zan sha riba buhu buhu
.
********
.
HALACCI
.
Bansan abunda ya sanya mummy cewa mu hallara agidanta ba sai dai koma menene na san muhimmi ne, musamman danayi la’akarri da cewa da tarewarmu ba afi sati uku ba, muka shirya tsaf sannan muka nufo waje a lokacin da muke rike da hannun juna tafiyace irin ta ma’auratan dake cikin soyayyarsu
.
Muka kulle gidan sannan muka duru a mota na ja mu a lokacin da farin ciki ke mamaye da zuciyata kana iya gane hakan bisa ga la’akari da yanda muke hira cikin murmushi, hatta kallon da mukeyiwa juna na musamman ne, mai bada hannu ya tsayar damu alokacin da muka iso wani junction, sai na taka burki na juya ga abar kaunata muka cigaba da hira
.
Bayan dan lokaci na waiwayi gefena,waiwayar da ta sanya wani abu ya tuko min a zuicya, wani mutumne dake kan babur ya saki baki yana kalle min mata, don mayata ko kiftawa baya yi
.
Na miko hannu waje “haba malam me kenan haka?”
Ya gaggauta kawar da kansa ni kuma na shiga fadace-fadace ina ruwan matsiyaci anyi zakara, tsugunne bata kare ba, can na hango wani mai mota shima , haushi ya kamani na sa hannuna na janyo mayafinta ta yanda ya rufe fuskarta, ta aka nayi maganin mayu
.
Bamu isa gidan ba sai da muka bata mini talatin yayinda da muka isa kuma sai muka ga bakon abu, wata jibgegiyar motar jeep ce , motar da ba mu sani mai ita ba, haka muka shiga gidan cikin rudani, sallama muka fara yi muryoyi da yawa suka amsa sallamarmu
.
Mutum biyar muka samu a zaune Mummy sai wasu maza guda biyu, a gefe guda kuma wasu matan, to wayannan kuma su wane ne, tambayar danayiwa kaina kenan, bayan dana ga ita kanta farida bata shaidasu ba, muka gaisa da kowa , muka zauna sannan mummy ta dubi farida “kin gane su kuwa
Girgizaa kai “tayi ban gane su ba”
“To yayyanki ne”
A guje ta tafi ga matan suka rungume juna , dukkaninsu suka fashe da kuka , na ci gana da kallon ikon Allah lallai dan uwa rabin jiki an manta da duk abunda ya faru a baya, bayan ya n koke koke da maganganu suka saki juna sannan suka sake sabuwar gaisuwa da mazan
.
Ta share hawaye “ina baba take”
“Baba tana asibiti cutar paralise ce ke damunta “
Wannan jawabi ya sanya farida kara fashewa da kuka ni ma kuma sai dana tausaya
Mai kama da babban cikinsu. Yaci gaba “kamar yadda kika san cewa akwai mu to yau gamu, nasan kin san sunayenmu amma da wuya ki iya bambancemu, to ni ki kirani kamal, shi kuma faisal waccan kuma fauzah yar uwartta salimah
Kuma abunda ke tafe damu neman gafara ne da afuwarku bisa abunda ya afku a baya mun ga abubuwa da zamu iya kira isharori wallahi ni din nan sama da shekara kenan kullum ina mafarki da baba, yakan nuna ni da yatsa yace”Allah na jiran isowata ” to hakan ya tashi hankalina, kuma nasan ko me nene ya jawo ga kuma mahaifiyarmu yau shekararta goma da cutar kullum abu kara muni yake kuma na tabbata ba komai bane illa hakkinku”
Ya share hawaye “ku duba zumunci ku kuma dubi ‘yan uwantaka ta addini ku yafe mana abinda ya faru ku dauka cewa shaidan ne ya rudemu, domin raba kawunan mu”
.
Mummy ta share hawaye “ku manta da komai Allah ya yafe mana gaba daya, mu dama ba mu dauka da zafi ba”
Ya shiga godiya yan uwansa ma suka taya shi bayan da aka natsu sai ya jawo wani akwati ya dubi mummy
“To hajiya kudinku dake wajenmu sun tunkari bilyan daya, to amma wallahi babu inda zamu samo su domin duk dukiyar ta lalace, yanzu dai mun taho da dan abinda ya samu in ya so sai a rubuta idan da raboon zamu biya saura zamu rinka kawo wa a hankali, har Allah yasa a warware komai”
Ta girgiza kai “sam mu baza mu biku bashi ba , abunda aka samu Allah ya amfana sauran mun yafe”
Ta waiwayi farida “koke me kika gani”
Gyada kai tayi “haka ne mummy”
Babban ya sake fashewa da kuka, da kyar aka samu yayi shiru yasa hannu ya bude akwatin tayi wata yar kara sannan ya dage murfin sai ga su kuru kur, tamkar wasu shashasun takardu, zallar dalar aamerica ce numfashina ya dauke ban taba ganin kudi masu yawa haka ba, da alama sun tunkari milyan dari
.
Yaci gaaba da bayani “ga sunana dalar america ce kwatankwacin naira miliyan saba’in idan an zanza su,
shi kenan anyi tsiyar zai rabani da mata ta, a kuma lokacin da bazan juri rabuwar da ita ba, nasan dai da wuya ta zauna dani alhali ta fini kudi, bisa kiyashi sama da naira milyan hamsin duk natane kaico ! Su umar an shiga bayan jaje
.
A washe garin ranar kawo kudi ta sake gayyatarmu , nidai nayi karfin hali muka je ia raina ina mai taraddadin kar tace na sakar mata yarta , yanzu wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa
.
AYYA UMAR
Na tayaka murna da wani daukaka daya ke zuwa maka nan gaba
.
Toh fa akwai dambarwa akan wata tsohuwar Al’amarin Umar, mai cikawa mutane angwa da kara, shin ko kunsa me wannan
.
Ina mika sakon ta’aziyata ga iyaye, da abokai na rashin Abokinmu da mukayi MALAM, wanda Allah ya dauki ransa shekaran jiya da daddare,
Allah ya jikansa
Allah yasa ya huta
Allah ya gafarta masa
Allah yasa Aljannah ce makomarsa
Allah yasa innamu yazo mu cika da imani
AMEEN summa AMeeen wa Ameeeeeeeeeen
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.