TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 7

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 7
.
.
Ya kunna wata yar karamar rediyo, daga ita ne muka ji duk abubuwan da ake tattaunawa, bamu mu rasa komai ba, har zuwa sanda suka rataye ka, da ace basu fito da wuri ba ritsa su yan sanda zasu yi, to amma fitowar da su sai ta taimaaka, domin da ba su fito ba din ba, za’ayi abin nan da ake kira anyi ba ayi ba, domin babu shakka da sunji alamar motsi harbinka zasuyi domin baza su so ka kubuta ba, suna kokarin hawa mota ne aka far musu in har kana cikin hayyacinka baza ka gaz jin harbin bindiga ba, suma fito na tasu sukayi akayi kare jini biri jini, sun raunata yan sanda uku su kuma an kashe musu mutum daya, biyu kuma sun shiga hannu bayan da akayi musu raunuka munana, akwai kato gabjeje shine mutumin dake wahal da kai ya kwana karkashin kulawar yansanda a daren jiyan dai an tura yan sanda uku asibiti su kula da farida gudun afkuwar wani abu”
.
Wani dadi ya cika zuciyata tuni na dungura goshi akas cikin sujjada dayiwa Allah godiya ban san adadin mintunan dana karar ba n dago fuskata cike da hawaye
“Lateef kayi min komai kayi min abinda ban san kalmomin da zanyi amfani da su ba domin godiya, kayi min abinda wani mutum ba zai taba yi min ba, ka ceci raina ka kuma kyautata rayuwata, ka tsamo zuri’armu daga bakin cikin da zai dauwama har abada”
.
Ya dafa kafadata “kar ka damu umar, nayi don Allahh don kuma kaunata da kai, zanyi farin ciki idan kuma na ganka da farida a matsayin miji da mata don kuwa kun sha gwagwarmayar da bata cancanci tashi a banza ba”
Na juya ga aziz hawaye na kwaranyowa daga idona “aziz me zance da kai? Na gode bata wadatarba, madalla tayi kadan to ina kalman?”
.
Yayi murmushi hutar da bakinka bana bukatar godiya wannan shine aikina akansa nayi rantsuwa , kuma don nayi ake biyana, abinda kawai nake nema kataya mu addu’ar Allah yaba mu damar sauke nauyi ya kuma bamu ladan abun da mukayi dai dai , inda muka kuskure yayi mana afuwa da rangwame idan ka yi haka shi kenan”
Ya mike tsaye “zan tafi wajen aiki kumaa zan kokarta wajen ganin na sami ganawa da yayanka, zan warware masa komai shi kuma sai ya tunkari iyaye”
.
Na fashe da kuka “na gode ! Nagode!! Aziz Allah ya cika maka burikanka”
Yayi murmushi “amin nima na gode”
Muka mike tsaye domin rako su waje shi da mutanen da suka zo tare
Ya fuskance ni bayan da muka fito “umar bincikenmu zai rutsa da mutum uku, principal malam Abba, da kuma Abokan zamanka na kasuwa da alama suna da hannu a abubuwa da dama
.
Yadan saurara daga bisani ya dora “zan yi iya yina don ganin shari’ar bata dauki lokaci ba! Za’ayi a kare a sati daya babu bukatar mai raunin ya warke, tunda raunin bai shafi gabobin hankali ba kafafu wane da hannu, zanyi wannan kokarin”
Na ci gaba da jera masa kundin godiya ahaka muka rabu
*********
Ina saka kafata dakin ta taso a guje na san nufinta shine rungume ni ni kuma bazan so haka ba musamman saboda ganin manya kusa da mu, cikin hikima na dan goce gami da riko hannunta don gudun kar tasha kasa
“Dakata farida da sauran lokaci”
Ta fashe da kuka “wayyo Allah umar da yanzu an cuceni da an takaita rayuwata”
Naja hannunta zuwa kan gado a hankali na zaunar da ita nima na zauna
“Umar barkanmu fa !”Zan cen mummy kenan tana mai zubar da hawaye,
Nayi murmushi barka dai”
Ta jinjina kai “wai hikimar Allah komai yana da karshe yau karshen wannan yazo”
Na sunkuyar da kai”wallahi kuwa haka lamarin Allah yake”
Ta mike domin ficewa daga dakin tasan tilas zamu bukaci ganawa
Futarta taba farida damar matsowa kusa dani “umar yaka ji da ranka?”
Nayi murmushi “naji abinda yafi dadi dadi abunda ya haure farin ciki fari abunda za a soma kwatanta shi da murna ba”
Ta lumshe idanu”naji wanda ya ninka naka sau dubu, shi yasa na warke a tsakanin awoyi goma kacal dana sami labarin cewa ka kusa zama angona”
“Aina kika sami labarin ke kuwa?”
Tayi “a cikin mafarki, naga har an daura mana aure ina baka madara a baki a cikin wani lambu mai matukar kayatarwa”
Raina yayi fari dajin kalaminta “to ni kuma fa me na baki ko ban baki komai ba”
Ta kara lumshe ido”ka dandana min zuma mai mugun zaki” na jinjina kai you’re right da sannu zaki dandaneta a farke da sannu zaki gane abunda ake kira soyayya atare da ni”
Tayi murmushi “ka cika garaje kai fadarce babu cikawa , ni kuma ka bari ka gani sai ka ringa kai karata wajen mummy”
“Wahalar dani zakiyi kenan?”
Ta gyada ki “kwarai kuwa,bazan barka ka sake ba sai ka dandana kudarka , amma fa da zunzurutun kauna”
Muka more da dariya
Tadan kimtsa “Umar za’abari ka aureni kuwa?”
“Me zai hana”
“An baka wata baka so”
“A ina ki kaji?”
Ta kwantar dakai “lateef ya fada min komai na dade ina mamakin yadda ka shirya wa kanka zafi saboda ni”
Nayi murmushi “manta d wannan na fada miki dalilin auren, kuma yanzu ya kau ki dauka cewa abubuwan da ki ka gani a mafarki ba mafarki bane, ki dauka cewa an yine a gaske, kuma. Za’ayi din”
.”Ka tabbta?”
“Na tabbta”
“Oh I love you”
“I too” muka kara morewa da dariya
……………………..
AYYA UMAR ANSHA DAKYAR
TO AMMAFA AKWAI WATA………..
.
www.facebook.com/hausaebooks

Subscribe to our newsletter
Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Leave A Reply

Your email address will not be published.