TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 6

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 6
.
.
Na tsakiyarsu ya zo gabana “malam umar sai defa kayi hakuri don kuwa yau zan aikaka kiyama , saboda na gama wasa da kai, dun haka yanzu zan rataye ka kowa ya huta
.
Daga nan kuma sai ace abun duniya ne sukai maka yawa ka kashe kanka,”
Yana zuwa nan a maganarsa sai ya kece da dariya mara dadin sauraro, suma gabza gabzan da suke bayanshi suka tayashi suna masu kyakyatawa
.
Sun dau lokaci suna wannan dariyar alokacin da ni kuma na gama sallama rayuwata jira kawai nake mutuwata ta zo ta daukeni don na tabbata bazan tsira daga hannun wannan mugun mutumin ba
.
Babu abun da ya fara zuwa araina face yadda farida zata kasance izan na mutu nasan watakila itama ta mutun domin kuwa babu ta yadda zata iya rayuwa in batare da ni ba saboda zunzurutun so da kauna da take yi min
.
Alokacin dana tuna da iyayena sai wani kwallan bakin ciki ya yagangaro daga idona, sai a sannan na fara nadaman irin abunda nai masu, nasan ba shakka nabar masu abun gori a zuria gashi ni kuma zan riski ajalina a hannun wayannan mugayen mutane,
.
Katon dazu ya sake dubana lokacin daya tsuke bakinsa ga barin yin dariya, yace “kash Umar da alama naga kana son rayuwa a bankasa sai de nayi maka kashedi kaki ji dun haka sai a gaida Kiyama, “
Yana gama fadin hakan sai ya sanya kafarsa ya ture teburin da kafana yake kai , teburin na faduwa sai na zazzago kasa,
Igiyar dake daure a wuyana ta shake ni tamau na dunga wuntsila kafa funa ina neman taimako a haka har wani hazo ya ziyarci idanuwana, daga nan ban san Abun daya fsake faruwa dani ba
.
*******
A firgice na. Farka ina kiran Inna lillahi wa inna ilaihirr ra’ji’un,
Na tsinci kaina acikin wani dan madaidaicin daki ina kwance akan gado ga mutane uku a gefen kaina,
Na mike na dubi mutanen wayanda sam basu yi mani kama da mutanen dazu ba, don kuwa wayannan sun yi shiga ce irin na ma’aikata, sunci zanzaro sai kace mr mugopark
.
Wani daga cikinsu ya kariso ya miko min I.D card ,na duba a gaggauce na Hukumar ‘yan sanda ne
Suna : Azizu jakande
Matsayi: Inspector
.
Take sunan ya fado min arai babu shakka kanin lateef ne wanda yace zai tuntuba da maganata sai na saki jiki
.
“Ka amice?” Ya nemi ra’ayina
Na gyada kai “na amince”
“To ina wanda ka kashe?”
Na girgiza kai “ban kashe kowa ba”
Duk suka bushe da dariya
Ya dubi wani dan sanda “ku mai da mu a motarku wajen yana da nisa”
Ya kame “an gama yallabai”
*****
Ina zaune a dakina mutane uku kewaye da ni, na farko lateef ne sai kaninsa Aziz da kuma wani ban san ko waye ba, na dubi agogon bango karfe takwas na safe da minti hudu
$
A sannane lateef ke cewa “Umar Allah ya kiyayeka ka tsallake rijiya da baya, ba dan an kawo agajin gaggawa ba da yanzu ana zaman jimami”
Na dube shi “wai yaya abun ya kasance?”
Ya gyara zama “izan zaka tuna min yi maganar kanina da kai, a daren jiya na taho da shi nufina ku gana, a sannan cikin sa’a na sami kofar dakin ka a bude, sai na kwankwasa amma shiru baka amsa ba, ganin ganawar dare ya kamata ayi saboda la’akari da cewa an zuba ido akanka, sai na yanke shawarar shiga na ta sheka, hakan nayi kokarin zartarwa ina saka kafa naji sailula na ringing dana duba sai na ganta kusa da kafata na sunkuya na dauka gami da nufar shimfidarka domin na baka ka amsa kiran, banga kowa a shimfidarba, na zaci bandaki ka shiga sai na danna ok domin baiwa mai kiran uzuri
Ina fadin “hello’
Wata kakkausar murya ta biyo baya “kai malalaci in ce ka shirya ko? Yanzu zamu aiwatar da nufinmu”
Nayi shiru ina sauraron murdadden sakon muryar kuma taci gaba “kana iya hutar da kanka, kayi zamanka a daki nan muka zaba maka amatsayin kabari, ko kaje wani wajen sai mun maido ka”
.
Da fadin haka na tsinke layin da wurwuri na gane mai maganar da kuma inda ta nufa sai nayi saurin durfafar ban daki na kwankwasa da karfi amma ban ji amsa ba jin haka ya sanya ni turawa wayam na sami shi babu kowa a ciki, da sauri na gayyato kanina na labarta masa abin da ake ciki
.
Ya jinjina kai “zo mu ja jiki, yanzun nan kaga sun zo”
Banyi musu ba muka fice daga dakin da sauri bayan da ya ajiye wata yar na’ura, mukaa nufi wani lungu muka rakabe, da labewar mu yayi waya head quarter’ din yan sanda ‘yan sanda goma ya nema masu zafi iya aiki, fadi inda zasu zo , ko minti ashirin ba ayi ba suka karaso, ‘yan dakiku suka harba agogo wadanda su suka isa tattaunawa a kuma kaso rukuni-rukuni
.
A cikinsu ne kuma fitilar mota ta hasko layin ta durfafo kai tsaye yadda muka zata din haka ta afku a kofar dakinka ta tsaya bayan dan lokaci wani ya fitoo, kwankwasa kofar dakin yayi, kafin daga bisani ya tura kai ciki, ya dan jima kadan me yiwuwa minti biyu, watakila kuma uku ko hudu a cikinsu ya fito ya sake dawowa ga motar bayan ‘yan maganganu duk kofofin suka bude, wasu kartin mutane biyun suka fito, ‘but’ suka daga inda anan suka kinkimo buhu, bamu raba daya biyu ba wajen tabbatar da cewa kai ne a ciki, suka shige dakin da kai
.
Na dubi kanina “mukai agaji
Girgiza kai yayi “tukunna dai akwai sauran lokaci”
.
Kuyi hkri da short page dinnan
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
www.facebook.com/hausaebooks

Subscribe to our newsletter
Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Leave A Reply

Your email address will not be published.