TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 5

Posted by | Mr Hausa Ebooks |
Price | GPL |
Category | Uncategorized |
Uploaded On | 05 Sep, 2018 |
Upload Time | 6:27 pm |
Hits | 169 Hits |
Comment | No Comments |
Description
TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 5
.
.
Muna nan tsugunne cikin jimami, wata nurse tazo tayi mana sallama, sannan taci gaba” hajiya an fito da yarki daga dakin na’urori an bata daki mai lamba sha hudu, zo muje ki gani”?
.
Muka mike gaba daya babu wani alamun karfi a jikina tamkar wanda aka wuni laftar masa jiki,
Mummy ta dubi nurse din “a wanne hali take yanzu?”
“Eh to mu karasa din ina ga ana iya cewa da sauki tunda tana iya yin numfashi sama sama”
Tsoro ya kara cika zuciyata, a wannan hali muka isa dakin tsa hannu ta tura kofar ta shiga sannan muka bita abaya,
Kwance tage rigingine idan baka kura ido ba bazaka ga alamun numfashinta ba, tamkar wata gunki ce ko zane
Na girgiza kai cikin tausayawa a kuma lokacin da zubar hawayena ke daduwa
Mummy kuwa tagumi tayi da alama ta gama fidda rai hawaye a fuskarta wani na bin wani
.
Nurse din ta dafa kafaddarta “ki kwantar da hankalinki hajiya me yiwuwa nan da awa biyu zata iya wartsakewa, damuwa ce tayi mata yawa kdan ya rage jininta ya hau, amma Allah ya kiyaye, wata kila gobe iwar haka ma ta iya takawa da kafafunta”
.
Daga ni har mummy babu wanda zancen ya shiga akwai shakku cikin tashin farida a irin wannan dan kankanin lokaci, tana iya yiwuwa tunda su jami’an lafiya ne, suna da sani akanta, tana kuma iya kin yiwuwa jawabin nata ya kare ne a matsayin wani salon kwantar da hankali
Muna nan zaune cikin halin zama mai kama da makoki ga wadanda radadin mutuwar ke cinsu, sai kofa ta bude wani ne dan siriri dogo da ganinsa kasan kwararren likita ne,biye da shi akwai wasu nurse guda biyu
.
Ya dubemu “ku dan bamu dama, zamu dan bata wani taimako’
Muka mike a tsaye tare batare da bata lokaci ba muka nufi waje
Na duba agogona karfe goman dare na juya ga mummy” zan je na dawo in Allah ya yarda nan da minti talatin
Ta gyada kai “to shikenan”
*****
Na san makulli na bude dakina batare da bata lokaci ba nasa kafa ciki ba komai ne ya maido ni illa na kwashe yan tsirarun kudadena da suka rage, aniya ta shine siyawa mummy abinci da su, bayan dana kula cewa itama bata ci komai ba, sai dai ba anan gizo ke sakar ba ko na kai mata ma ba lallai ba ne taci
.
Bayan dana debe sune na fara kokarin ficewa a daidai lokacin ne wata kara ta gauraye ko ina na,cike da mamakin abunda ke iya yin wannan kara, shakka babu agogon bangona bashi da alarm , ban kuma mallaki wani abu mai alarm ba
.
Shawarar dana fara yankewa itace nayi ficewata , amma sai karar taci gaba abinda yasan ya ni canza shawara , na fara yan dube dube domin gano daga inda karar ke fitowa, bayan dan lokaci na fahimci wajen akan katiata ne sai na nufi can ina mai kwadayin ganin ko me ne ne, mamaki ya kama ni yayin da na yi arba da mai yin, na’urar sadarwa ce ta hannu, ni dai ban mallaketa ba kuma baki nake yi ba ballantana nayi zaton wani ne ya manta ta,
Na kasance cikin shawarwarin abunda ya kamata nayi wata zuciyar tace tsallake ka fita,wata kuma tace dauki ka saurari kiran daga nan ma sai ka san ko ta wace
.
Nayi kasadar durkusawa na dauka kirar samsung ce mai kyawun gani, har yanzu bata daina callara kara ba, cikin ganganci da karambani na danna O.K ban bata lokaci ba wajen karata a kunne na
“Hello wane ne”
Aka amsa a daya bangaren “Mala’ikan mutuwane”
Error page error page error page
An samu matsalar fallayen littafin anan amma ga abuinda ya kunsa
.
“Hello wane ne”
Aka amsa a daya bangaren “mala’ikan mutuwane”
Gabana ya buga, hankalina ya tashi sakamakon muryar danaji, ba kokonto tabbas na shaida wannan murya, ba muryan kowa bane illa na mugun mutumin nan daya jefa rayuwata cikin tashin hankali
Mutumin ya cigaba da fadin “kai yaro ka tsorata ne , to gwamma ma ka saduda don kuwa mun riga da mun gama wasan da mukeyi da kai, don haka yau zaka bakunci kiyama dafatan kayi aiki mai kyau, sannan ina shaida maka gwamma kayi zamanka a cikin dakinka domin kuwa anan muka zaba zamu kasheka, amma in kaso kana iya tafiya duk inda zaka, mu kuma zamu bika mu kamoka sannan mu dawo dakai har dakin naka sannan mu hallakak…”
.
Ban tsaya ya karasa maganar ba na datse kiran ta hanyar kashe wayar, sannan nayi cilli da ita ta gwaru da bagon dakina
.
Gabana sai faduwa yake , na fito daga cikin dakin na kulle sannan na nufi hanyar asibiti ,
Ina tafiya ne kawai amma hankalina bashi a jikina, tunane tunane kala kala babu wanda banyi ba acikin zuciyata,
Domin kuwa nasan wannan mutumi bashi da imani kuma baya da tausayi tabbas zai iya aikata abunda ya furta
.
Ina cikin tafiya ko lura da gabana banayi, kwatsam sai ji nayi wani abu ya dake ni akai zan yi ihu amma naji wata basamudiyar hannu tayi caraf ta rufe mani baki,
Koda na lura sai naga wani katon mutum ne ya rungume ni ta baya ya kuma sakayo da hannunsa ya rufe min baki, ina ta wutsil da kafafuwana domin na kwaci kaina daga hannunsa amma yafi karfina, babu irin kokarin da banyi ba , haka wannan mutumin ya dauko wata hankici daga aljihunsa ya sanya a hancina, wani daddan kamshi na sheka daga nan ban san me ya faru dani ba
******
Farkawa nayi a gigice sakamakon ruwan sanyin daya sauka a fuskana, cikin firgici na bude idanuna, ba karamin razana da kidima nayi ba sakamakon yanda na tsinci kaina,
.
Igiyane mai kauri daure a wuyana igiyar an jashi yaje sama aka daurashi a jikin fankan dakina,
Hannuna suma a zagaya da su ta bayana sannan suma aka dauresu tamau
kafafuwana kuwa suna saman wani dan karamin kujera wanda da ba don shiba toh na tabbata da yanzu ina kiyama,
.
Hahhahahahahahah, sautin dariya naji acikin dakin nan idona yakai wajen da nake jin dariya take idona yai arba da wasu girda girdan karti su Uku, dukkansu suna sanye ne da bakaken kaya, jaket, da kuma jeans,
Na tsakiyarsu ya zo gabana “malam umar sai defa kayi hakuri don kuwa yau zan aikaka kiyama , saboda na gama wasa da kai………
.
KAI UMAR
A TUNANINKU UMAR ZAI TSIRA
KUWA
Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel
Leave a Reply
Related Files
-
TARAR ARADU littafi na daya page 4
4 years ago
199 Hits -
ABOKAI littafi na biyu 2 part 6
3 years ago
157 Hits -
TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 9
4 years ago
224 Hits -
TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 8
4 years ago
178 Hits -
RANA DA WATA littafi na biyu 2 part C
4 years ago
147 Hits -
MAZAN KO MATAN part 1
4 years ago
621 Hits -
MAZAN KO MATAN part 4
4 years ago
144 Hits -
TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 6
4 years ago
197 Hits -
TASKU littafina daya 1 part 5
4 years ago
131 Hits -
RANA DA WATA littafi na daya 1 part D
4 years ago
363 Hits
Hausa Ebooks
-
BAKAR INUWA complete hausa novel written by Bilyn Abdul
5 hours ago
50 Hits -
DAMUWATA complete hausa novel written by Mrs J Moon
5 hours ago
31 Hits -
RASHIN JITTUWA complete hausa novel written by Mrs J Moon
5 hours ago
39 Hits -
RUMASA’U complete hausa novel written by Mrs J Moon
3 days ago
229 Hits -
MUTUNCI MADARANE complete hausa novel written by Mrs J Moon
3 days ago
385 Hits -
ZEENATU complete hausa novel written by Queen Meemi
1 week ago
336 Hits -
KOFAR AJALI return complete hausa novel written by Abdul Alhaji Musa 10k
1 week ago
465 Hits -
SAIFUDDEEN complete hausa novel written by Billy Giro
1 week ago
1068 Hits -
NAGARTACCE complete hausa novel written by Oum Hanan
1 week ago
1053 Hits -
SHIN SO DAYA NE complete hausa novel written by Hafnancy
2 weeks ago
542 Hits
Movies and Films
-
Download Kalubale indian hausa fassarar Algaita
1 day ago
82 Hits -
Download Jaruman Kasa indian hausa fassarar algaita
1 day ago
70 Hits -
Download Inuwa Indian Hausa Fassarar Algaita
1 day ago
48 Hits -
Download Hatsabibi Indian hausa fassarar Algaita
1 day ago
76 Hits -
Download Fusataccen Dan Sanda indian hausa fassarar algaita
1 day ago
77 Hits -
Download Gadar zare indian hausa fassarar Algaita
1 day ago
54 Hits -
Download Barkonu Indian Hausa Fassarar Algaita
1 day ago
56 Hits -
Download Fuska Biyu indian hausa fassarar Algaita
1 day ago
65 Hits -
Download Dan Baiwa indian hausa fassarar algaita
1 day ago
60 Hits -
Download Farcen Gumurzu indian hausa fassarar algaita
1 day ago
52 Hits
Musics
-
Download Music: Adam Zango – Amarya
3 days ago
84 Hits -
Download Music: Adam Zango – Diana
3 days ago
81 Hits -
Download Music: Adam Zango – Allah ya gyara
3 days ago
53 Hits -
Download Music: Adam Zango – Manyan Mata
3 days ago
52 Hits -
Download Music : Adam Zango – Matan Aure
3 days ago
63 Hits -
Download Music Auta Mg Boy – Amana da amana mp3
6 days ago
111 Hits -
Download Music Farfesan Waka – Damfara Mp3
6 days ago
106 Hits -
Download Na Baki Soyayya – Adam A Zango Ft. Sals Fateetee Mp3
3 weeks ago
196 Hits -
Download Soja Boy – Nishadi Mp3
3 weeks ago
142 Hits -
Download Music: Sarkin Waka – Sai mun bata wuta Atiku
3 weeks ago
398 Hits