TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 4

 TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 4
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 05 Sep, 2018
Upload Time 6:26 pm
Hits 190 Hits
Comment No Comments

Description

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 4
.
.
A guje na shige babbar rigar liman ina neman ceto” ka ceceni liman , idan suka tafi dani kasheni zasu yi”
.
Da nasan haka ce zata faru da ban kwatanta shiga rigar ba, wani rin dundu yayi min da naji tamkar zan amayar da kayan cikina
.
Yafara fada cikin bambami da daga murya “mutumin banza suma kashe ka din mana, wacce tsiya barawo zai tsinana idan an kyale shi? Ni dai Allah ya ceceni da ban riga na aura maka ‘ya ba , ace kamata ya aurawa barawo ‘ya”
.
Wani sabon salallami ya fito daga bakin wata mata”lailaha illallahu, dama barawo ne malam”
“Barawo ne mana motar mutane ya sato, masu ita ne suka zo masa da ‘yan sanda, bakanikensa ne ya tona shi”
“Amma Allah wadaranka” inji wata ‘yar tsohuwa, ko rara daya biyu banayi mahaifiyar liman ce, sai dai ba zanso addu’arta ta karbu ba
.
Cikin halin riko na sai na dubu ta taru ‘yan bangar suka nufi waje dani, kafata ko takalmi babu tuni na watsar da su, cincirindon da jama’a sukai a waje yayi matukar girgizani, da ganin fitowarmu suka dauki hayaniya, kowa yana fadin abinda yake ganin yayi daidai da shi, cikin motar aka watsa ni, batare da saurarawa ba aka nufi nahiyar gida dani
.
Tarar da mahaifina zugum a soro yana hawaye ya rikitani, na tabbata bakin cikin abinda ke faruwa ne yake cinsa, naji tamkar na tashi drama din na dakatar da ita na kuma fayyace gaskiya, sai dai xuciyata bazata bari ba, ita take jagoranta ta, yayin da ita kuma so yake sarrafa ta, abinda yafi hakan tashin hankali shine samun mahaifiyata tayi zaman dirshen a tsakar gida, kuka ,karaji da kururuwa duk tana yinsu, wannan ya sanya na tsani kai na, bakin cin takaici da damuwa duk suka baibayeni, na amincewa raina na fayyace komai domin samawa iyayena kwanciyar hankali, babu shakka hakan shine zai fi
.
Da wannan tunani na fara kokarin banbare wandona dake rike a hannun wani kato , shi kuwa sai ya kara dakume ni a zatonsa wani salon ne na kara kyautata drama din
“Sakar ni malam” na fada afusace
Ba sakin nawa yayi ba, matse ni yayi iya kacin matsewa gami da yarfa min biyar yana huci, tamkar na rama naji yayin da zogi ya ratsani, to amma sai nayi ta maza na kasance cikin halin daure fuskata hawaye ya zubo min dana kara nazarin halin da mahaifiyata take ciki, ba zan iya kiyasta bakin cikin da take ciki ba na dai tabbata tana tattare da damuwa.
.
“Dauko lambar mu tafi” wani kato ya daka min tsawa, bana bukatar shiga wani waje hannu na tura cikin rumbu na fito da ita, abinda ya sanya yan kato da goran kara tasa keyata, gab da zamu shige soro na kara waiwayowa na dubi mahaifiyata, kafin kuma na tarar da mahaifina a soro, lissafi duk ya dagule , ina ma zuciyata zatayi min alfarma na fayyace komai, sai dai ina ba zata yi min ba, soyayya dake cike da ita ta baibaye ta, wanda hakan ke sauyata gargadi ne cewa farida kubuce min zata yi
******
Ina zaune shiru cikin tariyo abinda ya wakana akauyenmu , a lokacin da su kuma yan kato da goran ke tariyo abubuwan dariya, sai dai atare dani banga abun daya isa ya sanya ni dariya alokacin ba, na rinka tuno halin tashin hankalin dana bar iyayena aciki, na sani izan ba sa’a ba na bar abun da za’ aita goranta wa zuri’armu har a nade kasa, wannan itace dabi’ar zaman kauye, barawon Albasa ma akan haana jikansa diya, ballantana kuma ni aka ce barawon motane
Toh ya kukejin littafin (Shuraih Usman)
.
Lateef ya danka masu kudin aikinsu naira dubu biyar, suka watse suna godiya, suka bar mu mu biyu ni dashi,
Ya dubeni “ina fata komai yayi yanda ake so”
Na gyada kai “komai yayi lateef sai dai kuma ina mai jimamin abubuwan da suka faru, ko tantama bana yi iyayena suna cikin bakin ciki”
.
Ya girgiza kai cikin jimami daga bisani ya kara matsowa kusa dani
“Umar na shawarce ka da wani abu mana”
“Wani abu kemar me fa”
Ya sunkuyar da kai “ka gafarce ni bisa abin da zan fada a gani na ka hakura da farida zai fi sauki”
Na kura masa ido kawai a kuma lokaci guda hawaye ya fara gangarowa daga kumatuna nasa hannu na share sannan na mike tsaye
“Lateef da ace zuciyata zata iya jure haka , da tuni na aiwatar da shi, sai dai ina! Ba zayta jure ba tun farkon gani na da farida ta rigaya ta mallake ni, bana aiwatar da komai sai abinda zan faranta ranta, kuma kasan wani abu a halin yanzun ba auren tane abin daya fi damuna ba, burina shine na tsamo ta daga kangin rayuwar data ke ciki, na daura niyya kuma zan cigaba da fafutaka iya raina, ko bani ba farida zata auri wanda ranta ke so, ta dandani dadin rayuwar aure ita da mijinta?” Na sunkuyo kusa da fuskarsa “ka shaida lateef na rantse da Allah na bayar da rayuwata fansa ga murmushin fuskar masoyiyata”(ina masoyan gaskiyan suke)
(Ga ni nan Shuraih Usman
.
Ya jinjina kai gami da kuramin idanu, daga bisani ya ajiye wani ingarman numfashi
“Lallai umar kayi nisa, ba kumaa zaka taba jin kira ba, saidai duk da haka ina da wata shawarar, ka mika rahoton hannun ‘yan sanda zasu taimaka wajen zakulo duk abinda ke faruwa”
Na girgiza kai “bazan yi haka ba lateef , irin wannan binciken yana bukatar hanya ko kudi, ni kuwa hanya ta zuwa masallaci kawai, ka sani kudi kuwa bana bukatar cewa da kai komai”
.
Ya mike tsye gami da dafa kafadata “Umar nima bani da kudin amma ina da hanya kuma hanya wadda take da karfi, yaya zaka yi idan nace kanina inspector ne? Da taimakon Allah da jajurcewa ta muka samu yakai matsayin, sa’arda yana karatu ko naira daya ya kashe, nine na bashi ita, to zan taimaka maka zan tuntube shi da batun, kuma zai yi duk abinda ake so batare da ka kashe koda naira daya ba”
.
A wannan lokaci danake cikin tashin hankali abune mai wuya na iya yin murmushi, saidai na jibgewa lateef kundi-kundi na godiya, yayi murmushi ‘kar ka damu Allah ne ya hada mu, bamu san irin amfanar juna da zamuyi ba arayuwa”
*****
Ban tsaya yin komai ba in banda wanka , haka na nufi asibiti yunwa na kwakular cikina, tunda na saka kafata a ginin asibitin tunane tunane suke ta tsere a raina, mafi muni shine mai cewa mai yiwu wa farida ta rigamu gidan gaskiya
A inda na bar mummy jiya, yau ma anan na tarar da ita bata canza kaya ba, ban kuma ga alamar tayi wanka ba, canji daya dana iya gani shine yau tafi jiya rama, ta dago kai sa’ar da na tsaya a kanta ba gaisuwa ce agabanmu ba mai jiki na fara tambayarta,
.
Ta kwantar dakai “to ina iya cewa da sauki tunda dai shi ake nema, amma ni tun jiya har yanzu ban ganta ba, kowa na tuntuba sai yace na dai saurara wai ana cigaba da kokari , umar ina zaton ma mutuwa tayi suke boye mun”
Hawaye ya zubo a fuskata, shiru nayi cikin rashin sanin me zance da alama fitar da rai da farida ne, ya mantar da mummy tambayata yanda na karke da iyayena, to ana ta kai waya ke ta kaya?.
.
Jama’a sai fa kunyi hakuri kwana biyunnan don ina busy sosai, amma zan ringa kokari koda short ne ina kawo maku
.
Sannan ina taya Abokina YARIMA A GANGARIYA murnar , domin kuwa iyalinsa ta haifa masa ya mace , Allah ya rayata, ya sa mahaddaciyar Alqur’ani,
Ameen
.
Nidinne dai Shuraih Usman
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: