TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 3

 TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 3
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 05 Sep, 2018
Upload Time 6:26 pm
Hits 170 Hits
Comment No Comments

Description

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 3
.
.
Na marairaice “tawace baba”
Bai kara komai ba sai ya tafi ya rabu dani na dan tsaua jim sannan na nufi cikin gida
.
A wajen mahaifiyata farin ciki na tarar da kyakkyawar maraba, ta gabatar min da abinci da kuma fura, Na fito wajen lateef gayyatarsa nayi muka shiga cikin dakin da aka ce nawa ne nida laraba, na ajiye masa abincin ni kuma na koma gefe guda.
“To taso muci mana”
Nayi tsaki “bai da muhalli a ciki na”
Hakika bai kamata nayi haka ba, ko don gudun kar ya zargi wani abu musamman saboda bambancin kabila dake tsakaninmu ga kuma dukiyarsa da muka taho da ita, Amma ina! Shi sam bai kawo haka arai ba tuni yaci tuwo yasha fura, daga bisani yaja fulo ya tuntsure, anan yabar ni ina ta kulle kulle arai har safe,
.
Tun da sassafe lateef ya hau tabe tabe ! Ba wani gyara ne na gaske ba, juyen baikin mai ne da yan abubuwan daba a rasa ba, wajen karfe dayan rana ya kammala, na sallame shi ya tafi, bayan da nace ina zuba idanu, wani lamarin da mahaifina ya tuhume ni akai shine ganin na kwance Number plate(Lamba) na ajiye, wannan ma ya sanya masa shakku a zuciya, na shiga gida na sami mahaifiyata, izini na nema akan ina so mu gana da amaryata, ban sami matsala ba, kai tsaye ta aika gidan ta sanar da su, aka ajiye karfe hudu a matsayin lokacin daya kamata na je, wanka na yi na yi fess dani sannan na hau mota na shiga zagaya gari, duk inda na bi sai abini da kallo, wai su abin mamaki ne saurayi kamata da mota mallakin kansa, ni abin har ya kan bani da riya, ba wata motar kirki bace, irin tsohuwar yayin nan ce da ake yiwa lakabi ajalin tafiya(tab
.
Kafin wani lokaci labari ya game ko’ina Umar ya sayi mota, aka rinka zuwa yiwa iyayena barka, sai dai abinda basu sani ba gab barka take da komawa jaje, meyi wuwa awoyi biyu nan gaba
.
Karfe hudu shaura na durfafi gidan liman , bayanda nayi sallar la’asar, kafin n kara sa, shi ma ya fito daga masallaci yana zaune a wani katon buzu yana jan carbi naje na durkusa gwiwa biyu na gada shi, ya amsa gami da shi min albarka, wai har yarom kirki yake kirana, na tashi zuwa gindin mota ta bayan da muka kammala
.
Na harde hannaye a kirji, gami da jingina sosai da motar daidai nake kallon mutane taamkar wani dan birni mai ji da kansa a taron kauyawa
.
A karo na tara na kai idona ga kofat gidan liman , babu abinda nake son gani illa fitowar laraba yarinyar da aka ce da ita ake shirin daura mana aure gobe, koda yake fuskarta bata nuna komai ba, amma amma adadin majalisun tattaunawa dake zuciyata har sun wuce kirge, wadda nafi jin haushi itace mai cewa idan bayeraben ya gaza aiwatar da shirin yaya zanyi.?
.
Shakka babu wannan tunani ne dana ke wwadai da shi, koda a mafarki kuwa ba zan so ya wakana ba, duk kuwa da cewa aiwatar da shirin wani tashin hankali ne babba, amma a wajena tashin hankalin shirin yafi rashin masoyiyata, a wani sashin kuma tafarfasa zuciyata take yi tana kuna, ba don komai ba, sai don abubuwan uku da ahalin yanzu suke tare da ni, Na farko tsana ta da ganin yarinyar dana aika ayo min kiranta, araina zan fi son kallon abu mafi muni fiye da kallon fuskarta, ba don komai ba sai don kasancewarta mai son mallake wani matsayi dana alkawartawa farida shi, hali na biyu kuwa zulumi da jimamin abinda zai biyo bayan shirin danayi, ko tantama babu zai zamo bacin rai da bakin ciki mai girma ga iyayena, zan tafi na barsu cikin tashin hankalin da ban san abinda ya kamata na kwatanta shi da shi ba, tun da na gano haka kuwa kamata yayi na fasa sai dai ina, zuciyar ta yi nisa ban da tunanin mallakar farida bata tuna komai
.
A gefe guda kuwa rashin sanin halin da farida ke ciki ne ke dagula min lissafi, ko ba komai dai na tabbata tana jin jiki, in haka ne kuwa dole ne nayi gaggawar komawa kusa da ita, a cikin wannan hali na hango ‘yan mata biyu fitowa daga gidan liman
Fuskar daya na iya gani ma’abociyar tsage ‘yan baka da uku-uku dayar kuwa ta rufe fuskarta da farin mayafi, abun d ya tabbatar min da cewa itace wadda ake so na aura, tsayuwarsu a kusa dani ta sanya wani abu yuko min arai, na tsane su iya tsana tamkar na rufe su da duka naji araina, dayar ce ta fara gayar dani, karfin hali nayi na amsa batare da nuna wani abu a fuska ba
.
Daga bisani ta juya ga dayar “laraba baku gaisa ba”
“Ina wuninka” ta maganar ne cikin murya mara kara
Na amsa “lafiya lau” daga haka ban kara komai ba
Batare dana shirya ba , dayar ta janye mayafin da yarinyar ta rufe fuskarta, hakan yabani damar ganin abinda fuskarta ta kunsa,
Doguwa ce ma’abociyar dogon hanci da dan karamin baki idanunta dara dara farare da suka wadatu da gashin gira, idan aka cire hassada mai wannan siffar ita ake kira da kyakkyawa, irin kyawun da duk wanda matarsa ta zama haka bazai rinka nisa da ita ba kuma na sani hikimar mahaifina kenan ta nema min aurenta, sai dai hikimar bata amfanar ba , domin ina tare da wadda ta dame ta ta sahnye, kyakkyawar da idan tana nan duk wata mai kyau ta kan dusashe
.
A zahiri na san yadda ake hira da masoyi sai dai ban san yadda ake hira da mutumin da bai da kima a rai ba, shiru nayi ina sake saken wani batun da bam, abinda na tabbatar zai jefawa ‘yan matan shakku a rai, kuma a lokacin na tabbata fuskata ta nuna damuwar dana ke ciki
Kamar an watso su sai gasu suna nufo mu da gudu-gudu, bakake wuluk da su kamar tawagar tururuwa, gayyar irin yan kungiyar nan ne vigilante group (kato da gora) suna cikin motarsu kirar hyundai samfurin pick up (a kori kura) duk da cewa na san su wakilai ne na tashin hankali, wadanda. Lokacin dauke suke da manyan kwandunan takaici, sai na kasance cikin farin cikin zuwansu, ko shakka bana yi a yau din nan maganar auren zata ruguje, sai dai na tabbata duk wani mutunci da kima dana ke da su zasu bi hadarin kaka
.
Na kai idona ga nahiyar da liman yake zaune yana aikin jan carbi, nayi farin ciki dana ga cewa shima yaga zuwansu, ba shi kadai ba hatta ilahirin jama’ar dake rukunin hankalinsu yana kansu baya ga wata gayyar ‘yan bin kwakwaf da sukaa biyo su da gudu ban yi mamaki ba a kauye dan kato da gora da dansanda duk sunansu daya
.
A guje yan matan suka nufi gida yayin da motar taja birki gab da mu, wata kura ta turnuke tamkar a fagen fama , suk kuwa ba su bata lokaci ba wajen durowa, kai kace wasu kwararrun sojoji ne da suka sami horo
“Yawwa shine, ga motar nan” lateef kenan wanda yake daure da ankwa, ala dole wai shi bakaniken mota ne,
Dajin haka sai nayi fitar burgu, ni ma gidan liman din na shiga,
“Ku tare shi, kar ku bari ya sha”
Zancen wani gabjeje kenan daga yan kato da goran, saidai ya makaro domin tuni na tsunduma aciki
“Ku ceceni zasu kasheni” wannan shine abin da nake fada. Banyi wata wata ba na nufi wani lungu dana ke zaton na ban daki ne, bayan dana yi fatali da wata kwaryar nono na kuma firgita agwagi, abinda ya sanya matan dake gidan fara salallami, iya kacin iya wata nake makyarkyata da kuma kumfar baki, harshena kuma yana furta na banu na lalace
.
Hakan sai ya sanya matan kasancewa cikin rudani bisa rashin sanin abinda ya firgitani, a wannan hali liman ya ba zamo cikin gidan da sauri, akwai gayyar yan kato da gora biyar biye dashi, na tabbata iznin shigowa suke nema, na fara kwalla ihu, ina shirin kama katanga, biyu ne daga cikin yan kato da goran suka rike min kafafu, jawo ni sukayi na fado kafin wani ya dubi fuskata ya yarfa min biyar, wani irin radadi gami da zogo suka keta fuskata naji kamar ance masu su dakata , to amma sai naci gaba da jurewa, ……..
WAIWAI TOH FAH
YAU UMAR DAKANSA
YA YAYIMO KATON DUTSEN RIGIMA
DON TOSHE DUK WANI RAMI DA ZAI KAWO CIKAS A TSAKANINSA DA FARIDA
.
Nidinne dai shuraih Usman
Inkiya 99%
Kuyi like na shafinmu www.facebook.com/hausaebooks

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: