MAZAN KO MATAN part 4

Duk da cewa na san ta Gane ni amma sai na matse nayi tamkar ba nine jiya muka hadu ba
Na matso kusa da ita fuskata na kallon kasa cikin boye murya nace
“Dan bani hanya yan mata”
Batare da musu ko gardama ba ta matsa mani na wuce,
Zuciyata sai bugawa take ina tunanin shin bata ganeni ba kuwa,
Wata zuciyar tace ai data ganeka da iyanzu baka kawo nan ba,
,
Daidai ina shirin ficewa daga gidanmu naji muryanta tana kiran suna na
Duk da banso na tsaya ba amma sai na tsinci kaina ina mai tsayawa
,
Cikin takunta na rangwada fuskarta a bace ta tako wajena,
“Yan mata naji kaman kin kirayi sunana”
“A,a ni ba sunanka na kiraba, this property is not for sale nace”ta bani amsa
Zuciyata ce tai dumm nan take naji kunya ta lullubeni,
Nai karfin hali cikin borin kunya nace
“Dun Allah sadiya ki hakuri da karyan dana shirshirga maku jiya, dun Allah kar ki fadawa wa umma na”
,
Tai murmushi wanda ya bayyana kyawawan hakoranta kafin tace
“Hmm shuraih kenan, shin an gaya maka ni karamar yarinyace, ko ce maka akai ni ban sanka ba, ai tun da dadewa na sanka kuma har wajen kanikancinku na sani, kai ne dai nake tunanin baka waye ni ba, sai gashi jiya kai fakare kanata shirgawa kawayena karya”
,
Na saki baki galala ina kallonta da mamaki
Nace “yo amma mei yasa tun jiyan baki tonan asiri ba”
Tai murmushi kafin tace
“SO, “
Na jaddada kalman a zuciyata SO kuma
Tamkar taji abun dana fada a zuciyata
“Eh shuraih , tun ba yau ba ziciyata ta kamu da tsananin sonka, hakan yasa na dunga bibiyan al’amarinka,a kowacce rana sai na tafi wajen aikinku domin kawai naga fuskarka, da sonka nake kwana da shi nake tashi, saide na rasa ta yadda zan sanar maka,
Cikin sa’a sai gashi jiya Allah ya wullo ka gareni, naji dadi sosai daka yaba ni, duk da cewa a jiyan tafarkin daka kama na karyace, sam ban ga laifinka ba, domin da bakai hakaba toh kawayena ma ba za su tsaya ba bare har takaisu ga sauraranka, ina Sonka Shuraih, ina sonka”
,
Sam ban gaskata abun da kunne na suka jiyemun ba don na fi daukan hakan ga rudana da kunne na suke mani
Wai tayama za’ace ni da nake m…….
“Ina sauraronka shuraih, shin kana sona kuwa”
Sadiya ta katse mani zancen zucina da fadin haka
,
********************
Ta fiya nake kaina a kasa ina tunanin abubuwan da suka faru dani cikin dan kankanin lokaci haka
,
Shakka babu wannan rana ta zo mani da sa’a
Duba da yadda lokuta kankani da suka wuce
Kyakkyawa kuma dirarriyar budurwa ta furta cewa ni take so,
,
Yanzu kam ko tunanin safiyya bana yi
Har ga Allah naji darsuwan Son sadiya a zuciyata
Duk da cewa bata kai safiyya komai ba, amma itama Allah ya azurtata da kyakkyawan sura dadai gwargado
,
“99%! 99% !! 99!!!”
Tamkar daga sama naji ana kwala min kira
Na gane muryan mai kiran
Ya karaso ya bani hannu muka tafa
Mujahid ne yana sanye cikin farar riga mara hannu, a gabanta an rubuta FILA da manyan baki, sai bakar jeans mai aljuhu biyu a kaurinta (two pocket)
Yaci zanzaro sai kace wani tsohon hedimaster,
” mj ya akai ne”
“Dai dai wallhi kasan meye?”
Ya tambayeni
“A’a”
“To Dangado fa yana ta nemanka don yanzu na hadu da shi, malam ranshi ya baci,ya tambayeni kai nace mai ban ganka ba,”
Nayi murmushi kafin nace
“Dan Allah kyaleshi”
“Wai me ya hadaku da shine” mujahid ya tambayeni
Ban boyemai komai ba na fede mai biri har wutsiya dan gane da abun daya faru da wayan dangado,
Mujahid ya fashe da dariya bayan daya gama sauraran labarin,
,
Dariyarsa bata bani haushi ba don mun ruga da mun saba haka da shi
“Kai amma 99% yarinyar nan ta raina maka hankali wallahi”
Na dubeshi cikin rashin fahimtar yanda zancen nashi ya nufa
“To wani rainin hankali ne taimun “
Na tambayeshi
“Ta boye waya tace maka an sata kai kuma ka yarda, wallahi ni banga ranan da zaka wayeba 99%, ga ka dai kaman wayayye”
Kirjina yaba dumm sakamakon jin abunda mujahid ya fada
Na dubeshi nace “to kai ya akai kasan cewa ta boyene”
Ya sake fashewa da dariya akaro na biyu
Wannan karon kam ya bani haushi, naja tsaki nace “kaga malam tambayrka nake fa “
“Yo kai 99% sai kace kwakwalwanka bayaja, haba, tayaya za’a ce barayi sun shiga gidan Alhaji Kawu sunyi sata anma mutanen angwa basu ji labari ba har yanzu, ai kaima kasan inda da gaskene har Gidan rediyon N B S sai sun san da labarinnan “
Na jinjina maganarsa kafin nace “tabbas maganarka abar dubawa ce, amma yanzu yaya zamuyi mu amshe wayar din a wajenta”
Yayi murmushi yace
“Ai maganin biri karen maguzawa,allah na tuba mu yanzu har wata tayi mana wasa da hankali, ka ganni nan Na mijine ni, nasan mata sosai duk wani takunsu a kaina yake, dun haka zo kaji”
Na matso kusa da shi ya kitsamin
********************
Kofan tangamemen gidan ne ya bude
A yayinda kyakkyawar budurwan ta fito daga ciki ba wata bace face safiyya tana sanye da rigan kanti da wando ta yafa wani dan bingilallen gale iya kirjinta,
Turus tayi tana kallonmu cikin razana
Yayinda bakinta yafara rawa “shuri-shur-shuraihu me a faru”
Nai murmushin mugunta kafin nace
Bakinki ne safiyya
.
Mu hadu a part na gaba
,
Toh wasu baki kenan

Subscribe to our newsletter

Leave A Reply

Your email address will not be published.