MAZAN KO MATAN part 3

 MAZAN KO MATAN part 3
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 12 Sep, 2018
Upload Time 10:19 am
Hits 331 Hits
Comment No Comments

Description

Duk da na dan razana sosai da jin muryansa amma hakan baisa na mike naje na bude kofan ba
Illa ma kasake danayi ina kallon kofan
,
Shakka babu nasan muddin na bude kofan toh fa sai dangado ya tayar mani da hankali,
Don in ta kai ta kawo ma cewa zaiyi mu tafi gidan su safiyya,
,
Kofan dakin ne ya cigaba da kara yayin da dangado yake dukansa iya karfinsa,
,
Nai ja tsaki sannan na rarumo bargona wanda a nai filo da ita na lulluba a jikina, nai kwanciyata
**********
,
Sauri nake ta zabgawa , burina shine na isa gidan su safiyya duk da nasan cewa zan fuskanci matsala a wajenta wajen karban wayan amma na ruga dana hattama irin karyan da zan lauya mata ,
,
Yo dama gani da dogon kafa uwa wani rakumi,
Cikin kankanin lokaci na isa kofan
Cikin sa’a na hango yaron dana aika jiya yana wasa a gefen gidan, na yafuto shi da hannu,
Da gudunsa ya iso gabana
.
Na jingina da bangon gidan bayan na aika yaron ya kirawo min safiyya na duba agogon hannuna
Karfe bakwai da minti goma sha uku na safiya
Nai mamaki ainun, da yadda lokaci baya ja da gudu
.
Yaron dana aika ya futo yace dani “wai tana zuwa”
Hankalinsa gaba daya yana wajen wasan daya ke yi,
Na sallameshi da cewa “toh”
,
Ban wani dade ba safiyya ta bude kofa ta fito
Kayan da suke jikinta jiya sune haryanzu amma a wannan lokacin hulan sanyine akanta sabanin Fatala(kallabi)
,
Tayi zunzurutun kyawu amma ni bata kyawun nake ba yanzu duk matsala ta ta bani wayan dangado ne,
Bayan mun gaisa nace da ita
“Safiyya dan bani wayannan danA baki jiya da dare”
YaDda nayi maganar ma kadai zai tabbatarmata da cewa cikin Ujila nake
,
Tai kasake tana kallona kafin daga bisani tai murmushi, don ta jawo hankalina gareta, a zuciyata nace aikin banza, ayanzu kam murmushin kinnan bazai tasiri ba”
Afili kuwa cewa nai “yi sauri dun Allah wallahi sauri nake ,”
.
Sai waige waige take tako ina a haraban angwan
Nasan ba komai take nema ba Illa mota, a zuciyata nace KARSHEN MAKARYACI tazo,
,
“Yo amma ina motarka”
Safiyya ta tambayeni tana kara kallon wajejen
Nai murmushi “tana gida, me yafaru”
“Babu komai kawai de ina tambaya ne,”
Tai shiru bata sake cewa kala ba
“Akwai wasu muhimman documents a cikin wayannan kuma yanzu nake so nai amfani da su, dan Allah yi sauri ki dauko mani,”
,
Na lura da yadda yanayinta ya canza ya koma salon tausayi, ta kankantar da murya can kasa tace “dama jiranka nake kazo na sanar da kai abun daya faru”
,
“Me yafaru ” na fada cikin zazzaro idanuwa don na dauka screen din wayar ta fashe ne
“Wallahi jiya da daddare barayi suka shigo gidanmu, sun yi mana sata mai yawa kuma sun amshe wayarka”
**************
Wasu taurari idanuwana suke hango mani, taurarin sun kasu kashi biyu kashi na farko jajayene kashi na biyu kuwa bakakene
Jajayen taurarin nan suka hadu da babaken to amma maimakon su bada haske kala daya, sai suka bada wani bakin haske mai dauke da dugo dugon jajaja,
,
“Shuraih ga kokonka, kosen yana cikin dakinka”
Na mike tsaye ina kallon mai maganar kanwata ce, banyi kasa a guiwa ba na dau kokon na nufi cikin dakina,
Abun dana fara cin karo da shi shine kosen da aka ajjiye mani,
Na zauna na dau kosen na cilla cikin bakina, maimakon naji dandano mai dadi, sai naji akasin haka, wannan yasa na mike tsaye na fito bakin kofan dakina na tofar da ragowan kosen dake bakina
,
Tun da safiyya ta fada mani wai wayan an sace naji gabadayan lakan jikina ya mutu, babu yadda na iya haka na barta tai shigewarta gida
,
Da kyar na dawo gida don kuwa juwa ke dibata a hanya sai tangadi nake tamkar dan giya sabon shiga,
*
Na dau kosen da kokon na fice daga dakin ba inda na nufa sai wajen ummata don kuwa ita ke toya kosen , tun daga nesaa na runga jiyo hayaniyar mutane sama sama ,
“Baba sai nine”
“Na riga shi zuwa”
“Na naira hamsin zaki samun baba”
,
Irin wayannan hayaniya suke tashi a rumfan umma mai kose sunan da jama’a ke kiranta da shi kenan sabanin ni da Umma kawai nake kiranta
,
Dukda tarin mutanen dana tarar a wajen tuyan kosen sun zagayeta hakan bai hanani cusa kai ba na rrunga tutture su dolensu suka bani hanya na iso gindin wutan na durkusa nace
“Umma bazan iya cin wannan kosen ba , wallahi daci yake min”
“Toh yau kuma salon iskancin da ka fito da shi kenan ko kaka?” ta bani amsa lokacin datake kokarin saka dusan kosen cikin mangyada
Nai shiru kafin daga bisani nace
“Allah kuwa umma daci yake”
“Toh me kake son nai maka”
“Naira hamsin zaki bani naje nasha farin shayi”
“Toh amshi” ta mikomin hamsin din
Na amsa ina mai cewa “na gode umma”
Na mike tsaye da nufin na fuce daga rumfan
Idanuwana ne sukai arba da ita, nan take kirjina ya buga da karfi, nai tunanin ko idanuwana ne keyimin gizo hakan yasa na mummutsikesu da hannayena, amma har yanzu ita nake gani a tasaye a gabana hannunta rike da gudan naira dari , ranta a bace,
Ba kowa bace illa Sadiya budurwan dana runga shirgawa karya jiya ahanyata na dawowa Gida
.
Toh ya zata kaya
Ku biyo alkalamin Shuraih 99%

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: