TARAR ARADU littafina daya 1 page 9

 TARAR ARADU littafina daya 1 page 9
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 17 Aug, 2018
Upload Time 5:44 pm
Hits 296 Hits
Comment No Comments

Description

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 9
Saida nashafe wata guda cur harda kwana shida amma
kullum naje sai yace ba’azo an tayaba dana lura sai naga
nima in naje har nadawo ko kuda ban taba gani ya sauka
akai ba .
Wannan ya sanyani yake shawarar na bari sai sati-sati
narika zuwa.
Ina nan ahaka atsakiyar sati nabiyu wanda har nafara cin
bashi saiga wani yaro har gida
“Wai kazo anzo sayen baburrinka”
Nan danan na zari takalma .
Don tsabar sauri kamar na tsahi sama.
Duk da cewa yaron da gudu ya koma amma duk kusan
tare muka isa.
Wani dattijone rigarsa duk dauda yayi furtutu dashi.
Da gani sana’arsa bazata wuce saida harawar dabbobi ba
na sunkuya na gaidashi
“Kaine me wannan babur din”
” Nine baba “
Na amsa masa
“To nasaya naira dubu uku”
Kaina yasara jin kudin tamakar za’asiyi mataccen keke
“Haba baba kadai fadi gaskiyar abinda kasaya”
Ya kalleni
“Kai yaro dattijo kamata baya ciniki da tayi inka sayar to
inbaka sayar ba nakara gaba”
“Kadai kara baba”
Nasake cewa dashi, sai kawai yakada kai yatafi hakika ba
zai kara ba.
Na tuna da dadewar baburdin awajen kotayawa ba’ayi
ba.
Kuma lallai innabari dattijonnan yatafi balallaine asiyaba,
sai kawai nabishi dagudu ina cewa
“Dakata baba”
Baiko saurareni ba ganinhaka yasanyani shan gabansa
“Ansiyar maka baba”
Ya kalleni fuska a turbune yacoi gaba da tafiyarsa,
Nan nashiga hadashi Allah da annabi da kyar na samu
yadawo yabiya .
Na baiwa mai gyaran dari uku yaron daya kirani kuwa
naira hamsin.
Sauran kudin nayi aniyar in na biya bashi sai in ajiye in
rika gutsura ahankali.
***** ************ ********
Nayi tagumi sakamakon wannan tsaka mai wuya dana
shiga al’amarine da banga alamun karewarsaba
“Salamu alaikum”
Akafada daga kofar shagon muryar yaya nane.
Na amsa gami da kokarin mikewa ,sai gashi yashigo.
Nayi masa sannu dazuwa da kuma barka da yamma .
Yasami kujera yazauna
“Umar nasamo maka aiki awajen wani mutum
akasuwarmu”
Sai naji tamkar natsahi narungumeshi tsabar farin ciki,
nafara jero godiya kala da bam da bam
“Ya’isa ya’isa”
Yace dani sa’arda yake dagamin hannu
“Tsaya kaji yadda al’amarin yake”
“To yaya”
Nafada sa’arda na kara matsowa .
“Kasaida hankalinka sosai ayaransa na yanzu babu wani
cikakken mai ilmi.
Shi kuma burinsa akullum yasamu wanda zai
taimakamasa wajen harkar oda.
To ammam shiru kakeji, duk wanda yasamo daya fara sai
cin amana ya biyo baya.
Saboda haka inhar kai gaskiya ka gama warkewa”
Bakina har kunne saboda tsabar farin ciki
Na cigaba da godiya shi kuma yatashi yafita.
Na daka wani tsalle nafada kan katifa.
Waini umar nine zan zama dan kasuwar kwari.
Dama gani dason birni.
Kawai sai nafara mafarkin zaune
Wai ganinan nasha boyel zan hau mota kawai sai sailulata
tayi kara.
$dana fiddo sai naji ashe farida ce kecewa
“Mai gida kayo sauri kazo muatafi yawon shakatawar”
Sai nace
“To ganinan zuwa “
Kawai sai nabude motata na shiga kai naitayin shirme
kala kala tun kafinma naje naga kasuwar.
Da dare banyi wani barcin kirki ba saboda tsabar doki.
Sau uku ina murda hannun agogona ina kara awa guda
guda wai don saboda gari yayi maza ya waye.
Sai na tuna ashe saurin ba’a agogo bane.
Ahaka na hakura saidai naita duba loakci.
Akalla dai naduba sau saba’in ahaka akayi assalatu da
mukaje masallaci muka dawo sai kawai nashiga wanka .
Alhali yayan nawa sai karfe goma yake fita
Akalla dai jiran awa hudu nayi
Da lokaci yayai muka fita .
Rumfar da mukaje katotuwace dabana zaton tana dana
biyu.
Rumfar kawai dazata fita sai dai na Alhaji saminu da
umar lawan yabada labarinta acikin littafinsa “SAURA
KIRIS”
Mutum biyune aciki kuma duk matasa ne kamarni
yayana ya tambayesu Alhaji sukace karfe uku yake fitowa
Wannan yasanya ni faduwar gaba
“Ai munyi dashi nazo dashi da safe”
Yayana yace daso
“Ok kudanyi jiransa”
Wani acikin yaran yafada
Anan muka samu benci muka zauna
Nayi taraba idanu ina kallon masu wucewa.
Aciki na hango wani mutum yana tafe ana faduwa ana
gaisheshi.
Farine dogo mai dan kauri.
Badomin nasan mai martaba sarkin kano ba to da sai
nace shine wannan .
To ammma ko babu komai wannan bai kai mai martaba
sarkin kano farin jini ba.
Amma shima yana dade daidai nasa.
Sai naga yana matsowa garemu
“Ga shinan”
Yayana yafada sai muka mike tsaye domin karramashi.
Daya iso sai nayi kamar yadda naga yayana yayi wato
muka durkusa har kasa muka gaidashi,
“Yaya sunanka dana”
Alhaji ya tambaya , na sunkuyar dakaina yayin danake
cewa
“sunana umar”
“Allah sarki”
Yace dani
“Sunan naka da dadi”
Ya hadani dana cikin kantinan yace sununamin abinda
zanyi.
Aranar wuni nayi ina mimmiko kayayyaki.
Da akatashi aka bani dari biyu na hau mota sallama kuma
akace sai sati sati.
********** ********** ********
Ahankali kwanaki suka cigaba da zukewa irin zukar da
takarda ke yiwa ruwan biro.
TO FA ABI YAFARA KYAU GA UMAR
KUTAYASHI MURNA SAIDAI BANSAN
KO NAN GABA BA
@mr shuraih 99%
.zan ci gaba

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: