TARAR ARADU littafina daya 1 page 8

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 8
Fuskata cike da alamun karaya
“Don Allah yallabai ka taimakeni”
“To wane tai mako kuma zanyi ma?
Kai dana fadamak maganar har taje ma’aikatar ilmi.
Katashi kawai kabani waje kaine kajawo wakanka”
Nayi tsawon minti biyu awajen banko motsa ba.
Daga bisani sai na tattara takarduna na dube shi
“To shikenan yallabai Allah ya taimaka”
Bai amasa maganar tawaba na fito daga ofis din cike da
mamakin wannan lamari.
$hakika zancene mara tushe ballantana makama.
Kuma lallai anzalunceni ayanda aiki yake wuya.
Ballantana kuma a wannan lokaci danake kokarin
mallakar masoyiyata farida.
Hawaye yazubo min daga idona lokacin danake kokarin
barin ginin ofis din.
Ahaka nanufi wajen babur dina saidai na yanke shawarar
na tura shi waje tukuna.
Domin tashinsa anan ciki zai iya juyo da hankalin kowa
nikuma banaso aga tafiyata.
Nafara turawa ahankali
“Mallam umar ina zuwa hakane”
Tambayar mai gadi lokacin danake kokarin fita”
” zanje nagabatar dawani uzurine”
“To adawo lafiya”
Ya maido amsa naci gaba da turawa , saida nayi nisa da
ginin makarantar sannan na tasheshi.
Nahau zuciyata na mai matukar tafarfasa saboda wannan
al’amari ahaka na karasa gida cikin rashin kuzari.
********* ********** **********
Nan fa aiyuka suka yimin yawa kullum inafama da
matsaloli guda biyu
Neman aiki da kuma zaman banza.
Aduk sanda nake zaune nakan debe kewa da littatafan
hausa na(umar lawan)
Kamar su LINZAMiN DAN ADAM’
BABBAR MADAFA
SaURA KiRIS
Kai dama wasu masu dama.
Kwanaki suka cigaba da karfa karfa.
Akalla ko wacce ta maimaita sau takwas.
Wato wata biyu kenan.
Amma har yanzu banga wata alama dazata bani karfin
guiwa akan samun aiki ba.
Na ziyarci kanfaninuwa da ma’aikatu amma shiru kake ji
Kai kace wani arnen dajine yaje neman aiki da takaradan
tsire .
Tuni yan kudaden dake hannuna sun tafi karaye.
Wannan ya tilasta min canja salo.
Idan wajen dazanje ba mummuman nisane dashi ba
nakan daba sayyada.
Badon kamai ba sai don tsadar man fetur .
Wanda kudin rabin galan sun isheni sati uku ina gwaguya.
Da lamari yakai yakawo sai nadaina zuwa ko’ina,
Daga gida sai gidansu farida.
Ahalin yanzu ina gindin babur dina ba ko’ina zani ba sai
gidansu farida.
Na tashi babur din bayan dana sha fama.
Nahau na nufi goron dutse.
Bada jimawaba na’isa gidan
Tun kafin na sauka farida tafito domin tarata.
Muka rankaya cikin gida .
Muka gaisa da babarmu wadda ayanzu sai ka rantse ni ta
haifa ba farida ba.
Muka zarce falon shakatawa na zabi kujera daya na
zauna.
Farida ta zauna akan hannun kujerar idanuwanta kyar
akaina .
Kullum nazo haka take taraiyarayata takasa tsaye takasa
zaune.
Itace ta zauna ahaguna,
Ta dawo dama ta tsaya akaina , ta zauna agabana kaidai
abubuwa da bam- da bam nikaina nasan farida tana
kaunata irin kaunar da bantaba zaton zata yiminba ta
dubeni bayan data ajiye min tataccen lemo
“Umar dan Allah ina roko agareka”
Na kalleta bayan dana zuki ruwan lemon
“Inajinki”
Taci gaba
“Kaje ka kawo sadaki sai adaura mana aure izan ma baka
da kudi bari na baka”
Na kalleta a firgice
“Farida bari ma wannan zance ni da yanzu bana aiki yaya
za’ai nayi maganar aure? Dame zan rikeki farida”
Tayi dariya
“Kaji ka da wani zance to menene amfanin albashina?
Albashina ya ishemu
Wajan zama kuwa dama basai nafada ba, mummy ta
koma sama sai ta barmana nan kasa idan kuma bakason
zama da’ita sai nakama mana haya.$
To me kuma yarage? Ballantana kasan mummy ba’irin
sauran mata bane.
Kaima kagani dakanka “
Nagirgiza kai
“Duk naji jawabinki amma ban karbi rokonkiba.
Ki kuma tuna nayi miki alkawarin akwati biyar kuma
bazan saba ba “
Ta dakatar dani
“Bari wannan zancen umar aicewa kayi idan kana da hali.
Kuma baka dashi yanzu kaga ba saba alkawri kayiba”
Nayi dariya
“Ai halin danake nufi farida shine rai da lafiya , ahalin
yanzu ban rasa ko dayaba”
Ta daure fuska
” Nidai inhar nizakayiwa to banaso, mummy ma kuma
bazata karbaba “
Nayi dariya
“To mummy din taki ce ke kadai”
Ta kalleni
“Naji batawabace nikadai ba kuma bari ganin kafini gata
agunta dakayi magana sai tace haka za’ayi bama ta
sauraron zancena, to wallahi akan wannan bazata
goyama bayaba.
Kawai saita goyi bayanka akan abin dzaka takura? To akan
wannan kam gakucan da mummy arana”
Na mike tsaye
“To zaki gani nasan yadda zanyi na shawo kanta”
Itama ta tashi
“Barima zato bazata taba yarda ba”
****** ************ *******
Zama yayi zama tuni kudaden hannuna sun gama karewa
.
Wannan ya tilastamin saida akwalar baburdina.
Na turashi inda akeyimin gyara nace asanyamasa ganye.
Haka kuwa akayi.
To ashe aiki aka samamin bansani ba
Saida nashafe wata guda cur harda kwana shida amma
kullum naje sai yace ba’azo an tayaba dana lura sai naga
nima in naje har nadawo ko kuda ban taba gani ya sauka
akai ba .
TOFA GA BABUR INA MAI SAYA
SAIYA TUNTUBENI
@mr:- shuraih 99%

Subscribe to our newsletter

Leave A Reply

Your email address will not be published.