TARAR ARADU littafina daya 1 page 7

 TARAR ARADU littafina daya 1 page 7
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 17 Aug, 2018
Upload Time 5:42 pm
Hits 232 Hits
Comment No Comments

Description

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 7
Domin ahalin yanzu inna rasata ma zuciyata na iya
bugawa to kaga da wuya ya kasheka gara dadi ya kasheka
to waima da yake cewa zai yi wasa dani kamar dani biri
yana gani mutane zasu bari a dauramin igiyya a kuguna
arinka ja a kasuwa ne?
Ashe makenan dubunsa ta cika .
$sai najini ina mai murna da wannan matakin dayace zai
dauka ,
To amma karramani dayace zai yifa yadda ake karrama
kudi.
Nadade ina tunani daga bisani nagane babu wani karamci
da kudi suke samu fiye da kashe su,
To kasheni za’ayi kenan kwarai kuwa babu tantama
kasheni zaiyi kamar yadda ya kashe uku abaya,
To amma wannan bai dameni ba dukwanda ya mutu
kwanansa ne ya kare.
********* ********** ********
Na dubi farida bayan dana lume acikin kujera
“Allah yakaimu ranara daza mukasance kamar haka
acikin daki daya a matsayin miji da mata”
Tayi murmushi
” Amin umar Allah yakarbi addu’arka har yanzu banji
kana maganar daurin aureba”
Nakai idona gareta
“Akwai dalili farida shiyasa kikaga banyi magana ba”
Ta maido hankalinta gareni
“Wane dalili”
“So nake nagama hada lefe”
Tarike baki
“Wani irin lefe kuma umar”
Nakalleta lefe kala nawa kika sani?
Aiduk inda kikaji ance lefe akasar hausa ana nufin kayan
da mai nemar aure zai kaiwa wadda yake nema”
Ta karkada yatsa
” Sam karma ka soma don kokayima bana so mummy
ma bazata karbaba.
Sadaki kawai zaka kawao shima bamai yawa ba”
Nayi dariya
“Farida arayuwar da akeyi irin na yau duk masoyi yakan
nuna kaunar dayake yine ta hanyoyi irinsu lefe.
Bawai ina nufin wajibi bane kokuma abin dayake makale
da shari’a
A’a saidai inda hali akwai bukatar kayi lefe mai yawa
domin toshe bakin masu kushewa. Saboda an riga anbata
lamarin aure
” Tayi tsaki
“To kai ina ruwanka da masu kushe kabi hadisi mana
daya kecewa mafi albarkacin mace mafi karancin
sadakinta”
Najin jina kai
“Babu shakka farida hakane ni kaina na kanki abubuwa
na bidi’a
To amma tunda wannan baisabawa shari’a ba nayi aniyar
yi miki lefe na ban mamaki.
Domin kaucewa wasu kananun maganganu, kisani yanzu
duniya ta zuba ido akanki , idan muka yi aure babu lefe ,
maganar daza ta yi ta yawo shine neman kai ake daka
shiyasa ko lefe ban yimiki ba.
Ni kuma inaso innuna ma duniya cewa kaunar ki nake
jini da tsoka don babbar abinda natsana bai wuci ace ba
auren soyayya mukayi ba”
Ta bata rai
“Tokai ina ruwanka afadi duka abinda za’afadi magana
zata warwaremana aurene”
“Jini farida na rantse da Allah indai ina da iko sai nayi miki
akwati biyar”
Ta mike tsaye
“Kasan kuwa abin da kake fada? Ni yar gidan wata
shugaban kasace daza’a yimin akwati biyar”
Nayi murmushi
“Kinfi yargidan ko wane shugaban kasa a wurina babu
kamar ki aduniya.
Farida ki shaida ina yimiki kaunar dazan iya bada sadaki
da raina”
Ta girgiza kai
“Gaskiya umar banyadda kayimin akwati biyar ba”
Na mike tsaye
“Bakin Alkalami yabushe farida “
******* ********* *********
Na zage rubutu da cak , yaran anaji shida sun nutsu,
Inajin dadin yadda yara ke bani hankalinsu izan ina bada
assignment.
Najuyo na dubesu adaidai lokacin dana kare rubutu.
Ian shirin fara bayaninewani yaro ya durkusa agabana.
“Sir principle yana magana”
Nayio mamakoin abinda zai sa principle kirana awannan
lokaci.
Hakika yakan kiarani fiye da kowani malami wani loakcin
kira mai ma’ana wani lokacin kuma hayaniya kawai.
Na ratsa yara kai tsaye kuma na nufi kofa .
“Gani yallabai”
Nafada aloakcin danake kokarrinn zama akan kujera
hannuna furtutu da garin cak.
Yadago daga barin rubutun dayake ,ina iya hango
idanunsa kadan kadan ta cikin bakin gilashin daya
makala.
Fuskarsa kuma ta nunamincewa yana so ya gabatar da
wani bayani dayake dauke dashi muhimmi
” Wato umar nakirakane saboda wata matsala data dade
tana faruwa nasha ji da kunnena kuma andade ana kawo
min kara, wani irin turancine kake koyar dayara abin ko
ka’ida babu?
Ya zakarinka koyar dayara turanci broka , ko anfada
maka nan kasuwar sabon garice?
Gaskiya bazai yiwu mu tafi dakaiba mai cigaba muke
nema bawai mai kawo ci baya ba.
Saboda haka daga yanzu……….”
Yayi shiru baiyi magana ba na cika da mamaki wainine
nake koyarda turanci broka .
Wannan zacene mara tushe shi kansa pricinple din
baikaini iya yturanci ba.
Nakan fitar da kalma bayan kalma yadda kasan baturen
gaske
Wanda hakan yasa ake min lakabi da toni blayer.
Amma duk gashi ana kokarin kiransa a matsayin broka.
Na dubi principle
“Yallabai wayanda suka kawo maka koken sun gabatar
maka da shidace”
Yadaka min tsawa
” Wata shaida tunda nima naji da kunnena”
Ya watsomin takardu
“Tuni mun rika mun mika matalarka a ma’aikatan ilimi
kuma sun bamu madadinka, kana iya hangowa ta
window gashi can atsaye”
Nawai waya domin ganin wanda ake kira madadina wani
mutum ne mai yawan suma da gashin baki.
Najuwo ga principle fuskata cike da alamun karaya………

TOFA UMAR YaFARA SHIGA
@mr:- Shuraih 99%
To be con………
Keep followin…..

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: