TARAR ARADU littafina daya 1 page 14

 TARAR ARADU littafina daya 1 page 14
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 17 Aug, 2018
Upload Time 5:51 pm
Hits 194 Hits
Comment No Comments

Description

Tarar Aradu
Littafi na daya 1
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 14
.
.
Toh jama’a sakamakon rashin sauran fallayen littafin
hakan yasa, dole da kaina zan karasa maku wannan labari
sai ayi hakuri da kura kuran da za’ai arangama da su
.
Ahalin yanzu nida tsuntsun da’ake kiwonsa akeji duk
daya
muke ,
Domin kuwa bana fita ko’ina daga shago sai shago,
Sai idan angama abinci a miko min ta kofa mai shiga
cikin
gida ,izan kaga na fita to da daddarene ko da asubah
idan
zamuje sallah nida yayana
.
Wata rana da asubah na fita sallar asubah nida yayana
toh dama ni idan na fita salla nida yayana bama dawowa
gida sai safiya domin kuwa tsayawa muke a masallacin
muita karatu har sai gari ya waye, kaman kullum yau
hakan ta faru,
Mun fito muka nufi gida ina zuwa kofan gidan gabana ya
buga sakamakon ganin kfan dakina danayi a bude,alhalin
kafin na tafi masallaci sai dana sanya dan makulli na kulle
dakin gaba daya
.
Na dai daure na doshi dakin ina bude dakin na saki wani
salati sakamakon abunda nagani acikin dakin,
Wata mata daga ita sai shimi iya cibiya da wani dingilallen
wando iya cinya tana kwance kan katifar barcina,
Ina bude dakin matar ta tashi tayi mika, sannan tadan
mummustsuka idanuwanta ta dubeni tace yauwa malam
kai nake jira dama tun dazu nake son na tafi,
.
Na dubeta baki bude cikin mamaki nace mata wacece ke
sannan meya kawoki cikin dakina,
Tayi tsaki tace kaji rainin hankali kadauko ni kuma kana
tambayata ko waye ni lallaima, malam ka bani kudina
yanzu ina son zan tafi
.
Ke dan ubanki wani kudin zan baki, yi maza ki fice daga
cikin daki yar iskan karya, na fada cikin fusata,
Ai nan matannan tai tsalle ta cakumemin gaban riga
muka fito daga waje tana cewa wallahi sai ka biyani kudin
kwana na, tayaya za’a yi ka dauko ni ka kwana dani
sannan kace baza kaa biya ba ai wallahi sai ka biya,
.
Ba’a bata wani lokaci ba har matannan ta tara min jama’a
nan raina ya baci na tsinka mata mari ai ba shiri ta sakeni,
na cigaba da jibgarta da kyar mutanen angwa suka
kwaceta a hannuna amma duk da haka matannan sai ihu
take ita sai na biyata kudinta, a haka yayana yazo ya
samemu
.
Yayi bakinciki sosai kuka ne kawai baiyi ba ya tambayeta
nawane kudin bakunya bare tsoron Allah matannan tace
dari uku ne, cikin kunan rai yayana ya ciro kudin ya bata,
matar ta wuce dakina ta kwashe kayanta tazo wucewa ta
dubeni tace Assha, ai wallahi daga yau baka dauko ni
dakinka, sai de mu ringayi acan yadda muka saba,tunda
kai kace tsiyane aranka,, ko kallonta banyiba donni abun
har mamamki nake ni daban taba ganinta ba,
.
Na dafa yayana nace wallahi yaya….ya katseni ta hanyar
daga mani hannu yace umar da na zata abun naka zai
tsaya kan sace sace ne toh tunda takai ga sai ka bata bin
suna ka kawo karuwa cikin gidana toh ka kwashe naka ya
naka ka kara gaba kasan inda dare ya maka daga yau
kabar gidannan kenan
.
Iya tashin hankali yau na gani, kuka ne kawai banyi ba,
Cikin kankanin lokaci na shiga shagona na dauki wata
tsohuwar jakar kayana, na dauki hanya wacce bansan ina
na nufa ba
Tafiya kawai nake zuciyata sai radadi take yimin A lokacin
da hotunan abubuwan da suka faru dani suke yawo a
kwalkwata tamkar a majigi,
Duk da ya kasance wunin ranan bansa ka komai a cikina
ba, amma hakan bai sa naji yunwa ba
Na isa wata angwa na samu gindin wani waje na zauna na
kifa kaina a cikin guiwowina, ayayin da tunani iri iri keta
zarya a kwakkwana, ji nake tamkar na kashe kaina na
huta
.
******
Na tashi na nufi wani masallaci domin yin sallar Isha’I
domin kuwa yanzu na tabbata mutane ko sun gani ba
zasu shaidani ba, bayan na gama sallar ne sai kwanta a
masallacin da nufin na kwana a masallacin in yaso gobe
da safe sai in wuce kauyenmu wajen iyayena,
Mutane daddaiku ne sukayi saura a cikin masallacin har
barci ya fara dibana sai naji ana tashi na na dago da kai
domin naga waye wannan
“Malam tashi koh zamu rufe masallacin ne “
Su biyune suna sanye da manyan kaya
Kallo daya nai masu na ayyana araina kodai limaman
masallacin ko kuma wasu malamai na daban
na tashi cikin rashin jindadi na fita daga masallacin na
samu wani dan kewaye a jikin masallacin na kwanta,
Bayan sun kulle masallacin ne zasu tafi sai naji dayan
yace “malam ladan kaga wannan yaro ya koma can ya
kwanta kuma, da alama matafiyine don ga shi dauke da
Jaka”
Wanda aka kira da ladan yace”malam liman kenan ai
wannan yaro daka ke gani kasurgumin barawo ne, sau
uku ana kamashi a kasuwar kwari, yanzuma daka ganshi
anan inaga koh ya lababo ne ya sace mana mita,ko kuma
mic”
Liman najin haka sai ya rike baki yace “assha “
Sai ya daga murya da alama wasu yakewa magana yace
“kai samari kuzo ku jibgi wannan mara kunyar barawon,
tun kafin ya kassaramu”
.
Ina jin haka ban san lokacin dana zabura a guje ba na
tsallake, dan karamin katangar daya katange gewayin
dana ke kwance na ranta ana kare, inajin ihu da
kururwan mutane suna cewa atare barawone atare haka
na ringa cin uban gudu har na fice daga angwar gaba
daya, ina shawarar na tsaya kenan sai naji wani Abu mai
nauyi ya bugi kaina daga nan kuma sai ji nayi na kife akan
wani ruwa ruwa mai wari, daga jin wannan wari na gane
warin giyane ko na aman giya,
Idanuna dishi dishi suke gani, wani katon mutum nagani
ya tsaya akaina yana rike da wata katako 2 by 2, mutumin
ya sunkuyo da kansa daidai kunne na yace
“Umar dan wasa daga yau wasanka ya kare , dun kuwa
yanzu zan aika ka kiyama, dama sakamakon irinku kenan
masu taurin kan tsiya”
Ya daga wannan katakon sama da nufin ya buga mini
aka………
.
Masu karatu anan muka kawo karshen littafin TARAR
ARADU na daya 1
Kaman yadda kamin mufara wannan littafi na fada maku
cewa 1 and 3 kadai nake da su bani da 2, dun haka gobe
zan fara post na TARAR ARADU littafi na uku 3 Allah ya
kaimu da rai da lafiya
$
TARAR ARADU
(m) Umar Lawan Abdul
Littafi na daya 1
Typing Shuraih Usman
.
.
Domin download na wannan littafi dama wasu sauran
littatafan sai ku shiga shafinmu anan kuyi like
Like:- www.facebook.com/hausaebooks

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: