TARAR ARADU littafina daya 1 page 13

 TARAR ARADU littafina daya 1 page 13
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 17 Aug, 2018
Upload Time 5:49 pm
Hits 238 Hits
Comment No Comments

Description

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 13
aranar unguwarmu sai da daddare nashiga……..
********* ************ ********
Ahalin yanzu nida tsuntsun da’ake kiwonsa akeji duk daya
muke ,
Domin kuwa bana fita ko’ina daga shago sai shago,
Sai idan angama abinci a miko min ta kofa mai shiga cikin
gida ,izan kaga na fita to da daddarene ko da asubah idan
zamuje sallah nida yayana.
Shi kansa rashin jituwa mai karfi ta shiga tsakaninmu.
Abisa abunda yakira cimasa mutunci.
Nayi masa rantsuwa da Allah akan duk abubuwanbani da
hannu aciki yaki yarda.
Sai yanzu na fuskanci ashe irin wasan da mutuminnan
yake nufi kenan.
Hakikanin gaskiya wasan nasa bantaba ganin wanda
yakaishi muni ba, sai dai duk wannan bana zaton zan bar
farida,domin kuwa kaunarta ta rigaya tabi jikina.
Yau iatace rana ta farko dana shirya zanje wajenta tun
bayan da’aka yimin sharri.
Bakomaine yasa na daga kafa illa tsabar bakin cikin dake
damuna.
Ahalin yanzu kuka awajena babu wuya domin kuwa da
zarar na tuna bana control na kaina abinci ma kadan
nake ci.
Na isa goron dutse da kimanin karfe tara na dare .
Badon komai ysa nayi dare hakaba sai don gudun kada
wani wanda yake kasuwar kwari yaganni ya tona min
asiri.
Tuni su farida rufe gida, nasani abune mai wuya ace wai
bacci take kasancewarta mai matukar kwazo, na
kwankwasa kofa.
Bada jimawaba naji takun kafa
“Waye”
Aka tambaya muryar farida ce
“Umar ne”
Na bada amsa tuni ta gama shaida muryata nan da nan ta
zare sakata takuma bude kofa kawai naga ta fashe da
kuka.
Nayi mamakin abinda yasa haka , kodai dun na dade
banzo bane?
Muka dunguma cikin gida kukantane yafoto da hajiya yau
maimakon gaisuwa kuramin ido kawai tayi,ta kuma rike
baki
“Ashe zaka sake dawowa gidanmu umar, na dauka bazaka
kara takowa ba”
“Me zai hanani zuwa mummy?”
Itama sai naga tafara kwalla
“Kai kuma umar hanyar da za’abi da kai kenen”
Sai nagane ashe labarin abin dayafaru tuni ya iso
garesu.banyi mamaki ba domin kuwa goron dutse
unguwace data kushi yan kwari da dama.
Nida farida muka zarce daki alokacin datake ta faman cin
kuka.
“Umar nafadamaka muddin kana tare dani bazaka sami
kwanciyar hankali ba amma ka ke keshe kasa kaki yarda
to yanzu daka gani da idonka ai ka hakura”
Tacigaba da kuka
“Dakata farida”
Nace da ita
“Shin wai kin daina kaunatane ko yaya”
Ta tsuguna agabana
“Umar bazan daina kaunar kaba har abada”
Nayi murmushi
“To indai hakane farida banga wani abin dazai sani in
janye ba,kisani na dora tubalin soyayyarmune akan gini
biyu,imma dai nasami cikar burina imma a kirgani a
mutum na hudu daya rasa ransa, kisani ahalin yanzu
cigaba da kaunarki ya fiyemin sauki,domin kuwa mutuwa
afagen dagar neman aurenki yafiyemin mutuwa
asakamakon hauhawar jini”
Na sunkuyo gareta
“Farida izan narasaki bazankai labaraiba”
Kuramin ido kawai tayi tana kallona , unkai tsawon minti
daya mun zurawa juna idanu, daga bisani fuskarta ta
yaye izuwa murmushi.
“Oh! Umar Allah yabar mu tare har abada”
Na mayar da murmushinta sa’arda bakina yake motsawa
a kokari na lalubo kalmar amin .
Tamike tsaye akuma loakci guda da tazauna akan hannun
kujerata ta dubeni fuska da fuska
“Da ka gujeni umar da mutuwa zanyi, bazan iya rayuwa
babu kai ba “
Na girgiza kai
“Bazan gujekiba farida har abada koda kuwa za’rika
yankan naman jikina
(Kaji soyayyar gaskiay kenan
Its shuraih 99%)
******* *********** ********

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: