TARAR ARADU littafina daya 1 page 12

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 12
Nayi mamakin irin wannan sammako da alhaji ya bugo a
yau mu dukkaninmu ya rigamu zuwa.
Hatta ibrahim wanda shi yake tafiya da makullai………
Naga saukar ibrahim daga mota kafin mu karaso to
menene ya fito dashi?
Kodai irin abinnane domin yakama mai kin fitowa da
wuri.
Na durkusa na gaidashi jamilu ne kawai bai iso ba.
Ba ‘afi minti biyar ba shima ya’iso akafara hada hada
“Kuzo inji alhaji”
Ibrahim yafada yana raba mana idanu
Muka nufi wajensa cikin rashin sanin abin da kiran ya
kunsa.
“Ku zauna “
Yace damu lokacin daya ke nuna mana benci.muka zauna
daura da juna
“Bawani abune yasa na kirakuba illa wani abu daya afku
wanda banji dadin saba.ya nunani nida jamilu jiya ku na
aika cikin motata , to amma dana isa gida sai natarar da
abin da baiyimin dadi ba, wanda banga amfanin abar min
kes ba alhali an dauke agogon.
Wand yin hakan babbar rainin hankaline da bazan juraba
.
Abin dana keso nasani shin jamilu kaine ka zare agogon
ka kai kedin kawai ko kuma umar kaine ka dauki agogon.
Kuna iya bani amsa anan izan bahaka ba kuwa kuna iya
shaida ma yansan da”
Uka kalli juna nida jamilu akuma lokaci guda muka fara
rantsuwa ,wallahi mu bamu dauka ba.
Alhaji yayi murmushi
“To shikenan kuzauna anan “
Yazare sailula bisa ga dukkan alamu yana ma yansanda
wayane. Bada jimawaba sai gasu sun iso su hudu
“Gasunan ku tafi dasu gida jensu ku bincikomin agogona

Aka tasamu agaba .
Nidai babban abin daya dameni aga nazo da yansanda
gida a matsayin ana zargina da sata.to amma badan
hakaba to da ina iyayin komai ma
Musamman tunda nasan bandauki agogoba.
“Ku hau nan”
Yansandan sukace damu lokacin da muka iso gindin
motarsu.
Bayan mun zauna kan bencinne aka fara tambayar inda
za’a nufa .
“Ana iya zuwa ko’ina ma “
Nabada amsa cikin halin yarda da kaina .
“Wanene umar”
Daya daga cikin yansandan ya tambaya.
Na dora yatsana a kirji lokacin da nake nuna kaina
“Gidan ku za’anufa”
Dansandan yacigaba da fada.
“Dama kana da kyasa kyasan sata harbiyu abaya”
Nazare idanu sakamakon jin kazafin da bazai yiwu na
musa shi ba.aka sanar da direban inda za shi.
Bai gushe yana tuki ba saida muka iso kofar gida.
Bakom al’amarin ya sanya tulin yara taruwa, cikin
kyarma nasa kuba na bude dakin , tare da yansanda
muka shiga.
Suka shiga laluben kowanne lyngu da kowanne kusurwa.
Badon bakin cikin daya ke cina ba da babu abinda zai
hanani dariya.
Sakamakon dagewar da yansandan sukayi neman agogo.
Wanda hakan tamkar leka tundin kulline domin gano
rakuminka daya bata.
Tuni sun gama birkita ko’ina amma haryanzu ba’a ga
agogo ba.
“Muje a duba cikin gida”
Daya daga yansandan yafada.
“Dakata tukunna”
Inji wani dayake kokarin daga katifata.kyalkyalin daya
bayyana a karkashin katifar shi yasanar dani akwai wata
ajiyar da bansan da’ita ba,
Ba komai bane illa kyakkyawan agogo yana walkiya,
daukewar numfashina yazo daidai da lokacin dawani
radadi ya ratsa kuncina.
Sakamakon wani bahagon mari da daya daga cikin
yansandan ya kwadamin.
“Kace bakai kasata ba”
Nan danan bakina yafara fadin abin dani kaina nasan
baza a yarda da shi ba.
“Wallahi yallabai sharri akayimin”
“Barawon banza barawon wofi dama tun sa’arda kazo
kake yimana sace sace kaboye kudin alhaji, kaci sailula ,
yau luma gashi ka saci agogo”
Jamilu kenan ya hauni da bambami sa’arda muka fito
waje!
“Barawo! Barawo!! Mai kasata? Agogo ya sunan ka? Umar”
Wata kwarya kwaryan waka kenan da yara suka kirkirota
bayan da’aka watsani mota akafara tafiya.
Aguje sukabi motan suna raira waka , basu rabu da muba
saida muka hau titi.
Nasha zagi kala kala da kuma mari dabam dabam kafin
mu karasa.
Ahaka muka iso har kasuwar kwari daya da ga yansandan
na cumuimiye da kuquna . Ya kwadamin mari sa’arda
yake kokarin dankwafar dani agaban alhaji
“Alhaji yaron tsinannen barawone daya kamata a
ladabtar dashi”
Yamika ma alhaji agogon kafin kace meye tuni mutani
sun cika wajen.
Kama daga kwastomomi zuwa masu kanti.
“Allah wadaranka”
“Allah tsinema”
“Allah watsa ka”
Sune mabambantan lafuzzan dake fita daga bakin
mutane.
Wadansu har basa samun daman ganina sabida
cunkosan mutane.
Zazzafan radadi yarinka bin jikina, ba radadine na zafin
duka ba ‘a’A radadine na mamakin sharrin da’aka yimin
da babu daman na musa shi, babban abinda yafi damuna
shine sunana daya riga yabaci akasuwa da
unguwarmu,toni yanzu da wacce fuskar zan ringa kallon
mutane.
“Wayyo Allah umar kacuceni kaci mutuncina”
Muryar yayanace lokacin daya iso yana kuka, ya nufo
kaina da gudu yansanda suka rirrikeshi.
“Ku kyaleni na kasheshi tunda bashi da sauran amfani”
Da kyar yansanda suka janyeshi baya
“To shikenan daga yau umar na sallameka kar ka kara
fitowa indai akwai mutumin da bama shiri dashi bai wuce
barawo ba”
Alhaji kenan loakci na farko dayayi magana tun bayan
isowar mu.
Ya sallami yansanda, da sunso abarsu su tafi dani alhaji
ya hana ‘aka barni anan .
Har saida jama’a suka watse sannan na. Tashi, aranar
unguwarmu sai da daddare nashiga……..
AYYA JIKI MAGAYI
DAMA DUK WANDA YACE ZAI TARI ARADU DAKA TO
LALLAI SHIMA YASAN SAKAMAKON
(Maudu’I)
Izan da kaine umar zaka cigaba da soyayya da farida ko
ko zakayi hankali
Waitin for sharhi
Zanci gaba
Its shuraih 99%

Subscribe to our newsletter
Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Leave A Reply

Your email address will not be published.