TARAR ARADU littafina daya 1 page 11

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 11
Bayan dana karya kumallo sai najawo wata bakar jaketna
na dora sakamakon sanyi da akatashi da shi.
Sai kawai na nufi kasuwa muka ci gaba da hulda kamar
yadda muka saba ……..
Da rana ta raba sai kuma zafi ya kori sanyi,
Wannan yasanya kowa cire rigar daya kara .
Muka rarrataye.
Da alamun yau alhaji agajiye yake ,domin kuwa tunda
yazo ya dare kujera yake ta gyangyadi abinsa.
Sailularsa kashe alarm din yayi domin kar adameshi.
Kawai ya dorata ahannun kujera .
Bai farkaba sai bayan la’asar shima sai da muka yo sallah
sannan na tasheshi
Yayi mika da hamma sannan yafara lalube-lalube ba
musan kome yake nema ba sai bayan daya rasa sannan
ya dubemu
“Wai ina sailulata take?”
“Ina kuka sanya min sailulata”
Duk muka yi shiru,kawai sai muka fara rantse-rantse
kowa yana fadin bai gantaba.alhaji yafara salati
“Da batan sailular nan gwara batan kudin da’aka
sayeta,manya manyan abokan mu’amalata ta taurai suna
tuntubatane ta wannan layin,akwai kuma nombobi da
dama wanda a sailular kawai na shigar dasu,ciki kuwa
harda wani mutumin danakeso na tuntuba in anjima don
Allah duk wanda yasan inda take yafada zan bashi dubu
hamsin”
Babu wanda yayi magana acikinmu.
Ahaka alahaji yafita akaba da cigiyar sailular duk
kasuwa.amma shiru kakeji.
Duk yanda akayi de wanine ya lababo ya saceta.
Bayan alhaji yadawo daga sallah sai ya zauna akan
kucjera.
Ko magana ma bayayi saboda tsabar takaici yananan
zaune har kusan sallar magriba.
Dif nepa suka dauke wuta ba’aganin komai agurin sai dai
in ka kura ido sosai zaka hango irin kwaronnan
“makyallu”
Koriyar wuta nata fita daga bindinsa
Yayi kememe abinsa ajikin bango.
Jamilu ya tabo ibrahim “dubi hikimar Allah”
Wai duk wannan haske daga bindin kwaro yake
Ya jinjina kai
“Kadan kenan daga hikimarsa”
Alhaji ma ya waiwaya wajen domin yagane ma idanunsa ,
Jamilu kuwa yace sai ya daukoshi.
Adai dai lokacin haske yagama kantin sakamakon
generator da’aka tayar,
To amma kwaron ya shige cikin kaya wutar kawai ake
gani.
Dana kura ido sanaga ashe ma rigata ya shiga.
Jamilu ya laluba ,sai naga ya hada. Gami da fadin “kai”
Ya kuma ja dabaya
“Menene?”
Ibrahim ya tambaya
“Ba kwaro bace ashe sailulace”
“Wace irin sailula”
kuma na tambaya fuska a yakune
“Sailula nawa kasani”
Jamil yafada loakcin dayake dauko rigar,
Akazo da ita gabanmu aka sanya hannu aikuwa sailular
alhajice, wai ashe kyallin danjar sabis muke hangowa
Alhaji yai gauron numafashi ya mika hannu ya karba ,
nikuwa alokacin nawa numfashi ya dauke (nima nawa ya
kusan daukewa da kyar na seta hanaklina ,lol Shuraih
99%)
Akwai kallon yaya haka ?
Da fuskokin mutanen ke dauke dashi bayan kallona na
tsayin lokaci da alahaji yayi sai kawai yakada kai ya fita .
******* ************** *********
Ahalin yanzu duk wani amincin dake tsakanina da jama’a
akasuwa yakau .
Hakan bakaramin kuntata min yakeba
Alhaji dai yadena aikena ko’ina izan kuwa nazauna kusa
da mutum ko carbi ya fitar sai ya mayar da abinsa aljihu.
Wai gudun kar na faki idonsa na dauke.
Duk inda na nufa kuwa kaga ana C.I.D na hatta da randa
izan zan sha ruwa sai atsareni da ido wai duk karna faki
ido na tura modar aljihu
(hahaha sai ni masoyi shuraih 99%)
Kai abubuwan takaici dabam-dabam
Ahaka na cigaba da zama cikin zullumi da bakin ciki .
Izan kaga na saki raina to tabbata muna tare da farida
don gudun karta gane halin dana keciki.
Inanan rakube a cikin kanti sai gwani alhaji ya shigo .
Da ganinsa kaga babban mutum akwai wani mutum biye
dashi alhaji ya mike tsaye suka gaisa
Sannan ya sami waje ya zauna
“Alahi agogonne na kawomaka”
Yafada lokacin dayake duban mai gidan mu
“Yauwa! Ansamo”
Alhajinmu ya tambaya
“Kwarai kuwa”
inji wacan mutumin
Lokacin dayake karbar wani dan akwati daga hannun
mutumin da suka zo tare,
Da bude akwatin sai ga wani walwali, agogone na danyen
gold mai matukar tsari ,
Alhaji ya jinjina kai
“To shikenan sai mun hadu”
Mutumin ya mike
“To sai na ganka”
Suka yi sallama yatafi alhaji yaba ma jamilu akwatin
“Ungo wannan kaimin motata, ka bude aljihy(glove
compartment) ka sanya min aciki”
Ya karba yatafi ba’a jima ba ya maido wa alhaji makullin
“Nakai”
Aka cigaba da harkoki anahaka har loakcin sallar la’asar
yayi , nida Alhaji muka fara tafiya masallaci da muka
dawo sai jamilu da ibrahim suka tafi,
Ana haka ne akayo wa alhaji waya ya dauka suka fara
tattaunawa,
Wani mutunne yakeso abashi cikakken addreshin wani
kamfani a ingila
Alhaji ya dubeni loakcin daya ke mikomin makulli
“Don Allah kaduba kan seat din baya akwai wani karamin
littafi kadauko minshi kayo sauri”
Na karba na tafi aguje ba’adadeba na dawo da littafin
.Alhaji yabashi adreshin sannan yabani na mayar ,
akacigaba da sabga .har lokacin tashi yayi akabani kudin
mota kamar yanda aka saba nakama hanyar gida.
********** ********** *********
Nayi mamakin irin wannan sammako da alhaji ya bugo a
yau mu dukkaninmu ya rigamu zuwa.
Hatta ibrahim wanda shi yake tafiya da makullai………
YAU KUMA WATA KALUBALECE
KE KALUBALAN TAN UMAR
Don’t trouble troubles
Till troubles trouble you
Shuraih 99%
Zan cigaba

Subscribe to our newsletter
Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Leave A Reply

Your email address will not be published.