TARAR ARADU littafina daya 1 page 10

 TARAR ARADU littafina daya 1 page 10
Posted by Mr Hausa Ebooks
Price GPL
Category Uncategorized
Uploaded On 17 Aug, 2018
Upload Time 5:46 pm
Hits 206 Hits
Comment No Comments

Description

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 10
********** ********** ********
Ahankali kwanaki suka cigaba da zukewa irin zukar da
takarda ke yiwa ruwan biro.
Ahaka nafara kirga makonni
Ko kusa bazaka hada samuna na kasuwa dana makaranta
ba.$
Bada dadewaba nafara haskaka kantin.
Sakamakon iya mu’amala da jama’a da kuma ilimina
hatta kantinan makota idan akayi bakon bature ni suke
zuwa su kira.
Wannan si yasa akafara yimin lakabi da bakin bature.
Na shiga ran alhaji matuka sai yafara aikena wurare
dabam dabam sai ya zamto kullum da alhaji yafito toni
nagama zama .
Jeka nan tafi can kai wannan karbo wancan, kai dade
sauransu.
Amma duk samunnan danake yi dinki daya kawai nayi.
Sauran kudadena kuwa nakan kashesune aharakan hada
lefena.
Wannan yasanya watarana daya daga cikin abokan aikina
yake tambayata
“Wai kai umar mai kake da kudine?’Ullum kana samu
amma ba’agani jikinka”
Nayi dariya
“Jamil kenan kowanne mutum kasan yanada manufa,
abin dayasa kake ganin halka bawai kwalliya kuka fini son
yiba.
Bukatun kudi danakedasu shiyasa kukaga ina tattalawa”
Yarike baki
“Kai kuwa wani irin bukatune wayannan dahar sai ka
takura kanaka zaka biya?
Nagafa ko aure baka dashi”
Nakalleshi
“To mai aurene kawai yake da manyan bukatu?ka tsaya
idan lokaci yayi zaka gni”
Dai dai wannan lokaci alhaji yashigo ,wata kyakkaywar
sailulace ahannunsa.
Ni dai tunda nake bantaba ganin kan waya mai kyawun
na Alhaji ba.
Wannan yasanya akullum alhaji yana waya nakan bishoi
da ido har yagane yanda nake nuna sha’awata da kan
wayar wannan yasanya shi yimin karin bayani akan
muhimmancin kan wayar.
Ya kuma shaidamin naira dubu dari biyu yasiya nayi
matukar mamaki da jin haka .
Dubu dari biyu ai kudin kyakkyawar motane .
Da alhaji yazo ya tsaya akusa damu
Sai naji ashe suna tattaunawa ne da wani mutum mai
harkar setlit.zance da akeyima zai kawo setlit ne guda
biyar.
Kuma duk za a sanyasune a sabon gidan da alhaji yake
ginawa.
Ni alahaji har mamaki yake bani komai nasa sai ya
burgeka.to amma mai zaiyi da wannan sabon gidan alhali
ko haihuwa bai taba yiba.
Hirar tasu takare akan cewa za’a aikomasa da kudin gobe
da rana.
(Umar harka fara bani tausayi)
Shuraih 99%
********** ************* ********
Ina cikin cin abin ci alhaji yakirani sai yamiko min key din
motarsa
“Je ka kabude but akwai wata jaka kadaukomin”
Nakarfa na tafi da gaggawa
Ina dauko jakan saina gane kudine aciki babu tantama sai
na baiwa alhaji zan tafi ya tsaidani
Ada nayi zaton zasukai miliyan daya ashe dubu dari da
hamsinne bako maine yajawo hakan ba sai kasancewarsu
yan wazobiya
Ya dubeni
“Kaga kudinnan kakai wa malam abba mai dishi su”
Anan IBB malam abba yake amma naira dari biyu
akabani kudin mashin.
Nafito na tsaya abakin titi shiru babu wani dan acaba
mara fasinja .
Wannan yasa na yanke shawarar nafara tattakawa akafa
har zuwa loakcin da zansamu dan acaba.
Nayi tafiya mai dan nisa .
Kawai sainaji anyayimeni nayi sama bansan
komaeneneba.
Saidai na jini acan gefe guda nayi kokarin namike amma
ina juwa ta daukeni dole nakoma na zauna .
Sai bayan yan dakiku nayi kiliya .saboda haka na lalubi
jakata
Amma babu ita kuma babu dalilinta .
Tashin hankali shin wai meyafaru danine
Bandai san takamaiman abinda ya yayimeniba.
Kuma gashi babu mutane a eriyar wajan
Na duba jikina babu inda naji ko da kwarzane toni yanzu
yazan saka kaina zuwa zanyi wajen alhaji ko kuwa
karasawa zanyi inda aka aikeni?
Duk biyun dai kusan ma’anarsu daya kusan duk inda naje
dai bani da abin fada.
Wannan yasa na share waje kawai na zauna (da yafimaka
umar lolx shuraih 99%)
Ina wajen la’asar tayi.nahada kai da gwuiwa na rasa me
yake min dadi.
Kawai sanaji ana tabani.
Dana daga kai sainaga ashe jamil ne.
“Lafiya kazo nan kazauna”
Na maida kaina batare dana bashi amasa ba
“To kazo alhaji yana kira”
Da kamar bazani ba sai wata zuciyarta ce jeka.
Na bishi muka rankay zuwa kasuwa.
Alahaji ya dubeni
“Ya akayine umar nayi waya ance baka kai kudinba”
Na sunkuyar da kaina kasa cikin rashin sanin abinda
yakamata nafada
“Ina kudin suke”
Sai naji bakina suna fadin
“Sun bata”
“Kamar yaya sun bata?”
Yatambaya cikin mamaki.
Ni kaina nasan bakina yayi gidadanci daya bada wannan
amsar.
Na bayyana masa duk abinda nasani.
Ya dade yana kallona daga bisani ya mike tsaye game da
faidn
“Allah ya kyauta”
******* ************ ********
Nacigaba da zama akasuwa cikin rashin jin dadi
dominkuwa ina fuskantar wani irin kallo daga abokan
aikina .
Alhaji ma kuma ya canza taku .
Ahalin yanzu baya aikena nakai kudi ko kuma na karbo
,nasan bakomai bane ya jawo hakan ba illa bacewar jakar
kudi.
Wannan yasanya akullum takaicin duniya na damuna .
To amma yana iya abin sai hakuri .
Bayan dana karya kumallo sai najawo wata bakar jaketna
na dora sakamakon sanyi da akatashi da shi.
Sai kawai na nufi kasuwa muka ci gaba da hulda kamar
yadda muka saba ……..
WATA AZAL DIN KUMA
Keep following
Its shuraih 99%
Zan ci gaba

Join Our Telegram Group
Join Our Twitter page
Join Our Facebook page
Join Our Youtube Channel

Join Our Telegram Group

Download Hausa Films

Download Hausa Musics at Viralnorth

Leave a Reply
Related Files

Hausa Ebooks

Movies and Films

Musics

error: Alert: Content is protected !!
%d bloggers like this: